Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

2 weeks later

Munje school din dazanyi exam nida yaya Saddam angamamun komai na exam din. goma ga azumi zamu fara exam din insha Allah. Zamanmu da heartbeat jiya ie yau babu abunda yasauya, tsakanina dashi gaisuwa ce, ko abinci bana zuba masa da kansa yake zubawa yaci. Amma yanzu kullum kafin yafita seya duba yanda natashi kafin yayi baccima seyazo ya Dubani. bantaba shiga dakinsaba, koda da sunan gyara danbanga wannan fuskarba. Kullum yana fita ina gama ayyukana zantafi part din ammi muyita hira da Aunty zuhura. Umaimah kuwa bama magana kwata_,kwata, da ina gaisheta naga bata amsawa nadena. Inta ganni setayi ta hararata tana bata rai, niko da ita da banza duk ɗaya na daukesu gurina. duk abunda ke faruwa tsakanin Maryam da umaimah zuhura tana hankalce dasu kuma tasan Umaimah son mustapha takeyi. shima Mustapha’n zuwa yanzu yagane inda umaimah ta dosa akansa. yana zuwa part din ammi zata fara shishshige masa ta kawo masa ruwa da lemo, tana iyayi tana fadin. “Yaya NOOR inkawo maka abinci, kokuma yaya NOOR mezakaci indafa maka” haka zataita masa iyayi da neman suna, shiko yamata banza abunka da miskilin mutum, gashi yarinyar bata burgeshi kokadan. Muna waya da Aunty da saleemat akai akai a wayar ammi, dan har yau besaimun wayarba, yace sena gama exam da ammi ta kuma masa maganar.

Yau ma kamar kullum Muna zaune a falon ammi, yau nida itane kadai Aunty zuhura taje gidansu ita da umaimah ta rakata, munata hira da ammi akan azumi daya rage saura kwana uku. wayar ammi ce ta kawo haske alamar kira, dauka tayi taduba. mikomun tayi tana fadin, “gashi ke ake nema ɗiyata” tasowa nayi na karba nadaga. Saleemat ce, tace. “hello mairota” ina murmushi nace, “na’am kawata yakike” “lafiya kalau, naje asibitine gurin gwaggo tace nakira mata ke” cikin tsananin mamaki nace, “gwaggo kuma bakincemun tayi tafiyaba?” “a’a batafiya tayiba Maryam”….. Nan saleemat tabawa Maryam labarin abunda yafaru da gwaggo. Hawaye shabe_shabe a fuskata nace, “yanzu saleemat kin kyautamun kenan, ace kamar gwaggo bata da lafiya amma kiƙi fadamun seyanzu, idan da mutuwa tayifa?” cikin kwantar da murya saleemat takeson ta fahimtar da Maryam dalilinsu nayin hakan, amma Maryam taki saurararta se kuka take. Ammi dake ta tambayar Maryam a rude ganin kukan datake ta kwace wayar tunda Maryam din taki mata bayani se kuka. Tambayar saleemat tayi, saleemat tayiwa ammi bayanin komai harda boyewar da Aunty tace suyiwa Maryam. Ammi tace. “Ayya Allah yabata lafiya, amma meyasa Hajiya sauda tayi haka, aida tabari anfada semuje harmuma mudubota, amma yanzu bari na lallami Maryam ɗin, zankiraki anjima seki kaiwa gwaggonnata wayar” salimat ta amsa mata cikin girmamawa sannan ta kashe wayar. da kyar ammi ta shawo kan Maryam tayi shiru ta dena kukan. Kiran saleemat ammi tayi ita kuma ta kaiwa gwaggo. gwaggo jiki yayi sauki sosai tunda yanzu har zama tanayi da kanta, sedaifa bata magana ta zama shiru_shiru, dantafara saduda da duniyar, tasan alhakalin Maryam ne yafara kamata. jiya da Aunty takara dawowa dubata take fada mata Maryam tayi aure, da kuma yanda auren yakasance. Gwaggo seta sawa abun albarka, da dane kuwa da tuni tahau tijara tana masifar ita bazata yardaba sai’andawo mata da jikarta. Ta waya Aunty ta hada daddy da gwaggo, ya mata yajiki yakuma bata hakuri akan auran daya yiwa Maryam batare da saninsu su dangintaba. Gwaggo tace bakomai ahakanma sun gode, daddy besan dadine yacikataba na wayar datayi dashiba. se washe haƙora take kamar ba mara lafiyaba ita tayi waya da alhaji mai nasara Aunty ta cika gwaggo da kudi da kayan masarufi masu yawa kafin su tafi, ita da megidanta sukazo. Seda ammi suka gaisa da gwaggo sannan tabawa Maryam wayar. “Gwaggo!” Maryam ta fada cikin zumudi. cikin karaya da nadama gwaggo tace, “na’am Maryama” “gwaggo yajikinnaki?” “Dasauki Maryam” “sauki sosai, wlh gwaggo bansan baki da lafiyaba” Maryam ta fadi haka tana hawaye. “Nasani Maryam, nasan dakin sani datuni kinzo dubani, aike yarinyar arziki ce yar albarka” tsananin mamaki ne yacika Maryam dajin abunda gwaggo tace, kodai mafarki take kokuma tsananin ciwo ne yasa gwaggo saduda, har take kiranta da yar albarka, abunda bata taɓa ji gwaggon ta faɗa mataba tunda suke. Numfashi Maryam tasauke tace, “gwaggo zanzo kafin azumi insha Allah, nadubaki.” “A’a Maryama kizauna tunda kinga ba gari ɗaya mukeba, bayan sallah in Allah yakaimu sekizo, tunda naji sauki yanzu” dagewa Maryam tayi setazo amma gwaggo tahanata, tace ta bari ko cikin azumi ne tazo. Ammi ma ta roki gwaggo suzo koda a gobene, amma gwaggo tace suyi zamansu. Suna gama wayar ammi ta dubi Maryam tace, “ki kwantar da hankalinki gobe insha Allahu zamu sedai kawai su ganmu kwatsam.” Daɗine yacika Maryam gobe zata je taga gwaggon ta da saleemat dinta,kuma hankalinta ya kwanta dasukayi waya da gwaggo taji jikinnata da sauki, dan da saleemat ta fada mata ta dauka gwaggo magashiyyan take a kwance. domin Maryam bazataso gwaggo tamutuba, dan ita kadai gareta yar uwa ta jini sosai, shinema abunda yasata kuka dan idan gwaggo ta mutu bata da wani sauran dangi najiki dazata bugi kirji ta nuna. Da yamma bayan nagama aikina nadawo part din ammi. Kitso zatamun danbansan zuwa Kano kaina babu kitso, namanta rabon danayi kitso ma. Manya_manya nace ammi tamun dan tundaga tazar gashin nafara jin zafi. Aiko gaba-daya kannawa yaɗaure se zafi yakemun saboda nadade ba kitso. se tauna lips nake ina runtse ido. kafin magriba muka gama na mata godiya sosai nakoma part dinmu. Ina zuwa dakina na lambace mai akan kozanji sauƙin radadin dakan yakemun amma a banza. falo na dawo na zauna a kasa, ko dankwali bandauraba balle nasa ribbom nasaki jelar kitson har gadon bayana, dama shukune kitson. dafe kan nayi saboda ciwon dayakemun, nayi dana sanin yin kitsonnan ni banma taɓa yin kitso yamun zafi kamar hakaba. Da sallama dauke a bakinshi ya shigo falon, tsayawa yayi cak yana kallon gashin kan Maryam cikin mamaki. jin kamshin turarensa yasani dago da kaina dasauri dan bansan yashigoba, Banji sallamarsaba. kasa nayi da kaina gabana na faduwa ganin ya nufo inda nake. Fuskarsa a daure yace, “waya miki kitsonnan?” Kaina nakasa bandagoba nace, “ammi ce” “ammi?” Ya maimaita da alamun mamaki. gyada masa kai nayi. Yana kallon gashin yace, “ammin ce ta miki kitso da attachment?” dasauri nadago na kallesa. “Attachment kuma?” Namaimaita araina. A hankali nace, “A’a ba attachment bane” harararta yayi ganin ta raina masa hankali duk wannan tulin gashin tana nufin tace masa gashintane. zama yayi akan kujerar dake fuskantar ta, yadora kafa ɗaya kan ɗaya. Babu wasa a fuskarsa yace. “Dakkomun abun da ake kitso dashi” kallonsa nayi nace, “wanne abun kitson?” Banza yamata bekuma mata maganaba, shi bayason ayita jan magana shiyasa bekuma tambayarta me aka kara mata a kitsonba, amma yasan mezeyi yagane da kansa, kuma idan har karya ta masa seyayi maganinta, danshi baya kaunar musu. toni bangane meyake nufiba, “abun da ake kitso? Kibiya kenan yake nufi watakila” nafadi haka araina. batare da tunanin komaiba na mike nashiga daki nadakko masa kibiyar bayan nasaka dankwalina na rufe kaina. tsugunnawa nayi sannan na mika masa kibiyar, ina kokarin tashi kawai naji yasa hannunshi ya mikar dani tare da jawoni nafada jikinsa………✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button