Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

By
zeey kumurya

5️⃣3️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

…………. Umaimah har wani zunkuɗowa take daga kan kujera tana sakin baki da hanci tana binshi da mayen kallo, Saddam da zuhura tare da Maryam ne suka lura da kallon da take masan, ammi kuwa hankalinta yana kan ɗanta bata luraba. wani kishine yazo ya turnikemun zuciya irin me dacinnan, nibanmasan haka kishin yakeba dan bantaba jin na Aunty suhailat irin hakaba, yanda take kallonsa kamar idonta ze cire, tabe Bakina nayi nadauke kaina daga kallonta zuciyata namun kuna. Ita kuwa zuhura murmushi tayi dantasan za’ayi haka. Saddam ma murmushin yayi yakau da kansa daga kallon Umaimah. Mustapha seda yagaida amminsa da mama sannan ya zauna a kusa da Maryam, dan babu wani gurin zama da yay saura a falon senan, kuma shima ya lura da kallon da umaimah take masa. Lumshe idonsa yayi saboda kamshin Maryam daya shaka kamshin ya masa daɗi sosai. Ita kuwa Maryam bata rai tayi hartana turo dan karamin bakinta gaba batasaniba saboda zafin kishi. A hankali ya bude idanunnasa ya kalli Maryam ta gefen ido. Umaimah wadda takasa dauke idonta daga kansa sekara sakar baki da hanci take tana kallonsa, a ranta tace. “Wowww, wowww amma guy dinnan ya haɗu iya haɗuwa, yatafi da imanina, amma daga gani brother din yarinyarnanne” dan ita kama taga Maryam da Mustapha sun mata. danna wayar ammi kawai nake amma bansan menake dannawaba tunda yazauna a kusa dani nanemi nutsuwata na rasa, kawai daurewa nake ga kamshinsa gaba-daya ya cikani.

kara kallonta nayi naga har lokacin bata dauke idonta daga kansaba, sonake na kalleshi naga ko shima ita yake kallo amma nakasa. Mamace tatabo umaimah tana cemata. “Ke! Mekike kallo hakane?” Ajiyar zuciya umaimah ta saki ta juyo ta kalli mama a hankali tace, “mama suwaye wadannan wai? daga ina suke?” mama tace. “Bakin amminki ne” umaimah na far da ido tace, “amma suna da kyau sosai kamar ammin, musammanma namijin yafi kyau ga muryarsa me dadi” cikin tsokana mama tace, “yau wacce rana umaimah ta yabi wani ɗa namiji arayuwarta” tana satar kallon Mustapha tace, “mama ai yakai a yabeshinne, wlh bantaba ganin namijin daya mun kyau kamarshifa, guy ɗinfa yayi mama” murmushi kawai mama tayi batace komaiba. Maida kallonta tayi ga yayanta tace. “Yaya Saddam ina yini” “lafiya kalau sisina, aitunda nashigo nakeson na miki magana naga kunata sirri da mama senace bari najira ku gama.” Dariya tayi tace, “kasan tsakanina da tsohuwarnan da amana” “hakane yar lelen mama, kindawo lafiya” “lafiya kalau yayana” maida kallonta tayi ga Mustapha tana wani fari a kokarinta nata dauki hankalinsa tace, “ina yini” sarai yasan dashi take amma ya mata banza tamkar bejiba. Ammice tace dashi, “NOOR ana gaisheka” batare daya kalletaba yace. “Lafiya” atakaice. hira suka shiga yi dukansu amma banda Maryam da Mustapha dasukayi dif tamkar basa falon, umaimah se wani iyayi take idan zatayi magana tana wani fari da ido, wanda takeyi danshi bemasan tana yiba. Bayan sunyi sallar la’asar ammi zata kaiwa Mustapha abinci, umaimah ta karba ta kai masa har daki tana wani yaya NOOR, gabadaya tabi ta susuce dataga mustapha. Shiko mustapha haka kawai yaji yarinyar bata masaba dan daga ganinta zatayi rawar kai, data kawo masa abincinma hade ransa yayi, a niyyar umaimah ta zauna suyi hira dashi amma ganin ba fuska seta fice badan tasoba. Yana gama cin abincin ya fice daga gidan.

Misalin ƙarfe biyar da yan’mintuna bayan nagama haɗa komai nawa kamar yadda ammi tace, ina zaune adakinta akan gado nikadai, ammi da Aunty zuhura suna part dinmu suna kara gyarawa. Ammi tace ta shigo dakin da sallama, amsa mata nayi cikin girmamawa. Ammi tana kallona tace, “yawwa Maryam kingama haɗa komai, har su turarukan da mayukan?” cikin sanyin murya kamar yadda jikinama yake a sanyaye nace, “ehh ammi nagama” wayarta ta mikomun tana fadin, “yanzu aka kirani da wata number wai ana nemanki” nace “ba Aunty bace kuma” ammi tace, “ehh ba ita bace wannan ma kamar yarinya” cikin mamaki na karbi wayar na duba number senaga kamar nasan number’n. danna kira nayi nakara a kunnena. Ammi ta dauki jakar da Maryam tahada kaya tafice. seda wayar takusa katsewa sannan aka daga da sallama. wayyo daɗi, wani farinciki naji ya lullubeni danaji Muryar sahibata kawar asali, kawar rufin asiri saleemat. cikin ɗoki nace, “saleemat!” itama tana dariyar jindadi tace, “na’am kawata nayi kewarki sosai wlh” “hmmm, kedai bari saleemat dazunnan nagama zancenki acikin raina, ya gida yasu umma da baba da kowa da kowa” “duk lafiya kalau Maryam” “Masha Allah, ina Habibi Adam?” “Habibi yananan kalau, ke ankawo lefenafa tun waccen satin” “kai haba, shine ba labari” “wlh Maryam nakai wata ina neman wayarki bata shiga” “wayar ta fadine, wai dagaske kike ankawo lefennaki saleemat” “dagaske mana, zan miki wasane dakina chat ma dana turo miki kingani” “kaii, amma naji dadi kawata Allah yasanya Alkhairi, Allah yasa damu za’ayi.” “Ameen” hira muka shigayi irinta amininan juna, harna tambayeta inata samu numbar ammi tacemun aunty ce ta bata. muna cikin hirarne nace mata, “ina gwaggo kuwa saleemat? Aunty tacemun idan tazo zata hadani da ita inata jiranta naji shiru” saleemat tace, “gwaggo tananan lafiya kalau” (dayake Aunty tarokesu karsu sanar da Maryam ciwon gwaggon dantasan halinta tada hankalinta zatayi tayita koke_koke, tafison idan tazo kafin azumi seta taho da ita ta duba gwaggon.) nace, “kigaidamun da ita sosai, kikarbomun number’n tama kituromun nakirata” “toh” kawai saleemat tace, ta kawar da zancen da fadin. “Yanaji wai muryarki kasa_kasa, kodai angonnaki ya tumurmushekine a gado” ta karasa zancen tana dariya. Cikin jin haushi nace. “Bansaniba yar iska, ni kaiwa umma wayar mugaisa” dariya tacigaba dayi harta kaiwa umma wayar, mungaisa sosai da umma na mata Allah yasanya Alkhairin lefen saleemat. Umma tamun yar nasiha akan aure na mata godiya mukayi sallama. banbari saleemat ta karbi wayarba na kashe dannasan tsokanata zata cigaba dayi. Haka kawai naji ina hawaye, dama jikina duk a sanyaye yake yau. goge hawayena nayi da sauri jin tafiya a falo, dan kofar dakin abude take. Ammi ce kuwa ta shigo dakin, bata lura da halin da Maryam take cikiba dan tayi kokarin boye damuwarta. Ammi tace, “Maryam kungama wayar” nace “ehh, wata kawatacema ashe Aunty ce ta bata number’n ki” tace. “ayya, kema Yakamata ace kina da waya a hannunki, bari NOOR yashigo sena masa zancen yasiyo miki” ban iya cewa mata komaiba dan kuka ze iya kufcemun” zama ammi tayi akan gado tana fadin “washh” araina nace. “Ai dole kigaji” saboda ammi kwata_kwata bata zama, koyaushe cikin dawainiya take damu nida yaya Mustapha, har tausayi take bani. “Sannu ammi” na furta a hankali. “Yawwa Maryam” mikewa nayi nace “ko in miki tausane” muryar ammi na nuni da gajiya tace, “dakuwa kin kyauta ɗiyata” kwanciya tayi akan gado nikuma nashiga yimata tausar…………

KANO

Suhailat tunda suka dawo gida taketa baza ido taga ta inda zata ga Mustapha, amma ko alamarsa bata ganiba. kasa hakura tayi taje har part dinsa, amma setaga a kulle. Da hanzarinta ta dawo bako kunya tatambayi aunty. Aunty kawai tace mata yayi tafiya ne. bataji dadiba kuma bataso hakaba, ta koma daki ta ɗauki wayarta taita kiransa amma wayar bata shiga, haka ta hakura zuciyarta babu daɗi kokaɗan. Aunty sunyi waya dasu daddy sun isa lafiya. wajen karfe biyar tasa suhailat ta hada kayanta danda ita zata wuce Kaduna, suhailat bata iya hada kayanba saboda batajin dadin jikinta. Se aliyace tana kunkuni ta hada mata, bisa tursasawar Aunty. Aunty kallon suhailat kawai take tunda ta dakkota yanda gabadaya ta zabge ta rame, se uban fari kamar zabiya. gashi sebin tiles take tana kwanciya, Aunty dai takasa hakuri tatambayeta meke damunta. setace mata wai malaria ce. Aunty baiwar Allah babu tunanin komai aranta seta yarda ta mata fatan samun sauƙi…….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button