Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

KANO

Mommy tun sassafe suka doka sammako suka wuce nijer, bayan ta dokawa suhailat uban warning akan ko kofar gida kartayi gigin lekawa, kuma karta fadawa kowa tana ciki koda wasa, tasa asamo mata wadda zata dinga kula da ita, anjima zatazo. mommy ta a jiyewa suhailat ishashshen kudi da kayan abinci daze isheta kafin ta dawo.

Likitoci basu karbi gwaggo ba, seda aka kira dan sanda sannan suka karbeta. inda suka kwada mata karfe a kafa ta samu karaya a gurin, sun mata dori sannan kuma suka mata ɗinki a kafadarta inda suka yanketa da wuka, anmata karin jini kuma saboda jinin data zubar. Duk abinda aka bukata na kuɗi kona wani abun, baban saleemat da umma ne sukeyi. Allah yatakaita barayin basu tafi da wayar gwaggo ba, da ita aka kira yan’uwanta na kauye aka sanar musu….

Bayan Aunty sungama waya dasu Maryam dan har Mustapha ma takira sungaisa. wayar faruq takira tace yazo ya sameta a falon mommy. Da sallama ya shiga yazauna a gefen Aunty Bayan ta amsa masa. Aunty ce kadai a falon Aliya tana daki tana hada musu kayansu. “Ina kwana Aunty” “lafiya kalau faruq, yau baka fita aikin bane?” “Ehh, Aunty yanzu nake shirin fita, dan tun safe daddy yamun magana to nadanyi wani aikine a system” “ok, Allah yataimaka” “ameen” “dama maganar Sadiq zan maka, yakamata zuwa yanzu mudubashi musan halin dayake ciki, danbazeyiyu a barshi hakaba, ace mutum ya kulle kansa a daki babu ci da sha na kirki, jiya damuka dawo naje nadubashi naji kofarshi a rufe, idan kana da extra key na dakinsa ka bude muga halin dayake ciki, hankalina ya kasa kwanciya. Ai hannunka baya rubewa kayanke kayar. Dazu danayiwa yaya maganar seyace in kyaleshi, amma yanzu tunda yafito kaje kadubomunshi.” numfashi faruq yasauke yace, “shikenan Aunty, Bari naje naduboshi” “yawwa faruq ina jiranka.” Mikewa yayi yakoma part dinsu, dakinshi ya shiga ya binkico key din dakin Sadiq dayake dashi. A mawuyacin hali yasamu Sadiq jikinshi ya wani sandare kamar gawa, gashi ko numfashi bayayi. Hankalin faruq a tashe yasanar da yan’uwansa da Aunty, babu bata lokaci suka daukeshi zuwa asibiti……….

Bayan sati daya

Har yau mommy bata dawoba kamar yadda tacewa suhailat, suhailat ta kira wayarta amma bata sametaba. Su faruq ma sunkikkira mommy dansu sanar mata ciwon Sadiq suma basu sametaba, suhailat kuma idan suka kirata bata dagawa. Su Hajiya gwaggo an farfaɗo amma batasan wake kantaba, sesunbatu take tana kiran “kudadenta,kudadenta.” An kawo lefen saleemat Masha Allah kaya sunyi kyau sosai, ansaka bikinta bayan karamar sallah da sati hudu.

Abangaren su Maryam kuwa komai natafiya yadda yakamata, gidan kowa haba_haba yakeyi dasu. Ammi tayiwa Maryam da Mustapha siyayya ta kaya sosai. Mustapha tun kwanansu uku a Jos din, yakebin Saddam kasuwa domin yacewa Ammi baze iya zaman gidaba kamar wata mace. Motarta ammi tabasa yake zirga_zirga da ita. Tsakaninsa da Maryam gaisuwace kawai take hadasu. Part din mijin ammi, nan ammin tasa aka gyara musu aka yimasa fenti da dan gyare_gyare. Falone da 2 bedrooms a part din se kitchen da ɗan karamin store. komai sabo dal ammi tasa aka samusu, amma Mustapha ne yabiya kudin. danda tace ita zata biya yahanata. Kullum suna waya dasu Aunty, mustapha yaso zuwa yaduba jikin Sadiq, amma daddy yahana. Danyace idan yataho Maryam bazataji dadiba, idan ya barta ita kadai. Yau juma’a, kuma yaune ango da amarya zasu koma part dinsu subar na ammi, yau kuma umaimah zata dawo daga hutun dataje gidan kakanninta na wajen uwa………..✍️

By
Zeey kumurya
5️⃣2️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

……….Da misalin ƙarfe 11 na safe muna zaune a falon ammi nida Aunty zuhura, yaronta yana hannuna ina masa wasa muna hira jefi_jefi. kamar a mafarki naji kamshin turarensa, nidai nasan yana kasuwa kuma baya dawowa a irin wannan lokacin. dago kaina nayi da sauri yayi daidai da shigowarsa falon bakinsa dauke da sallama. maida kaina kasa nayi zuciyata na ɗan bugawa, a hankali na amsa masa sallamar dan dakyarma inyaji, saɓanin Aunty zuhura da har gaisawa sukayi ta masa sannu da zuwa, nidai daga amsa masa sallamar bankara koda kallon inda yakeba nacigaba da yiwa Abul wasa. yanda Maryam bata kalli Mustaphaba, haka shima ko kallon inda take beba yashige dakin ammi bayan sungama gaisawa da zuhura. kallon Maryam zuhura tayi tana sakin murmushi, miskilancinsu na bata dariya, yanda idan suka haɗu suke wani basarwa tamkar ba ma’aurataba, zataso taga wanda zefara aje miskilancinsa tsakanin Maryam da Mustapha. Nikam banmasan tana kallonnawaba natafi duniyar tunanin yanda zamanmu ze kasance ni da shi a mahalli ɗaya.

Ammi na zaune a bakin gado tana waya da wata cousin dinta datake Niger mustapha ya shigo dakin da sallama, zama yayi a gefenta yana jiran ta gama wayar, befi 1 minute da zamaba sukayi sallama ammi ta aje wayar. tana dubanshi tace.”NOOR, yanaga kadawo daga kasuwar dafatan dai lafiya?” lips dinshi na kasa yaɗan lasa sannan yace. “Lafiya kalau Amminah, daddy ne yakirani akan karatun waccan” tsareshi ammi tayi da ido tace wace waccan kuma batasa suna ne?” shafa kansa yayi tare da lumshe idonsa a hankali kamar bayasonyin magana yace, “me sunanki” ita ammi ma dariya yaso ya bata, yanda ya wani basarwa, tace. “Uhm, inajinka meyafaru da karatunnata?” yana latsa wayarsa yace. “Daddy yace, anemi PRIVATE SCHOOL abiya mata tayi NECO, tunda WAEC lokaci ya kure, ran monday zasu fara. Idan Allah yakaimu November_december setayi PRIVATE WAEC” ammi tace. “Hakanma yayi Allah yataimaka yabada sa’a, kayiwa Saddam magana seya samo mata makarantar dazatayi” amsa mata yayi cikin girmamawa sannan ya mike yayiwa ammi sallama ya fice. daya dawo ze fitama bandago na kalleshiba, inaji dai Aunty zuhura ta masa Allah yakiyaye hanya. Lekowa ammi tayi takirani, da Abul a hannuna na mike nanufi dakinnata. Bayan na zauna ta bani abu a kofi kamar magani, tun washegari garin ranar danazo kullum seta bani nasha sau uku a rana. da daddare kuma kafin na kwanta tasani inci fruits. karbar abul tayi daga hannuna dayaketa bingira mata dariya. Seda na shanye tass sannan na ajiye cup din ina yamutsa fuska saboda rashin dadi. wani abu ta mikomun daban tace in lasa, maganine na gari aka kwabashi da zuma, shikam nasha sosai ta dadin rai saboda zaki_zakin zuma, a kunyace nakesha duk da ammi hankalinta nakan Abul. da farko data fara bani bansan amfaninsaba, seda ta hanani tsarki da ruwan sanyi saidai na dumi sannan na gane. kuma kullum kafin nayi bacci setasa na shiga ruwan zafi wanda ta tafasashi da lalle da wasu ganyayyaki masu amfani. da safe kuma ina tashi zata samun turaren tsugunno a kasko. inna gama dashi tasamun na turare jiki. banshanyeba na ajiye saboda cikar danaji cikina yamun, akan mudubi na ajiye robar bayan na rufe da murfinta. Ammi tace, “yawwa ɗiyata kinsha sosai ko?” A mutukar kunyace na dagawa ammi kai, kaina na kasa. kwantar da Abul tayi a kan gado sannan ta dakko wayarta tana fadin, “bari nakira antinku takirani tun dazu tace na baki wayar kina wanka, nace idan kinfito zankirata kuma na sha’afa” komawa bakin gado nayi nazauna ammi ta mikomun wayar bayan ta shiga, daukar Abul tayi suka fita parlour. “Assalamu alaikum” Aunty ta fada bayan ta daga wayar. amsa mata nayi na kara da faɗin, “ina kwana Aunty” tace. “Lafiya kalau, ya Jos din, ina fatan komaidai lafiya” nace, “lafiya kalau Aunty, yajikin yaya Sadik” tace, “jiki Alhamdulillah za’ace Maryam, dan yanzuma haka suna hanyar zuwa saudiyya shida yaya da zannurain, tunda nandin kullum ciwon kara gaba yake.” cike da tausayawa gami da jimantawa nace. “Allah ya bashi lafiya, yasa karshen wahalar kenan” Aunty tace, “Ameen Maryam, yau insha Allah zanje gidan gwaggonki saboda zirga_zirgar asibiti yasa bansamu najeba” “bakomai Aunty aikina kokarima sosai wlh” “to yaza’ayi Maryam girman kenan” “hakane ina aliya fa?” “Tanacan tana ta shiri kinsan yau zamu wuce kd” “kigaidamun da ita Aunty” “zataji insha Allah, ya angonki?” Murmushi nayi cikin jin kunya nace, “yananan kalau aunty” “amminku tacemun yau zaku koma bangarenku ko” “ehh Aunty” fada Aunty tashiga yiwa Maryam sosai, akan aure da yanda zata kula da mijinta da hikimomi da dabaru da kissa na zaman aure. mun dade muna waya da Aunty, dan munfi awa ɗaya, har aliya tafito itama Aunty tabata wayar muka gaisa sannan mukayi sallama, na koma falo. A kitchen na tarar da ammi da Aunty zuhura sunata aiki, nima tayasu nayi duk da ammi taso hanani amma nadage senayu……..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button