Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Se wajen magriba nabar gidansu salimat,bayan nabata kayan dana kawo mata taitamun godiya kuwa ita da umma, har gidan gwaggo salimat ta rakani,bayan umma ta karamun nasiha akan na tsare mutuncina. Koda na koma gida, gwaggo batanan ta fita, dama nayi mamakin yanda akayi har nayi wannan dadewar gwaggo bataje ta kiraniba, ashe batananne,amma da alamun ba nisa tayiba dannaga janyo kofar gidan kawai tayi bata rufe da kwadoba. Hajiya gwaggo anatafi kai kudi gidan adashi. Nanma seda muka kara wata sabuwar hirar sannan tatafi. se ana sallar magriba gwaggo ta dawo, time din data shigoma ni sallah nakeyi. “Sannu da zuwa gwaggo” nafada bayan na idar da sallah. “Uhm, aikece za’aiwa sannu kinje gidan uwartaki kinyi zamanki tana doraki akan hudubar banza ko” zanyi magana gwaggo ta hanani. “Rufemun baki ni, bansan jin komai daga gareki, gobe inkika zo base nakara barinki zuwaba, sannan abu nagaba danakeson fada miki, karki kara zuwamun batare da kudi masu yawa ko kayan masarufiba” “to ni inna ina zansamu kudi balle harna siyo miki wani abu, kudin aikatau dinma ko ganinsa banba, kawaidai matar gidan tacemun tabada ankawo miki lokacin danayi wata guda agidan” cikin fada gwaggo tace, “kajimun sakarar yarinya se’anbaki zaki kawomun, fakar idonta zakiyi ki dakko, kayanma kidinga sata da kadan_kadan kina boyewa idan yataru seki sato hanya kikawomun” dasauri na kalli gwaggo cikin matukar mamakinta ina maimaita Kalmar Hasbunallahuwani’imalwakil araina, narasa hali nasan abun duniya irin na gwaggo,yanzu ita danake kallo amatsayin uwa ita take umartata danayi sata. Cikin takaici nace, “gwaggo satafa kikace, idan wataran aka kamanifa,koba hakabama gaskiya bazan iya sataba, sedai na dinga tara miki kudin makarantata” “to yar bakin ciki, me shegen bakin hali, kar Allah yasa ki iya din” bala’i gwaggo tashigamun tana zagida da tsinemun, nidai shiru na mata bakin ciki cunkushe azuciyata, har hawayen bakin ciki seda nayi. Sallamar wani yaroce tasa nasamu salamar bala’innata. Yaya sadiq ne yazo zamu wuce gida, kafin nayi wani yunkuri gwaggo harta fice gurinsa. Jakata nadauka nafito nima. Gwaggo nata masa banbadancinta a son zuciya irinnata yakara bata kudi, sadiq ganin maryam tafito yayiwa gwaggo sallama ya nufi mota. Tsayawa nayi inayiwa gwaggo sallama, akokarina nasan takoma gida, dan idan tana tsaye agurin bazata barni nakoma nayiwa su umma sallamaba, kuma nasan baba yadawo yanzu inason shima nagaisheshi. Gwaggo kuwa tasan nufin maryam shiyasa taki komawa gida, wai ita kar sadiq yace zegaida umma balle yabata wani abun. Seda taga nashiga mota haryakunnan munfara tafiya sannan ta koma ciki,tana cewa sadiq setazo gidan. Nikuma ina ganin haka nace masa nayi mantuwa banwa umma sallamaba, kashe motar yayi yace muje shima seya gaidata. Abakin kofar gidan ya tsaya nikuma nashiga, gaisawa mukayi da baba nayiwa umma da salimat sallama nakuma sanar mata da sakon sadiq, hijabi umma tasaka ta leko soro suka gaisa cikin girmamawa, godiya sosai umma ta masa akan dawainiyar dayakeyi akan maryam. Kudi sadiq yadakko yabawa umma, amma umma Sam taki karba karshema tashi tayi ta koma ciki. Saleemat data rakoni yabawa kudin, itama kin karba tayi, dakyardai ta karba ahakanma seda nasaka baki, sallama mukayi cike da kewa da begen juna muka rabu.

Muna cikin tafiyane, yaya sadiq yadubeni yace, “wato zuwa kikayi kinata yayatani na miki abu ko?” Murmushi nayi nace, “a’a yaya kawaifa cemata nayi kamaidani makaranta,shine ta maka godiya” “Shikenan” yace atakaice.dubansa nayi dakyau nace, “yaya sadiq naga kamar wani abu nadamunka tundazu dazamu tafi, da’alamunma bakaje bikinba?” Numfashi sadiq yasauke yace, “banajin dadi ne maryam kuma gobe zanyi tafiya, daddy ya aikeni Abuja.” “ayya yayana sannu mekedamunka” nafadi haka cikin tausayawa. “cutar sonki” yafadi hakan aransa,amma a fili seyace, “ciwon Kaine da kuma gajiya” “sannu, Allah yakara sauki, kuma ahaka zakayi tafiyar,kadaga mana zuwa wani lolacin” girgiza kai yayi alamar a’a yace, “baze yiyuba abunda zanyi yana da mahimmanci.” “Tom shikenan yaya, Allah yakiyaye hanya yakuma kara sauki” “ameen” yafada cikin sanyin murna. Shiru sukayi na wasu mintuna kowa da tunanin dayakeyi aransa, ni ina tunanin halin dazan shiga idan baya gidan, domin shine garkuwata,acikin gidan. Shikuma sadiq yana tunanin tayanda zefadawa maryam yana sonta. Candai na katse shirunnamu dacewa, “kuma kwana nawa zakayi a abujan?” “Zakiyi kewatane idannatafi” sadiq yatambayeta yana kallonta. Batare da tunanin komaiba, nace, “sosaima yaya” wani murmushi yayi yace, “kozaki binine mu tafi tare” “ai mommy bazata bariba” “Injiwa zata bari mana” “tom shikenan zanbika” nafadi haka ina murmushi. Daidai nan muka karaso gida. Seda yayi parking sannan yadubeni yace, “tun yamma aliya take kirana nabaki waya zaku gaisa, kishiga ciki kihuta kiyi sallah kici abinci, zanzo muyi magana,sekuma nakira miki aliyan” “tom yaya nagode sosai, se’anjiman” nafadi haka ina bude motar na fice. Dai dai lokacin da maryam tafito haidar yakaraso parking space din, zedau mota ze fita. Tsayawa yayi yana kallon maryam cike da mamaki, shida farkoma beganetaba sedaga baya,takara masa kyau. “dama haka yarinyarnan take da kyawun sura, shiyasa kullum cikin zunbula hijabi take, gatadai yar karama amma akwai kayan aiki, lalle zeso ya more wannan kyakkyawan jikinnata” yafadi haka aransa yana lasar lips dinsa……….✍️

BY
zeey kumurya

ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

2️⃣4️⃣

………Tunda nafito daga motar na hango haidar,sanin danayi bawani shiri mukeba sena dauke kaina ina kokarin wucewa batare dana masa maganaba, kamar daga sama naji muryarsa cikin tattausan lafazi yana cewa. “Yanmata babu magana” cak na tsaya cike da mamakinsa da wanine yacemun koda a mafarki haidar zemun magana irin haka zan karyatashi domin tsakanina dashi magana cikin tsawa da masiface take hadamu. Murmushi na kirkiro nace, “ayya yahaidar bangankaba ina wuni” “lafiya kalau” ya amsa yana bina da wani shu’umin kallo, nidai daga haka bankara maganaba nayi gaba danse naji abun wani banbarakwai. Shiko haidar binta yayi da kallo yana ayyana mummunan kudirinsa akanta harta kulewa ganinsa. Ahankali nake tafiya ina zancen zuci harna karasa part dinmu, su mommy basu dawoba, me’aikin danake gani kullum tana zaune a falo tana kallo, gaisawa mukayi na wuce sama. Jakata na ajiye a daki nashiga kitchen nadibo abinci domin wata yunwa nakeji, a falo na zauna naci bayan na kunna kallo. Inagama cin abincin na shige daki, domin yin sallar isha’i. Bansan sanda su mommy suka dawoba, seda nagama duk abunda zanyi adaki na fito falo naga mommy ta fito daga kitchen. “Sannu da dawowa mommy” “yawwa maryam yakika baro mutan gidan” “lafiya kalu sunata agaisheku” “toh muna amsawa, yawwa maryam shiga kitchen zakiga nahada wa alh, abinci bari na dakko mayafi kibini part dinshi, dashi” cikin ladabi na amsa mata sannan na shige kitchen din na dakko, seda nadan jira sannan mommy tafito muka tafi. Daddy yana zaune a falonsa na tsakiya,yana karatun jarida yana kurbar ruwan shayi muka shigo falon. Wani sassanyan kamshine yadaki hancina, seyau nasamu damar bawa idona abinci a part din daddy. Gaskiya part din yahadu iya haduwa, danhar yafi na mommy kyau, amma nakasa gane wanne yafi kyau shida na mustapha, kawaidai abunda nagane yafi na mustapha girma. Masha Allah gaskiya kudi yana inda yake, komai najin dadin rayuwa akwai a part din daddy, duk da iya faluka biyu nagani a part din. Har kan hadadden dinning dinsa naje na’ajiye abincin, sannan na dawo gabansa na durkusa na gaishe sa. Amsamun yayi kamar kodayaushe cikin fara’arsa. Mikewa nayi namusu sallama nafice. Ina fita na hango yaya mustapha yana tahowa,ya kara waya a kunnensa,alamun waya yakeyi. Nandanan zuciyata tahau aikinta a duk lokacin data gansa, wata boyayyiyar ajiyar zuciya nasauke ina satar kallonsa ta gefen ido. Yayi kyau sosai yau shigar manyan kaya yayi, kansa harda hula. fitinanne kamshinsa yacikamun hanci,tun kafin yakaraso. Cikin takunsa nakasaita da daukar hankali yake tafiya. Wata nutsuwace naji ta lullubeni, dana gansa se ajiyar zuciya nake saukewa akai akai. Ahankali nake tafiya har mukayi clash, dakyar na harhado kalmomi abakina nace, “ina yini” ina dan rissinawa batare daya kalleniba yadagamun hannu ya wuce abinsa, yabarni da mayen kamshinsa. Lumshe idona nayi wani murmushin daban shirya masaba ya subcemun. Yanayin dana tsinci kaina na farin ciki baze misaltuba a wannan lokacin. Tunaninsa manne acikin zuciyata nakoma part dinmu, a falo na tarar da yaya sadiq yana kallon news shikadai azaune.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button