Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tsayawa yayi cak tare da juyowa ya kalleta, idanunta a rufe amma se shafa gadon take tana kiran sunansa, be ankaraba yaga tazo bakin gado garin lalubenta zata fadi, kafin yayi wani yunkuri harta fado kasan gadon. da sauri ya karasa ya tallafota jikinsa a hankali yace, “sorry” yana gyara mata gashin kanta dayake ƙoƙarin rufe mata ido. buɗe idonta tayi a hankali cikin shagwaba tace, “shine zaka tafi ka barni nikadai seya ƙara biyoni” cize lips dinsa yayi, cikin gajiyawa yace. “Babu wani lizard fa” tana matso hawaye tace, “Allah akwai nafa ganshi da idona” bece mata komaiba ya maidata kan gadon ya direta ya juya. kudundunewa nayi acikin blanket, har yanzu a tsorace nake da ganin kadangaren danayi. seyanzu na tuna babu komai a jikina se towel, gabanane yafadi dana tuna shifa ya daukoni ya kawoni dakinsa tunda bada kafata nazoba. “Yanzu haka ya ganni babu kaya fa” na fadi haka a raina. ganin ze shige toilet din nayi sauri nace, “nifa Allah tsoro nakeji bazan iya zama ni kaɗaiba” akufule yajuyo yace, “toilet din zan shiga dake?” ganin yanda yayi maganar fuskarsa a hade senayi ƙasa da kaina na fara hawaye. siririn tsaki yaja sannan ya shige toilet din. yayi danasanin sakawa Maryam lizard dinnan, gashinan yanzu bayajin daɗin jikinsa kokaɗan. ya dade yana a toilet din kafin ya fito, niko na makure a karshen gado cikin blanket, duk da da haske a dakin amma a matukar tsorace nake. kuka na fara ganin yaƙi fitowa da wuri. ɗaure da towel iya kugunsa ya fito, da wani ƙarami kuma yana goge sumar kansa. Tunda yafito yajita sarai tana shashsheka amma yaki kallon inda takema. karasawa gaban mudubi yayi ya farawa shafe_shafe. Ina ganin ya fito na sauke ajiyar zuciya amma bandena kukanba, ganinshi a haka yasa na runtse idona da sauri kirjina na dukan uku_uku, bantaba ganin namiji babba haka ba rigaba. juya masa baya nayi na kwanta badon babu kaya ajikinaba tashi zanyi infice inbar masa dakin. Duk abunda takeyi yana kallonta ta cikin madubi, tabe bakinsa yayi yacigaba da shirinshi. har ya gama shiryawa cikin wata jallabiya milk colour me kyau, maryam batayi shiru da kukan tabarar datakeba. dafe kansa yayi dayake matukar sara masa, yarasa dame zeji da kukannata dayake taɓa masa zuciya kokuma da abunda ke damunsa. ganin bata da niyyar yin shiru cikin tsawa yace mata. “Ki rufemun baki ko kuma na zaneki yanzunnan” hadiye kukan nawa nayi da sauri cikin tsoronsa. Ajiyar zuciya yasauke jin tayi shiru, ya lura shagwaba ce kawai ke damunta, seya mata da zafi_zafi sannan zasu shirya. zama yayi a bakin gadon, kallonta yayi yace, “tashi ki barmun ɗaki” a hankali nace “ni tsoro nakeji” “to tashi muje na cire miki lizard din” “um’um, nidai kakaini gurin ammi” na faɗi haka kamar zan fashe da kuka. shiru ya mata be ƙara ce mata komaiba. ƙasa ya sauka ya zauna kawai ya lumshe idonsa. har kusan ƙarfe ɗaya be ƙara koda kallon inda takeba yananan a zaune cikin yanayin damuwa. Maryam kuwa tuni bacci ya ƙara daukarta bayan tagama cin kukanta. har lokacin bayajin daɗin jikinshi, a hankali ya mike ya fice dankar ta farka. dakinta ya shiga ya dauke lizard din robar daya ajiye, har ya juya ze fita sekuma ya dawo ya buɗe wardrobe dinta, dogowar riga kawai ya ɗaukar mata da hijabi saboda sallah, kashe light din dakin yayi sannan ya fice. seda ya kashe na faloma sannan ya koma dakinsa. tananan yanda yabarta, kayan ya ajiye mata a gefen gadon, ya boye lizard din sannan ya shiga toilet ya dauro alwala, cikin dauriya yakeyin komai. be kashe mata light din dakinba, dan yanda take zabuwannan idan tatashi taga duhu seta cika gidan da ihu. fita yayi zuwa Masallaci.

Ƙarfe biyu da ‘yan mintuna, na dare Maryam ta farka. A hankali ta buɗe idonta tana miƙa da salati dauke abakinta. yunkurawa tayi ta tashi zaune, domin tayi sallah kamar kullum tunda goman ƙarshe ta shiga. mararta taji ta daure tamau. yatsina fuska tayi ta janye blanket din data lullube jikinta. sakkowa tayi daga kan gadon tana daura towel ɗin jikinta. ware ido ta hauyi kozata ganshi a dakin ganin bayanan ta sauke ajiyar zuciya me ƙarfi, tama manta ba dakintabane seyanzu data mike ta ƙara wartsakewa. abunda ya faru kafin baccinta ne ya dawo mata kwanyarta. dakin na fara bi da kallo, domin yau shine shigowata ta farko tun tarewarmu. komai tsaf a kintse fes_fes, mayen kamshinsane kawai yake tashi a dakin. A fili nace “ashe ya iya gyaran dakin, amma da a gida ake masa.” kayana na gani akan gadon, cike da mamaki na karasa ina dubawa. daukar rigar nayi nazira na daura towel a samanta, tunda babu komai a jikina kuma rigar shara_shara ce. toilet na shiga nayo alwala, masallaci har sun kusa idarwa, ƙarfe uku suke tashi dama. tunda zanyi fitsari nasan da matsala, dan inayin fitsarin marata na ƙara daurewa. ina tada sallah naji tsaiwar ta gagareni saboda juyamun da cikina ya farayi daurewa nayi, nayi raka’a biyu. ina sallamewa na durkushe a gurin hannuna dafe da cikina ina taune lips ɗina. “Ya Allah” na furta saboda wani murdawa da cikin yamun. kwanciya nayi akan dardumar ina juyi na rasa inda zan tsoma kaina, ciwon karuwa yake. ina nan kwance ina kuka da murkususu ya shigo dakin. ganinta a haka yasan ba kalauba. karasawa yayi kusa da ita ya tsugunna batare daya taɓataba yace, “menene?” jin muryarsa yasa natashi zaune da sauri, cikin azabar ciwo nace masa. “Ci..cik…cikina” muryarta na rawa saboda kukan danakeyi. wata murdawa da cikin yamun bansan sanda na faɗa jikinshi ba, hakan yayi dai_dai da fara zubowar jini daga ƙasana……….✍️

BY
Zeey kumurya
ABINDA KASHUKA….

BY
ZEEY KUMURYA

5️⃣9️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

……….Inajin dumin jinin nabin jikina amma nakasa motsawa balle nayi yunkurin tashi domin na tsafta kaina dan gudun kar jinin ya ɓata ni. Taune lips ɗina kawai nayi saboda azabar murdawar cikin, hawaye na zuba daga idona. sannu kawai Mustapha yakewa Maryam amma bata masan yanayiba. Dagata yayi da niyyar ya dakko wayarsa ya kira likitan ammi ganin ciwon bana ƙarau bane, da sauri ya saketa ta koma kijinnasa yana yamutsa fuska ganin jini ajikin rigarta kasancewar rigar tana da haske kuma babu komai acikinta. maida kaina nayi na kwantar a kan kirjinsa ina sauke ajiyar zuciya, idona na lumshe saboda fara sararamun da cikin da yayi, runtse idonsa yayi zuciyarsa babu daɗi, hakan yasashi kasa aiwatar da komai. A hankali na buɗe idona tare da yunkurawa na sauka daga jikinsa cikin tsananin jin kunya da takaici. cize lips ɗina nayi na daure na mike na fara jan kafata cikin dauriya na fice daga dakin zuciyata cike da tsananin kunyarsa, banajin ko ido zan iya ƙara haɗawa dashi a yau, gaskiya abunnan bemun adalci ba, yarasa a inda zezomun se’agabansa. ina shiga daki na cire hijabin jikina na wuce toilet. wanka nayi da ruwa me dumi na tsaftace jikina. Bayan na fito na dauko magani nasha sannan na kwanta, nama manta da wani batun lizard din jiya, ta kaina kawai nakeyi….. Cike da kyankyami ya buɗe idonsa jin tafice daga ɗakin, waro idonsa yayi waje yana bata fuska saboda ganin jinin har jikin jallabiyarsa ya ɓata. tsaki yaja ya mike da sauri ya shige toilet ya cire jallabiyar zuciyarsa harta fara tashi. dana sani kawai yakeyi akan sakawa Maryam lizard din da yayi a daki, da duk haka bata faruba, yana zaman_zamansa yajawa kansa ganin kazanta. yana jan tsaki ya wanke jallabiyar. cike da kyankyami ya goge dakinsa duk da jinin be diga a ƙasaba, tare da saka Room freshener. koda lokacin sahur yayi beci komaiba, ko ruwan tea beshaba, saboda tashin zuciyar dake damunsa, ze iya yin aman abu idan yaci shiyasa yakicin komai. Bayan ya dawo daga masallaci ya nufi dakinta domin yaga jikinnata. A Hankali ya tura kofar dakin ya shiga, tana kwance can ƙarshen gado ta takure jikinta kamar me jin bacci. karasawa kan gadon yayi yana kallonta, bacci take hannunta dafe da mararta. “Sleeping sickness” ya furta hakan a fili. juyawa yayi ya fita bayan ya duba maganin datasha ta ajiye sauran akan madubi. Bantashiba se wajen ƙarfe 11:00 am, Alhamdulillah cikin yasararamun sedan abunda baza’arasaba. Ayyukana nayi kamar kullum dana saba. Tea kawai nasha na nufi part din ammi……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button