Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Anyi bikin saleemat Lafiya, angama lafiya, kwana uku akayi ana bikin, ran Friday akayi bridal shower, asabar kamu, Lahadi aka daura aure aka miƙa amarya gidanta, amarya da ango sun sha kyau ranar bukukuwa, kuma ango yayi ƙoƙarin kama guraren biki masu kyau daidai ƙarfinsa, kullum sai munyi waya da yaya, amma har yau Monday bai dawo ba, ayyuka sun sha masa kai, kullum saidai ya lallaɓani. ina zaune bayan sallar azhar ina cin dubulan da alkaki na garar saleemat wayata ta fara ringing, na dakko na duba ganin suna ammi yasani dagawa da sauri tare da yin sallama, ammi ta amsamun nace “ina wuni ammi” tace “lafiya kalau ɗiyata, ya taro?” nace “Alhamdulillah, yasu Aunty zuhura da mama?” tace duk sunanan kalau, yaushe zaku dawo ne?” nace “ammi har yanzu bai dawo daga Abujan ba” ammi tace “haka yacemun da mukayi waya, yace ayyukan da yawa” nace “haka yacemun nima, amma insha Allah wani satin zamu dawo” ammi tace “Allah yakaimu, ki gaida gwaggon naki da maman amarya” nace “zasuji insha Allah” mukayi sallama ta kashe wayar. kiran wayar yaya nayi bai dauka ba, na ajiye wayar cike da takaici, tashi nayi na dakko turarukansa daya bani, kullum sai na fesa su duka a jikina amma basa mun irin kamshin jikin yaya, kuma na masa complain yacemun da iya su kaɗai yake amfani, kwanciya nayi akan gado ina tunanin yaya, nayi missed komai nasa over, muryarshi, maganarshi, murmushin sa, kamshinsa, lallausar fatar jikinsa da nake lolewa kullum. na daɗe a kwance har saida gwaggo ta shigo tana faɗin, “Maryam kina d’aki a kwance, bazaki gidan amaryar bane? gashi can za’a tafi” na ɓata fuska nace “ehh” gwaggo tace “saboda me?” na mata shiru dan bazan iya ce mata kewar yaya ce take damuna ba, gwaggo  tace “ai shikenan, ki tashi kici abinci to” nace “naci dubulan na koshi” gwaggo tace “ke, Maryam ki raba kanki da shegen cin zakinnan, sai kinje kin haifi ɗa mara cikakkiyar lafiya ko?” nace “gwaggo nifa banda komai, tun da nazo kike fadar haka” gwaggo tace “to ai duk wanda ya san ciki, yana kallonki ya ga mai ciki” nayi shiru amma ban ɗauki zancen gwaggo da mahimmanci ba, tunda nasan nidai bani da komai, har dare yaya bai kirani ba, ni kuma ban ƙara kiranshi ba, ga kewarshi na daɗa addabata, har kuka nayi. Har washegari bai kiraniba, kuma banga ya hau online ba, hankali na ya fara tashi, yau babu walwala kokaɗan na tashi, jikina ma kamar mai cuta, ko abinci ban ciba, dama kwana biyu bana iya cin abincin. Wajen sha biyu na rana umma ta aiko in shirya zamuje gidan saleemat nida kanwarta, banso zuwaba amma haka na shirya muka tafi, mun jima a gidan kuwa muna shan hira, dan sai bayan la’asar muka dawo.

Mustapha sai yau ya samu kansa ya baro Abuja, ayyuka sun sha masa kai ba kaɗan ba, yana abujanne amma hankalinshi gaba-d’aya yana gurin Maryam, yayi matuƙar kewarta, ji yake kamar baya tare da wani ɓangare na jikinsa, bai taɓa tunanin a rayuwarsa zai so mace irin haka ba, sati ɗaya da yayi basa tare, jinsa yake kamar wani mara lafiya, baccima dan dai ya iya sata ne, yake sake ci, gashi bazai iya barin aikin Daddy ya taho ba, amma da tuni ya dawo yaga ƴar matar tasa, jiya da yau baisamu kansa ba sai cikin dare, saboda yanda ya matse aikin yanaso yayi ya dawo, shiyasama bai samu ya kira Maryam ba, Bayan la’asar jirginsu ya sauka a Kano, yana zuwa gidan Daddy wanka kawai yayi,  yayi Sallah, ko abinci bai tsaya ciba ya nufi gidan gwaggo. ina kwance akan gadon gwaggo ina kallon pics ɗinmu da mukayi ranar a mota,  fitowata daga wanka kenan ko kaya bansaka ba. Mustapha ya turo yaro gidan gwaggo ya sanar da zuwansa, gwaggo tana zaune a tsakar gida tace aje ace ya shigo, ya shigo suka gaisa da gwaggo, gwaggo ta shiga masa godiyar kuɗin daya bata, shidai ya mata shiru, ta kwalawa Maryam kira, maryam bata jiba tana can duniyar begen hearbeat ɗinta, gwaggo tace masa ya shiga ɗakin, ya mike ya shiga. tsayawa yayi a bakin kofa yana kallonta, saboda ta juyawa ƙofar baya batasan da shigowarshi ba, Lumshe idona nayi jin kamshinsa da nayi missing na mun gizo a hanci, yanda kamshin yake ƙara ziyartar hancina yasa na buɗe idona tare da juyowa da sauri, gabana nane ya yanke ya faɗi, lokacin da nayi arba dashi tsaye a bakin k’ofa ya harɗe hannayensa a kirji, na rufe idona na ƙara buɗewa dan gani nake kamar gizo yakemun, wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyata dana tabbatar da shidinne, yayi mun murmushi tare da waremun hannayen sa, na tashi da sauri na ƙarasa na faɗa jikinsa, ya rungumeni tsam ajikinsa tare da sakin ajiyar zuciya yana faɗin “i missed you” na ɓata fuska sosai zanyi kuka nace “Ni ban yarda ba” yace “really” nace “bacin kaje ka daɗe, kuma jiya baka kirani ba, yauma haka” yace “kar kice haka, kinsan bazan taɓa kin kirankiba, duk a ƙoƙarin son nazo na ganki ne nayi busy” nace “to amma…” Ya katseni da faɗin “Am sorry, yanzu gani ai na dawo, mai kika ajiyemun?” na bar jikinshi ina murmushi nace “me kake so?” be amsa mata ba, sai bin jikinta da yayi kallo, kasancewar daurin kirji ne kawai a a jikinta, yana jin wani feeling ɗinta na bijiro masa, ya sauke numfashi ya shafi fuskarta yace “kinsan ke kaɗai nake so ai” na kwanta a jikinshi ina boye fuskata a kirjinshi, a hankali ya zare ta daga jikinshi yana fesar da numfashi yace “ki shirya, ina jiranki a mota zamu wuce gidan Daddy” nace “toh” ya juya ya fice dan idan yana kallonta zai iya yin abin kunya a gidan surukai. Cikin mintuna ƙalilan na shirya cikin wata doguwar riga mara nauyi irin me bin jikinnan, na ɗora hijabi akai, wayata kawai na ɗauka na fita tsakar gida nacewa gwaggo “gwaggo zamu gidan Daddy tare da yaya” gwaggo tace “to sai kun dawo, Allah ya kiyaye” nace “ameen” a cikin motar na samesa, yana latsa waya, ganin ta shigo ya ajiye wayar ya bita da kallo, na ɗan ɓata fuska nace “wannan kallon fa?” yace “naga kin ƙara kyau abinki” nace “hmmmm, nayi muni dai” zai yi Magana wayarsa tayi ƙara, dubawa yayi tare ɗagawa, bayan yayi sallama, an amsa yace “na ɗan fita ne, amma yanzu zan dawo” ya katse wayar, ya janyoni jikinsa, na lumshe idona nace “turarunka daka bani, basa mun irin kamshin jikinka” yace “kuma duka wanda nake amfani dasu na baki” nayi shiru kawai ina shaƙar kamshinsa da yake saukarmun da nutsuwa, ya kunna motar muka tafi.

Bayan fitar Mustapha zuwa gidan gwaggo ba jimawa sukayi sabani da su Aunty sukuma sun zo, a part ɗin mommy suka sauka, babu kowa a gidan sai masu aiki da faruq dake kula Sadiq, Daddy da su Haidar duk suna gurin aiki basu dawo ba. Ko zama basuyiba Aunty taja suhailat  part ɗin Daddy suka duba jikin Sadik, suna zaune a falon Daddy, Aunty tacewa Faruq “Muhammad bai dawo daga Abujan bane? Munyi waya ɗazu yacemun before 5 jirginsu zai sauka, yanzu kuma naga 6 saura. Faruq yace “yadawo tun ɗazu, may be yana part ɗin shi yana hutawa” suhailat na jin haka ta miƙe ta fita ta nufi part dinnashi, Aunty batayi tunanin komai akan fitar suhailat ɗin ba, ta ɗauka part din Mommy zata koma, wayarta ta ɗakko ta kirashi, yace mata yafita amma gashinan zuwa. Muna tafe ina bawa yaya labarin bikin saleemat, har muka ƙaraso gida, beyi parking a parking space ba, har ƙofar part ɗinsa ya ƙarasa damu, suhailat dake tsaye a bakin k’ofar ɗinnasa tana jiransa, tana ganin mota anyi parking tasan shine, nufo gurin motar tayi da sauri, Mustapha ya buɗe murfin motar ya fito ya zagaya ya buɗewa Maryam ta fito itama, dai_dai lokacin suhailat ta ƙaraso gurin motar……….✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button