Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan mun idar da sallah,talatu ta gyara zamanta ta fara bani labarin gidan.”kamar yadda kika sani,sunan me gidannan alh.sulaiman menasara.fitaccen dan kasuwane,Wanda yake da shaguna a kasuwannin garinnan da kuma kamfanoni da dama.alh.mutumin kirkine,gashi da kyauta kuma shi baya wulakanta talaka.sedai kuma gaskiya bashida iko da gidansa,domin matarsa tafi karfinsa juyasa takeyi, abunda tace shiza’ayi a gidannan.ita kuma hajiya,gaskiya batasan talaka,ya rabeta.idan kazo da Neman taimako zata taimaka maka,amma fa ita Sam bata Hulda da talaka.macece ita meson a girmamata,ana nuna mata kuma ita tafi kowa.gata da bala’in son ‘ya’ya,kamar me.idan kinaso Ku shirya da ita to kiso ‘ya’yanta.wadannan samarin dakika gani duka ‘ya’yantane.kome zasuyi mara kyau bata kwabarsu,akwaima daya babbansu me suna mustapha,Wanda hajiya duka tafi sonsa agidannan,tamkarma tsoransa takeji.tana masifar sonsa,bata boye soyayyar datake masa. Duka ‘yayan,gidannan basu da mutunci,nidinnan dakika ganni da girmana,dakamun tsawa sukeyi.guda dayane acikinsu me suna sadiq,shine na 2,shikadaine yayo halin babansa,yanda kamarsa take daban haka halinsa,yake daban.domin shi kowa nasane,kuma baya wulakanta mutane,kamar sauran ‘yan uwansa. Se kuma uwar gayya,wato suhailat,taci uwar kowa a rashin kunya da wulakanta mutane a gidannan. Bata tsoron kowa,duk girmanka idan ka mata badaidaiba setace zata tsinka maka mari.mustapha ne kadai,take tsoro kuma take shayi agidanna.shine Wanda zata aura kuma.ita ‘yar kanwar hajiyace,mahaifinta kuma kanin alhajine.ita kadai suka haifa,ankawota yaye gidannan,iyayenta sunyi tafiya sukayi hadari Allah ya musu rasuwa.hakan yasa zamanta yadawo gidannan gaba daya.hajiya da alh,da sauran yayyenta suka dauki son duniya suka Dora mata.kasancewarta ita kadaice mace. Ki lura,kisan irin zaman dazakiyi da kowa,domin yaran gidannan basu da mutunci ko kadan,wulakanta mutum ba komai bane agurinsu.dayannan Dana gaya miki shikadaine me hali na gari.sekuma babbansu,Wanda shi tsabar miskilancinsama ba’a gane halinsa.kinganninan nafi shekara 20 ina aiki agidannan, amma bazance miki ga abunda yafiso da Wanda bayasoba.wannan shine halayensu atakaice.

Ajiyar zuciya na sauke,nace.” Toh baaba,nagode sosai kuma insha Allah zan zauna da kowa daidai da halinsa. “Yawwa yarinya,sekuma maganar aikin daza kidingayi.zaki dinga gyara dakin hajiya Dana suhailat.da kuma duka falukan dake part din nan.se wanke_wanke.amma banda girki kuku ne, yake girki,kekuma idan suka hallara zasu ci abinci zaki dinga saving dinsu.sekuma wani aikin idan wani yagadama yasakaki dankaran Kansa. “shikenan baba talatu nagode sosai.Allah yasaka da alkhairi. Mikewa talatu tayi,har ta kai bakin kofa bankuma San meta tunaba, naga ta juyo ta dawo ta zauna.

“maryam! Takirawoni,cikin wata irin murya bata jira na’amsaba taci gaba da magana,tunda naganki naji kin shiga raina,kuma naga bakiyi kama da irin ‘yan kauyen da’ake kawosu aikatauba,dakika bani labarinki naji wani matsanancin tausayinki ya kamani,hakan yasa na kudiri niyyar taimakonki,kin rabu da masifar gwaggo,to nanma akwai wata babbar masifar.zanfada miki wani sirri na gidannan Wanda ba kowane yasanshiba,ko wasu masu aikin gidannan basu saniba,balle wani na waje.amma sekinmun alkawarin idanna fada miki bazakiyi yunkurin barin gidannanba.rasssss!!! Gabana yayanke ya fadi,duk da bansan meneneba,amma daga ji nasan ba’abun dadibane. “Insha Allah baaba,bazanyi yunkurin guduwaba, na miki alkawari.”kinsandai nauyin alkawari,kada kikarya. “Insha Allah,baaba.nafadi haka cikin zakuwar jin mezata cemun. Dogon numfashi baaba talatu taja,tace. “Hajiya bata taba daukar babbar mace a matsayin me aikin part dinnanba,tafison yarinya karama kamarkinnan.kuma duk yarinyar da’aka kawota.aikatau gidanna,sedai a wayi gari aga anmata fyade,anyiwa ‘yan mata masu aiki sama da 10,haka agidannan, kuma duk wadda aka mata fyaden bata jimawa take mutuwa…….✍️

BY
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

0️⃣8️⃣

………….mikewa tsaye nayi cikin tsananin kaduwa da razana.”innalillahi,wa’inna’ilaihirraji’un.naita maimaitawa saboda bugawar da zuciya takemun,tamkar zata Faso kirjina ta fito,haka nake jinta.mikewa talatu tayi ta kama,hannuna ta kara zaunar dani. “Maryam,ki kwantar da hankalinki,insha Allahu hakan baze faru akankiba.dasauri na dago ina dubanta.gyadamun kai tayi alamun tabbatarwa.taci gaba da bayaninta.”ba’ayiwa kowacce yarinya fyade setayi watanni,kuma abunda ze baki mamaki,ba’asan Wanda yakeyin fyadenba.duk da yaran gidannan basaji,rayuwarsu gaba daya a turai sukayita.a can suke karatunsu gaba daya,sesun gama karatu uban yake dawo dasu nan,suyi aiki.duk da basasan zaman kasarnan kokadan,amma kasancewar alh. Me kishin kasarsane,yasa baya barinsu acan yake dawowa dasu,nan.suhailat ce kadai,basu kaita karatu wajeba,duk da burinta kenan,amma hajiya Sam taki,saboda kaunar datake mata, bazata iya bari tayi nesa da itaba,sedai idan tayi hutun makaranta se taje duk kasar datakeso tayi Hutu acan.

Dafarko bangane fyade akewa yan aikin gidanba,sedai kawai na wayi gari naga basanan,seda akayiwa jikata sannan nagane,itace yarinya ta Biyar a wadanda akayiwa,na tambayeta wane tacemun bata saniba,bama ta hayyacinta aka mata kawai farkawa tayi ta ganta cikin mawuyacin hali. Kudi kawai hajiya tabamu metarin yawa tare da kaita asibiti,harta warke amma kuma bayan wasu kwanaki ta fara wani irin ciwo tamkar ana tsotse ta kafin kuma ta mutu.

Gaba daya bayanin da baaba,talatu takeyi bana fahimta,kokadan.saboda hankalina baya jikina.hannunta na kama cikin kuka nace.”nashiga uku ni maryam,baaba wannan kuma wanne irin bala’ine Allah yakawoni,dama shiyasa hajiya lami ta tambaya, bani da gata Ashe da wani Abu a kasa, akwai wani kulli da suke kullaw…..kukane yaci karfina na kwantar da kaina,akafadar talatu ina cigaba da fashewa da kuka.bubbuga bayana ta farayi alamun rarrashi. “Kiyi shiru maryam,na miki alkawari zan taimakeki,yanzu dai lokaci ya kure mana,idan hajiya ta fito taga har yanzu,inanan zata gane na fada miki wani Abu,zantafi da safe zanzo nanuna miki yanda zakiyi amfani da komai na gidannan ,alokacin idan kin samu nutsuwarki zankarasa miki bayani. Sannan kuma ina gargadinki da kada kinuna wata alama,da hajiya zata gane,wani Abu ya faru,domin idan ta gane Daga ni harke munacikin matsala.janyeni tayi Daga jikinta ta mike ta fice Daga dakin.gaba daya kwakwalwata ta kulle,tunanina ya tsaya narasa tunaninma mezanyi,mutuwar innatace ta dawomun sabuwa,nasan datananan da duk banshiga wannan bala’inba.knocking kofar dakin aka farayi da sauri na tashi na nufi toilet na wanke fuskata,sannan na fito,na bude kofar.

Matarnan nagani,hannunta dauke da faranti,da sauri nakakaro murmushin yake,ina mika hannu na karbi farantin hannunta,sannu na mata.tacemun bakomai ta juya ta fice.wasu hadaddun food flaks ne,masu matukar kyau akan faratin.murdawa na hauyi dakyar na samu na iya budewa,wani kamshine ya daki hancina,na abincin dake ciki.babu tantama Daga ganin abincin ze hadu,amm Sam naji bana sha’awarci ko yunwama banaji saboda zullumin dake addabar zuciyata.maida murfin nayi na rufe.na zabga tagumi……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button