Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

By
Zeey kumurya
ABIN DA KA SHUKA…!

7️⃣6️⃣

……….. Zama nayi a kan gado na dunk’ule guri ɗaya bance masa komaiba, jin shirun yayi yawa Mustapha ya juyo ya kalleta, keɓe fuska tayi tana turo baki gaba kanta a ƙasa, bece mata komai ba shima ya tashi ya ƙarasa gurin wardrobe ya buɗe ya dakko kayansa ya shirya, ƙofa ya nufa ganin haka Maryam tace, “yaya mezan saka?” batare daya juyoba yace “ki tashi ki dakko mana” bejira amsar taba ya fice, ɗakinta yaje ya dakko mata kaya da duk wani abu zata buƙata, inanan inda ya barni ina tunanin yanda zan iya fita a haka ya dawo, a ƙasan mak’oshi yayi mun sallama, nima na amsa masa a zuciya. Ƙarasawa yayi kan gadon ya ajiye kayan a gabanta, kallon kayan nayi na kalleshi nace “Nagode” ya gyada mun kai kawai, kasa shiryawa nayi duk da ga kayan a gabana, gashi ya ƙuramun ido kuma ya haɗe rai kamar ba shiba. Ganin tana ɓata masa lokaci yace “ke nake jirafa” nace “to ka fita inshirya Please” be tankamun ba, be kuma ɗauke idonshi daga kaina ba, turo bakina nayi hawaye na zubomun na fara shiryawa, tabe baki yayi ya tashi ya ɗauki wayoyinsa ya shiga latsawa, bayan tagama shiryawa tana d’aura ɗankwali ya dubeta yana murmushi yace “kinyi kyau sosai” nima kin kulasa nayi, murmushi yayi me sauti ya ƙaraso inda nake ya kama ɗankwalin yace “kawo in daura miki me kyau” sakar masa nayi, kasancewar kayan nata yadi ne me ɗan santsi saiya kasa daurawa, riƙeshi kawai yayi batare dayasan yanda ze fasaltashiba, cukurkuda mata yayi ya daura mata yace “nagama, kuma bakiga yanda ya miki kyauba sosai” nayi murmushi nace “Nagode bari na gani” na tashi na kalli madubi, dariya ce ta kusan kufcemun saboda wata inyamura dana koma, na danne dariyartawa nayi murmushi nace “kayi ƙoƙari amma bari na gyara maka” yace “ki mace banyiba” murmushi nayi na kunce daurin na sake wani. kama hannuna yayi muka fito falo, wayarsa ce ta fara ringing cikin sound me dadi, bebi takantaba ya zauna akan kujera tare da zaunar dani akan cinyarsa, wayar ya duba yabi bayan kiran ya kara a kunnensa. Ammi tayi masa sallama ɗaga ɗaya ɓangaren, ya amsa mata ya ƙara da faɗin “ina kwana ammi” ammi tace “lafiya kalau, NOOR naga har 10 ta wuce, ga breakfast ɗinkunan nagama tun dazu kazo ka daukar muku, danni bana iya fita idan ana ruwa, umaimah kuma bacci tace” yace “toh ammi ganinan” tace “toh” tare da kashe wayar, ya shafi fuskar Maryam datake kallonsa, a hankali nace “zan bika” yana saukeni daga jikinsa yace “part din ammi zani, na karbo mana break” nace “muje tare kaji” yace “ana ruwan zaki fita” ya ƙarasa zancen yana nufar ɗakinsa, Umbrella ya ɗakko ya fito ya tafi, be wani jimaba ya dawo, da kansa yayi sarving ɗinmu, ya ciyar dani, yace yau bazanyi komai ba shizemun. Soyayya,kulawa, da tarairaiya Maryam tasha su yau a gurin mustapha fiye da koyaushe tun auransu, ita kuwa se shagwab’a da taɓara take zuba masa, ya dakko wayar daya siyo mata ya bata, Maryam murna kamar ta kasheta……

Bayan sati uku

Mustapha ne zaune yana kallon labarai a TV, lolaci zuwa lokaci yana kallon kofar ɗakin Maryam, tunda ya dawo daga sallar magriba bai sata a idonsaba, tana ɗaki wai fushi take akan yaƙi siyo mata sweet, sosai shan zakinta ya karu yanzu fiye da da, wanda ya kawo mata daga Kano basu fi sati ɗaya ba ta shanye, ya ƙara siyo mata wasu harta ƙara shanyewa, gashi batason cin abinci yanzu sai yayi mata dagaske yake ta samu taci. wayarsa ce tayi ƙara, ya ɗakko ya duba, Aunty ce take kiranshi ɗagawa yayi da sallama, bayan sun gaisa Aunty tace, “Muhammad, dan Allah inason na haɗa ka da suhailat kuyi magana, kwana biyunnan ta dameni bata da zance sai naka, ko abinci bata ci wlh, sai aikin kuka, damuwarta kuma matsala ce a halin yanzu, because of another reason.” Mustapha yayi shiru na wasu sakanni kafin yace, “Aunty me zance mata kuma?” Aunty tace “just took to her koma mene Please!” yace “shikenan amma sai dai muyi chat” Aunty tace “why?” ya mata shiru, dan shi bayajin ze iya ƙara yin magana da suhailat a rayuwarsa, gwaradai chat ɗin, Aunty jin yayi shiru tace “ohk, kuyi chat ɗin” yace “Tom” sukayi sallama ya kashe wayar.

Maryam ce ta fito daga ɗakinta, ajiyar zuciya ya sauke cikin jin daɗin ganinta, kallonta yake ta ƙasan ido tayi masa kyau sosai, tana sanye cikin wani riga da wando ƴan Pakistan Red colour, ta ƙara kyau da cika, hasken fatarta ya ƙara fitowa. bata kalleshi ba, itama kamar Yadda shima ya ɗauke kai kamar bai san da fitowartaba, kitchen ta nufa duk da bata da abunyi a kitchen din, ta fito ne dan taganshi kawai taji daɗi, ita kanta ta gaji da fushin datake dashi shi kuma yaƙi lallashinta, takai 10 minutes a kitchen din sannan ta fito, wayam taga falon bayanan, zama nayi akan kujera na sauya tasha na fara kallo, sai da aka kira sallar isha’i naga ya fito ɗaga ɗakinsa, ƙara ɓata rai nayi sosai na turo bakina gaba, murmushi yayi kawai ya kalleta ya fice zuwa masallaci, ganin ya fita na tashi na koma ɗaki nima danyin Sallah. Bayan ya dawo Aunty ta ƙara kiransa, ɗagawa yayi Aunty tace “nasata ta kunna wayarta ka mata magana, dan ita tanata maka magana tun kafin yau amma baka gani, yana nuna kamar kayi blocked ɗinta” yayi ɗanjim kafin yace “bani da Number ta” Aunty tace “Bari na tura maka” shiru yayi bayan sun gama waya Aunty yana tunanin me suhailat zatace masa, danshi ya riga da yayi deleting ɗinta gabadaya a cikin rayuwarsa, amma zai saurareta yanzu saboda Aunty. miƙewa yayi ya nufi gurin ƴar rigimarsa. ina zaune akan darduma idanuna a lumshe, so nake kawai najini a jikinshi dan baƙaramin missing ɗinsa nayi ba, yariga ya sabarmun koyaushe idan yana gida muna manne da juna. da sallama ya shigo ɗakin, buɗe idona nayi da sauri na juyo na kalli k’ofa tare da amsa masa sallamar, ba yabo ba fallasa yace “ki fito kici abinci” tashi nayi nabi bayanshi, a tare mukaci abincin kamar kullum, kuma a baki ya bani amma fuskarsa a haɗe sosai, ɗakinsa ya koma bayan mungama, bin bayansa nayi bayan na kawashe kayan da mukaci abincin na d’auraye, yana kwance akan gado yana latsa wayarsa bayan ya rage kayan jikinsa, tunda ta shigo ya k’ura mata ido, sosai shima yayi kewarta yayi kewar ɗumin jikinta dake saukar masa da nutsuwa, a ƙasan gadon na zauna ina turo baki gaba bance komaiba, murmushi yayi kawai aransa yana mamakinta, gaba-daya yanzu ta sauya abu kaɗan sai ta hau fushi, gashi indai be lallashetaba bazata kulashi ba, idan ya shareta kuka taita kuka tana damuwa. Tashi zaune yayi yana kallonta ganin yanda ta keɓe fuska zatayi kuka yace “zo” tare da ware mata hannunsa, da sauri na tashi dama abunda nakeso kenan na faɗa jikinshi ina sakin ajiyar zuciya, rungumeta yayi tsam a jikinsa shima yana sakin ajiyar zuciyar, a hankali yace “am sorry tawan, mun shirya ko?” girgiza kai nayi alamun a’a, yace “why?” A shagwabe nace “ba kaine kak’i kulani ba tun dazu” yayi murmushi yace “yanzu aina kula ki ko? kuma ai duk kece rigimar ki tayi yawa yanzu” na turo bakina gaba bance komai ba, na dora hannuna akan kirjinshi ina wasa da kwantaccen gashin kirjinsa, kissing lips ɗinta data turo gaba yayi yace “i missed you so much” nace “nima haka” gashin kanta ya shiga shafawa yana shishshina wuyanta, lumshe idona nayi cikin sanyin murya nace “yaya” yace “uhm” nace “zansha sweet da choculate” yace “babu” gashin kirjinsa naja tare da mintsinar breast ɗinsa, runtse idonsa yayi dan yaji zafi amma bece komai ba, bubbuga kirjinsa na shiga yi ina ƙananun kukan da babu hawaye, ɗagota yayi daga kirjinsa cikin lallami yace “mene ne?” nace “Sweet” ajiyar zuciya ya sauke yace “da safe zamuje ki zaba wadda kike so da kanki kinji” nayi murmushi cikin jin daɗin zan fita nace “dagaske yaya” ya gyadamun kai yace “promise” nace “thank you” ya lakacemun hanci yace “murna kike zaki fita ko?” nayi dariya nace “eh mana” yace “ina wayarki?” nace “tana ɗaki” yace “when last da kuyi waya da Aunty?” nace “3 days ago” yace “to albishirin ki” nace “goro” yace “a’a Ni banason goro” nace “me kake so?” yace “two things, saboda albishir ɗin dazan miki biyu ne” nace “me kake so toh?” yayi kasa da murya yace “kiss” na ɗan waro ido nace “da me kuma?” yace “something special for your own choice” na ɗanyi jimm nace “na yarda faɗamun albishir ɗin, na matsu inji” Yace “result ɗinku na NECO ya fito, gobe idan mun fita zamu biya capay mu duba” cikin farincikin nace “Alhamdulillah, naji daɗi sosai yaya, mafarkina ya kusa tabbata” yace “wanne mafarkin?” nace “na karatu” yace “kinason karatu ne?” nace “sosai ma yaya, burin innatama kenan taga nayi na karatu” yace “me kikeson karanta?” Nace “inason na zamu likitar mata” ya shafi kuncina yace “gud girl, insha Allah Zaki cika burinki very soon, amma sai kin haifamun kids” ya ƙarashe zancen yana shafa shafaffen cikinta, na shagwabe fuska nace “sai na tsufe kenan” yayi murmushi yace “A’a, a shekara nawa ne, kin haifamun, ni ko 3 kika haifa sun isa seki tafi karatunki” nace “idan ina karatunma ai zan iya hai…..” sai kuma nayi shiru, yace “wahala zakisha, ga karatu ga rainon ciki ko baby, ki bari ki haifamun ko 2 ne, nayi miki alkawarin karatu har sai kince kingaji” na kwantar da kaina a ƙirjinshi, nace “Allah yakaimu lokacin” cikin jin daɗi yace “Amin” abunda yake ƙara burgeshi da ita kenan, kome yace mata tayi bata musa masa, koda bataso kuwa. nace “saura ɗayan albishir ɗin” yace “sai kin fara bani gorona” na dago da kaina nace to rufe idonka na maka, ya ɗan murmusa tare da lumshe idonsa, kallon small pink lips d’insa tayi na watsu sakanni, a hankali ta ɗora nata lips ɗin akan nasa ta fara tsotsa, hannunsa yasa abayanta ya ƙara mannata da jikinsa cikin jin daɗin yanda take tsotsar lips dinnasa kamar ta samu sweet, a hankali da dabara ya zira harshensa cikin bakinta ya fara bata wani hot kiss…. ya daɗe yana kissing ɗinta, da kyar ta samu ya barta, shima dan anata kiran wayarsa ne, kwantar da kanta yayi a kirjinshi yana shafa gashinta tare da sauke numfashi, luf nayi ajikinshi nima ina maida numfashi, a hankali ya ɗauko wayarsa, Aunty ce ta kirashi dataga be ɗagaba ta turo masa message na tura masa number’n suhailat ta whatsApp, baibi bayan kiran ba sai reply ya mata. cikin muryarshi datayi ƙasa sosai yace “Ummu” nace “uhm” yace “bacci” nace “um, um” yace “tashi inabaki ɗayan albishir ɗin” na tashi zaune yace “jibi Monday insha Allah Aunty tace zata zo ta ganki” na rungumeshi nace “Allah yakaimu, dama nayi missing ɗinta ita da Aliyata” yace “meyasa bakije kin gansu ba” nace “ai bazaka barni ba, kuma inaso inje sau ɗaya na taɓa zuwa fa” yace “ki bari zansa mana sai muje, bayan ta tazo” nace “toh” yace “to abani ragowar goro na” nace “kanason in maka waƙa?” yayi murmushi me sauti yace “banajin waka, amma indai ke zaki mun inaso, dannasan zatayi daɗi a wannan daddaɗar muryar taki” nayi murmushi na gyara zamana akan cinyarshi na fara rera masa wakar kamar haka:

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button