Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tafa hannuwa mama takeyi tana sallallami tace, “yanzu Alhaji macece ta aikata wannan abubuwan itama akan dukiyar, kai duniya ina zaki damune?.. wannan wanne irin masiface da bala’i, kadaukarwa kanka hakkin mutane saboda wani banzan burinka na duniya” “Gaskiya matarnan tacika shu’uma, kuma makira, Allah wadaran halinta” cewar nafisa. Maryam da aliya kuwa suman zaune sukayi dajin abunda mommy ta aikata, yanzu sungano dalilin dayasa mommy bata gida. Rungume Aunty ammi tayi ajikinta tana hawaye tace, “nagode sosai da yanda kika kula da ɗana, kika tsaya tsayin daka wajen ganin rayuwarsa ta inganta, Allah yasaka da alkhairi.” kara rungume ta, Aunty tayi itama ajikinta tace. “Babu komai ai yiwa kaine, kuma Ni haryanzu Muhammad, kallon ɗana nake masa, babu abunda yacanza.” sakin Aunty ammi tayi tana murmushi tace, “bazan gaji da miki godiyaba, Allah yaraya miki zuri’a ya kare gabanki da bayanki” “ameen” kallon Maryam ammi tayi, tundaga kallon farko data mata, taji kaunar yarinyar tashiga ranta. yarinyar ta burgeta ga nutsuwa a tattare da ita. yanzu kuma dataji abunda tayiwa ɗanta setaji kaunar tata ta karu aranta. “Zonan diyata yar albarka” ammi tacewa Maryam. A hankali ta mike cikin matukar sanyin jiki, ta nufi gurin ammi. rungumeta ammin tayi ajikinta, tana saka mata albarka, lokaci daya Maryam taji kaunar matar ta shiga ranta. Duban Zuhura mama tayi tace. “Zuhura, kije kidakko Abul mana magriba ta gabato.” “Toh, mama” zuhura ta amsa mata cikin girmamawa sannan ta mike tashiga wani daki ta dakko ɗanta, mesuna Nasir amma ana masa lakabi da Abul. Jaririne dan befi wata uku ba. Sosai su mama suka jimanta halin mommy, dana yayyin baban Mustapha, ga kuma mamakin yanda Allah, yasakawa dukiyar Mustapha albarka. Ammi ma tayi mamaki sosai, dataji wai dukiyar Mustapha ce, tazama haka, gashi Allah yasa mata albarka, mutane da dama sun amfana da ita. duban daddy tayi tace. “Yanzu ina matar taka, inason ganinta itama namata godiya, ko bakomai ta rikemun yarona, bazan gazaba zanta mata addu’ar shiriya, Allah yasa tatuba takoma ga Allah” kasa kawai daddy yayi da kansa yana jinjina kyawun hali irinna ammi, duk abunda akace mommy tayiwa yaronta amma bata zagetaba, kota aibatataba se fatan shiriyama data mata. kallon Mustapha wanda yayi shiru tamkar baya falon daddy yayi yakira sunansa. “Son!” A hankali ya juyo lumsheshshun idanunsa ya kalli daddy, tare da motsa labbansa ya amsa masa. “Ina son sanar dakai wani abune, duk da nasan namaka karfa_karfa a cikin rayuwarka, amma inafatan zaka yafeni kakuma fahimci manufata” kallon daddy kawai Mustapha yakeyi amma be fuskanci meyake nufiba. fahimtar hakan daddy yayi. a gogon hannunsa ya kalla a karo na biyu. dagowa yayi yadubi kowa sannan yace. “Lokaci na kurewa, gashi a yau nakeson mukoma Kano, amma akwai abu guda daya danakeson sanar daku. A ranar da Mustapha ya warke daga ciwon dayayi, naje masallaci bayan an idar da Sallah nasamu liman mukayi magana akan wata bukatata,liman ya amincemun. batare da wani bata lokaciba nasa aka daura auren MUSTAPHA da MARYAM ni nayi waliccin mustapha,liman yayi na Maryam, tsirarun mutanen dasuka rage a masallaci suka zamto shaida”………..✍️

By
zeey kumurya
4️⃣9️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

……….A razane Maryam ta dago ta kalli daddy zuciyarta na tsananta bugu tamkar zata faso kirjinta ta fito. gabadaya yawun bakinta kafewa yayi,kallon daddy take a matukar razane, kana ganinta kasan a matukar rude take dajin al’amarin. shiko mustapha lumshe idonsa yayi cikin yanayin da baze misaltuba. cikin tsananin farin ciki ammi tace. “Kaii, Masha Allah Alhaji, Allah yasanya albarka Allah yasa hadinnan yazame mana alkhairi, kai Masha Allah, amma naji dadi sosai Ubangiji ya tabbatar da alkhairi yabasu zaman lafiya da zuri’a dayyiba” “Ameen” Aunty ma kallon daddy kawai takeyi cike da dunbin mamakinsa bata taɓa tunanin abunda ze fadaba, kenan. amma kuma taji dadin wannan hadin da yayi sosai, dama kalar matar data dace da Mustapha’n kenan ba kalar su suhalat ba. tasan Maryam bazata taɓa bawa daddy kunyaba da yardar Allah. Aliya kam se murmushi take saki, najin dadi dakuma na shakiyanci ganin yanda Maryam duk tabi ta firgice. gashi kuma sun bala’in dacewa seyanzuma take ganin haka. sotake su hada ido da Maryam,amma ta sunkuyar dakanta. Maryam Sarkin kuka, se hawaye takeyi tarasa na farinciki ne, kona me?… gashi dai zuciyarta ta jima da kamuwa da kaunarsa, amma kuma hada aurensu da dady yayi yazo mata a wani irin yanayi na fargaba da tsoro. Daddy kam, nazarin Maryam kawai yakeyi yasan ya mata katsalandan acikin rayuwarta, shikansa yasan be kyauta mataba. besaniba kotana da wanda takeso. Amma shi yanada dalilin dayasa ya aura mata Mustapha’n, kuma yana fatan aurennasu yazamo musu alkhairi gabadayansu. cikin sanyin murya me nuni da rarrashin wanda akewa maganar daddy yafara mata magana. “Maryam! Bansan da kalmomin dazanyi amfani dasu gurin baki hakuriba akan wannan auren dana miki batare da yardarkiba, a matsayina na wanda bakomai bane a gurinki, amma duk da haka lokaci bekure mikiba, idan har kinga zaki cutu, kokuma kina ganin natauye miki wani hakki na rayuwar ki, karkiji komai ko wani nauyi ko kunya, tunda rayuwarkice. kifadamun idan bakyason aurennan, kamar yadda nasa aka daura yanzu senasa a warwaresa.” Ajiyar zuciya nasauke, kaina na kasa bandagoba. kukan dake kokarin kufcemun na danne nace. “Babu komai daddy, aikaima ka isa dani, insha Allahu zanmaka biyayya gwargwadon iyawata bazan baka kunyaba” daga haka nayi shiru a raina ina fadin, “tayaya zan yarda a warware wannan auren da…..” “Masha Allah, haka nakeson ji Allah yamiki albarka, yabaki yaya masu biyayya kamar yanda kikamun” daddy yakatsemun tunani da fadin haka. Addu’a sosai daddy yaita kwararawa mustapha da Maryam. kowa nagurin sesawa auren albarka yakeyi. nikuwa nayi shiru ina saurarensu jinakeyi tamkar mafarki nake zan farka wani lokaci. sonake na kalli fuskar gogannawa naga a wanne yanayi yake ciki amma nakasa. Ammi ko se kara rungumeni take ajikinta. Mustapha kuwa ko kwakkwaran motsi beyiba, miskilancinsa kuwa baze bari kagane yanayin dayake cikiba game da maganar aurannashi…..

Sallar da aka shiga a masallaci ta tarwatsa zaman, dady da Mustapha suka nufi masallaci. Aunty tana da alwalarta,dadduma kawai zuhura ta kawo mata tatada sallah a falon. Maryam da aliya ne suka shiga daki domin yin Sallah. zaune suke akan darduma bayan sun idar da Sallah. “Mairota how market?” Aliya tafadi haka tana kwashewa da Maryam da dariya, ganin yadda take komai jikinta asanyaye. banza Maryam tamata bata kulataba, dan ita haryanzu zuciyarta takasa yarda wai yanzu aure yashiga yatsakaninta da heart beat dinta. matsowa jikinta Aliya tayi ta fara mata magana seriously. “Wlh Maryam, kinyi dace da miji bakadanba domin yaya Mustapha irin mijin dakowacce mace zataso ta mallakeshine, amma ke nasan mene damuwarki akan wanan aurennaku. abu na farko dake damunki saboda kina da wanda kikeso wato yaya Sadiq, na biyu kuma kina tunanin yanda zakiyi rayuwa da wanda baya sonki” da mamaki Maryam ta kalli aliya, tamkar ta shiga zuciyarta dan abunda aliyan tace shine abinda take ta tunani tun dazu. daga mata gira aliya tayi tace, “koba haka bane” numfashi na sauke nace. “Hakane aliya, ni namafi tunanin yaya Sadik, dan yana matukar sona nasan bakaramin tashin hankali ze shigaba idan yaji wannan abun” “gaskiya abun babu daɗi rana daya arabaka da masoyinka dake da yaya Sadik dole zaku shiga damuwa, daman, amma kuma hakuri zakuyi dan bamusan alkhairin dake cikin wannan aurennakuba. shikuma yaya Mustapha kisha kuruminki, dan idan ana kuka akan soyayya seya miki shaɓe_shaɓe har da gunji, nina fada miki kuma.” “Hmmm, aliya kenan bana tunanin haka agurinsa tunda shima kinsan yana da wadda yakeso,kawai babu yanda zeyine” tabe baki aliya tayi tace. “Wai ant suhalat kike nufi, tabb aiba wani sonta yakeba,kawai biyayya yayiwa mommy yake kulata, banda haka mezeyi da wata suhalat mace ba kamun kai” shiru namata domin nikadai nasan halin da zuciyata take ciki. baki aliya taita bani akan aurennan da dady yamun tana tausata. batasan nafi kowa murna da aurannanba kawai dai fargabata daya yanda zamuyi tarayya matsayin miji da mata dashi,nasan akwai ja. daga karshe kuma seta koma tsokatana wai zanyi fama da miskilancinsa. Ammi ce dakanta tazo takiramu domin Muci abinci. Da kyar daddy yayarda su tsaya suci abincin dan da cewa yayi tafiya zasuyi, mama ta masa magiyar yabari su kwana da safe sesu wuce, amma yace mata hakan baze yiyuba. Domin bakaramin ayyuka ne agabansaba, dan missed called din dake wayarsama kadai ya ishe sa, ga harkar kasuwancinsa yanaso gobe yakoma acigaba da daga inda aka tsaya. kadan sukaci abincin kowa yace yakoshi, Maryam kam batafi lauma biyuba tace takoshi. Mustapha kam beciba, Aunty ce tacewa ammi haka yake, bedamu dacin abinciba sedai coffee ko tea. ammi bata bata lokaciba ta shiga kitchen ta dafa masa hadadden shayi dayaji kayan hadi, ta kawo masa. tamkar zata bashi a baki saboda kauna. kafin isha’i su dady sungama shirinsu na tafiya. ammi tacikasu da kayan su bagaruwa da dabino datazo dasu daga Saudiyya, suna kewar juna sukayi sallama,bayan sunyi musayar numbobin juna. Maryam se kwakube Aunty take, batasan anan za’a bartaba tunda mijinta bandashi za’a tafi ze zauna gurin mahaifiyarsane. Afarfajiyar gidan Aunty ta tsaidata da fadin. “To, Maryam saduwar alkhairi, insha Allahu gobe kafin na koma kd, zanje gidan gwaggonki na mata bayani, inda halima har kauyennaku semuje da yaya suma mumusu bayani” Maryam bata amsawa Aunty ba, se kuka data fashe dashi tare da riketa. tausayintane yacika Aunty, aliyama se hawaye na tausayin maironta. rungumeta Aunty tayi tana bubbuga bayanta alamun lallashi. cikin kuka tace. “Aunty dan Allah nidai zan biki mutafi” duk dauriyar Aunty seda kwalla ta cika mata ido, domin itama bakaramin missing Maryam zatayiba. maida kwallar data cika mata idon tayi tadago da Maryam daga jikinta. cikin lallami tace mata. “Kiyi hakuri diyata, ai zandawo nanbada jimawaba, kuma aikinyi sabuwar mommy, gaki ga amminki zata miki fiyema da abunda zanmiki, kikwantar da hankalinki kidena damuwa, idan kuma mukayi waya da ammi tacemun kina damuwa tobazanzo intafi dakeba.” Aunty ta karashe zancen tana sharemun hawayen fuskata. gyada mata kai nayi alamun gamsuwa. Addu’ar fatan nasara ta mun. rungume juna mukayi da aliya cikin shaukin juna muna kuka, da kyar Aunty ta rarrashemu muka yi shiru. harta juya zata tafi nace mata. “Aunty yaya Sadik fa, inajin tausayinsa.” maganar Maryam karaf a kunnen Mustapha daya baro gurin daddy, yazo sukara yin sallama da Aunty. “Karki damu Maryam, nasan mezance masa dabaze damuba” Aunty tafadamun haka tana kallon Mustapha. cikin karayar zuci najuya nakoma cikin gidan dazan fara sabuwar rayuwa a cikinsa,jikina a matukar sanyaye. a zaune nataddasu dukansu a falon sunata maida zance. kaina na kasa na musu sallama, gefen Aunty zuhura datake bawa yaronta nono na zauna. jana ammi da mama suka shigayi da hira duk dan insaki jiki dasu musammanma ammi. seda kusan mintuna 20, suka shude sannan ya shigo falon, bakinsa dauke da sallama. amsa masa mukayi gaba-daya, ammi fuskarta dauke da fara’a ta nunawa mustapha gefenta yaje ya zauna. kallo daya zakayiwa ammi katabbarta da tana cikin tsananin farin ciki. fuskarta cike take da annuri, tarasa ina zata tsoma kanta saboda jindadi da murna. harta kira mahaifiyarta da kaninta tasanar musu. kaninta yace ze kirata anjima ta video call suga mustapha. muna zaune a falon Saddam da mijin A’isha suka shigo. suna zama mama tafara rattaba musu bayanin abunda yafaru………..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button