Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kiran sallar magriba da ladanin masallacin gidan ya kwalla ne yasani nufar kofa daniyyar fita,amma kamar saukar aradu naji wata daddadar murya,amma a dan kaurare take. “Ki hadomun wani” tsayawa nayi cak nibanyi gababa ni banyi bayaba,saboda matukar firgita “Ashe dama yana magana na tambayi kaina,ga zahiri nan kuma,wata zuciyar ta bani amsa. too!, shiko wannan wanne irin mutum ne,daga ganinsa zeyi murdadden hali,da muskilanci bana wasaba. Motsin bude kofar toilet yasani juyowa da sauri,harya shige toilet dinsa.da sauri nima na juya na fice daga dakin.cikin sauri_sauri, gudu_gudu na fice daga part dinnasa gaba daya. Ina kokarin shiga part din mommy yaya sadiq yana fitowa da alama masallaci zashi. “Maryam.lafiya naganki a firgice kuma kin Dade,tundazu naketa zaman jiranki zamuyi wata magana.tattaro nutsuwata nayi ina murmushin yake nace babu komai yasadiq kawaidai ina saurine zanyi sallah. “Anya kuwa maryam? Yakara tambayata yana tsareni da idanuwansa. “Dagaske yaasadiq babu komai. “Toh shikenan ni zan tafi masallaci idannadawo zamuyi magana.kai kawai na gyada masa na wuce ciki. Babu kowa a falon duk sun fice.ajiyar zuciya na sauke ina godiya ga Allah. Cikin mintuna kalilan na tafasa masa coffee din,Allah yasoma bansha wahalar ganinsaba. A wani flaks din na zuba masa. Acikin hijabina na zura,ina addu’ar kar Allah ya hadani da kowa harnaje na dawo.

Cikin ikon Allah kuwa bangamu da kowaba,se tsirarrun masu aiki.wlh na matukar gajiya,zaryarnan danayi ga yunwa jinake tamkar zanci babu,ga nauyin sallah akaina dan har an idar. Baya dakin,alamun bedawo daga masallaciba. Ajiyar zuciya na sauke,ajiye masa flkas din nayi. Se’a lokacin na samu nutsuwar karewa dakin kallo. Bansan yazan misalta muku kyawu da tsaruwar dakinba,amma fa ya bala’in haduwa. Juyawa nayi dan karyazo ya sameni,na fice daga dakin. Ina sauka falon kasa naci karo dashi wani na biye dashi abaya,nandanan zuciyata ta hau luguden bugu,tafiya nafara yi tamkar kazar da kwai ya fashewa aciki,cikin matsanancin tsoronsa. Ko kallon inda nakema beyiba yayi hayewarsa sama. Na bayannasane kawai yamun magana.gaishesa nayi muryarsa namun kamar na Santa,ko kuma nataba jin irinta,amma nakasa tuno inda nasantan.

Kawar da tunanin nayi daga raina na koma part dinmu. Seda nafara cin abinci sannan nayi sallah,abincinma kadan naci saboda yunwar taci ta cinyeni.falo na dawo na tarar da yaa sadiq,shikadai a zaune. Yana latsa wayarsa. Zama nayi a kusa dashi akan kujera,saboda yanzu nariga na saba dashi. ina maida numfashi. Kallona yayi, “anya kuwa lafiya kike maryam naga gaba daya dukkin canza. “Bakomai fa yaasadiq da gaske,gajiyace kawai Kasan yau munsha aiki. Gyada kai yayi yace. “Hakane dama maganar danakeso muyi akan karatunkine,a ina kika tsaya,akaratunki kinga zaman gidan haka babu dadi sekicigaba ko? Dasauri na dago ina kallonsa saboda jin yasosomun inda yakemun kaikayi. Cikin matukar murna nace,”yaya! Makaranta kuma,kana tunanin hajiya zata bari. Murmushi yayi yace “indai mommy ce bata da matsala,zata bari. Dafe kirjina nayi cikin matukar murna,Ashe inada rabon cigaba da karatu a duniya,Ashe idan Allah yaso zan iya cika burina na duniy…katsemun tunani sadiq yayi, “ki shirya zuwa Monday zamuje school din se’asan yanda za’ayi. ina shirin magana mommy ta fito daga dakin ta. Sallama tayi mana ta zauna akan kujera. Dubanta yaasadiq yayi. “Mommy ina mata maganane akan zanmaidata school zaman haka babu dadi. Kamar daga sama naji muryarta tana tambayata. “A wanne class ta tsaya,akaratun?. Satar kallonta nayi nace “ss 1,amma yanzu yan mate dinmu this year zasuyi candy.gyada kai kawai tayi batacemun komaiba.tana bina da kallon data saba bina dashi,Wanda bansan kona meneneba. Yaasadiq ne yace. “Babu matsala idan mukaje za’asan yanda za’ayi. Godiya na masa,hajiyama na mata na tashi na koma daki.kamar na taka rawa dan murna. “Gaskiya yaasadiq yamun komai arayuwa,idan yamaidani makaranta,yataka babbar gudunmawa arayuwata.bazan taba mantawa dashiba,na bashi babban matsayi a zuciyata.gashi dadin abun hajiya bata hanaba. Wazanwa wannan daddadan albishirdin. Saleemat ce ta fadomun arai. Allah sarki yar’uwata me kaunata,gaskiya gobe zangwada tambayar hajiya kozata barni naje unguwarmu.ko minti talatinne nayi na dawo,Allah yasa ta barni………

Dauriya kawai yakeyi amma kafarsa tana masa zafi kadan_kadan. A falo suka yada zango shida lukman.dubansa lukman yayi yace. “Abokina wai meyake damun Kane naga gabadaya ka canza. Lumshe idansa kawai yayi bece komaiba, wani Abu yake tunani aransa,game da yarinyar dazu. Mikewa yayi ya shiga dakinsa ya dakko flaks din data kawo masa. Dakansa ya dakko musu cup,ya tsiyaya musu.shi mutum ne me tsantsani,da kyankyami.amma kwata_kwata seyaji baya kyankyamin yarinyar. Kodan bega wata kazanta a tattare da ita bane. yafison shan coffee da zafinsa,kurba daya ya masa. yaji kamar ba kalar Wanda yasabasha kullum ba, ya masa dadi sosai.haka yaita kurba yana lumshe ido se cup din kawai ya dire.hira sukayi sosai da amininsa,amma karfin hirar lukman ne yakeyi……

Danazo serving dinsu banganshiba, hamdala nayi araina danbansan da idon dazan kallesaba.gani daya dana masa wani mugun tsoronsa yakamani.ga wasu idanuwansa dayake tsare mutum dashi,duk subi su rikirkitaka.inajin suhailat tana tambayar mommy shi,mommy tace,yace zeyi dinner sa a part dinsa.nidai ina gama abunda zanyi na wuce dakina.yau kam bansamu rabon zagi daga kowaba kuma bansan daliliba……

Suhailat, suna gama dinner ta nufi part dinsa.yana zaune a bakin gado ya tasa laptop agaba,yanata latsawa. Da sallama ta shiga bedroom dinnasa,dan tasan halinsa idan batayi sallama cin ubanta zeyi.a saman lebbansa kawai ya amsa batare da dago ya kalletaba.zama tayi agefensa tana masa wani shu’umin kallo tamkar zata cinyesa.

Tana matukar son mustapha arayuwarta,ta matsu ta karasa karatu asha bikinsu,yazama mallakinta ita kadai.bata fuska tayi cikin shagwaba tace.”yaya baka ganni bane.dagowa yayi ya kalleta yana sakar mata tsadadden murmushinsa me zautar da ita.ido daya yakashe mata bece mata komaiba.ya maida hankalinsa kan aikinsa.kwantar da kanta tayi a kafadarsa tana shakar daddadan kamshinsa. Ya dauki tsawon 15 minutes sannan yakashe laptop din.hira sukayi sama_sama.tana fada masa yanda tayi missing dinsa,murmushi kawai yake mata.ita kadai taketa masa surutu. Seda yace mata yau agajiye yake,yanason yayi bacci. sannan ta barshi badon tasoba ta tafi.

Missed call din kamal ta gani har 5,bin bayan kirannasa tayi amma shima bedaukaba. ajiye wayar tayi ta shige toilet tayi wanka.kayan bacci tasa,ta haye luntsumeman gadonta. tafara sana’artata wato chatting. Kullum seta raba dare sannan take bacci,banda chat da samari babu abunda takeyi, suyi ta hirar batsa.kokuma video call da kamal.kiranta kamal yayi sukasha hira,akarshe yasanar mata da zezo gobe ya gaida mum dinta.batare da tunanin komaiba ta amince masa yazo gidannasu……

Washegari,ta kama juma’atu babbar rana. tunda na tashi sallar asuba bankomaba,sonake nayi aikina da wuri naje gida.karfe 8 nagama shara da moping gyaran dakinsune kawai banyiba da wanke_wanke. Kukune ya fito daga kitchen yana jera kulolin abinci akan dinning.gaisawa mukayi dashi,hira yafaramun cikin gurbatacciyar hausarsa. Na lura shi mutum ne me shegen surutu ni kuma bana shiri dame surutu. Amma shi yana bani nishadi saboda hausarsa dariya take bani. Wajen 8:30,samarin gidan suka shigo falon,mikewa tsaye nayi na gaishesu,kamar kodayaushe babu Wanda ya amsamun se yaya sadiq. direct kan dinning suka nufa suka zauna,nima kasa na samu na rakube. Cikin wata uwar tsawa haydar yacemun, “ke mahaukaciyar inace kina ganinmu, mun zauna amma bazaki taso kiyi serving dinmuba. Dasauri na mike ina basa hakuri,saboda naga mommy da suhailat nasu fitoba shiyasa banyi yunkurin zuba musuba. Ina cikin zuba musu mommy ta fito daga dakin ta.gaisheta nayi,kamar kodayaushe ta amsamun babu yabo babu fallasa. Itama zuba mata nayi na koma gefe ina jiran hamshakiya. Mintuna kadan ta fito itama,cikin shrinta. Bakar abayace ajikinta wadda ta matukar haska farar fatarta.tayi kyau sosai. “Ina kwana,aunty suhailat” wani mugun kallo ta watsomun “daban kwanaba,zaki ganni” kasa nayi da kaina,meye lefina a ciki kuma danna gaisheta ita komai Lefine agurinta. Tana zama itama naje na zuba mata break dinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button