Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Har aka sharuwa bansakashi a idonaba, jikina yau duk a sanyaye. Maganganun Aunty zuhura se yawo suke a kwanyata. “Tabbas duk abubuwan data faɗa hakane, karnaje natsaya kallon ruwa kwado yamun kafa, yazama dole nima nadage dan ganin na jawo hankalinsa gareni, tunda ina tsananin sonsa, ga kuma masu kawo masa farmaki daga waje, amma matsalar bansan ta ina zan faraba, ko shawarar Aunty zuhura zannema, takaramun haske da dabarun yanda zanjawo hankalinnasa.”…. Haka dai naita tunane_tunane nikadai. Be shigo gidanba seda aka idar da da sallar asham, ina jinshi ya kunna kallo a falo amma nakasa fita falon, duk da zuciyata na azalzalata naje nafara aiwatar da abunda naji aunty zuhura nafadawa kawarta amma nakasa, hakura nayi na kwanta bacci saboda tashin dare….. Washegari bantashi daga barci da wuriba saboda yau se 11 mukeda exam, kafinma na tashi daga barci ya fita. seda na gyara gidan tsaf nayi wanka na shirya cikin Uniform dina sannan na nufi part din ammi domin na gaisheta. Suna zaune a falon ita da umaimah nayi sallama na shiga, ammi ta amsamun amma umaimah se bina datayi da kallon banza. muka gaisa da ammi cikin fara’a. duban umaimah nayi dan kar ammi ta zargi wani abu nace mata “Aunty umaimah ina kwana?” Umaimah da tunda Maryam ta shigo taji wani baƙin ciki ya turniketa, saboda ganin Maryam yanzu ya kara tuno mata da abunda yafaru jiya. maimakon ta amsawa Maryam gaisuwarta seta faki idon Aunty ta galla mata harara tare binta da wani wulakantaccen kallo, ran Maryam ya ɓaci taji babu daɗi sosai, amma ta daure ta dubi ammi tace. “Ammi zan wuce naga 10:20 tay…” Bangama rufe bakina sassanyan kamshinsa ya ziyarci hancina. Lumshe idona nayi cikin jin daɗi ina sauraren daddadar muryarsa yana sallama. Rabona dana ganshi tun jiya daya dakkoni daga school, da asubama daya tasheni sahur ban wani ganshiba ina buɗe kofa ya juya ya tafi.. muryarsa naji yana faɗin, “taso mu wuce” mikewa nayi cikin jin daɗi dannasan dani yake. Ammi tana murmushi tace, “har ina zanyiwa yiwa Ali driver magana yakaita, ashema kana tafe” kallon Umaimah data kura masa ido da mayen kallonta yayi, sannan ya maida kallonsa kan Maryam, yana wani kankanne ido irin kallon luv dinnan yace. “Nafison na kaita da kaina ammi, karnaje amun gudu da ita a mota a wahalarmun da ƴar matata.” yana gama faɗin haka ya juya ya fice abunsa. Naji daɗin abinda yafada sosai ko ba komai ya wankemun bacin ran da umaimah ta samun, duk da nasan ba har zuciyarsa haka bane, dan umaiman yayi, kamar jiya daya ɗaukeni amma farincikin danaji baze misaltuba, dandai ammi tana gurinne dase na faɗa masa magana nima wanda zata kara kular da umaimah’n. Cikin jin kunya nayiwa ammi sallama nabi bayanshi. Aiko Umaimah ta shaka ba kadanba. Amma duk da haka ba gudu ba ja da baya a son mustapha yanzuma ta fara, wannan soyyayar dayake nunawa Maryam setayi duk yadda tayi ta dawo kanta seta jawo hankalinsa gareta kota yayane…….✍️

Kuyi hakuri da wannan na koma school ne.

By
zeey kumurya
5️⃣7️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

……….Ammi ta rakasu da murmushin jin daɗi, dama ita burinta kenan taga sun haɗa kansu kuma Alhamdulillah ta lura babu wata matsala a zamannasu…. Yana gaba ina binsa abaya har muka karasa gurin motar, na zagaya na shige bayan shima ya shiga. kafin ya kai ga kunna motar wayarsa ta hau ruri cikin amo me daɗin sauti. dagawa yayi ya kara a kunne tare da yin sallama. Amsa masa akayi sannan yace, “Aunty ina kwana, ya ibadah?” Da sauri na kallesa jin ya ambaci sunan Aunty. daga can ɓangaren bayan Aunty amsa masa gaisuwar ta ƙara da faɗin, “Muhammad suhailat ce keson magana dakai, ta dameni inkira mata kai, wai ita idan takiraka baka samun wayarka.” Cikin matukar mamaki yace, “suhailat kuma?” Gabanane yayanke ya fadi jin sunan Aunty suhailat daya ambata. Aunty tace, “ehh” bekara cewa komaiba duk da zuciyarsa cike take da mamakin meyakai suhailat gidan Aunty, tunda yasan ba zuwa takeba. nikuwa tsumu nayi ina saurarensu. Suhailat bayan Aunty ta mika mata wayar cikin azabarbi tace, “yayana! I missed you, dan Allah yaushe zaka dawo, wlh gaba-daya duk nabi nadamu, ganinka kawai nakesonyi” lumshe idonsa kawai yayi bece mata komaiba. suhailat taita masa magana amma kememe yaki cemata ko “kala” harda kukanta amma yayi biris abunsa karshema kashe wayar yayi dan kar Aunty ta karba ta masa faɗa akan kin kula suhailat ɗin da yayi. kallon Maryam yayi ta kasan ido, ta haɗe rai sosai an tsuke bakinnan. tabe bakinsa yayi ya tada motarsa suka wuce….yauma damuka tashi shiyazo ya ɗaukeni, Ni mamakinshi nake yanda yake barin kasuwa yadawo ya dakkoni sannan ya koma. Bayan ansha ruwa kafin sallar isha’i, su Maryam suna zaune a falon ammi dukansu suna hira. Ammi ta dubemu nida umaimah tace, “ɗiyata ku tashi kuje gurin Musa tailer, seki zabi ɗinkin da kikeso ya miki ya kuma gwadaki” a hankali nace “to ammi, da nisane gurin?” Aunty zuhurace tace, “da ɗan nisa kadan gaskiya” umaimah kuwa kallon su kawai take tana tabe baki, dan zuhuranma ba wani shiri suke da itaba. Ammi ta dubeta tace, “Autatah ki tashi kuje tare, bari nakira NOOR yakaiku idan babu abunda yake idan kuma yana wani uzurin sena kaiku da kaina.” Da umaimah harzatace kanta na ciwo bazata raka maryamba, amma jin ance mustapha ne ze kaisu seta fasa. Ammi ta dakko waya takirasa ta sanar masa, yace mata su jirasa gashinan zuwa. ammi na sanar musu Umaimah ta tashi da sauri ta shige daki, turare ta bulbula har yayi yawa. Tana fitowa Aunty zuhura tace, “kai umaimah wannan turaren dakika saka yayi yawa har yana hawa kai fa” murguda baki tayi ta zauna batace komaiba. Ammi ce tace, “gaskiya autah yayi yawa” cikin sangarta tace, “ammi feshi biyu nayifa haka turaren yake” ammi zata kuma Magana wayarta tayi ƙara, dagawa tayi mustapha yace mata yana jiransu a mota. Bayan ta kashe wayar ta dubemu tace, “ku tashi kuje kunsan bayason jira” Zuhura na dariya tace, “ai da gimbiyarsa dole yajirasu” murmushi nayi kawai, na musu sallama muka tafi.

A gajiye nake tafiya yau nagaji sosai kuma azumin yaɗan kolani. ina gaba tana bina a bayana danna rigata fitowa daga falon. yana zaune acikin motar ya buɗe murfin ƙafarsa ɗaya na waje yana latsa wayarsa. zagayawa nayi na buɗe front seat na shiga da sallama ɗauke abakina. batare ɗaya dagoba ya amsamun acan ƙasan makoshi. Yana ganin umaimah tataho ya maido ƙafarsa ya rufe Kofar, kunna motar yayi, ya kuma kunna light din motar. kallon fuskar Maryam yayi yaga itama shi take kallo karaf suka haɗa ido. Hararata yayi nayi sauri na ɗauke idona daga kansa ina kebe fuska. umaimah ta buɗe bayan motar ta shiga sannan tace, “yaya NOOR ina wuni, dafatan kasha ruwa lafiya” “lafiya” yabata amsa atakaice yana tada motar. reverse yayi megadi ya buɗe mana get muka fice daga gidan. umaimah na masa hanya har muka karasa. A kofar wani shago mukayi parking, umaimah ta fito ta dubi Maryam daketa lumshe ido bacci fal cikinsu tace, “ki fito” mustapha na kallon Maryam yace, “ina zata?” Umaimah tace, “ciki zamu shiga ze aunatane ta kuma zaɓi ɗinkin datakeso” fuskarsa a tsuke yace, “bazata ta shiga cikin wannan mazanba” galala umaimah tayi tana kallonsa baƙin ciki fal ranta yanda mustapha yake nuna kishin Maryam akan komai. Maryam kam sama_sama take jinsu amma bata fahimtar mesuke cewa bacci yafara fuzgarta. umaimah batace masa komaiba ta juya ta nufi cikin shagon, bayan kamar 10 minutes suka fito tare da toilor ɗin. gaishe da mustapha yayi, Maryam kuma data wartsake dakyar ta gaisheshi. Ya dubeni yace, “Hajiya wanne irin ɗinki za’a miki?” Nace masa “style me kyau kawai” yace, “doguwar riga ko riga da skirt koda zani?” “Kamata doguwar riga” mustapha dake latsa wayarsa tamkar baya saurarensu ya fadi hakan. na kallesa kawai bance komaiba. Toilor’n yace, “angama ranka ya dade” umaimah ma ta faɗa masa irin ɗinkin takeso. Toilor’n yace to nafito ya gwadani, amma Mustapha ya hana. Toilor’n yace masa, to umaimah seta gwadani amma kememe bawan Allah nan yahana waishi baza’a gwada masa mata a titiba. Dariya kawai toilor’n yayi yacemun muje to zezo har gida ya karbi measurement ɗina. muna cikin tafiya a mota naji mutum ya janyoni jikinsa. lumshe idona nayi ina sauke ajiyar zuciya. daidai kunnena yakai bakinsa cikin wata sanyin murya yacemun “kin sakarmun nauyi fa” aiko kamar ya tunzurani nakara manne masa a jiki. umaimah dake baya ta hadiye wani yawu me daci a ranta tana faɗin. “Tsabar jaraba yana tukinma amma seya wani rungumeta, gashi se wani rada_rada yake mata, kamar sun manta da ni a motar” mtss taja siririn tsaki tana hararar bayan Maryam. Mustapha sarai yaji tsakin da umaimah tayi kawai sharewa yayi. kafin suje gida Maryam tayi bacci ajikinsa. yanayin parking umaimah ta buɗe kofa ta fice. Kallon Maryam yayi yaga baccinta take hankali kwance, se numfashi take saukewa a hankali. Kurawa fuskarta ido yayi a karo na biyu a rayuwarsa bekuma san dalilin kallonnata dayakeba. tabe bakinsa yayi bayan yagama ƙare mata kallon, a hankali yafara ƙoƙarin rabata da jikinsa. Maryam kuma ta ƙara kankameshi. Lumshe idonsa yayi ya ƙara rabata da jikinnasa. Maryam ta buɗe idonta a hankali tana jingina jikinta da kujera, buɗe murfin motar yayi ya fice abinsa, bekara koda kallon inda nakeba . da kyar nima na daure na fito, wani irin bacci nakeji. Kulle motarsa yayi yanufi masallaci dan har anyi isha’i anfara asham. Ban koma part din ammi ba, na koma namu……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button