Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

fahimtar hakan yasa aunty mikewa da sauri, ta kare maryam, tare da tsaida haidar da fadin, “haba haidar mekake shirinyine dukanta zakayi kome, aiba itace da lefiba tunda ba ita ta mari suhailat dinba” tsayawa haidar yayi, jikinsa na tsuma se huci yakeyi, yana jifan maryam da wani mugun kallo,amma bece komaiba. “Haba aunty,kibarshi mana ya hukuntata,bakiji me suhailat tace bane, aikome meyafaru itace sila” cewar zannurain. Hararsa aunty tayi tace, “kai kazo kahukuntata dinmana” nidai ina bayan aunty na boye, ina zubar da hawayen bakin ciki. Cikin fusata mommy tasauke suhailat daka kan cinyarta ta mike tsaye tana duban aunty tace, “menene hakane saudart, yazakihana yara su hukuntata, wato kinzabi bare akan yar,dan’uwanki kenanan, gaskiya ni kidenamun irin wannan,tunda kikazo gidannan sewani jajjan yarinyarnan kikeyi ajiki, sekace kekika kawota, ina ni nakawota gidannan,dan haka dani da yayana, muna dadamar yimata duk abunda mukaga dama.” Masifa sosai mommy tahauyi, mamakintane yacikamun zuciya dama masifaffiyace haka, wani matsanancin tsoronta ne yashigeni, danni arayuwata banason masifa da fada. Girgiza kai kawai aunty tayi, amma batace mata komaiba, hartakai aya. Yanda ta wani hakikance tana bala’i, duk maganganu na rashin tarbiyya da da’a, dayarta ta fada,tare da muggan kalamai akan yarwani bata kwabetaba, sema goyon bayanta datayi. “Allah yabaki hakuri, aunty atika, nibanyi haka da wata manufaba,banyi kuma danna bata miki raiba” aunty tafadi haka, tare da kama hannuna, tajani zuwa dakinta. Aliya dakebin kowa da kallo, tamkar TV tasauke numfashi tare da juyawa tabi bayan uwarta. Da harara suhailat ta bisu duka, cikin jin takaicin hana dukan maryam da aunty tayi tace, “yanzu mommy kina kallo ta janyeta,amma bazaki hanaba, nidai gaskiya mommy yarinyarnan tabar gidannan kawai, hakanne zesa hankalina ya kwanta,danni gaskiya nafara tunanin mayyace” cikin rarrashi mommy tace, “kiyi hakuri daughter, nikadai nasan matakin dazan dauka akanta, ai saudat din zata bar gidan ba dawwama zatayiba, seta gwammace kida da karatu,” lallaba yayanta mommy tahauyi, musammanma suhailat da haydar, harta samu suka sakko, takuma cewa suhailat ta kwantar da hankalinta zataje ta samu mustapha har part dinnasa da kanta,ta masa magana,takuma basa hakurin fushin dayayi da ita.

Adakin aunty kuwa, maryam sekuka takeyi ita setabar gidan, saboda ta matukar tsorata dasu mommy, tasan daba aunty yau, kashinta ya gama bushewa, gashi shima yaya sadiq bayanan, dama shikadaine me kaunarta agidan. Aunty ce, tahau lallacinta tare da lallabata akan ta kwantar da hankalinta babu abunda zasu mata, masifar iya yauce kawai daga yanzu angama. Aliya tambayar aunty tahauyi wai meyafaru?” Dubanta aunty tayi tace, “bansaniba sarkin son zance, naga ai tare kuka je, komai agabanki yafaru” shiru aliya tayi, dantasan idan tacewa aunty batashiga ba fada zata mata. Ajiyar zuciya kawai nake saukewa, saboda kukan danaci. Kaina nakan cinyar aunty, itakuma tana shafa kaina cikin tausayawa. Kiran sallar, isha’i ne yatadamu, aunty tashige toilet din dake dakinta, nikuma nida aliya muka fice zuwa dakina. Suna zaune a falon dukansu har yanzu, sunkuyar da kaina kasa nayi banyarda nahada ido da kowannensuba. Suhailat kuwa bin maryam take da wani mugun kallo, cikin tsana, tanajin wata matsananciyar tsanar maryam nakara mamaye zuciyarta. Nidai banmasan tanayiba, daki muka shige. Muna alwala ina bawa aliya labarin abunda yafaru apart din yaya, saboda addabamun din datayi da tambaya, tun shigowarmu dakin……

Tunda yazauna bayan fitarsu ko motsawa beyiba, ko abincinma be kallaba, duk da yunwar dake nukurkusarsa. kiran sallar isha’inne shima ya mikar dashi, dakinshi ya shiga yadauro alwala yafito yanufi masallacin dake manne da gidannasu. Ana idar da sallah, yataso ko gaisawar dayasabayi da mutane yau betsayaba, saboda ciwon dakansa kemasa,burinsa kawai yaje ya kwanta ya huta. A palonsa na sama yatarar da mommy, hakimce akan kujera, cikin mamaki yake kallonta. Fadada fara’a mommy tayi akan fuskarta, cikin tausasa lafazi,da nuna tsantsar kulawa tace, “welcome my son” tamkar ba itace, tagama zuba masifa dazuba. sakin fuskarsa yayi daga tsuken datake, yazauna agefen mommy yana sauke numfashi tare da daga mata kai alamar amsawa. Shafa fuskarsa mommy tayi cikin tsantsar kulawa tace, “meyafarune son naganka cikin damuwa” kallon mommy yayi bece mata komaiba, yasan suhailat tasanar da ita komai,shiyasama tazo part dinnasa. “Nothing mom” yafada cikin sanyin murya, yana lumshe idonsa. Matsawa jikinsa mommy tayi, ta kwanto dashi jikinta,cikin so da kauna. Ahankali takai hannunta tana shafa bayansa,tasan halinsa idan ransa yabaci befiyason doguwar maganaba. Ajiyar zuciya yahau saukewa,yayi luf ajikin mommy,yanajin kaunar mahaifiyarsa harcikin ransa. Yanason mommy fiye da kowa a duniyarnan. “Son meyasa ka mari daughter akan waccan yarinyar kuma agabanta.?” Mommy tajeho masa wannan tambayar. Taune lips dinsa nakasa yayi, sannan yace, “mom, suhailat bataji, yarinyarnan babu abunda tamata amma tahau zaginta,da marinta. tare da siffantata da dabbobi, dan’adam da Allah yayishi da daraja,da kima, amma tadinga kamantata da dabbobi,shine abunda yafi komai konamun rai mom, banmasan sanda natashi na maretanba.” cikin bacin rai yayi maganar. Shafa kwantacciyar sumar kansa mommy tahauyi tace, “kasan suhailat fa yarinyace, sekana hakuri da ita, kuma zanjamata kunne akan takiyayi hakan anan gaba, naga ranka ya baci, kasan banason abunda zebata maka rai kokadan, ayi mana hakuri nasan munyi lefi.” Mommy ta karasa zancen tana sakin murmushi. Kaikawai yagyada mata, ya lumshe idonsa tare da gyara kwanciyarsa ajikin mommy. Kallon dinning mommy tayi, taga babu alamun antaba abincin dake kan dinning din. cikin dan kaduwa tace, “yasalam, my son, haryanzu bakaci abincinnanba, haba son dan Allah kadena zama da yunwarnan seta maka illa,pls son kadinga kokarin cin abinci akan lokaci” kama hannayenta yayi cikin tsananin kaunarta, yana murmushi yace, “insha Allah mom” murmushi itama mom tamasa, tare masa kiss agoshinsa. Rabashi tayi daga jikinta, ta mike. Dakanta ta shiga kitchen dinsa ta dakko plate da serving spoon, ta zuba masa abincin ta kawo masa hargabansa takuma bashi abaki. Mommy na matukar sonsa fiye da tunanin me tunani, Wanda shikansa yana mamakin hakan, musamman dayakasance bashi kadai tahaifaba, bata boye sonsa ko’agaban kowaye. shikadaine yake taba mata suhailat dinta yazauna lafiya, amma da wanine ya mari suhailat yau, dabataza kyaleshiba koda kuwa acikin sauran yayantane. Seda tatabbatar dayaci yakoshi sannan tabarsa, ta masa sallama tatafi. Dakinsa yashige ya kwanta akan makeken royal bed dinsa, haryanzu yanajin zafi da haushin abunda suhailat tayi, amma taci darajar mom dinsa, daseya kara hukuntata. Yanajin karar shigowar sakonni, amma yayi banza da wayar yasan baze wuce suhailat dinbace…….

Tunda muka idar da sallah aliya taketa mita da masifa,akan abunda yafaru, nidai shiru namata na kwanta, saboda matsanancin ciwon dakaina yakemun. Seda aka kirata awayane nasamu sa’idar mitartata. Dukda matsanancin ciwon dakaina yakemun haka na yunkura, nafito falo saboda ganin 9 harta gota, nasan ni suke jira inyi serving nasu. Ilai kuwa, dukansu suna zaune a kan dinning din harda yaya sadiq. Kuramun ido yayi yana kallona, amma becemun komaiba,harna karasa garesu, inadan jin tsoro ganin babu aunty a falon, karnaje sumin wani abun dadintama da yaya sadiq. Amma senaga babu yakoda kalleni, ajiyar zuciya nasauke. Cikin sanyin jiki nafara serving dinnasu, inayi ina taune lips dina saboda azabar ciwon kai. Takan yaya faruq nafara, inakan yaya sadiq,aunty tafito. Kallon maryam kawai aunty tayi, tagane batajin dadi, dama tasan kukan datasha seya samata ciwon kai. “Maryam, kibarshi kikoma daki kikwanta, aliya tazo ta karasa,tunda naga bakyajin dadi.” cewar aunty, bayan taja kujera tazauna agefen mommy. Dama hutunnakeda bukata, dan harwani jiri_jiri nakeji. Kai nagyadawa aunty kawai najuya, aliyanma harta fito, sannu tamun takarasa dinning din,nikuma nashige daki. Ajiyar zuciya sadiq yasauke, bayan maryam tabar falon yadubi aunty yace, “aunty meke damuntane wai, nagama idanunta kamar kuka tayi” “ciwon kai” aunty tabashi amsa atakaice. Aliya ta bude baki zatayi magana aunty ta harareta, dauke kanta tayi tafara rattabowa yaya sadiq bayanin abunda yafaru, duk hararar da aunty take aika mata kuwa, seda takai aya, ta tsaya. Suhailat ma cike da jin haushinta take harararta, itafa shiyasa batason yarinyarnan shegen surutu gareta da shishshigi. Jinjina kai kawai sadiq yake cikin takaicin halin mahaifiyarsa da yan’uwansa. Shiyasa tunda yashigo yaga fuskokinsu babu walwala, kamar ko yaushe. Hakadai sukayi dinner yau kowa zuciyarsa babudadi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button