Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Dana dawo daga school yau senaga aunty suhailat bata dawoba, kuma yanzu da wuri take dawowa bata kaiwa yammannan kamar da, abun mamaki harnayi aikina nagama suhailat bata dawoba, nikuma gani nikadai a part gashi duhu yafarayi tsoroma nakeji, haka nazauna nikadai tsuru a falo, se kunna kallo nayi danya debemun kewa. Suhailat tasha bacci sosai se dafda magriba ta farka, mamakin dadewar datayi tana bacci tayi. Dasauri ta mike tashiga toilet jikinta duk ya mata tsami se zugi datakeji kadan_kadan akasanta, wanka takarayi tare da gasa jikinta tafito tashirya ta dauki jakarta tafito falo inda kamal yake. cikin yaudararsa yatareta,ya kama tarairayarta yana lallabata,itadai kawai cemasa tayi yakaita gida,cikin tsananin farin ciki kamal yadauketa cak a hannu har bakin mota yakaita yadireta,sannan ya bude mata motar tashiga shima yazagaya yashiga driver seat yajasu zuwa gida. shiru suhailat tayi a motar ko uffan bataceba,duk kuwa da kokarin janta hira da kamal yakeyi, wani iri takejinta kamar ba itaba, duniyar gabadaya ta sauya mata,gashi tasan su mommy sunata nemanta basu sameta a wayaba danta kashe wayar gabadaya. har cikin gida kamal yakai suhailat ya’ajeta,yayi kokarin kara rarrashinta amma tafito dasauri tashige gida. Ina zaune a falo nikadai tsuru naga taga shigo tamkar ancillota ko sallama babu, gabanane yayanke yafadi ganin yanayinta kamar Mara lafiya duktayi wani iri, senayi tunanin ko wani abune yasamu yaya mustapha. Kasa hakuri nayi nace mata, “aunty suhailat lafiya kuwa naga yau kindade baki dawoba ko baki da lafiyane?” Cak suhailat ta tsaya daga kokarin shiga dakin datakeyi, juyowa tayi ta gallawa maryam harara tayi wucewarta,daki. bandamu da abunda tamunba,hasalima ni wani matsanancin tausayintane naji yakamani,batare danasan daliliba,cigaba nayi da kallona har akayi sallar isha’i sannan na tashi nakoma dakina. Suhailat kuwa tana shiga daki ta zube akan gado tana maida numfashi, wayarta ta zaro acikin Jakarta ta kunnata,bayan ta kunnu ta kunna data tahau online. tana hawa taga mommy online dasauri ta danna mata voice call,danbataso takirata video call taga halin datake ciki. Mommy tana kwance a masaukinsu tana hutawa tana chatting dinta,bama ta asibin a wannan lokacin, kiran suhailat yashigo wayar ta, dasauri ta daga dama tanata nemanta tundazu bata shigaba. “Hello mom’nah” “na’am, daughter ina kika boyene yau tun dazu nake nemanki a waya bansamekiba” cikin son boye damuwarta tace, “mom yau bandawo da wuriba kuma dana dawo bacci yadaukeni seyanzu natashi nayi wanka na kunna wayar” “ayya,daughter sannu,inafatandai bakyashan wahala a school din” “um,banasha mom, kewarkuce dai kawai tadameni data yayana” murmushi mommy tayi tace, “muma munyi kewarki sosai,kodayaushe daddy cikin zancenki yake.” “Yawwa mom,kirokarmunshima dan Allah inason zuwa a week dinnan.” “kibari next weekend su haidar zasuzo sekibiyosu kuzo tare” wani irin dadine ya lullube suhailat zataje taga life dinta nankusa, hira sukacigaba dayi da mommy tanata tambayarta abubuwan gida dayanda abubuwa suke tafiya,kafin daga bisani sukayi sallama. kwanciya suhailat tayi bayan sungama waya da mom tana tunani akan abunda yafaru da ita yau ita da kamal, tana ganin yanata kiranta amma taki dagawa, ko abinci bata nemaba balle tayi tunanin yin sallah tacigaba da kwanciyarta…………..

Kwanci tashi babu wuya agurin Allah, yausu mustapha sunfi wata daya a India,amma dai jikinnasa gashinan gashinanne,har wanna lokacin besan wake kansaba bashi da aiki se bacci kuma komai sedai a masa,sedai a kwantar a tayar gashi memakon yarame sewata irin kumbura yakeyi. Yaya sadiq yazo gida sau biyu, daddyma yazazzo gida su suhailatma sunje can Indian saudaya sunduba jikinnasa. Aunty tazo kano itama taga yanda muke nida suhailat, mommy ce dai bata taba zuwa tunda suka tafi. Suhailat daa abunda yafaru tsakaninta da kamal yadameta, amma daga baya kuwa seta ware tamaida komai bakomaiba,kuma sukacigaba da mu’amalarsu da kamal. Munyi hutu a school na jaranawar second term da mukayi, yanzu saurana term daya nayi candy, a islamiyyaba munsauke alkur’ani amma a biye, bikin sauka kawai yarage mana shima ankusa samana rana. Acan India kuwa daddy ganin jikin mustapha yakiyin yanda akeso yace gaskiya gida za’adawo amma mommy taki yarda, seda aunty taje taga jikindai basauki sannan ta matsawa daddy dole badon mommy tasoba ta bari adawo gidan. yau talata yaune kuma su mommy zasu dawo, farin cikin danake ciki baze misaltuba yau zanga heartbeat tun safe muka gyare masa a part dinsa saboda acan zeyi jinyartasa. Aunty ma tazo kanon amma banda aliya. wani malami a Zaria,daya shahara a karya sihiri da cire jinnu daga jikin mutum,da maganin mayu dadai sauran lalurori, aunty tayi tattaki dakanta harzuwa kauyen dayake ta masa bayani akan ciwon mustapha, domin taji ana fadar kyan maganinsa sosai. dafarko cewa yayi akawo masa mustaphan har inda yake, sekuma aunty ta rokesa akan idan babu damuwa sutafi kano tare dashi, saboda yanayin da mustapha yake ciki, idan akace za’azo dashi garin wahala kawai za’asha saboda kauyen dayake basuda titi me kyau hanyoyin duk a rube suke. beyi wata doguwar gardama ya amince yabiyo aunty kano, amma da sharadin baze kwanaba aranar zejuyo gida saboda masu zuwa karbar magani, aunty tace babu komai ahakanma sungode.

Karfe biyu na yamma a naija taiwa su mommy, haidar ne yaje ya dakkosu a airport zuwa gida. ina zaune ina karatun alkur’ani aunty tashigo dakin danake da sallama,amsa mata nayi bayan na kai aya narufe alkur’anin. “Maryam karatu akene” murmushi nayi nace “eh aunty” “masha Allah, yagajiyar aikin da kukasha” “babu gajiya aunty” gyara zama aunty tayi tace, “dama zuwa nayi nace miki,kije part din baki kitahoda malaminnan damuka zo tare,kirakashi part din Muhammad,nizan karasa kisameni acan” amsa mata nayi ta mike tafice, nima ajiye kur’anin nayi a ma’ajiyarsa nafito, na nufi part din bakin. Malamine me cike da kamala da nutsuwa,yanata lazimunsa naje nasameta. gaishesa nayi cikin mutuntuwa, sannan na isar masa da sakon aunty. biyoni yayi a bayana har zuwa part din heartbeat gabana sefaduwa yakeyi, ga farincikin zanganshi gakuma fargabar halin dazanje in riskeshi aciki. A falon sama na tarar da mommy, da aunty da daddy harda yaya mustapha. kallon mommy nakeyi kamar yadda itama take kallona irin kallon data sabamun, nikuma ina mata kallon mamakin yanda naganta,tamkar bame cinyaba, babu wata alamar damuwa a tattare da ita,amma fa aganina. cikin fara’a nakarasa gareta ina gaisheta dan itace acikinsu nadade bangantaba,amsamun tayi itama da fara’ar dauke a fuskarta takara da fadin, “maryama, ya gidan ya karatu?” “Alhamdulillah mommy, yame jiki” “jiki sai godiyar Allah” “Allah, yakara sauki yasa kaffarace” “ameen, duka dakin suka hada baki gurin amsawa” gaishe da daddy nayi dasuke magana da malam,shima ya amsamun da fara’arsa. Daddy nema kanaganinsa kasan yana cikin damuwa,dan har yar rama yayi. inason na tambaya ina mara lafiyar amma na kasa, haka na mike nafice nabasu guri. jagora daddy da yaya sadiq suka yiwa malam har dakin mustapha inda yake a kwance akan gado yana bacci. itadai mommy ba’ason rantaba aka dauko malaminnanba shiyasama bata wani bashi mahimmanciba. sadiq ne yakara yiwa malam bayanin abunda yake damun mustapha dalla_dalla, duddubashi malam yayi da baiwar da Allah yabasa. Shikansa malam yayi mamakin ciwon mustapha amma ko tantama bayayi aikin sihirine ko jinnu a ciwon mustapha. jakar magungunansa ya dakko yabawa daddy wani kullin magani, na karya sihiri. Za’a kwabashi da man habbatussauda se’adinga shafe masa jiki dashi safe da dare, se kuma ruwan jarka dayace abashi yayi tofi aciki shima yace kullum adinga diga masa abaki, atabbatar yana shiga cikinsa,insha Allahu ko wanne irin sihirine ajikinsa seya karye. godiya sosai daddy da aunty suka masa, kudi masu kauri daddy yabashi a matsayin sadaka danyaki fadar abunda za’a bashin. Bayan anyi sallar la’asar daddy yasa driver ya maidashi gida……..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button