Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Misalin ƙarfe uku da ‘yan mintuna uncle ɗin Mustapha suka ƙaraso gidan su Ammi cikin k’oshin lafiya. Ammi tana harabar gidan tana jiransu, ganinsu yasa ta nufesu da sauri tana ƙara faɗaɗa fara’a akan fuskarta, mahaifiyarta ta fara rungumewa tana mata sannu da zuwa, sannan k’aninta MUHAMMAD mai tsananin kama da ita, sai matarsa kyakkyawa da ita da yaranta twins mace da namiji. Aunty ta jasu zuwa part d’in baƙi na gidan, wanda yasha gyara saboda zuwansu, bayan sun zauna aka ƙara gaggaisawa, Mama, Zuhura, mama Nafisa da Umaimah suma sun ƙaraso falon dan tarbarsu, UNCLE MUHAMMAD wanda yaranshi suke kiranshi da ABBU, sai baza ido yake yana son ganin ta inda d’anshi Mustapha zai ɓullo, mahaifiyarsu su ammi wadda suke kira da HAJJA itama haka dan dama ganin ɗan jikallennata ne ya kawo ta Nigeria. Da sallama ya shigo falon gabad’aya suka zubo masa ido zuciyoyinsu cike da d’okin ganinsa, shi kanshi a nashi a ɓangaren haka ne, fuskarsa ɗauke da murmushi ya ƙarasa ya rungume UNCLE d’insa, wanda ya k’ura masa Ido, cikin Muryar mai cike da zallar farin ciki yace, “welcome my dearest uncle” Abbu ya shafa kansa fuskarsa ɗauke da yalwataccen murmushi yace “welcome Son like no other, nice to meet you” cikin tsananin kaunar uncle d’innasa yace “me too” tare da sakinshi ya nufi gurin wadda yake da tabbacing itace grandmother d’insa saboda yadda take kama da Amminsa duk da ta manyanta, Hajja wadda ta saki baki da hanci tana kallonsa cike da tsananin mamaki ta fashe da kuka cikin hausarta da bata fita sosai “Allah k’adiran, mai girma da juya al’amari a duk yadda yaso, tabbas wannan babu tantama jininmune kuma jinin modibbo, lallai ikon Allah ya wuce gaban komai, yaro mai tsananin kama da ubansa, yanda kasan modibbo haka nake ganinsa” mustapha ya ƙarasa gareta ya rungumeta, ta rungumeshi itama tana cigaba da kuka tana faɗin “ashe da rabon zaka dawo garemu, Allah ya jikan mahaifinka adalin mutum mai farar zuciya wadda ke cike da alheri” Mustapha ya amsa da “ameen” tare da sakinta ya shiga share mata hawaye, yanajin wata irin kaunarta na ratsa masa zuciya, Ammi tayi ƙasa da kanta tana ƙoƙarin maida kwallar data taron mata a ido saboda tuno mata da mutumin da bata da kamarsa a duniya, Hajja ta ƙara ruk’unk’ume Mustapha a jikinta tana kuka, ya samu ya lallasheta tayi shiru, amma fa duk inda yayi idanta na kansa, gurin matar UNCLE d’insa wadda yaranta suke kiranta da Ummee yaje ya gaisheta, twins suka taho jikinsa gabad’aya suna gaisheshi, yara kyawawa ‘yan kimanin shekara 7, sai larabci suke zuba masa, Mustapha ya ƙurawa macen ido saboda yadda take acting ɗinta sai yaga kamar Maryam ɗinsa, musamman idan ta waro manyan fararen idanunta ko kuma ta turo ɗan ƙaramin bakinta gaba idan, ya rungume yaran a jikinsa cikin kaunarsu. Su ammi suka cikawa su Hajja gabansu da lemuka nasha kala_kala da ruwa, Abbu kuma sanin da Ammi ta masa baya shan abu mai sanyi, sai ta kawo masa had’add’en shayin data masa na musamman. Ammi ta dubi Mustapha tace “ina ɗiyata kuwa, ko batasan sun ƙaraso bane” Mustapha ya ɗan shafi kansa yace “tana bacci ne, amma bari na taso ta” Hajja ta amshe zancen da faɗin “a’a, karka tasota barta tayi baccinta, abunda muna gidan ba yau zamu tafi ba, idan ta tashi ma gaisa” Mustapha yace “ai lokacin Sallah ma yayi kuma ta jima tana baccin” Ammi tace “katasota toh tunda ko abincin rana bata ciba” ya amsa tare da miƙewa, Umaimah ta bishi da kallo cike da kaunarsa, twins suka ce zasu bisa, umminsu ta hanasu.

Na farka daga baccin tun ɗazu amma ban tashi ba, ina kwance akan gadon jikina yayi wani irin sanyi sai faduwar gaba da nake tayi, addu’a na shiga yi a cikin raina kona samu sauƙin abunda yake damuna, idona a lumshe yaya ya shigo ɗakin, gadon ya hawo ya janye blanket d’in dana lullube jikina, ya shafa fuskata tare da faɗin “princess har kin tashi?” na buɗe idona a hankali na sauke su akan kyakkyawar fuskarsa, kai na gyada masa alamar eh. Ya janyoni jikinsa yana faɗin “time ɗin Sallah yayi, muje muyi alwala” bance komai ba, ban kuma yi yunkurin motsawa da niyyar tashi ba, sai kwanciya da nayi a jikinsa nayi lamo, ya d’ago fuskata fuskarsa na nuna damuwa yace “Princess me yake damunkine wai, ko jikinne?” na girgiza masa kai alamar a’a, ya taɓa wuyana yaji zafin jikina ya ragu sai gumi dake tsatstsafomun alamun zazzaɓin ya tafi. Bai ƙara cemun komai ba, ya ɗauke ni ya kaini toilet, shap_shap yamun wanka nayi brush, muka dauro alwala sannan muka fito. Yana ƙoƙarin fita yace “kiyi sauri ki shirya kije part d’in baƙi su uncle sun ƙaraso tun ɗazu, bai jira amsataba ya fice jin antada sallah a masallaci. Shiryawar na shiga yi cikin sauri kamar yadda yace, sai dai bansan Meyasa ba nakejin zuciyata na wani irin bugu tun ɗazu, yanzu kuma daya sanarmun da zuwansu uncle sai bugun zuciyar ya k’aru. Bayan na idar da Sallah na nufi part d’in baƙin, da sallama na shiga falon kyakkyawar matar dake zaune wadda bazata wuce shekara 38 ta amsamun tare da bina da kallo, na ƙarasa gabanta na durkusa har ƙasa na gaisheta domin nafahimci itace matar uncle, ta amsamun da fara’a a fuskarta ta ƙara da faɗin “kece sirikartamu kenan” nayi murmushi tare dayin ƙasa da kaina cikin jin kunya, Hajja ta fito daga d’akin da tayi Sallah Hanifa na biye da ita a baya, haka kawai Hajja taji gabanta yayanke ya fad’i, ummee ta dubeta tace “Hajja ga kishiyar taki fa, kyakkyawa da ita kamar mijinta” Hajja ta zauna akan kujera tana bin Maryam da kanta ke ƙasa da kallo tace “to sannunta, amma dai nasan duk kyanta na fita shiyasa ta kasa d’ago kai ta kalleni” nayi murmushi tare da tashi na nufi gurinta muna haɗa ido gabana ya faɗi sosai, hasbunallu….. na shiga karantawa a raina saboda faduwar gaban ta isheni, itama Hajja anata ɓangaren haka, kafe Maryam da ido tayi ko kiftawa babu, na daure duk da abunda nakeji a raina na gaisheta cikin girmamawa, tsohuwar mata ce amma hutu da jin daɗi ya boye tsufanta, tana kama da Ammi sosai, ta amsamun gaisuwata tare da cigaba da tsokanata. Haneefah ta matso jikina tana mun murmushi tare da mun magana cikin harshen larabci, na shafa kanta inajin wata kaunar yarinyar lokaci ɗaya ta shigemun zuciya, itama kuma lokacin dana kalleta sai da gabana ya faɗi, surutu take tamun, cikin abunda na fuskanta ta faɗamun sunanta Haneefah, tana da ɗan’uwa Haneef yabi Abbunsu masallaci, ummee tacemun nayiwa Haneefah turanci tana ji. Muna zaune muna shan hirarmu da Haneefah ammi ta dawo ɗakin, Hajja da Ummee kuwa kallonmu kawai suke kamar sun samu TV, Ammi ma data shigo sai da ta kalli Maryam ta kalli Haneefah, ta ƙara kallousu, tayi haka ya kai sau uku, sannan ta sauke numfashi ta amsa sannu da zuwan da Maryam ta mata, tare da tambayarta ya jiki, dan Dr husnah, ta biya sun gaisa ɗazu tace Maryam tazo dubawa. Haneef na gaba Abbu na binshi a baya suka shigo falon, Hannef ganin yar’uwarsa gurin Maryam shima ya nufi gurinta ya zauna a jikinta yana gaisheta, amsawar da Maryam tayi yasa Abbu wata irin juyowa yana kallon Maryam a wani irin yanayi na rud’ewa, dan jin Muryar da tayi kama data wadda bazai taɓa iya mantawa da ita ba a rayuwarsa, a hankali na d’ago kaina jin wanin yanayi na baƙuntar zuciya da gangar jikina, na kalli mutumin da Haneefah take nunanmu tana faɗin “ga Abbunta ya dawo” cikin harshen turanci, wani abu da bansan ya zan misalta muku shiba ya ziyarci zuciya, kasa gaisheshi nayi Saboda wani nauyi da harshe na yamun, Abbu dayake ganin tamkar Maryam ɗin shi daya bari tsawon shekaru masu yawa yace “Maryam!” cikin ƙaraji, Ammi ta dubeshi da tsantsar mamaki tace “kasanta ne ɗan’uwa?” Bai iya bata amsa ba sai jikinshi daya ɗauki wani irin rawa nuna Maryam yake da hannunshi amma ya kasa magana, ƙasa yayi luuu zai fadi Mustapha da shigowarsa kenan ya tafi da sauri ya riƙeshi, zaunar dashi yayi akan kujera gabad’aya su Ammi suka yo kansa suna masa sannu cikin tsananin al’ajabin abinda yasashi a cikin wannan hali lokaci ɗaya. Hajja ta dafa kafadarsa cikin yarensu na buzaye a ɗan ruɗe take faɗin “Muhammad meyafaru?” Abbu ya sauke wani gwauron Numfashi yana fitar da numfashi da k’yar yace “Hajja gamo nayi, naga wata kamar matata Maryam danake baku labarinta kuma tayi magana har muryarsu iri ɗaya” Ammi ta juya da sauri jin abinda yace ta kalli Maryam data kasa koda motsi, idanunta a lumshe hannunta dafe da kanta, Ummee ta mik’o masa ruwa mai sanyi wanda ta tsiyayo masa a cikin wanda ammi ta kawo musu, ya karba yayi bismillah ya fara sha, ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama shan ruwan ya dafe kansa daya fara sara masa. Mustapha kallonsa kawai yake bece komai ba zuciyarsa na bugawa shima, Ammi ta tattaro dauriyarta dan itama a ruɗe take tace “Muhammad ba gamo kayi ba, wadda kagani akwaita a zahiri kuma itace matar NOOR kuma itama sunanta Maryam, amma nasan ba ita bace wadda kake nufiba” Abbu ya mike da sauri yana faɗin “ina take?” Ammi ta nuna masa Maryam dake zaune kamar mutum mutumi, ƙarasawa yayi gurin Maryam da sauri ya rungumeta a jikinsa cikin tsananin zak’uwa yace “dan Allah wacece ke? ya akai kike tsananin kama da Maryam d’ita? dan Allah ki faɗamun ko kin santa ki kaini inda take dan Allah” Maryam tayi tsit tana jin wani irin abu na ratsa jikinta a sanadiyyar jinta a jikin Abbu, Abbu ya saki Maryam ya dubi Ammi a ruɗe yace “ƴar’uwa ki mata magana ta faɗamun dan Allah, inason ganin Maryam d’ita kullum da tunaninta nake kwana nake tashi a raina ita da cikina dana tafi na barshi a jikinta” Ammi ta kama hannunsa ta zaunar dashi cikin kwantar da murya tace “ka nutsu Muhammad ka mana bayanin waccen Maryam kake nufi” yace “Matata! Matatace, itace matata ta farko wadda mak’iya suka shiga tsakaninmu suka rabani da ita da garin Kanon gabad’aya shekara kusan 20 kenan yanzu” Ammi ta zauna dab’as a kusa dashi dan ita bata taɓa sanin da batun wata matarsa Maryam ba, Hajja ta zauna a ɗaya gefennashi tana faɗin “wai kana nufin matar Muhammad itace kagani kamar Maryam ɗin da kake bamu labarinta?” Ya gyad’awa Hajja kai idanunsa a kan Maryam, da kanta ke ƙasa har lokacin, Mustapha ma kallonta kawai yake. Ummee ta ƙarasa ta zauna a kusa da Maryam ta rungumeta a jikinta tana addu’ar fatanta ya zama gaskiya akan Maryam, ko dan ta samu nutsuwar mijinta da kwanciyar hankalinsa gami da farincikinsa ya dawo, dan yasha faɗa mata bazai taɓa samun hakan ba, harsai yaga Maryam d’insa ya nemi yafiyarta akan tafiya da yayi ya barta. Ammi ta dubi Hajja so surprise tace “kema kinsan Maryam ɗin dayake magana akanta ne?” Hajja tace “eh matarsa ce daya aura a Kano tun bayan barowarsa daga nijer” ammi tace “to me ya rabasu, kuma a yanda na fuskanta tunda ya barta bai waiwayetaba” Hajja tace “shi zaki yiwa wannan tambayar” Ammi ta maida dubanta ga Abbu tace “Please Muhammad ka fitar dani daga cikin duhu, I want know alot about what you said” Abbu yaja wani gwauran numfashi yace “labari ne mai tsayi ya Maryam, amma zanyi ƙoƙari na tak’aita miki, amma kafinnan inason nasan wacece ita wannan Maryam ɗin” Ammi tace “forget about this bro, ka fara bamu labarin taka Maryam ɗin, zakasan ko ita wace daga baya” ganin yanda Ammi ta damu Abbu basan ransa ya fara basu labarin kamar haka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button