Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Adaidata sahu mukahau nida lami har lokacin hawaye kawai nake fitarwa Daga idanuwana,munyi tafiya me nisa sannan muka iso wata unguwa,wadda bansantaba,lokacinma dazamu hau adaidaita sahun banji inda lami tace masaba,saboda hankalina baya jikina.sallamarsa tayi muka nufi wani madaidaicin gida me kyau.matane dayawa a falon da muka shiga kala_kala.sannu lami ta musu muka nufi wani daki dake cikin falon.nidai binta kawai nakeyi tamkar rakumi da akala.wata matace kwance akan gadon dakin da muka shiga,farace sosai amma kana ganinta kasan ta kara Dana kanti,tana dan kiba.tana ganinmu ta tatashi zaune da fara’arta tana mana sannu da zuwa.”kai gaskiya lami naji dadin ganinki,dama hajiya tanata kirana.tsugunnawa lami tayi agabanta tana kwasar gaisuwa,nima tsugunnawa nayi kamar yadda lami tayi cikin ladabi na gaisheta.wani kallo naga tana bina dashi Wanda nakasa gane ma’anarsa.murmushi tayi tare da kamo hannuna. “Matsonan ‘yata kinji.shiru nayi tare da sunkuyar da kaina kasa.ina wasa da yatsun hannuna.kallon lami tayi tace”lami ina kika samo wannan kyakkyawar yarinyar haka.inafatadai kamar irin wadda nace miki anaso kika samo wato Mara gata.wani irin harbawa zuciyata tayi,araina nace.Mara gata kuma,to ina matarnan zata kaini,mezasuyimun da suke bukatar mata gata,Irina. innalillahi wa’inna ilaihirraji’un,ya Allah kakawomun dauki a duk….maganar lamice ta katsemun zancen zucin danakeyi. “eh hajiya kamar irin wadda kikace kinaso nasamo,insha Allah baki da matsalar komai.dasauri na dago ina duban. Lami.idanuwana gaba daya sunyo waje,zuciyata na bugawa da sauri _dasauri.alamun tsoro da razani sun bayyana karara akan fuskata. Dafa kafadata matar tayi “kada kidamu ‘yata ba wani Abu bane,gidan Hutu zakije dan aikin dazakiyi kadanne.ga fuskarkinanma kinci kuka kin koshi,nasan kewar gidane,amma candinma a hankali zaki saba dashi.maida kallonta tayi ga lami. “lami nagode sosaifa,barina kawo miki sakonki.itama zatayi wankane taci abinci sannnan na kaita gidan hajiya. Kudi me yawa ta bawa,lami Wanda bansan konawa bane,tatafi.kamar yanda ta fada haka tasa aka kawomun abinci me rai da lafiya,da farko kinci nayi amma matarnan tatakuramun dole naci.sejana takeyi ajikinta.bata nunamun kyamar komaiba,abun har mamaki ya bani.wanka tasa nayi ta kawo wata doguwar Riga me kyau,me adon duwatsu.rigar tamun kyau sosai,hijabin danazo dashi na Dora ajikina.umartata tayi na kwanta akan gadonta na dan runtsa,domin taga da alamun gajiya a tattare dani.kwanciya nayi tare da lumshe idona na fada duniyar tunani.saboda halin danake ciki bazan iya wani bacciba.

Kafin la’asar ya gama bucking komai na tafiyarsa,karfe biyar jirginsu ze tashi.misalin karfe hudu ya fito cikin shirinsa tsaf,fuskarnan kamar kodayaushe babu walwala,a tsuke take.musammanma yauda yake jimamun barin gida.gaba daya kannensa da mahaifiyarsa ne zasu masa rakiya zuwa airport. Amma banda suhailat,har time din tana school.Mommy tace akirata,yace ta kyaleta idan yaje ze kirata. domin yasan makarantarma seta baro gaba data tazo tayi ta masa kukan shagwaba,shikuma babu abunda ya tsana sama da kukan mace arayuwarsa.haka suka rankaya suka rakashi,seda jirginsu ya tashi sannan suka nufo gida cike da tsananin kewarsa………

Nikadai kwance a daki matar gidan ta fita gurin bakinta,har akayi sallar azhar na kasa bacci,sakawa da kuncewa kawai nakeyi,ina tunanin rayuwata.tashi nayi nayi sallar azhar bayan na idar na jero nafiloli tare da mikawa me duka kukana,akan yakareni aduk inda nake.nadade a zaune akan sallaya harsaida naji zuciyata tayi sanyi,kafin na mike nakoma kan gadon na kwanta.mintuna kadan bacci ya daukeni,abunka da babu a house,najini akan lallausar katifa.cikin baccina naji ana bubbugamun bayana ahankali.bude idanuwana nayi,ina karewa inda nake kallo.da sauri na tashi zaune saboda tunowa da inda nake.matar nance tsaye akaina tanamun murmushi. Shafa kumatuna tayi tace,am sorry natasheki Daga baccin ko,lokacine yana kurewa kitashi kiyi sallah semu wuce.kaina kawai na Daga mata,ina bin bayanta da kallo.mamakinta gaba daya ya cikani yanda kokadan bata kyamata.sauka nayi daka kan gadon na nufi toilet na dauro alwala.kafin na idar da sallah Ankara kawomun wani abincin.shima cewa nayi bazanciba,saboda akoshe nake.amma matarnan tatakuramun na tsakuri kadan naci.inagama ci muka dauki hanya,saboda kar dare yayi. wata mota me kyan gaske,muka shiga,abaya muka zauna nida ita se direbanta agaba.yana tukamu.

Tafiya mukayi me dan nisa,sannan muka shigo wata unguwa,me matukar kyau da tsari.yanayin layikan unguwarma kadai abun burgewane.kowanne layi da get dinsa,gashi kowanne gida andankarashi wannan yana wane wannan, wannan yana wane wannan. Araina nake cewa dama da irin wannan unguwannin a garin kano,wani layi naga mun karya kwana munshiga get dinsa.wani makeken gida nagani a hannun damana,Wanda tunda nashigo unguwar banga me kyau da girmansa da tsaruwarsaba.sakar baki nayi ina kallonsa,ko wanene me wannan dankareren gidan oho,kai wannan sedai gidan wani babban dan siyasane.wannan gida haka sekace akasar turai.get din farko na gidan muka wuce,tafiya kadan na kara ganin wani get din agaba.Wanda anan drivan hajiya ya fara horn.rasss,gabana yayanke ya fadi,badai wannan gidan za’akaini aikatauba,shikenan lami ta saidani,gidan ‘yan yankankai akakawoni.tunanina ya tsayane daidai lokacin daka wangalemana kofar get din gidan,me matukar girma.harabar gidan kanta katuwace ta isa a gina kamar gidanmu uku acikinta,wannan ma hasashenane kawai amma banga karshentaba.parking space muka nufa,Wanda aka lullubeshi da wata runfa,motocine dayawa a gurin.nidai sakar baki nayi ina kallon ikon Allah.ga wasu mutane datunda muka shigo gidan nake ganinsu,masu korayen kaya,suna shawagi kamar dai security ne.kama hannuna matar tayi tana murmushi. “Maryam mun iso gidanfa,seki fito mu nufi ciki.wani gwauron numfashi na sauke,ina dubanta.bude murfin motar tayi bayan ta sakarmin hannuna,bin bayanta nayi nima na fice Daga motar.ina rungume da ‘yan kayana.

Bansan tayaya zan misalta kyawu da tsaruwar gidanba,tare kuma da girmansa.part,part ne da yawa agidan,tsakanin kowanne da dan’uwansa akwai tafiya.mun wuce na1,na 2.na uku naga ta nufa,Wanda yafi duka wadanda muka wuce kyau da tsaruwa.

Matattakala muka fara takawa,wadda take abakin part din,hawa hudu muka iso bakin kofar part din,wani Abu naga hajiya ta danna Wanda bansan komeneneba.mintuna kadan wata mata da bazata wuce shekara talatinba tazo ta bude mana kofar.aljannar duniya na fada lokacin Dana ganni acikin wani hadadden falo,Wanda ko’a mafarki bantaba tunanin shigarsaba a rayuwata.lallai kudi yana gurin masu kudi.ga wani kamshi da sanyin a.c daya ziyarceni a lokaci guda.ban boye kauyancinaba na fara bin ko’ina na falon da kallo.sannu da zuwa matar tayiwa hajiya.jagorarmu ta farayi da’alama ita zata kaimu wajen matar gidan.wata kofa muka kara shiga,nanma wani falonne Wanda yafi na farko haduwa.gaba daya na manta da abunda ya kawoni gidan,na manta da wata fargaba.abinci kawai nake bawa idanuwana.

Matattakalar bene,naga matar ta nufa damu.nidai kawai binsu nakeyi abaya zugwi_zugwi.se tuntube nake tayi.hannuna hajiya ta kama ganin yanda nakeyi.ita a tunaninta tsoro ne ya kamani. “Kikwantar da hankalinki kinji ‘yata,babu abunda zefaru dake,tunda naganki naga kin shiga raina,dabadan hajiya ta tsanantaba dani zan rikeki a wajena.saboda kin burgeni gaki da nutsuwa.babu abunda zefaru dake agidannan,kisaki jikinki kinji.gyada mata kai kawai nayi,amma zuciyata na bugawa.wani matsanancin tsorone naji ya lullubeni.addu’a nafara karantowa acikin zuciyata ta Neman taimakon Allah,da tsarinsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button