Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sasai Abbu yake nunamun k’auna da tarairaya gami da kulawa, haka ma Ummee da Hajja da Ammi wadda take bani wata sabuwar kulawa fiye da ta da, ga ƙannena da kodayaushe suna manne dani, sosai nake son yaran, tabbas jini da mahaifa ba ƙarya bane soyayyarsuma daban take. Bayan babbar Sallah da sati ɗaya mukaje Kano, Hajja da Abbu suka yiwa Daddy godiya akan riƙon Mustapha, sannan mukaje gidan gwaggo, Abbu yayi mata ta’aziyyar inna da mahaifiyata, gwaggo ta dinga kuka cikin nadamar abubuwan data aikata a rayuwarta, musamman zalintar Maryam da tayi, gashi duk mugunta da cutar da ita datayi Allah ya kareta, ta kaita aikatau da niyyar ta wulak’anta mata rayuwa, sai gashi sanadin aikatau ɗin ta haɗu da mahaifinta tare da auran miji na kere Sa’a, kuma ta zamo yanzu itace gatanta. Lokacin da muka biya ta asibiti duba Mommy sai da nayi kuka, Saboda mawuyacin halin da take ciki, kafarta data karye ta rub’e sai d’oyi da wani ruwa mai wari take fitarwa, ashe tana da sugar a jikinta hakan yasa ƙafar ta rub’e, waje za’a fita da ita a yanke ƙafar. Suhailat kam zuwa yanzu ta gane Mustapha ya riga da yayi mata nisa, Saboda yadda yake bawa Maryam kulawa da nuna mata soyayya a gaban kowa tamkar ita kaɗaice mace a duniyar. Tayi kuka kamar ranta zai fita, taji duk duniyar babu wanda ta tsana sama da Mommy, domin itace tun farko bata ba ta tarbiyyar ingatacciyaba, gashi yanzu tana ji tana gani ta rabu da Mustapha wanda take masa masifar so, ƴar aikin datake gani a wulak’ance ita ta sameshi. Da mukaje duba yaya Sadiq ya dinga roƙona gafara yana kuka, ni bansan abunda yamun ba amma duk da haka nace masa na yafe masa, sai da mukaje Kaduna nake faɗawa Aunty, tacemun ai shine wanda yaita ƙoƙarin ketamun haddi, baƙaramin ɗimuwa nayi ba dajin wannan mummunan labarin, nayi mamaki kwarai da jin yaya Sadiq ne yakeyin fyad’en, nayi kuka kuma saboda tuna yanda ya nunamun k’auna, ashe duk ta yaudarace, ni ina ganin duk gidan babu wanda ya kaishi hankali ashe fuska biyu gareshi, na masa addu’ar shiriya da kuma roƙon Allah ya ƙara karemu daga mutane irinsu da duk wani mai nufinmu da sharri. Daga Kaduna muka dawo Jos mukayi shiri muka ɗara zuwa ƙasar NIJER dukanmu, mun zaga ‘yan’uwa da dangi namu dana mahaifin yaya, har kukan daɗi sai da nayi ganin jinina da yanda suke rububinmu da nuna mana k’auna nida yaya, watanmu guda acan muka dawo gida Nigeria cike da kewar asalinmu, kamar karmu taho suma can da ƙyar suka bari muka taho. Bayan mun dawo da sati biyu muka dawo Kano da zama gaba-d’aya, inda muka tare a k’aton gida mai kyau da Daddy ya bawa Yaya, Walima Ammi ta shirya mana bayan muntare saboda farinciki da faruwar abubuwa, aka tara yan’uwa da abokan arzik’i akaci akasha, kowa ya tafi, gida ya rage daga ni sai Yaya sai baaba Talatu da yaya yasa Aunty ta ɗakkota dan tadinga ɗebemun kewa idan bayanan, ta kuma tayani aikace_aikace.

Mustapha na zaune a ɗakinsa yana operating system, Maryam ta turo ƙofar ɗakin ta shigo a hankali, tana sanye cikin bubu da’aka ɗinka mata ita da wani yadi mai kyau red colour, cikinta ya fito ɗan wata shida kuma ta ƙara k’iba da murjewa, sai tashin k’amshi take me daɗin gaske, sallama ta masa cikin zazzak’ar muryarta. Mustapha ya lumshe idonsa cikin jin daɗin ƙamshinta daya kaiwa hancinsa ziyara, ya amsa mata sallamar tare da buɗe lumshashshun idanunsa ya zuba mata yana jifanta da wani fitinannen kallo, Maryam ta ajiye teaflaks d’in hannunta a kan bedside, zama tayi a kusa dashi tana murmushi ta hura masa iska a ido, Ajiyar zuciya ya sauke ya kwantar da kanta a kafaɗarsa, sumar kansa ta shafa tace “sannu da aiki hubby” ya shawabe fuska yace “yawwa” Maryam tana murmushi tace “ka gaji ko?” ya gyada mata kai, kuncinsa ta shafa tace “sorry ka kusa gamawa ai” ya ƙara gyaɗa mata kai tare da shigewa jikinta, hannunsa yasa ya shiga shafa cikinta, Maryam tace “ga cofee ɗin na kawo maka, kasha sai kacigaba da aikin” ya bar jikinta yana faɗin “Toh Princess” zuba masa coffe ɗin tayi a cup ta miƙa masa, ya karb’a yayi bismillah ya fara kurb’a idanunsa k’ur akanta, tayi masa kyau ba kaɗan ba. Bayan ya gama shan cofee ɗin na kwantar da murna cikin ladabi nace “yaya yaushe zamuje dubo Mommy” yamun shiru ya janyo laptop ɗinsa yacigaba da aikinsa, na matsa jikinshi na kwantar da kaina a kafaɗarshi cikin shagwab’a nace “yaya kamun shiru” batare daya kalleniba yace “ba zamu bane” nace “why?” yace “kawai” shiru nayi kawai ina kallonsa, tun shekaran jiya Mommy’n suka dawo, amma nayi_nayi muje mu dubota yaƙi. ya d’ago ya kalleta jin tayi shiru, na ɓata fuska tare da turo baki gaba, numfashi ya sauke yace “bari na ƙarasa aikinnan, idan anyi sallah sai muje” nayi murmushi nace “thanks” yaja karan hancina yace “shikenan anbar ɓata rai” nayi dariya ina ƙara lafewa a jikinsa.

Bayan sallar isha’i mukaje gida gidan Daddy muka dubo Mommy, mummunan halin da Mommy take ciki bazai misaltuba, ta rame tayi baƙi ga babu kafa ɗaya, ga kuraje sun ƙara feso mata ta ko’ina a jikinta, ɗakin da take gabad’aya wani irin ƙarni da wari yake, Mommy tana ganin su Maryam ta fashe da kuka, kasa haɗa ido tayi da Mustapha saboda tsabar kunya da nadama, su da take nufa da sharri gashinan suna rayuwarsu hankali kwance cikin jin daɗi, ita kuwa gatanan kwance da rayuwar wahalar da take ta gwammace gwara mutuwa, ɗayar ƙafar ta tama taji ciwo annannad’eta da bandeji, itama likitoci sunce idan ciwon bai warkeba sai dai a yanke ta itama. Maryama kuka ta saka dataga halin da Mommy take ciki, Mustapha ya rungumeta ya rarrasheta. Sosai na tsorata da duniya ganin halin da Mommy ta tsinci kanta, lallai rayuwa kayi da kyau sai kaga da kyau, amma Mommy ABIN DA TA SHUKA SHI TA FARA GIRBA Suhailat tana Kaduna gidan Aunty ta haihu sati biyu da suka wuce ta haifi yarta mace, Sunan Mommy Aunty tasawa yarinyar, Lokacin da sukazo dubata Mommy taga yarinyar ta dinga kuka da ihu abun duniya duk ya isheta ta zama kamar mahaukaciya, sai surutai da faɗar abubuwan data aikata takeyi.

BAYAN WATA UKU

Rayuwa mai cike da jin daɗi, farin ciki da kwanciyar hankali Maryam da Mustapha suke gudanarwa cikin tarairaya gami da tsantsar kaunar juna, burin kowannensu yaga ya faranta ran ɗan’uwansa. Anyi Engagement ɗin Aliya da saurayinta da suke shan soyayya, bikinta kafin azumi ita dasu haidar da zannurain harma da faruq, duka za’a haɗa a sha Shagali, Mommy ta haukace hauka tuburan, hakan yasa aka maidata gidan mahaukata ake kula da ita acan, Suhailat kuwa Daddy yace tana yaye yarta zai d’aura mata aure da Kamal, Kamal beyi musu ba lokacin da Daddy yace ya auri Suhailat, dan har yanzu bai dena santaba kuma ko ba komai ze auri ‘yar shahararren mai kuɗi, Suhailat cedai batayi farin ciki da auran kamal ɗin ba, dan son Mustapha nanan daram a ranta, kullum cikin kuka take da damuwa taƙi haƙura, Aunty kuwa bata kulata sai kallo da ido, abu ɗaya take maimaita mata shine “Mustapha ya riga daya mata nisa, nisa na har abada” Sadiq ya koma abun tausayi, ko cikin mutane baya iya shiga saboda kunya da nadamar abunda ya aikata, sai dai ya kulle kansa a daki yayi ta kuka yana neman gafarar Allah akan abunda ya aikata, ga ciwo yaƙi barinsa ya tafi ya dawo yake masa. Daddy ya bayyanawa Ammi abunda yake ransa game da ita, da farko ta bujire dan bata da niyyar ƙara aure a arayuwarta, amma da Daddy ya haɗa ta da Hajja, Hajjan ta mata nasiha sai ta amince zata auri Daddy’n, amma tace sai bayan ta aurar da Umaimah, tunda Umaimah’n ta samu wani mutum mai mata biyu zai aureta, itama ta haƙura da Mustapha tunda baya sonta, dan bayan dawowarsu Kano ta ƙirashi a wata ta sanar masa tana sonsa, shikuma ya mata wankin babban bargo, hakan yasa ta haƙura ta karb’i ƙaddararta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button