Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mustapha yana shiga part ɗinsu ɗakin Maryam ya nufa direct, tunda beganta a part din ammi ba yasan tana ɗakin. ɗakin dulum babu haske ko kaɗan, yana mamakin yanda take bacci a haka bata barin hasken ko kaɗan. Torch light din wayarsa ya kunna ya haska kan gadon. tana ƙudundune kamar koyaushe kamar wadda take kwanciya a tsorace ta dunkule guri ɗaya. A hankali ya ƙarasa kan gadon ya haye yana ƙara haskata. Blanket din data rufa ya janyeshi daga jikinta a hankali juyi tayi ta matso daf dashi hannunta ɗaya ta ɗora akan cinyarsa tana sauke numfashi taci gaba da baccinta hankali kwance, fuskarta ya haska sosai kifkifta ido ta fara yi saboda haske mata idon da yayi. Ajiyar zuciya ya sauke, ya ɗauke idonsa daga kallon fuskarta. Blanket din ya janye gaba-daya daga jikinta, ya gyara mata kwanciya, yana yin komai cikin dauriya ne, amma tuni ya fara neman nutsuwarsa ya rasa saboda rigar jikinta shara_shara take, kuma duk ta dage sama santala_santalan cinyoyinta duk suna waje. ga kamshin jikinta dake ƙoƙarin hargitsa masa lissafi. kwanciya yayi a gefenta ya janyota jikinsa yana sakin ajiyar zuciya tare da lumshe idonsa, blanket yajanyo ya lullube musu rabin jikinsu. Maryam se ƙara manne masa jiki take, kanta ya ɗora akan hannunsa guda ɗaya, ɗayan kuma ya fara yawo dashi a jikinta yana shafa lallausar fatarta me sulbi yana sakin numfashi a hankali a hankali cikin jin daɗi, Maryam kuwa jitayi tamkar susa yake mata baccinma se ya ƙara mata daɗi. seda ya shafeta san ransa amma a hankali yadda bazata tashiba sannan ya kyaleta badon yasoba, se dan karya wuce gona da iri ya kai matakin dabaze iya hakura da itaba. rungumeta yayi tsam ajikinsa kamar ze maidata ciki, addu’a ya tofa musu bajimawa bacci ya ɗaukeshi…..

MOMMY

Yau da wani a zababben ciwon kai tatashi ko idonta dakyar take iya buɗewa, shine dalilin dayasa ba fita dan fara shirin tafiyarta Landon ba, a daren jiya bata samu ishashshen bacciba saboda tunane_tunane data dingayi. Haka ta wuni kwance akan gado tana juyi saboda kannata kamar ze tsage gida biyu haka take jinsa. Se bayan la’asar ta samu ya ɗan sassauta mata harta kira likitanta ta zo ta dubata. Magunguna ta rubuta mata, ta kuma ce mata ta rage yawan damuwa domin a halin yanzu jininta ya hau sosai. Megadinta ta bawa takardar da Dr. Ta rubuta mata magungunan ya siyo mata a wani pharmacy, shine da tasha ta samu bacci ya ɗauketa…..

BAYAN KWANA UKU

Tattali sosai mustapha yake nunawa Maryam, kodayaushe yana gida manne da ita yana bata kulawa, sallah ce kawai take fitar dashi. maryam kuwa se taɓararta take zuba masa son ranta kusancinsu na ƴan kwanakinnan ba ƙaramar shakuwa ya haifar a tsakaninsu ba, wanda su kansu basu gane hakanba. Kullum tare suke kwana manne da juna, amma Mustapha be ƙara yiwa Maryam komaiba saboda yadda take a tsorace da shi, kullum idan zasu kwanta a ɗari_ɗari take, duk abunda take yana sane da ita, kyaleta kawai yayi tagama abunta. Maryam tama manta da magungunan da zuhura ta bata, bata amfani dasu. lalle kawai take tafasawa tana tsarki dashi safe da dare, se ruwan ɗumi da datake tsarki dashi parmanantly. Taji sauƙin jikinta sosai, yanzu batajin komai na ciwo a jikinta ta koma normal kamar da. Yau talata gobene kuma mustapha ze tafi Kano dubo Sadik jiya monday suka dawo, maryam batamasan da tafiyar tasaba har yau dan be faɗa mata ba. Yau mustapha ya fita kasuwa tun safe, Maryam setaji gabadaya yau bata jin daɗi a cikin zuciyarta, gashi kuma se dare suke dawowa. Bayan sallar la’asar ina zaune a falo na ina karatun Al_Kur’ani megirma. kamar a mafarki naji kamshin turarensa ya cika falon, dago da kaina nayi da sauri na kalli bakin kofa, shine ya shigo bakinsa ɗauke sallama. cikin tsananin farin cikin ganinsa na amsa masa, sannu da zuwa na masa ya amsa ya wuce ɗakinsa. rufe Alkur’anin nayi na ajiyeshi a gefen darduma sannan na mike na nufi kitchen na dakko robar ruwa guda ɗaya tare da ƙaramin cup na nufi ɗakinnashi, yana zaune a bakin gado ya cire takalmin kafarshi, yana cire rigar jikinshi na shiga ɗakin. “Slm alkm” na faɗa cikin sanyin ina satar kallonshi. batare daya kalleniba ya amsa. Ajiye ruwan nayi na gabansa na koma gefensa na zauna, kallon ruwan yayi ya kalleni. ɗan zamowa nayi daga kan gadon danake na buɗe robar na tsiyaya masa ruwan na miƙa masa. karba yayi tare da furta “thanks” a hankali. tass ya shanye ruwan, ya tambayeshi a karo masa ya girgizamun kai alamar a’a. bance komaiba na ɗauki ruwan da cup din na fito falo bin bayanta yayi da kallo harta fice, ajiyar zuciya ya sauke ya ƙarasa cire kayan jikinsa ya faɗa toilet. ban koma dakinnashiba bayan na ajiye ruwan zama nayi a falo ina tunanin rayuwa. Se wajen ƙarfe 6 ya fito daga ɗakin cikin shirinsa na ƙananun kaya, kallonsa nake ta ƙasan ido yamun kyau sosai, kowanne kaya yasa amsar jikinsa suke kamar danshi aka yosu dama can, gashin kannannasa yasha taza ya kwanta abun sha’awa, dama shi bama’abocin saka hula bane koda yasa manyan kaya. kasarowa cikin falon yayi ya zauna a kusa dani, lumshe idona nayi saboda daddaɗan kamshinsa daya cikamun hanci. A hankali batare dana buɗe idonaba nace, “in kawo maka abinci?” “Later” ya faɗa yana ɗaukar remote ya kunna TV ya fara kallon Labaran yamma. yanayi yana kallon fuskar maryam data ɗauke masa kai tana kwabe fuska, yasan ko meyasa take hakan murmushi yayi kawai ya shafi gefen fuskarta yace, “yadai? ƴan mata” shagwabe fuska nayi sosai nace, “ina alawata?” ɗan buɗe bakinsa yayi kaɗan yana fito da kyawawan idanunsa waye alamun shock dinnan yace, “oh, sorry namanta ne” kallonsa nayi na ɗauke kai ina turo baki gaba, tun jiya alawar da Aunty zuhura ta bani ta kare, yau tun safe dana tashi naketa bashi sallahun ya siyomun na maimaita masa sau da yawa saboda karya manta,amma seda ya manta. murmushi mustapha yayi ganin yanda tayi da fuska. Janyota yayi jikinsa ya kwantar da kanta akan kafadarshi tare dasa hannunshi ya zagaye bayanta, Ajiyar zuciya na sauke na ƙara lafewa ajikinnasa. A haka muka kasance harya gama kallon. Tashi yayi yacemun zashi gurin ammi daganan ze wuce masallaci, Allah ya kiyaye na masa tare da fatan dawowa lafiya.

Tunda ya fito daga part ɗinsu ta hangoshi ta fito ne itama zata fita, ajiyar zuciya ta sauke cikin jin daɗin ganinsa, rabon data ganshi tun jiya da safe, tsayawa tayi cak tana kallonsa. Wani tunani ne ya darsu a cikin zuciyarta akan shawarar da fareeda ta bata, duk tana jin tsananin tsoro amma haka ta ƙarfafa zuciyarta akan ta jarraba kawai kozatayi nasara, tunda tabi duk hanyar da zatabi dan ganin yasan da ita amma duk a banza, ita kuma a yanda takejin sonsa acikin zuciyarta da burin datake dashi na auren mijin kece sa’a bazata iya hakura dashiba, dole tayi duk yadda zatayi wajen ganin ta samu gurbi acikin zuciyarsa, ga kuma dama ta samu bazata bari ta kufce mataba. tana ganin ya ƙara kusantota ta tafi da gudu tana faɗin “yaya NOOR oyoyo” tare faɗawa kirjinsa.????……..✍️

By
Zeey kumurya
ABINDA KASHUKA….!

BY
ZEEY KUMURYA

6️⃣9️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

……….Kamar ta watsa masa garwashin wuta a jiki haka yaji saboda tsabar takaici, da ƙarfin gaske kamar ze ballata ya rabata da jikinsa wani wawan mari ya wanketa da shi, seda jinta ya ɗauke na wucen gadi saboda ƙarfin marin. kamar wata kara ya cillar da ita ta fadi ta baya yayi gaba abinsa yana jin wani irin zafi a cikin ransa. “wanne irin sakaci yayi da har yarinyar ta rainashi haka” ya faɗi haka a ranshi danshi a ganinshi wannan ba ƙaramin raini bane. kwafa yayi kawai ya danne ɓacin ransa ya shiga part din ammi. Umaimah da kyar ta yunkura ta iya tashi hannunta dafe da kuncinta cikin tsananin baƙin ciki da kunar zuci, part din mama ta nufa tana hawaye dan fitarma da zatayi gabadaya taji ta fitar mata a rai, kuma bazata iya komawa part din ammi ba dan batasan da idon zata kalleshiba. mama na ɗakinta Umaimah ta shiga falo ta zauna akan kujera tana rusa kuka, haushin fareedah gabadaya ya cika mata zuciya, tunda gashi ta aiwatar da abunda tace ɗin tayi kuma ba’aci nasaraba, yanzu batasan wanne mataki ze ɗauka akantaba akan abunda ta masa….Mustapha sama_sama suka gaisa da ammi, duk da yadda yaso boye ɓacin ransa amma seda ammi ta gane. harta tambayeshi da faɗin “NOOR kana lafiya kuwa?” daga mata kai kawai yayi alamar eh. Ammi bata kuma ce masa komaiba se ido data tsareshi dashi, dan tasan ba haka bane faɗa kawai yayi. seda aka kira sallar magriba ya mata sallama ya nufi masallaci. Bayan anyi sallah mama tataso umaimah a gaba suka zo part ɗin ammi, ammi na kitchen tana ƙarasa girki ita da zuhura taji mama na kwada mata kira. Fitowa tayi tana faɗin “lafiya mama?” Mama ta dubi umaimah dataci kukanta ta koshi tace, “yarki ce na fito na sameta tanata kuka kamar wadda aka ce mata kin mutu, kuma na mata tambayar duniyarnan meyafaru taƙi bani amsa, shine nace bari inzo ko ke kinsan meyafaru” ammi ta dubi umaimah da kyau tace, “Auta meyafaru?” Umaimah ta girgiza mata kai alamar a’a. Ammi tace, “baki da bakine ina tambayarki kina gyada mun kai kamar kadangaruwa” umaimah cikin muryar data ci kuka ta koshi tace,”ba komai” ammi tace, “kukan daɗi kike kenan?” umaimah data fara tsorata da yanda ammi take mata magana tace, “A’a” ammi ta tabe baki tai komawarta kitchen. umaimah ta shige ɗakinta cikin mamakin yanda ammi ta mata, tasan halin ammi zata yi ta tattalinka tana rarrashinta akan abu, amma idan ka isheta seta kyaleka tayi banza dakai. mama tabi ammi kitchen tana faɗin, “dama wai ba daga nan take bane?” Ammi tace, “nifa lafiya kalau muka rabu da ita, zataje gidan zulfa (kanwar mamanta) data kirata tace taje, toni banmasan bata tafiba ashe part ɗinki tayi tana kukan banza.” Mama tace, “to me akai mata?” Ammi tace, “wlh mama bansaniba, kwana biyunnan na lura akwai abunda ke damunta bata da aiki sedai ta zauna taita kunci ita kaɗai, na tambayeta, na tambayeta meyake damunta amma yarinyarnan kullum setacemun ba komai shiyasa na watsar da ita kawai” zuhura dake jinsu tayi murmushi kawai dan tasan meke damun umaiman. Mama tace, “ikon Allah, to ko dai rashin auren dabatayi bane ya fara damunta yanzu?” Ammi tace, “Rashin aure kuma?” mama tace, “eh mana, kila yanzu abun ya fara damunta” ammi ta tabe baki tace, “tasan ze dametan take korar duk wanda yazo da sunan aurannata” mama tace, “ai kinsan yarinta, yanzu kuma ta fara hankali shine abun ze dameta.” Ammi tace, “to ai ba damuwa ya kamata ta zauna tayi tayiba, setayi addu’a Allah yakawo mata mijin nagari tayi auran” mama tace, “hakane, Allah ya kyauta” A bakin part ɗin ammi muka haɗu da mama zan fito ita kuma zata fita, gaisawa mukayi cikin fara’a na wuce ciki. har bayan sallah isha’i ina part ɗin ammi, tare muka ƙarasa girki da muka gama muka zauna nida aunty zuhura muna hira. umaimah ce ta fito daga ɗakinta bata kalli kowa a cikinmu ba ta wuce ɗakin ammi. Ammi na toilet tana wankewa umaimah ta shiga, har toilet din umaimah ta bita, tsayawa tayi a bakin kofa tace, “Amminah sannu da aiki” fuska babu walwala ammi tace, “yawwa” umaimah ta ƙarasa cikin toilet din tana faɗin “ammi kawo na tayaki” ammi tace, “barshi” a taƙaice. umaimah jiki a sanyaye ta koma ɗaki ta zauna a ƙasa ta dafe kuncinta da har yanzu take jinsa wani dimmm saboda marin datasha. 5 minutes later ammi ta fito, bata ko kalli inda umaimah takeba ta nemi guri ta zauna a bakin gado ta mike kafarta cikin gajiya. umaimah tatashi ta hau kan gadon, kwantar da kanta tayi a jikin ammi cikin shagwaba tace, “Amminah dan Allah kiyi hakuri kidena fushi dani, wlh bana iya jurar fishinki ko kaɗan” ammi ta harareta tace, “me kikamun dazanyi fushi dake” umaimah tace, “kiyi hakuri dai amminah Please” ammi ta sauke numfashi tace, “to naji, meke damunkine kwana biyunnan? kinsan dai bazan juri ganin ki a haka ba cikin damuwa” umaimah ta kama kame_kame ta rasa me zata cewa ammi. Ammi ta mata wani kallo tace, “Aure kike so ko umaimah?” gaban umaimah ne ya yanke ya faɗi ganin ammi ta ramkota, tabbas a yanzu babu abinda takeso sama da taga tayi aure. ƙasa tayi da kanta batace komaiba kwalla na cika mata ido. Ammi ta ɗan sassauta murya tace, “ki faɗamun mana daughter idan baniba waza ki faɗawa” umaimah ta ƙara rungume ammi tace, “Eh” tana sakin kuka ammi ta dubeta cike da tausayawa tace, “to ai ba kuka yakamata kiyiba, ko kuma kiyita kunci ba addu’a zakiyi Allah ya kawo miki mujin kiyi auren…” faɗa ammi tashiga yiwa umaimah sosai akan korar samari data dingayi a baya, ta faɗa mata. “Itafa rayuwa komai yazo maka a matsayin kaddararka karba kakeyi hannu bibbiyu, idan kace dole bazakayi aure ba, seka samu irin mijin da zuciyarka takeso zaka mutu bakayi aureba ballema ita umaimah data tsawwala akan yanda takeso mijin dazata aura ya kasance zeyi wuya ta samu, yanzu gashi ta doshi kusan shekara 30 a gida babu auren babu manemi, tunda manemanma yanzu babu, dama ita mace ai lokaci gareta, idan ta kai wani munzalin samarin ma ɗauke ƙafa suke” nasiha dai sosai ammi ta mata, umaimah harda kuka, ammi ta rarrasheta tace ta dage da addu’a kawai. umaimah kamar ta faɗawa ammi son mustapha ne ke damunta, amma dai ta daure bata faɗa matanba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button