Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ranar dana tsinci kaina bana k’aunar ƙara zama a ƙasar nijer, na tattara yan kuɗaɗen hannuna na biyo motar haya zuwa ƙasar Nijeriya, a garin Kano muka sauka, bansan kowa ba, ban kuma san inda zan nufa ba, tunda ban taɓa zuwa garin ba, wata makarantar Allo naje na zauna cikin almajirai, malamin Allon ya kirani yamun tambayoyi akan rayuwata, nace masa ni Maraya ne bani da kowa daga garin nijer nake, malamin ya tausayamun sosai yace in zauna tare dashi a cikin almajiran, haka nacigaba da zama anan a matsayin almajiri, tun ina jin ba daɗin zaman garin harna ware na saba da mutane. Anan nayi shekaru tare da malamin, inayin yan ƙananun sana’oina irin su wankau da aikin gidan masu kuɗi, nasha wahala ba kaɗan ba a zaman danayi a Kano, amma ko kaɗan bana tunanin gida da ƴan gida rayuwata kawai nakeyi. Allah ya haɗani da wani Alhaji mai kuɗi dayake da shaguna a kasuwar kantin kwari, yana zuwa gurin malaminmu sosai yana kawo sadaka ana masa addu’a, Allah ya haɗa jinina dashi yana sona sosai harya ɗaukeni nake masa yaron shago, lokaci ɗaya na fara samun ‘yan kuɗaɗena, sai na bar cikin almajirai na dawo unguwar darmanawa na kama shago haya nake kwana a ciki, anan Allah ya haɗani da Maryam, yarinya mai kyau kirki da ladabi ga kunya, munyi soyayya sosai da Maryam duk da nasan be zama lalli na auretaba tunda ni ba ɗan gari bane, mahaifiyarta taso hana aurenmu Lokacin da Maryam ta fitar dani a matsayin miji amma mahaifinta yace tunda taji ta gani tana so yabani ita, munyi farin ciki sosai da hukuncin da mahaifinta ya yanke akanmu, akayi auranm muka tare anan unguwar ta darmanawa na kama haya, matsala ta farko dana fara fuskanta tunda nazo garin Kano itace ta mahassada a gurin sauran ma’aikatan da muke aiki a ƙarƙashin maigidana, saboda yanda yake fifitani akansu yajani a jiki kamar ɗansa ya aminta dani, komai ni yake ɗorawa akan gaba a harkar kasuwancinsa duk da akwai yaransa da suka fini dad’ewa a gurin, ranar da Alhaji ya yayeni ya buɗe mun shago na karan kaina ranar na bar Nigeria bisa layar zanar da akamun, ban tsinci kaina a ko’inaba sai a ƙasar Sudan, wata irin tsanar garin Kano aka sanyamun araina wanda ko tunawa da ita nayi sai inji wani irin zafi a raina, duk da na baro matata mafi soyuwa a gareni da bani da kamarta a wannan lokacin, gashi tana ɗauke da juna biyun dana kwallafa rai a kansa amma sai naji duk sun fitarmun daga rai, nasha wuya ba kaɗan ba a garin Sudan, wanda idan na tsaya fayyace muku ita zan ɗauki lokaci mai tsawo, Amma dayake Allah mai jinkan bayinsa ne a kodayaushe sai ya haɗani da wani Balarabe ɗan ƙasar Saudiyya, ta sanadiyyar uban gidan wani abokina da suke harkar kasuwanci na haɗu dashi, shima ya haɗamu. Mutumin ya ɗaukeni har ƙasa mai tsarki inda muke zaune a Jidda, ya ɗorani akan harkar kasuwanci, anan nayi arzik’i ba kaɗan ba, da addu’a da taimakon Ubangiji hankalina ya fara karkata ga gida na fara tuna ƴar’uwata da mahaifiyata, watarana na katse komai na shirya na tafi ƙasa ta haihuwa, nayi sa’ar tarar da mahaifiyarmu da rai saidai cikin mummunan hali na ciwo, a sanadiyyar rashina dana yayata. Hakan yasa na ɗaukota na dawo ita garin Saudiyya na mata magani ta warke rass sai damuwar rashin ƴar’uwata kawai dake damunta, kullum cikin addu’ar Allah ya bayyana mana ita muke. Na haɗu da khadija (Ummee) anan Saudiyya dan itama mazauniyar cance ita yan’uwanta sunayin aikatau, amma asalinta haifaffiyar garin Katsina ce, anan Nigeria. A wani aikin hajji da mukaje kamar a mafarki Allah ya haɗamu da Yar’uwata, a ‘yan shekarunnan tunanin Maryam ya yawaita a cikin raina musamman dana fara zuwa Nigeria gidan Yar’uwata, amma da zarar nayi yunƙurin zuwa Kano sai inji wani k’unci ya cikamun zuciya, akwai randa na daure nazo garinnan na shirya babu wanda ya sani na tunk’ari hanyar Kano da nufin naje na dubo matata, jin da nayi kamar ana zaremun numfashi yasa na juyo ba shiri na fasa zuwa, na kwatanta hakan sau da yawa amma azabar da nakeji a jikina yasa na kasa zuwa Kanon har yau danake baku labrinnan.” Abbu ya sauke numfashi yana kallon Maryam da take ta kuka a jikin Ummee tamkar ranta zai fita, ita kanta batasan dalilin kukannata ba, addu’a takeyi a ranta Allah yasa ta farka daga baccin datake yi, dan tasan mafarki take ba gaske bane ta gamu da Mahaifinta, abunda ta daɗe da fitar da rai da ganinshi a rayuwarta, Mustapha ya lumshe idonsa yana jin kukannata har cikin ransa, Ammi da jikinta yayi sanyi ba kaɗan ba ta miƙe ta nufi inda Maryam take, janyota jikinta tayi ta shiga rarrashin ta, da ƙyar ta samu Maryam ɗin tayi shiru, ta rok’eta ta basu tarihin rayuwarta, Maryam tana kuka ta basu labarinta kaf, Mustapha kuwa tuni ya fice dan baze juri sauraren kukannataba, Abbu na kuka ya taso ya rungume Maryam tsam a jikinsa yana faɗin “ashe da rabon zanga jinina na jikin Maryam kafin na mutu, ki yafemun ɗiyata na rashin waiwayarki da banyi ba tsawon rayuwrki har ake miki kallon mara uba da asali, Allah yajikan Maryam ɗita da inna” Maryam tayi luf a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya, amma duk da haka ta kasa yarda ba mafarki takeba wai k’anin ammi shine mahaifinta, mijinta mafi soyuwa a gareta ɗan’uwantane na jini, amminta yar mahaifintace, tanajin abun kamar almara wai yau itace a jikin mahaifinta, Hajja na hawaye itama ta taso ta rungumesu duka a jikinta, ammi ma hawaye take ummi ma haka abun gwanin ban tausayi, su Haneefa sunyi tsuru kawai suna kallon ikon Allah. Bayan angama koke_koken da al’ajabi Ammi ta kira su Mama ta sanar musu da abun farinciki da tsantsar ikon Ubangiji, sunyi mamaki suma sosai, amma ikon Allah yafi gaban komai. Maryam tayi lamo a jikin mahaifinta daya yaƙi yarda tabar jikinsa, kallonta yake kawai cike da tsantsar kaunarta da mamaki, shiyasa tun sanda suka taɓa yin waya da Maryam yaji muryarta zuciyarsa ta d’okantu da son ganinta ashe yarsace ta cikinsa. Yau kam farinciki da yana kisa daya kashe Maryam, harta kira gwaggo da Aunty da saleemat ta sanar musu, gwaggo kusan zaucewa tayi dan mamaki, taji kamar tayi tsuntsunwa tazo taga Ahmad ɗin, danta tabbatar da shi ɗinne. Ammi sosai tayi farinciki da wannan al’amari, shiyasa ashe tun randa ta fara ganin Maryam taji ta shiga ranta sosai, kuma ta daɗe tana mamakin yanda idanun Maryam yake irinnasu ashe itama jininsuce. Har dare Maryam tana cikin danginta anata hira, abincima da ƙyar ammi ta tilasta musu sukaci, ganin dare yayi Ammi tace Maryam ta tashi ta koma part d’insu, ta kwabe fuska sosai tace a anan zata kwana, Hajja tace Ammi ta k’yaleta su kwana tare, babu alamun bacci a idanun su Maryam hirarsu kawai sukesha Hajja na basu labarin yan’uwa, sai can dare Maryam taga message ɗin Mustapha buɗewa tayi sauri ta karanta “I MISSED YOU SO MUCH MY PRINCESS” Maryam tayi murmushi ta tura masa reply da “MISSED YOU TOO YAYANA” yayi murmushi lokacin dayaga reply ɗin, dama yasan yau tare da Abbunta zata kwana, shiyasama bai koma part d’in ba, danyasan indai yaje zatace zata biyoshi, shikuma yau ya mata uzurin ta kasance da mahaifinta a wannan daren, dan yasan yanda suke d’okin ganin juna darenma bazai ishesuba, ya ƙara tura mata wani text ɗin da Ina tayaki murnar haɗuwa da mahaifinki, nayi farin ciki sosai da hakan matata.” na tura masa reply da “Thank you” sannan na kashe wayata, muka cigaba da shan hirarmu. Da safe na koma part d’inmu, gyaran gado na tarar da yaya yana yi, na tsaya a jikin kofa ina kallonsa ina murmushi, sai yanzu dana gansa nasan nayi missing d’insa, ya juyo ya kalleni, waro idonsa waje yayi sosai yace “yaushe kika shigo?” nace “tun ɗazu, har nayi sallama bakajiba” yace “tunaninki nakeyi” na ƙarasa kusa dashi cikin girmamawa nace “Gud Morning” ya rungumeni a jikinsa tare da faɗin “morning princess, how was your night” nace “Alhamdulillah and very very sweet” yayi murmushi tare da jan karan hancina yace “sure?” na gyada masa kai ina kallonshi cike da k’auna nace “I’m sorry na barka jiya kai kaɗai” yace “babu komai ai dear, kuma ko kaɗan ban damu ba ko kuma nayi fushi, farinciki kawai nayi tare da raya daren ta hanyar yin Sallah, dannuna godiyata ga Allah na ganin mahaifinki da kikayi tare kuma da murnar matata ƴar’uwatace ta jini” na lumshe ido ina ƙara kwanciya ajikinshi hawayen farin ciki na taruwa a idona, har yanzu mamaki da al’ajabin abun be barniba, amma idan na tuna ikon Allah ya wuce gaban komai sai nayi godiya ga Allah kawai. Cikin sanyin murna nace I LOVE YOU MY HEARTBEAT k’ura mata ido Mustapha yayi cikin tsananin jin daɗin kalamanta, cikin tsananin shauki yace “repeat it again please” nayi murmushi hawayen idona na zuba aka fuskata nace “I love You so much, I love you more and more, my hero, my husband, my besty, my everything, I love you for today, for tomorrow and for ever” Rungumeta ya ƙara yi a jikinsa sosai kamar zai maidata ciki, so da k’aunarta na ƙara ninkuwa a cikin ransa, kalamanta sun sanyaya masa zuciya ba kaɗan ba, murya ƙasa ƙasa yace “thank you so much, and I love you too” nayi luf a jikinshi ina shaƙar daddaɗan kamshinsa, ya shafa cikina yace “nayi missed baby’nmu” na d’ago da kaina nace “shima yayi missing ɗinka sosai” ya ƙara shafa cikin yana kallon cikin idona yace “dagaske” na daga masa kai tare da lumshe idona dan bazan juri kallon ƙwayar idonsa ba” yasa tattausan tafin hannunsa ya sharemun hawayen fuskata tare da jerumun wasu tsadaddun kalaman soyayya wanda suka sa najini a duniyar sama, saboda shauk’i, daga ƙarshe kuma ya zarce da romancing ɗina……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button