Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani tunanine yazomun cikin zuciyata.dasauri na tashi nanufi gidan su umman saleemat,dake jikin gidanmu. Umma! Umma! Nashiga kwala mata kira. “Na’am maryam wannan kiran hakafa,lafiya? “Umma innace bata da lafiya,tana kwance jikinta se rawa yakeyi. “subhanallah, shiyasa yau banji hayaniyar masu siyayyar abinciba,muje inga jikinnata.bari in dakko hijabina……..✍️

sannu bata hana zuwa,sedai adade ba'ajeba.kada kudamu da sannu zamuzo inda kukeso.????????

By
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

0️⃣7️⃣

…………..Muna shiga dakin nida umma,mukatarar inna har lokacin jikinta se rawa yakeyi.dasauri umma ta karasa kanta dagota tayi taji jikinnata yayi zafi sosai,”maryam debomun ruwa abaho,kitaho da towel. “To umma” har lokacin kuka kawai nakeyi.da sauri na debo ruwan nakawo mata.harta fara cirewa inna rigarta,kara umartata tayi naje nakirawo wani isa me chemist dake bakin layinmu.

Cikin yan mintuna muka iso gidan nida Dr isah,a lokacin har umma ta gama gasawa inna jikinta.dubata yayi ya mata allura tare da sanya mata Karin ruwa.se alokacin nasaki wata ajiyar zuciya.saboda ganin jikin innata ya dena rawa,numfashinta yana fita dai_dai alamun ta samu bacci.magunguna ya rubuta ya bani yace kafin tatashi naje na siyo,kuma atabbatar tasha koda ruwan tea ne idan ta tashi.ranar ninayi duka aikin gida.saboda inna babu abun data iyayi.abinci kuma ummace ta kawo mana.washegari, jikin inna tatashi dashi da sauki.amma bata warke duka ba. Inna tayi_tayi inje school,amma nace mata nibazanjeba.seta kara samun sauki.haka ta hakura ta kyaleni.bayan nagama share_share da wanke_wanke.muna zaune adaki da inna,ta dubeni tace.

“Maryam,ina horanki daki kasance me juriya,akan duk halin dakika tsinci kanki aciki.komai runtsi komai wahala kada ki zubar da mutuncinki,domin mutuncinki shine kadararki.koda na mutu,kada ki koma kauye wajen ‘yan uwana,kici gaba da zama anan saboda kisamu ingantaccen ilimi,saboda iliminkine kadai ze taimakeki a rayuwarki.nasiha sosai inna tamun me ratsa zuciya me kama da wasiyya.rungumeta nayi ina kuka nace.”inna kidena fadar haka bazaki mutuba,insha Allah harse kinga yayana,kinci gajiyar ilimin da kika dorani akai.lallashina kawai inna tafarayi.itama tana zubar da hawaye.

Bayan kwana 2 inna ta warke rass,tamkar ba itaba.hakan yasa na koma makarantata.naci gaba da karatuna.sekuma wata sabuwa,bayan befi wata biyuba inna ta fara wani irin ciwo,cuta me tsanani.ko hannunta bata iya dagawa.sedai akwantar atayar.gashi babu me jinyarta ni kuma alokacin nayi kankanta.ummace take dawainiya damu da sauran makotan arziki.’yan uwan innata na kauye sunzo amma basu wani jimaba,suka koma.ciwofa yakici yaki cinyewa.babansu saleemat ne yakai inna asibiti.aiko ana zuwa suka bata gado.babu me jinyar inna,umma kuma ga ‘yayanta ga aikin gida,baze yiyu tazo asibiti jinyaba.hakan yasa akace dole wani Dan uwan inna seyazo jinyarta. Dakyar wani kanin babansu inna,yasamu gwaggo a yawon gagarinta.da farkoma datazo cewa tayi baza ta iya jinyaba,amma kuma kome tatuna Daga baya kuma seta amince.nidai banda insaka inna agaba ina kuka babu abunda nakeyi.makarantama dakyar umma ta lallabani na koma.inna tayi watanni a asibiti,a canza mata wannan a maidata wannan.gaba daya dan kudin data mallaka duk ya kare a yawon asibiti.amma cuta dai tananan a jikinta.ahaka har na shiga J.S.S 2,nida saleemat.bayan dogon lokaci da inna ta dauka tana jinya.cikin ikon Allah se sauki yafara samuwa har aka sallamota muka dawo gida.murna a gurina kamar me innata ta warke. A lokacin gwaggo ta nuna tanason tafiya amma inna ta hanata.taitai mata fada akan rayuwar datakeyi da girmanta bane dorewa bace.gwaggo tayi aure_aure,amma bata taba haihuwaba.kuma duk auran datayi bata jimawa take fitowa,saboda masifarta da rashin mutuncinta ba kowa ze iya zama da itaba.gashi taita Tarawa mutum kawayenta ‘yan duniya a gida.ta yarda ta zauna damu da kyar,duk da badadin zama mukeji da itaba. amma,kullum.seta fice yawonta.inna sedai kawai ta bita da addu’ar shiriya.

Watarana,danar dabazan taba mantawa da itaba arayuwata, na dawo daga school da murnata,saboda a makaranta anzabemu nida saleemat acikin wadanda zasuyi J.S.S.C.E EXAM. Saboda kokarinmu.base munyi j ss3,ba kawai zamu tafi senior class.kamar kodayaushe idannadawo daga makaranta gwaggo batanan,yauma haka,dakinmu na nufa,inna tana kan sallaya azaune tana lazimi.
“Innata! Innata! na shiga kwada mata kira tare da fadawa jikinta. “Oh ni,fateemah maryam koyaushe zaki girma.dariya nayi nace “kai inna na girma mana,amma agurinkine bana girma,tunda ni kadaice bani da kani.murmushi inna tayi ta shafa kaina tace. ” idan baki da kani maryam,ai wataran uwa zaki zama,dan ko yanzu akai miki aure zama zakiyi. Rufe fuskata nayi da hannuna,cikin jin kunya. “Kai inna aure kuma,nidai ban girmaba.sonake nayi karatu me zurfi,na zama likita idan baki da lafiya base munje asibitiba,nizan baki magani da kaina,in miki allura. Murmushi inna ta karayi tace.”Allah yasa maryam dita,Allah ya cika miki burinki,nima burina naga kinyi karatunnan maryam. ” Ameen innata,yawwa inna,nazo miki da wani daddadan albishir. A makaranta yau aka kawo mana form din makarantar science ta kano,shine aka zabemu hardani da saleemat,nanda watanni kadan zamu zana. “Wacce makarantar science din kuma maryam?. “makarantar da usainan bayan gida tayi me fararen uniform da ratsin Kore. ” to aike,maryam naga yanzu aji biyu kike,shine kuma za’akaiki babbar sakandire,ai bakiyi aji uku ba. “Principal din makarantarmuce,ta kirawo mu harda ‘yan aji 3,shine aka mana wata ‘yar jarabawa kuma naci,makina haryafi na ‘yan aji ukun. “Toh shikenan maryam,Allah yabada sa’a ya taimaka. “Ameen inna,nafadi hakan ina mikewa zuciyata cike da murna.na fara cire uniform dina.wani kallo naga inna tana bina dashi Wanda nakasa gane kona mene. ” inna lafiya naga kinamun wannan kallon. “Babu komai maryam.mikewa tayi taci gaba da jero nafilfilolinta.lafiya kalau muka wuni da inna,munata hirarmu cikin nishadi. Amma anayin magriba,tacemun kanta yana mata ciwo.ta kwanta,dakyar ta samu tayi sallar isha’i. Ta kara kwanciya.

Cikin dare naji inna tana wani irin nishi,sama_sama nakeji cikin baccina,tun tanayi a hankali harnaji ya hanani bacci.tashi nayi na lalubi makunnin kwan dakin na kunna.

Inna nagani,hannunta dafe da kirjinta,numfashinta na fita dakyar.”inna meyafaru,meyasameki.innalillahi…….kanta kawai take girgizamun tanamun nuni da hannunta,tana kokarin yimun magana amma ta kasa.dakyar nagane ruwa take bukata.da sauri na fita na dakko mata me sanyi na kawo mata. Seda tashanye Tass,natambayeta na karo mata tacemun A’a.

Gyara mata kwanciyarta nayi,saboda ganin numfashinta ya fara daidaita.ina jera mata sannu.hannunna ta kama cikin muryar marasa lafiya tafaramun magana.”maryam! Kidauki duk kaddarar datazo miki arayuwa,kada ki butulcewa Allah.jikina yana bani bazan kara wasu kwanaki masu yawaba.ki riki gaskiya aduk inda kike,sannan kuma jigon zaman duniya,hakuri. Kiduba kasan gadona,akwai wata akwatin karfe.cikin wata jaka,zakiga wata takarda da wasu hotuna.hotunan mahaifinkine Dana mahaifiyarki,takardar kuma mahaifiyar kice ta rubuta tace abaki.kirjina yanamun ciwo sosai maryam,tamkar andoramun dutse haka nake jinsa inaji ajikina ajalin……da sauri na rufewa inna bakinta ina sakin kuka,”inna kidena cewa haka,bazaki mutu yanzu ba insha Allah,kinyi cutama datafi wannan kuma gashi kin warke,wannanma insha Allah nasan zaki warke. Inna ta bude baki zatamun magana wani tarine ya sarketa,ta fara yinsa ba kakkautawa.tamkar numfashinta ze fita.da gudu na fice daga dakin na nufi dakin da gwaggo take kwana,na fara bubbuga mata kofa da karfi. Dakyar gwaggo ta tashi,cikin masifa take tambayata menene.cikin kuka na mata bayani tataimakeni mukai inna asibiti.amma gwaggo seta rufeni da masifa tana zagina,rokonta nakamayi amma Sam gwaggo taki yarda tace bacci takeji da safe, akaita asibitin babu abunda zefitar da ita cikin darennan.jikina a sanyaye na koma dakinmu.shiru na tarar da inna idonta,a rufe.abunka da yarinta,sena sauke ajiyar zuciya ina cewa,tama samu bacci ya dauketa. Bargo na lulluba mata,nima na kwanta,amma Sam nakasa bacci juyi kawai nakeyi.har asuba. Amma abun mamaki senaga inna bata tashi sallahba,kyaleta nayi saboda naga bata da lafiya.har gari yafara haske inna bata tashiba.kuma abunda yaban mamaki yanda ta kwanta haka take ko juyi batayiba. Tashinta na farayi ina bubbuga jikinta,amma shiru inna ko motsi.hannunta na daga naji yakara nauyi,ina sakinshi naji ya koma sharaf.wata irin bugawa zuciyata tayi,wani gumi yafara tsatstsafomun.kiran sunanta na farayi da karfi ina jijjigata da dukkan karfina,amma shiru.ihu na kurma,na nufin dakin gwaggo ina bugawa inacemata tazo inna ta suma,mukaita asibiti.amma gwaggo tana fitowa ta tsinkamun mari, wai tun cikin dare na hanata bacci.idan ban tafi na bata guriba seta babballani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button