Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani mugun kallo ya wurga mata tare da fadin”get out from my office.murmushi tayi tare da fadin,” aidama bakai kace inzoba,Nina gama nazo da kaina,dan haka bangama kallonka ka bari idannaga zantafi da….”I said get out” cikin tsawa ya fada mata hakan tare da mikewa tsaye yana nuna mata kofa. Idanuwansa har kada sunyi ja saboda bacin rai.jijuyoyin kansa gaba daya sun fito rudu_rudu.tashi tayi tamaida glass dinta tare da daukar Jakarta,tace. “Zantafi mustapha amma kasani,sekayi nadama da danasanin korata da kayi da kuma wulakantani,ni nafi karfin wulakanci, saboda ina sonka,kulkum nazo seka koreni,yauce rana ta karshe dazan kara zuwa office dinka,amma kajira matakin da zan dauka,zakasan kayi da laila,saboda ina sonka mustapha, wulakancin yau daban,na Gobe daban.kusan 2 years ina binka ina rokanka kasoni amma kaki,amma bakomai kajira abunda ze biyo baya.tana gama fadar hakan tafice fuu,tamkar zata tashi sama.ganin yanda ta fito ya bawa sakatariyarsa dariya,kyalkyalewa tayi da dariya,daman tasan karshen zancen kenan,domin bayau laila tasaba zuwaba,yana mata wulakanci.amma kota kanta batabiba tayi tafiyarta,saboda bata ita takeba.

Komawa yayi ya zauna tare da dafe kansa,jingina jikinsa yayi ajikin kujerar,tare da lumshe idonsa.yarinyarnan jarababbiyace,Daga zuwanta tasa masa ciwon kai.wayarsace ta fara ringing cikin amo, me dadin sauti.hartayi ringing ta katse be dagaba.kara kira akayi still beyi picking ba.ankira yakai sau biyar,amma yaki picking.amma anki hakura dadena kiran. Tsaki yaja,ahankali ya bude tsumammun idanuwansa,wayartasa dake gefensa,ya dakko ya duba. love one yagani yana yawo akan screen din wayar,suhailat ce.katse kiran yayi ya tura mata text. I will call you later

Suhailat data shirya cikin wani rantatstsen less dinkin Riga da skirt,ya matukar kamata,tayi kyau sosai.se tashin kamshi takeyi.murmushi tayi bayan taga text dinsa,kokadan bata fushi dashi,duk kuwa wulakancin daze mata,baya damunta. dama ta shiryane ta kirasa taji muryarsa.yau ma kamar jiya,ko mayafi bata daukaba.jaka kawai ta dauka ta nufi dakin mommy.mommy tana zaune akan makeken royal bed dinta, waya takeyi da daddy,suhailat ta shigo dakin. Murmushi mommy tayi tare da fadin “gatananma ta shigo bari na bata wayar.mika mata wayar mommy tayi tace” ga daddy nan zakuyi magana.karba tayi ta cikin shagwaba tace”morning my dad,”morning my daughter. “daddy,yaushe zaka dawone munyi missing dinka dayawa fa. “Inanan dawowa my daughter ayyukane sukai mini yawa.ya karatun dafatan dai ananan anayi ko? ” eh daddy”yawwa daughter kikara dagewa. “Insha Allah daddynah,bye. ” yawwa ‘yar albarka bawa mamanki wayar. Sallama mommy sukayi da daddy bayan ta karbi wayar. “Daughter har kin fito. ” eh mommy na fito, mom nifa nagaji da rashin ‘yar aikinnan,tsofaffinnan bawani Abu suka iyaba,dafa kafadarta mommy tayi tace”jiyama munyi waya da lami tacemun insha Allah yau zata binkito me aiki. “Yadaifi gaskiya mom,bari na karasa school sena dawo. “Adawo lafiaya my daughter,Allah ya kiyaye ya bada sa’a. “Ameen ta amsa tana fita daga dakin…….

Gudu takeyi sosai a mota ranta a matukar bace yake,daidai wani madaidaiçin gida ta tsaya ta fara danna horn ba kakkautawa,da sauri gate man ya taso ya wangale mata gate din gidan. Tura hancin motartata tayi da gudunta,dasauri megadi yayi gefe domin ta kusa bita kansa.parking motar tayi tare da fitowa,ko murfin motar bata rufeba ta nufi cikin gidan.

Suna zaune suna hira suka ganta ta fado dakin tamkar anjefota,jakar hannunta ta cillar tare da fadawa kan gado tana sauke numfashi,dan kwalin kanta ta cire tayi wulli dashi akan gadon.galala kawai suka saki baki suna kallonta. “Laila,lafiya kuwa meyafaru kika shigo mana a hargitse haka,ko wani abun mustapha ya miki. Tashi tayi zaune tana sauke doguwar ajiyar zuciya. Dayar da batayi maganaba ta tabe baki tare da fadin,dama nasan za’ayi haka, seda nace mata kartaje kotajema mustapha wulakantata zeyi,amma ta nace seda taje. “Haba Sakina kada kiga lefin laila,soyayyace taja mata haka.itama ba lefinta bane. Mikewa tsaye laila tayi ta fara zarya adakin, kafin ta dubesu,cikin tsananin bacin rai tace.” Sakina! Habiba!, Yau itace rana ta karshe dazan kara zuwa wajen mustapha,amma wlh wlh wlh zesan ya wulakantani,seya gane ni laila nafi karfin wulakancinsa.sena masa tabo a rayuwarsa Wanda baze taba mantawa daniba,sena illata masa rayuwa.tana gama fadin hakan ta fice Daga dakin. Binbayanta sukayi da kallo dukansu.habiba tace”hmm kamar zata iya,kullum tadinga tabar mustapha amma nasan baza ta iyaba,narasa wani irin so laila takewa mustapha.”hmmm, kyaleta kawai, batace zata dau matakiba,muzuba ido muga matakin dazata dauka……..

   **********

Yau tunda na tashi da ciwon jiki na tashi,amma haka na daure naketa ayyukana,domin nasan ban isa nace bazanyiba.karfe goma da rabi,na tashi Daga tuyar su kosai.kayan wanke _wanke na hada na koma bakin rariya na farayi.ina cikin yin wanke_wanken wata kawar gwaggo me suna lami tayi sallama,dam naji gabana ya fadi,Wanda bansan dalilin hakanba.addu’a na hauyi a cikin zuciyata. Amsa mata sallamar nayi ina mata sannu da zuwa.wani kallo naga tana bina dashi Wanda bansan kona meneneba. Nidai na gaisheta naci gaba da aikina. Yau kam naci sa’a data shigo bata zageniba,amma tabbas nasan kafin tatafi seta kullamun wani sharrin.

Gwaggo tana dakinta a kwance tayi shurum sekace kayan wanki,ta kure radio tana jin waka.lami tashigo dakinnata. “Hajiya lami manya manyan kasa yau kece a gidannawa,nasan ganinki alkhairine. Gwaggo ta fadi haka tana tashi zaune,tare da rage sautin radionnata.zama hajiya lami tayi agefenta ta bata hannu suka kashe,tace wlh kam ladi,yau kinganni wata samuwace tasa nazo gurinki,arziki ne na kawo miki idan kinaso. Gyara zama gwaggo tayi ta fuskanci lami tace” dagaske lami, fadamun menene? “To,dafarko dai kinsan alhaji sulaiman menasara. “Haba lami nasanshi mana,mutumin dayayi fice a garin kano dama kasar baki daya,saboda tarin dukiyarsa da ma’aikatunsa. “Yawwa ‘yar gari Ashe kingane,to nima wata hajiyace take zuwa gidansa,gurin matarsa.jiya jiyannan ta kirani tace mun nasamo,’yar aiki,gidan suna bukatar ‘yar aiki kuma yarinya sukeso me jini ajika shine nace bari nazo gurinki nasan zaki bada marya……me kike nufi lami duk ‘yan kauye da masu Neman aikatau kirasa wazaki ce zaki kai aiki sai maryam,gwaggo takatseta da saurinta. Dafa kafadarta lami tayi,kwantar da hankalinki kawata abun bana zafi bane,da arziki agidan wasu ai gwara agidanku,ki bar maryam din mana taje tayi aikin. ” Sam_Sam lami,bazata sabuba,yanzu idanna bada maryam aikatau Waze dinga kula da sana’ata,Waze dingamun aikin gida,kuma sannan ‘yan uwanmu na kauye,se sun tambayeni ina nakai maryam. “Wannan duk ba matsala bane ladi, nasan kudin da kike samu a sana’arki a wata bekai 200,000 to ita duk wata zata dinga biyanki 200,000.kinga ya isheki kinemo ‘yar aiki kema idan kinaso ta dinga miki,ko 30,000 kika bata zata miki,kinga kinci riba biyu gata Sana’a gata aikin maryam. Jinjina kai gwaggo takeyi cike da mamaki tace ” yanzu lami dan aikin gidan da maryam zata musu shine zasu ringa bata 200,000 anya kuwa lami gaskiyane. “To mene 200,000 a gidan alh,sulaiman menasara,kinga idan baza ki iyaba innemi wata.lami ta yunkura zata yashi. Dasauri gwaggo ta dakatar da ita,Haba lami karki tafi mana,200,000 aiba wasa bace,shikenan na amince,idanma yanzu kikeson tafiya da maryam din gatanan kutafi. Dariya lami tayi tace” shegiya kawata taji nera,daman nasan zaki yarda,kokefa yanzu zakiga kin canza kin fito gari. “Allah ko kawata gwaggo ta bata hannu suka tafa,wayaki kudi,ai kudi sine jin dadin rayuwa,barima na kirata ta hada kayanta seku wuce,aiba jira babu jinkiri. ” gaskiya kam,domin suna bukatar me aiki da gaggawa,ayanda hajiyar tacemun. “maryam,maryam maryam, gwaggo ta hau kwalomun kira rass!!! Gabana ya yankeya fadi domin nasan kiran gwaggo ba alkhairi bane,dama nasan za’a rina,da sauri na amsa tare da tashi na nufi dakinnata. Durkusawa nayi agabanta, “gani gwaggo. “Yawwa maryam koma dakinki ki hado kayanki zaku tafi da lami zata kaiki wani gida aikatau,gwaggo ta fadi haka cikin halin ko’in kula.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button