Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Zaku iya ƙara jina da daddare insha Allah

By
Zeey kumurya
ABINDA KASHUKA….!

BY
ZEEY KUMURYA

7️⃣1️⃣

SUBSCRIBE
DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

Bismillahirrahmanirrahim

……….Wunin yau gabadaya a ɗakin ammi na yishi, ina ta juyi akan gado ko aiki banyiba. Sosai kewar yaya ta cikamun zuciya, gashi Ni ba wayaba balle na kirashi koshi ya kirani. Bayan sallar la’asar ina zaune akan dadduma a ɗakin ammi, idar da Sallah ta kenan ammi tashigo ɗakin, zama tayi a gefen gado tana dubana tace, “ɗiyata ya kannaki?” Dayake dazu data tambayeni meke damuna nace mata kaina ke ciwo nace “da sauƙi” tace, “to Allah ya ƙara sauƙi, bari na kawo miki abinci kici kisha magani, gobe da safe idan Allah yakaimu da kaina zan kaiki asibiti, wannan ƙananun ciwukan su suke zama babba Allah ya kiyaye dai” nace “ameen” ammi ta ɗauki wayarta tayi dialing number’n mustapha, amma be ɗagaba mikomun wayar tayi tace, “gashi idan yakira ki ɗaga bari na kawo miki abincin. Karbar wayar nayi ita kuma ammi ta fice, number salimat na lalubo nayi dialing, karawa nayi a kunnena jin tana ringing, ringing uku ta ɗaga da sallama. Amsa mata nayi na ƙara da faɗin “Amaryarnan baki da kirki ko kaɗan” dariya tayi tace, “rashin kirkin menayi kuma kawata?” nace, “ko nemana bakyayi, rabon da muyi waya dake tun sallah” saleemat tace, “wlh bahaka bane, kinsan ba wayarki bace banason na kira bansamekiba” nace, “idan kika kira kodayaushe zaki sameni, sedai da daddare ne baza ki sameniba” saleemat tace, “to dama ina Ni ina kiranki da daddare ai nasan lokacin kina….” Katseta nayi da fadin, “naji karkimun iskanci da kika saba, ina ummata?” Umma tananan kalau wlh, ya Jos ɗin?” Nace, “Masha Allah kigaidamun da umma sosai dan Allah, Jos lafiya kalau” saleemat tace, “zataji insha Allah” nace, “saura kwana nawa ne bikin?” Tace, “saura sati huɗu duk da satin bikin” nace, “Allah yakaimu, baki turomun ankon ba to, kar lokaci ya kure na rasa ɗinki” saleemat tace, “ke umma ta sai miki ankon duka, dama guda biyu ne, harta bada a miki ɗinki.” Cikin jin daɗi nace, “Allah sarki ummata, ita datake da hidima amma shine harda saimun anko, Nagode sosai Allah yasaka da Alkhairi, ki bata wayar na mata Godiya. Saleemat tace, “ameen, amma ta fita yanzun taje kasuwa, anjima idan ta dawo zankiraki na haɗaku” nace, “to Allah yakaimu, ina gwaggotah” tace, “gwaggo tananan kalau, dazu ma ta shigo da rana” nace, “inason kiranta a waya ko har yanzu bata da wayane?” Saleemat tace, “akwai waya a hannunta bari yanzu zan fita sena karbo miki number ta, naturo Miki” nace, “to Nagode” mukayi sallama na kashe wayar. Ammi ta shigo ta kawo mun abinci da ruwa da maganin ciwon kai, ta tambayi har yanzu be kiraba, nace mata eh. Ina cikin cin abinci wayar ammi ta fara ringing, ni kaɗai ce a ɗakin ammi ta ƙara fita. Ɗauka nayi na duba gabana na faduwa, na ɗauka yaya ne senaga bakuwar number, kamar kar na daga se kuma dai na daga tana daf da tsinkewa. Muryar wadda naji tayi sallama yasani saurin cewa, “gwaggo!” Cikin doki, gwaggo ma a ɗaya ɓangaren cikin fara’a tace, “na’am Maryama” nace, “gwaggo nayi kewarki da yawa” tace “nima haka Maryama, ai bansan ana samunki a wayaba da tuni na karbi lambar na kiraki” nace, “nima gwaggo bansan kinyi wayaba ai, ya jikinnaki?” gwaggo tace, “jiki da sauƙi, amma har yanzu da sanda nake dogarawa nake tafiya” cikin tausayawa nace, “ayya Allah ya ƙara sauƙi, yaushe zakizo gwaggo?” gwaggo tace, “ina son zuwa naganki Maryama ko dan na nemi yafiyarki akan irin cutarwar dana miki, amma ƙafata bazata juri zaman mota ba” nace, “gwaggo dan Allah ki bar wannan zancen, Ni babu abunda kikamun idanma da akwai na yafe miki tuntuni” gwaggo cikin kuka tace, “kayya Maryam da akwai abunda na miki mana, gashinan yanzu tun ba’aje ko’inaba na fara ganin sakayya nasanma kaɗan nagani dan….” “Dan Allah gwaggo kidena faɗin haka karki sani kuka nima, Ni bakimun komaiba” gwaggo tace, “shikenan yar albarka nadena, Allah ya miki albarka, ya baki ƴaƴa nagari kamar ke masu hankali da biyayya, Allah yajikan mahaifiyarki Maryama da yaya Fatima(inna), ya kuma bayyana miki mahaifinki idan yana raye da danginsa” nace, “ameen gwaggo ina su baba Ilya da sauran mutan ƙauyen?” Gwaggo tace, “sunanan kalau, suna yawan zuwa suna dubanima ba subi ta halinaba” nace, “to duk a gaidasu” tace, “zasuji ya maigidannaki?” Nace, “yananan kalau, yau yama taho Kanon” gwaggo tace, “Allah yakawoshi lafiya, dafatan dai komai lafiya” nace “lafiya kalau gwaggo” mun ɗan jima muna hira da gwaggo sannan mukayi sallama, wayar da mukayi da gwaggo ta ragemun damuwar kewar yaya danake ciki, cin abincina nacigaba dayi…..

KANO

Tunda suka shigo Kano yake bin garin da kallo yanajin farinciki na ratsa zuciyarsa, ji yake kamar yayi wasu shekaru rabonshi da Kanon, wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da suka shigo katon layinsu ya hango gidansu. Sedai kuma lokaci ɗaya ya tuna wani abu daya dishashe masa farincikin da yake ciki, ba komai ya tuna face mommy. Lumshe idonsa yayi ya jinginar da kansa a jikin kujera yana ɗan jan numfashi. A ƙaton gate din gidan na tsakiya driver’n ya tsaya ya fara danna horn, bajimawa wasu daga cikin masu gadin gidan suka taso suka wangale musu gate din, dama already sun san da batun zuwansa. Buɗe idonsa yayi a hankali jin sun shigo gidan, glass din barin dayake ya zuge ƙasa a hankali, ma’aikatan gidan ya shiga ɗagawa hannu kamar yadda suma suke masa, kasancewar driver’n slowly yake tafiya da motar har sannu da zuwan da suke masa yana ji, parking space suka nufa yana cigaba da bin gidan da kallo, babu abunda ya sauya a gidan tun bayar tafiyarsa har zuwa yau. Zannurain, haidar da faruq da tundazu suke dakon zuwansa a harabar gidan suka nufo gurin motar tasu da sauri zuciyoyinsu cike da ɗoki da son ganin ɗan’uwansu. A hankali ya buɗe murfin motar ya ziro ƙafarsa guda ɗaya, seda ya ɗanyi wasu sakanni sannan ya ziro ɗayar itama, kafin ya fito dukansa daga cikin motar, dai_dai nan su haidar suka ƙaraso gurin, haidar ne yayi sauri ya rigasu ƙasarawa garesa yana dariyar farinciki ya rungumeshi yana faɗin, “welcome big bro” rungumeshi shima Mustapha yayi cikin tsananin farinciki yace, “Thank you dear” suma su faruq rungumeshi sukayi gaba-ɗayansu suna welcoming dinshi, abun gwanin ban burgewa. duka ya haɗa su shima ya rungume cikin jin daɗi da farin ciki mara misaltuwa, da kyar suka sakeshi kowa yana faɗa masa yanda yayi missing ɗinsa, shidai murmushi kawai yake saki yana binsu da kallo, haidar riƙe da hannun damansa zannurain kuma na hagu, faruq kuma yana gabansu suka nufi cikin gidan, bayan sun haɗa driver’n da wani ma’aikacin gidan domin ya kaishi masauki, part ɗin daddy yaga sun nufa dashi.

A main parlour suka tarar da daddy zaune shida wasu yan’uwansa har da wata mace cousin din su daddy ce, tun randa su daddy suka dawo tazo gidan, a gidan da aka riƙe Aunty take sunanta Hajiya zuwaira yara kuma na kiranta da mami. Daddy na hango mustapha ya mike ya taryoshi cikin farincikin ganinsa fuskarsa ɗauke da murmushi, Shima Mustapha sakin su haidar yayi, yayi hugging daddy cikin tsananin kewarsa. Daddy yace, “welcome son, dafatan kun ƙaraso lafiya” mustapha na sakin daddy yace, “thank you Dad, mun ƙaraso lafiya kalau” daddy ya shafa kansa cikin tsananin farin cikin ganinsa, yayi matuƙar kewar ɗannasa ba kaɗan ba. daddy riƙe da hannunsa suka ƙarasa cikin falon, gaishe da mutanen falon Mustapha yayi cikin girmamawa, suka amsa masa suma cikin fara’a. daddy se nan_nan yake da mustapha yarasa inda ze sakashi dan farincikin ganinshi. Bayan sun gama gaisawa daddy ya tambayeshi ya su Maryam da ammi, yace masa duk sunan kalau. daddy da kanshi ya masa jagora zuwa bedroom ɗinsa kamar wani bako, mustapha murmushi kawai yake ciki jin daɗin yanda daddy yake masa, a toilet din daddy yayi wanka, kafin ya fito faruq ya kawo masa wasu sabbin ƙananun kaya. Bayan yagama shiryawa yayi sallar la’asar dabe samu yayita akan lokaci ba, ya fito falo inda yatarar an shirya masa lifaya ta abubuwan ciye_ciye dana sha. Mami da kanta ta kama hannunsa ta kaishi har dinning, zama yayi yadubeta yace, “Nagode mami” mami na serving dinshi cikin tausayinshi akan abunda mommy ta aikata masa tace, “bakomai ɗana, ashe haka al’amura suka faru” gyada mata kai kawai yayi alamar eh, danshi bayason ana tuno masa da abunda ya faru abaya. mami tace, “Allah ya kiyaye gaba,ya rabu da mutane masu irin halin Atika, Allah ya rabamu da sharrin makiya” cikin sanyin murya yace “ameen” mami ta tura masa abincin data zuba gabansa tana faɗin, “ya iyalinnaka, Alhaji yace kayi aure” yace “sunanan kalau” mami tace, “Masha Allah, Allah yabaku zaman lafiya da zuri’a dayyiba ya haɗa kanku” yace, “ameen” yana cin abincin mami tana masa hira, harta masa murnar gamuwa da mahaifiyarsa. Bayan ya gama cin abincin daddy ya masa jagora zuwa ɗakin da Sadiq yake. Yana kwance akan gado yana bacci kamar gawa, ya rame yayi baƙi bakadanba. Mustapha tsayawa yayi yana kallonsa cike da tausayawa, kallon daddy yayi yace, “dad wai meke damunsa ne?” Daddy ya sauke dogon numfashi yace, “gashinan dai Son, ciwonnasane dai ankasa gane kansa, a Saudiyyan dai suna masa maganin Islamic, shine jikinnasa yayi kyau haka” jinjina kai mustapha yayi cikin jimantawa aransa yana mamakin abunda daddy yace, akan jikin Sadik duk yanda yaganshi ɗinnan ace wai ahakanma jikin yayi kyau. Kiran sallar magriba ne yafitar dasu daga ɗakin. Bayan sun dawo daga masallaci su haidar suka zagayeshi suna masa hira, shima sakin jikinsa yayi ya biye musu suka sha hira, hakan ya ɗauke hankalinsa be kira ammi ba, ya sanar mata sun sauka lafiya, saidai duk abunda yake tunanin Maryam na nan manne a cikin ransa…….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button