Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ina kwance bacci yaki daukata,aunty tashigo dakin hannunta dauke da plate da ruwa. Ajiyewa tayi tahau tashina atunaninta bacci nakeyi. Tashi zaune nayi, tace nasakko naci abinci nasha magani, senafi jin dadin baccin. Banmata musuba na sakkowa naci abincin kadan, aunty taitai nakara nace mata nakoshi, maganin tabani nasha nakoma na kwanta, itakuma tafice tanamun addu’ar samun sauki. Har bacci yafara daukata Aliya tashigo dakin, wayarta tasamu a kunnena wai yaya sadiq zemun magana. Karba nayi na rike, sallamar dayamun na amsa. Cikin murayata dako fita batayi saboda baccin danakeji. Sannu yamun, yakuma bani hakuri akan abunda yafaru, nuna masa nayi babu komai, mukayi sallama nabawa aliya wayarta, nagyara kwanciyata,nakoma baccina………✍️

BY
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

1️⃣9️⃣

……….Da matukar bakin ciki suhailat tayi daren yau, gashi ita babbar damuwarta fushin mustapha, idanunta kawai hasko mata sanda abunda yafaru sukeyi,yanda taga ransa ya matukar baci, ita bataga wani abun bacin rai acikin abunda tayiwa maryam ba, kuma koma metayi mata aiduk akansane. Juyi tayi akan makeken gadonta datake kwance, kusan 12 nadare Amma babu bacci Sam a idonta, tun dazu take kiran wayarasa taki shiga,gashi texts take tura masa naban hakuri tare da kalaman soyayya, amma shiru babu reply. Tafin hannunta takai ta shafi kuncinta, haryanxu tanajin wani dimmm akunnenta na Marin datasha. Mikewa zaune tayi saboda wani kunci dayaziyarci zuciyarta. “Wai yanzu akan wannan kucakar yarinyar ya mareni” ta fadi haka a fili cikin tsananin takaici, kwafa tayi aranta tana kissima irin muguntar dazatayiwa maryam kala kala a gidannan. Kiran wayarta da’akayine ya katse mata tunanin ta, koda bata dubaba tasan kowaye, kamal ne. Banza tayi da wayar, shikuma yayi ta nacin kira, tsaki taja a fili. Sannan ta tashi ta dakko wayar, tayi picking, suka fara hirarsu wadda rabi duk batsace,wayartasu da kamal dinnema tadan rage mata damuwa……

Abangaren mustapha kuwa besan sanda bacci yayi awongaba dashiba. Wajen 1 na dare, yafarka a matukar firgice bakinsa dauke da addu’a saboda wani mugun mafarki dayayi,wanda yakasa fahimtar me mafarkin yake nufi. Gaba daya yahada wata uwar zufa, duk da fankar dake kadawa a dakin, danya kashe a.c tun kafin yakwanta. Sosai mafarkin ya firgitashi amma yakasa tuno komai acikin mafarkin. Ajiyar zuciya yake saukewa akai_akai, abunda kwakwalwarsa ta iya tuno masa shine yaga wata yarinya a mafarkin, da wasu mata da wani namiji, kuma duk kamar yasansu a mafarkin,amma yakasa tunosu azahiri. Korar tunanin mafarkin yayi daga ransa, dan mafarki ba gaskiya bane. Mikewa yayi cikin sanyin jiki ya nufi toilet yadauro alwala,yadawo yafara jero nafilfili kamar yadda yasaba a kowanne daren Allah……..

Abangaren sadiq kuwa, tausayin maryam gabadaya yacika masa zuciya, baya kaunar halin mahaifiyarsa dana yan’uwansa kokadan,dandai babu yanda zeyine. Da tunanin maryam ya kwana aransa cikin wani irin bakon yanayi me wuyar fassaruwa agareshi……..

WASHEGARI

Mustapha kamar yadda yasaba, kullum bayan yafito daga masallaci ya nufi part din mommy, dakin mommy yafara shiga suka gaisa sannan ya nufi dakin aunty. Aunty na zaune akan darduma tana lazimi yashigo dakin, zama yayi agefenta. Yana fadin, “asamu a addu’a aunty” murmushi aunty tayi tace, “insha Allah, addu’a ai kullum cikin ymuku ita mukeyi.” Cike da kaunar kanwar mahaifinnasa yagaisheta. Amsawa aunty tayi tare da gyara zama tace, “dama tun jiya inason magana dakai, sekuma bamu haduba” maida hankalinsa yayi duka ga auntyn amma bece komaiba. Cigaba da magana aunty tayi. “Mustapha meyasa jiya ka mari suhailat, nayi mamaki gaskiya dan nasan hakan ba halinka bane?” “Aunty nikaina bansan sanda na maretanba,Abunda tayine ya matukar konamun rai shiyasa” yafadi ahaka muryasa adakile. “Shikenan mustapha amma adai, kiyaye gaba, dan wataran ma’aurata zaku zama kaida ita, jirama nake yaya yadawo kasarnan, ayi maganar aurenku, shekarunku sunja,karatun ta karasa adakinta. Danyanzu ko su haidar da zannurain sun isa aure, balle kuma kai.” Kwantar da kansa yayi ajikin aunty yace, “duk yanda kikace haka za’ayi little mom, Allah yatabbatar mana da alkhairinsa.” Shafa kansa aunty tayi, tace “ameen” cike da tsananin kaunarsa da tausayinsa, tarasa meyasa takejin tausayinsa aranta, kuma tun yana karami takejin hakan akansa, alhalin babu abunda yanema yarasa arayuwarsa. shiyasa duk miskilancinsa seda tajawoshi jikinta sosai, haryayi matukar sabo da ita, yake kuma sanar mata da duk wata matsalarsa. Hira suka dan taba akan kasuwanci da kuma halin rayuwa, duk da karfin hirar aunty cekeyi. Sannan yatafi….

Duk murna da dokin danakeyi na zuwa school, duk babu dana tashi saboda da bacin rai na kwanta. Ciwon kan dake damuna yasauka sosai, yanayin danake jima kafin na kwanta duk babu, amma zuciyata ce sam babu dadi. Ina idar da sallar asuba, nafara ayyukana, sharar falo nayi da mopping sekuma wanke_wanken kayan da’aci abinci dadaddare. Inagama wanke_wanken nashirya komai tsaf, tare da shareshi shima nayi mopping. Ina kokarin fita daga kitchen din, kuku yashigo, sama_sama muka gaisa dashi bakamar kullumba dayake tsayar dani da surutunsa, duk da hausarsa ko fita batayi,amma munashan hira dashi. harna koma dakina aliya baccintatake, dama tana idar da sallah ta koma. Toilet na nufa na wanke, sannan nayi wanka. Uniform din makarantar na dakko da nufin shiryawa, riga da wadone rigar har gwiwa, se wani karamin hijabi iya kafada.

Tsayawa kawai nayi ina kallon kayan, ina tunanin tayanda zansakasu, harna iya fita dasu ahaka. Ganin lokaci yana kuremunne yasa kawai na daure nasaka, sunkoyi dass ajikina, tsayawa nayi agaban mudubi ina karewa kaina kallo, kayan sunyimun kyau sosai,sedai rigarce ta kamani daga kirjina. Dankwali na daura,nadakko hijabin danayi sallah nafito falo. Kuku begama breakfast ba, gashi har 7/30 tayi. Babuma Wanda yafito acikin gidan. Dakin aunty nanufa, knocking nayi tabani izinin shiga. Da sallama nashiga. Zama nayi akan carpet din dake gaban gadon, ita kuma aunty tana kan dadduma da’alama karatun alkur’ani takeyi, saboda kur’anin dana gani agabanta. Gaisheta nayi ta amsamun cikin fara’arta. Bayan mungama gaisawarne, cikin ladabi nadubeta nace, “Aunty dama nashiryane zamu tafi makarantar, kuma naga haryanzu ko abincin kuku begama hadawa balle nayi serving dinku, kuma yaya sadiq 7/40 yacemun zamu tafi.” “Badamuwa maryam, kije kutafi schl din, tunda kinga yau zaki fara zuwa karki fara da latti, aliya tayi serving dinnamu, amma kafin ki tafi kishiga kisanar da aunty atika” “tom aunty nagode senadawo” “yawwa maryam, Allah yakiyaye yabada sa’a, kikula sosai kinji, banda kawaye barkatai,kiyi karatunki kawai” “insha Allah aunty zankiyaye” nafadi haka ina mikewa, tsaidani aunty tayi, hang bag dinta naga ta dakko, kudi ta dakko naira 500 ta mikomun. Girgiza kainayi nace, “kibarshi kawai aunty” batarai aunty tayi tace, “bansan musu maryam, bakici komaiba zaki tafi sannan kuma kiki karbar kudi, kiduba inda ake ajiye kayan snacks a kitchen kidauka kihada da yoghurt wannan kudin kuma kyayi break dashi” amsa nayi namata godiya nafice, cike da kaunarta dakuma yabon halinta. Cikin tsoro nanufi dakin mommy danbansan da fuskar dazata tarbeniba, amma abun mamaki senaganta kamar babu abunda yafaru, takarbeni kamar kullum fuskarta babu yabo ba fallasa, dana fada mata abunda kefaruwama tace muje bakomai, Allah yabada sa’a. Kitchen nashiga na dakko cake da yoghurt kamar yadda aunty ta umarceni, dakina na koma domin dakko school bag dina. Aliya natar tana waya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button