Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAYAN KWANA UKU

Rayuwata ta koma kamar tada agidan alh. Menasara,rayuwar kadaici da kunci da tsangwama agurin yaran gidan, a gurin yaya sadiq kawai nake samun sauki, bayan tafiyar su aliya munyi waya da ita har sau biyu, a wayar yaya sadiq, aunty ma haka. Harda yayantama mungaisa, yacemun aliya tanata damunsa da zancena. Dadin abunma ina zuwa makaranta, tanadaukemun kewa sosai, nasaba da zee sosai da sauran kawayenta, su salma da humaira. Kullum yaya sadiq ne yake kaini, driver kuma ya dakkoni. Yanzuma bana gamuwa da yaran gidan sosai, dan dasafe kafinma su fito natafi makaranta da rana idannadawo basanan sai dare muke haduwa.

Abangaren suhailat kuma, cin karanta take babu babbaka tunda aunty tatafi, kullum setaje gurin kamal sun sheke ayarsu, kuma ta dawo zuwa part din mustapha, danma yanzu kotaje bawani kulata yakeyi sosaiba sedai tagaji da zama da tatafi, babban abun dayake kara tada hankalinta yanzu ko hannunsa baya bari tataba. Ko zuwa tayi da niyyar tabashi kamar da, bata iyawa saboda babu fuska. Shikuma mustapha ayan kwanakinnan aiki yakeyi tukuru, gashi a week dinnan zeyi promotion na ma’aikata a companynsu dole ne ya nutsu yamaida hankali danganin yayi adalci ya’ajiye kowa a inda yadace dashi.

Yanzu kam yagane babban kuskuren daya tafka arayuwarsa na barin suhailat tana hugging dinshi da abubuwan dabasu daceba,ada baya daukar hakan amatsayin lefi saboda ganin suhailat cousin dinsace. Zuwannan da aunty tayi shiya kara tunatar dashi abunda yamanta, nasiha aunty tamasa sosai akan illar hakan,yasan aunty bata taba ganinsu a hakanba, kawaidai ta masa wa’azinne akan tunatarwa irinta da da uwa. shine dalilin dayasa yayiwa kansa alkawari idan ba aure sukayiba insha Allahu hakan bazata kara faruwa atsakaninsuba,sedai bisa kuskure. Mommy amatsayinta na uwarsu yakamata ace ita tafara nuna musu illar hakan, tunda sometimes agabanta suhailat din take hugging dinsa. Amma sedai tanuna jindadin hakan. Yana matukar son mommynsa amma bayason wasu halayennata, da first halinta dabayaso shine kyamar talaka, tana nuna musu takala bakowa bane, tana nuna musu talaka tamkar ba cikakken mutum bane. Alhalin Allah dakansa yafada shiyake bada wadata da arziki ga wanda yaso. Kuma badon yafisansa yabasaba, sedon ganin damarsa. kuma aduk sanda yaso ze iya kwacewa. To meyasa ita mommy bata tunanin wata rana suma zasu iya rasa tasu dukiyar, kokuma talakan datake rainawa yamusu ranar wani abun, domin kowa da irin baiwar da Allah yamasa. Sekuma hali na biyu na mahaifiyarsa dabayaso,macece ita me mugun son kanta da yayanta, kome yayanta zasuyi badaidaiba bazata musu maganaba, balle ta kwabesu. Komai sukayi nuna musu take daidaine, gashu kuma batadamu da musu wata kyakyakkyawar tarbiyyaba, ilimin addini kuwa duk basu dashi yanda yakamata, shima dan ya taba zama agurin auntyne lokacin su mommy dukansu suna america, shikadaine a naija, shiyasa yasamu ilimin addine sosai. Sekuma abu na uku, yanda mommy take juya mahaifinsu sekace wani danta, se’abunda tace yayi sannan zeyi, bayajin maganar kowa setata. Wadannan halaye na mahaifiyarsa bayasonsu kokadan, dandai babu yanda zeyine uwa, uwace tafi karfin wasa, sedai addu’a dabaya gajiyawa dayi mata akodayaushe akan Allah yaganar da ita gaskiya…..✍️

BA EDITING YAU????????

By
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

2️⃣1️⃣

BA EDITING YAU????????

……..Yau asabar babu school hakan yasa bantashi da wuriba se wajen goma na tashi, ayyukana nayi duka, saboda yau ina gida. Amma kwanakin da suka shude bakomai nakeba nake tafiya school cikin abunda banayi harda gyaran dakin suhailat da mommy, senadawo nakeyi. Yau time din dana shiga dakinta bacci takeyi bata tashiba, ko agurin break ma banga tafitoba. Se bayan la’asar nagama aikina, saboda har wanki nayi. Ina gamawa nayi wanka nashirya cikin wata doguwar riga mara nauyi da hijabi karami irinna makannan, acikin siyayyar kayan da yaya sadiq yasiyomun jiyane. Duk wani Abu na amfanin mata seda yasiyomun jiya har kayan unders yasiyomun dasu pad, siyayya yamun sosai ta bajinta, duk a kokarinsa na ganin narage damuwa, ga wani tattali da kulawa dayake bani na musamman. nikam nikadai nasan halin danake ciki saboda rashin ganin mustapha, zuwa yanzukam nafara tunanin akwai wani Abu dayake faruka dani akansa, tunaninsa da wani abu dabansa komeneba ya yawaita araina, kullum bana iya bacci sena dauko rigarsa dake gurina nashaki kamshinsa sannan nake samun nutsuwa. Yau kwanana biyar banganshiba tun ranar da abunnan yafaru, wata mahaukaciyar kewarsa naji tacikamun zuciya. Duk wannan abun dake damun maryam akan mustapha kokadan batayi tunanin so bane, dan ita bama tasan menesodinba, anata shirmen kawai burgeta yakeyi. Bayan na idar da sallane, nadakko addu’ar da aunty tabani nakaranta.

Wajen 2/30 mommy ta aiko wata me aiki kirana, a kitchen naje nasameta tanata hada kayan snacks tana package dinsu, sannu da aiki namata,amsawa tayi takara da fadin, “maryam Ku kwashi kayannan dakeda jummai kukai part din my son yanada bakine.” Cikin faduwar gaba na’amsa da to. Ambatarsa da mommy tayi kawai yajefani cikin wani irin yanayi na doki da zumudin ganinsa, a wasu kwanduna masu kyau madaidaita guda biyu mommy tajera kayan, daya na dauka itama jumman tadauki daya, mukanufi part dinnasa zuciyata na bugawa kadan_kadan. Sama_sama muke dan hira da jummai, har muka karasa part dinnasa. Wata bugawa zuciyata tayi lokacin damukasha part dinnasa, dan banyi zaton ganinsa a falon kasaba, amma muna shiga dashi nafara cin karo, se sauran abokannasa da sunkai su six, wata boyayyiyar ajiyar zuciya nasauke, daddadan kamshinsa gabadaya ya mamayemun hancina. Gaishesu muka hauyi daya bayan daya, suna amsawa cikin sakin fuska, shine na karshen gaisuwar saboda yanacan gefene yanata faman latsa waya, tun shigowarmu ko motsawa beyiba balle yadago ya kallemu, gaisuwarma da muka masa hannu kawai yadaga mana, batare daya dagoba. Kananun kayane ajikinsa, Wanda suka matukar yimasa kyau, idanunsa sanye da wani siririn glass baki, tsintsiyar hannunsa nadauke da wata azurfa, tunda nazo gidan duk sanda zangansa da ita nake ganinsa, se kuma wani zobe na azurfa me kyau shima, yasa adanyatsansa na tsakiya,dayan hannunnasa kuma agogene shima me kyau. Acikin yan sakanni nakaremasa kallo, jinakeyi dama karna dena kallonnasa, sefaman sauke ajiyar zuciya nakeyi ahankali. Cikin tsananin farin cikin ganinsa na karasa dinning na ajiye kayan hannuna, senajini nadawo daidai dana gansa. “Oh Allah ni maryam me nakeji haka akan wannan bawan Allan ne?” Nafadi haka araina cikin mamakin wannan bakon al’amari agareni. Daya daga cikin abokan musty mesuna fahad se kallon maryam yakeyi tunda tashigo yarinyar ta masa kyau matuka, nakusa dashine yazunguresa tare da fadin, “fahad kaga wata yar baby, mekyau ko?” Sauke numfashi fahad yayi yace, “hmmm kaidai bari faruq bakaga nasaki baki ina kallontaba” “wlh aboki babyn tayifa” cewar faruq dayakebin maryam da kallo dasuke kokarin fita. Dakatar da ita fahad yayi da fadin, “yan mata yazaki tafi baki gama aikinkiba?” jin maganar mutum kamar dani yake sena juyo ina kallonsa amma bance komai ba, dagemun gira yayi tare da fadin, “eh mana baki zuba mana abunda kika kawo manaba, gashi naga kina kokarin fita, danni nan dakika ganni bakaramar yunwa nakejiba, dan zuwa gurin dinning dinma wahala ze bani” lukman dasuke hira da sauran abokannasu yayi murmushi me sauti danya gano inda fahad yadosa akan maryam. Shikam tunranda yafara ganin yarinyar yaji ta burgeshi amma bawai sonta yakeba, dan yana da budurwarsa bikinsama saura 2 weeks dalilin bikinnema yahadasu anan dansu tattauna. Nima murmushi nayi ganin yanda yayi maganar na juya da nufin zubo musu. Mustapha dake zaune yana saurarensu yadago yace, “ke!” Cak na tsaya cikin matukar tsorata saboda cikin kakkausar murya yayi maganar, bejira amsataba yanunamun kofa alamun na fice. Sum_sum naja kafata nafice dama jummai tayi gaba abinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button