Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

          ***************

“Sunana maryam,na tashi na ganni a hannun kakata,wadda ake kira inna.a unguwar darmanawa dake nan kano.innata itace ta haifi mahaifiyata.ita kuma mahaifiyata ta rasune a wajen haihuwata hakan yasa bansantaba.innata kawai nasani.mahaifina kuma tunda cikina,inna tacemun aka nemeshi aka rasa.dama badan kasarnan bane dan Niger ne.bashi da kowa yazo kasarnan neman kudi.anan cikin garin kano yake sana’arsa.innata tacemun,itadai batasan sanda suka fara soyayya da mahaifiyata ba,kawaidai da mahaifinta yace ta fito da miji tace shitakeso,duk da tarin masoyan datake dasu,domin mahaifiyata kyakkyawace.kyawun asalin Fulani.

Nanfa inna tace bata isa ta auri,Wanda ba’ason asalinsaba,ita kuma mahaifiyata ta dage dole seshi takeso.inna kuma ta kafe tace sedai ta zaba,ko shi ita.amma mahaifiyata taki hakura dashi,har ciwo ne ya kwantar da ita.ganin tana kokarin mutuwa mahaifinta yace yabata shi.ita kuma inna tace be isaba.sedai idan mahaifiyata ta mutu.shikuma mahaifinta yace shiya haifi maryam,dan haka Wanda takeso ze bata baze mata auran doleba,kokuma yanaji yana gani ita kadai din dayake da ita yarasata.dama ita kadaice ‘yarsu.inna tanaji tana gani aka daura auran mahaifiyata da mahaifina.inna tacemun,kwata kwata batason auran tayi iya yinta kar ayi auran,amma Allah yayi dole se’anyi.haka inna ta hakura,amma tace babu ita babu mahaifiyata. Bayan bikin befi da wata dayaba,Allah yayiwa kakana rasuwa.halin dasu inna suka shiga baze misaltuba.a lokacin mahaifiyata tayi Dana sanin bijirewa inna,tazo tana kukanta ta nemi yafiyarta domin ta gane duniyar ba gidan zama bace.itama inna a lokacin jikinta yayi sanyi,hakan yasa ta sassauta mata,amma bata sakko dukaba.a lokacinma tanata fama da laulayin dan karamin ciki.

Haka sukaciga da rayuwa,tsawon shekara uku.inna tacemun mahaifiyata bata taba zuwa ta kawo mata karar mahaifinaba,akan ya mata wani Abu ba daidai ba koya muzguna mata.kana ganin yanda suke rayuwama,kasan cikin kwanciyar hankali da jin dadi sukeyinta.duk da mahaifiyata Daga ta samu ciki baya wuce wata uku ya bare.amma kokadan mahaifina be nuna damuwarsaba,ko kuma ya canzawa mahaifiyata.ita cema take damuwa akan haka, shikuma yana kwantar mata da hankali.

Tayi barin ciki,yakai biyar Allah yayi dai zanzo duniya. Mahaifiyata tasha wuya akan cikina tamkar zata mutu haka take shan wahala.hakan yasa inna ta dakkota ta dawo da ita gidanta.duk shima suna tunanin ze bare kamar sauran.amma abun mamaki ana wuce wata uku,hudu se ciwo ya dauke,ta komar sumul da ita.ta koma gidanta suka cigaba da rainon cikina ita da mahaifina.soyayya sosai mahaifina yake nunawa cikin,tun lokacin yaketa siyan kayan haihuwa. Saboda murnar wannan cikin ya tsaya tunda haryakai wata shida.mahaifina dama akusuwar kantin kwari yake a shagon wani uban gidansa.inna tace mun,yana samu sosai.yanada rufin asirinsa.wata rana yaje kasuwa mahaifiyata taga har dare bedawoba.shida yake dawowa kafin magriba.hankalinta ya tashi,ta kira duk Wanda take tunanin suna tare an tabbatar mata daya taho gida lafiya kalau.shiru_shiru tana jiransa,amma har wajen goman dare shiru,bedawoba.zarar hijabinta tayi ta nufi gidan inna tana kuka ta sanar mata.itama inna ta girgiza sosai,amma ta daure ta kwantar wada mahaifiyata hankali.shiru_shiru har cikin dare bedawoba.abun kamar wasa har washegari.duk inda ake tunanin za’a sameshi anje bayanan.hanakalin mahaifiyatafa ya tashi bataci batasha se aikin kuka.tun ana saran ganinsa har kwanaki suka shude babu shi,babu labarinsa.nan maganganu suka dinga yawo akan ya gudu yabar mahaifiyata,dama abunda yasa yake zaune da ita danbata haihu bane,yanzu kuma tunda yaga zata haihu shine ya gudu ya barta.bayason wahalar ‘yaya.tundaga ranar mahaifiyata ta koma,bata da aiki se kuka,tun inna tana rarrshinta harta zuba mata ido.haka tacigaba da rainon cikina cikin bakin ciki.ranar wata juma’a da yamma ta haifeni.a gida ta haihu.bayan an gama gyarata aka miko mata ni.inna tacemun kamarmu daya,hakan yasa ta kuramun ido tana kallonna.idanuwanta cike da hawaye.lafiya kalau ta haihu,amma bayan befi awa biyuba, wani ciwon cikina me tsanani ya kamata.ana kokarin kaita asibiti,tace kada su wahalar da Kansu ita mutuwa zatayi,amma tabar wasiyya,idan Allah yarayani a bani wata takarda data rubuta tana cikin kayanta.kuma asamun sunanta wato maryama,saboda shine sunan da mahaifina yace mata zesaka idan ya haifi diya mace.su inna basu kulataba da ita da maganganunta,suka dauketa zasu kaita asibiti domin sunyi tunanin zafin ciwone yasata fadar haka.amma kafin sukaiga asibitin Allah ya mata rasuwa.

Inna tayi kuka,tamkar ranta ze fita.mutuwar tilon yartata bakaramin dukan ta tayiba.ta gane rabonane yasa mahaifiyata ta dage seta auri mahaifina. Hakan yasa tayafe mata duniya da lahira.ita kanta shedace akan mahaifiya mutumin kirkine,kawai dai matsalarsa rashin sanin asalinsa.inna ta rungume ni,tacigaba da rainona cikin so da tsantsar kauna,tana jina tamkar maryam dinta data rasa.inna bata boyemun sunaba maryam take kirana dashi.

Nataso cikin gata da kulawa a wajen innata.innata bata rageni da komaiba.abincin siyarwa,dasu sobo da kunun aya, shine sana’ar da inna takeyi take rufa mana asiri.duk da girma yafara kamata.komai nakeso innata tanamun,tasani a private school. Tare da islamiyya.Burina arayuwata,inyi karatu me zurfi Insamu aikinyi,in hutar da inna Daga wannan wahalar datakeyi,kullum tana bakin wuta.inna bata da ‘yan uwa a garinnan,yan uwanta duk suna can kauye a garinsu.iyayenta kuma Allah ya musu rasuwa. ‘Yar uwarta guda dayace,da suke uwa daya,uba daya wato gwaggo.

Amma nidai tunda naso so daya nataba ganin gwaggo a gidan innata.innata batamun irin rikonnan da’ake cewa rikon kakaba,ta shagwabaniba kota sangartani.ta bani tarbiyya ingantacciya.tun ina karama take nunamun rayuwa,takemun nasiha,akan narike mutuncina.nakasance me hakuri a duk halin Dana shiga.bansan kowaba,se innata.itace uwata itace ubana,itace dangina.itace gatana.shakuwa me karfi,tare da tsantsar kaunace a tsakanina da innata.dominni a lokacinma saboda yarintata,bansan ba itace ta haifeniba.innata macece,ta mutane saboda kirkinta da mutunta dan’adam.

Dogon Numfashi,naja ina duban baaba talatu,nace “zan takaita miki labarinane,saboda yanayin lokaci.domin idannace zan fayyace miki komai,semu kwana anan bangama mikiba. “Tom shikenan maryam,kici gaba domin inason jin karshen labarinnannaki.

“Wata rana,nadawo Daga school, da misalin karfe biyu na rana.a lokacin shekarata goma shabiyu. Ina J.S.S 1. Da sallamata na shigo gidan da murnarta ina kwalawa inna kira,kamar kodayaushe,idanna dawo.turus na tsaya ganin banga innata a kitchen ba,agurin saida abincin ta.babu alamun ma tayi girkin yau.dasauri na nufi dakin da muke kwana ina kwala mata kira.Kudundune na hangota akan gado ta lulluba da abun rufarmu.jakar makarantata na cillar na nufi kan gadon.ina cigaba da kiranta.yaye bargon data lullaba nayi,jikinta se rawar Dari yake.wuyanta na taba naji zafi zau. “Innata baki da lafiya meyasameki meke damunki.na tambayeta kwalla na taruwa a idona.Bakinta ta fara motsawa alamun tanason tace wani Abu,amma maganar taki fita.jikinta serawa yake hakoranta na hadewa kamar me jijjiga.bantaba ganinta cikin ciwo irin hakaba.kuka na farayi ina girgizata.tare da tambayarta abunda yake damunta,amma inna ta kasa magana.abunda yafi tsoratani yanda naga idanuwanta sun juye.gashi gida ba kowa dagani se ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button