Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yau Litinin yau Maryam an ɗanɗana yaƙin mata wato haihuwa, tun cikin dare ta fara nak’udar sai kusan azahar Allah ya sauketa lafiya ta sunkuto ‘yarta mace kyakkyawa mai kama da Mustapha, da yamma aka sallamota suka dawo gida. Aunty da gwaggo da baaba Talatu ne tare da ita, Ammi kuma tana hanya bata ƙarasoba, Hajja da ummee ma sai gobe zasu zo insha Allah. Zaune nake akan gado jaririyar tana kan cinyata, Aunty tana gefe na, Aliya kuma tana ƙasan gado, gwaggo kuma tana falo tare da umman saleemat da saleemat, Kallon yarinyar nake inajin wata irin zazzafar k’aunar ta na ƙara ratsa zuciya, Aunty ta dubeni tace “Maryam ki bawa yarinyarnan nono tasha, tun ɗazu yarinya sai neman abinci take” na ɓata fuska bance komai ba kuma banyi yunk’urin ciro nononba, Aliya cikin shaƙiyanci tace “Nonanne ba’ason mugani kuma dole sai an fito dashi muganiba” na harareta, Aunty ta haɗe rai ta dubi Aliya tace “to baza ki ganiba tashi ki fita” Aliya ta tashi tana dariya ƙasa_ƙasa kafin ta kai ga fita Mustapha ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, muka amsa masa a tare, Aliya ta fice Aunty ta masa sannu da zuwa sannan ta mik’e itama tana faɗin “ki tabbatar kafin na dawo kin bata nonon tasha” nace “toh” Mustapha ya zauna a kusa da Maryam yana kallonsu ita da babyn cike da k’aunarsu da ban sha’awa, yarinyar ta fara mutsu_mutsu tana ƙoƙarin saka kuka, Mustapha ya dubi Maryam yace “yunwa fa takeji, ki bata abincinta mana” na turo baki nace “Ni bansan yadda zan ba taba ai” ya waro idonsa waje yace “You mean tun ɗazu baki bata tasha ba” nace “ehh” yace “meyasa?” nace “toh mutane sunyi yawa a ɗakin kowa saiya gama kalleni” baice komai ba ya zuge zip d’in rigata yayi ƙasa da rigar ya ciro nonon daga cikin bra, wanda ya ƙara cika da ruwan nono, ba tallafo yarinyar yasa mata a baki, aiko tayiwa nonon wata irin cabka, na runtse idona tare da janye nonon da sauri, yarinya kuwa tasa kuka ya kalleni da alamun tambaya nace masa “da zafi fa” cikin rarrashi yace “sorry ze dena ai, ki bata tasha kinga kuka take” na ƙara sa mata ta fara tsotsa tare yin shiru, ina kallonsa nace “wannan baby’ntaka daga gani zatayi ci, ba kaji yanda take zuk’eniba” yayi murmushi saboda yanda tayi maganar yace “ai ba’a ƙasa ta ɗaukoba kema waya sani ko haka kikayi” na turo baki nace “to ni banma shaba, sai dai inkai ta gado” ya kwantar da kanshi akan kafadata yace “nima bansha da yawa ba ai” na shafa fuskarsa ina murmushi bance komai ba.

Bayan tasha ta k’oshi bacci ya ɗauke ta, na cire nonon daga bakinta ina yamutsa fuska na maidashi cikin bra, Yaya ya ɗauketa yana kallona yace “zafinne dai” nace “eh, gashi duk yamun nauyi” yace “sorry idan muka shanye nida baby ze dena miki” nayi shiru ina kallonshi shikuma ya k’urawa babynshi ido, na kwanta a jikinshi nace “ya kake jinka yanzu, kazama Daddy” yayi murmushi tare da kissing goshin yarinyar yace “farin ciki mara misaltuwa Princess, Nagode miki sosai da…” na rufe mishi baki da hannuna nace “ka godewa Allah, domin shi ya bamu” yayi murmushi yace “Alhamdulillah, Allah ka ƙara bamu wasu masu albarka, ka shiryar mana dasu bisa tafarkin addinin Muslunci” nace “ameen, ya maganar karatuna tunda na haifa maka baby’n” yace “sai kin ƙaran uku, munyiwa Abbu da Aunty da Daddy takwarori” na waro ido nace “sai na tsufa kenan” yace “a’a bazaki tsufa ba tawan” cikin shagwaba nace “nidai yaya Please ka barni nayi yanzu” yayi kissed lips ɗina yace “kin zama mama yanzu ya kamata ki dena rigima” nayi murmushi nace “bazan iya denawaba, indai ina tare dakai kuma zaka rarrasheni” yace “i like it kuma bazan gaji da rarrashinkiba, maganar karatunki kuma idan little Maryam tayi wayo sai ki zaɓi duk ƙasar da kikeso a faɗin duniya muje kiyita karatunki harsai kin gaji” cikin farinciki nace “dagaske yayana?” yace “gasken gaskema, tunda kika haifamun baby kingamun komai a rayuwarnan, naduba_naduba naga babu abunda ya dace na saka mishi dashi face hakan, tunda shine babban burinki a rayuwa, nayi miki alƙawari insha Allah kina gama karatun zamu dawo nan gida Nigeria nagina miki k’aton hospital naki na kanki” na rungumeshi sosai cikin tsananin farin ciki nace “thank you so much hubby, Allah yakaimu time d’in da rai da Lafiya” ya musu kyakkyawar runguma ita da baby’n yace “babu godiya a tsakaninmu my love, kin cancanta na miki komai a duniyarnan my princess” nayi luf a jikinsa inajin k’aunarsa na ƙara ninkuwa a rai, tabbas nikam nayi dacen miji mai tsananin k’aunata da bani dukkan wata kulawa danake buƙata, a hankali nace “I LOVE YOU SO MUCH MY WORLD BEST” yace “love You too princess” na lumshe idona ina ƙara mannemasa inajin wata nutsuwa na ratsa zuciyata, a yanzu bani da wata sauran damuwa ko matsala a rayuwata, Mustapha ma a nasa ɓangaren ji yake duk duniya babu wanda ya kaishi dace da mace tagari mai haƙuri, tsafta, kyawawan d’abi’u da uwa uba tarbiyya da biyayya ga addini. Zuciyarsa fess yakejinta bashi da wata sauran damuwa tunda yayi dace da mace tagari, dama Manzon Allah (S.A.W) yace “mace tagari itace jin daɗin rayuwar duniya” (Allah ka haɗamu da abokan zama nagari, ameen.)

ALHAMDULILLAH, ALHAMDULILLAH, ALHAMDULILLAH. BAYAN DOGON ZANGO DANA ƊAUKA INA RUBUTA LITTAFINNAN YAU ALLAH YA NUFA NA KAMMALASA, ABUNDA NA RUBUTA DAI_DAI ALLAH YA HAƊAMU A LADAN, WANDA NAYI KUSKURE ALLAH YA YAFE MINI, MASOYAN ABIN DA KA SHUKA BANI DA BAKIN GODIYA A GAREKU SAI DAI KAWAI INCE, ALLAH YA BAR ZUMUNCI DA K’AUNA, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MUKU A DUK INDA KUKE A FAƊIN DUNIYA, SAI MUN HAƊU A SABON BOOK ƊINA WANDA ZAI ZO MUKU NAN BADA JIMAWABA INSHA ALLAH.

????????????????????????Wlh zanyi missing ɗinku sosai MASOYA, harnama fara tun yanzu.????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button