Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin baccina naji ana kiran sunana tare da tabani, ahankali na bude idona dasuka sauya kala saboda bacci, nace. “Uhm” muryar aunty naji tana fadin, “maryam, kitashi kiyi sallah baccin ya isa haka, har 2 tawuce fa” mikewa nayi zaune cike da mamakin dadewar danayi ina baccin ina yar mika nace, “aunty har 2 fa tawuce kikace banmasan nadade hakaba” “aitun dazu nashigo naga kina tashan bacci,nima baccinnayi banjima da tashiba” “bari naje nayi sallah aunty” nafadi haka ina sauka daga kangadon har yanzu idona begama budewaba kamarma inkoma baccin haka nakeji” bakina na wanke na dauro alwala nafito nayi sallah, har lokacin aunty tana kishingide akan gadona tana danna waya. bayan na idar aunty tadubeni tana murmushi tace, “kinjini da mutuniyar taki, wai yaushe zandawo kokuma ita tabiyoni” murmushin nayi nima nace, “gaskiya dai aunty dakin taho da ita, yanzu se ita kadai agidan ko?” “Maryam makaranta shiyasa bantaho da itaba,amma jibi Friday zance yayanta yakawota seta koma ran sunday, kuma bata gidama tana gidan kanwar abbansu dayake bamu da nisa” “yawwa aunty, harnaji dadi dakikce zatazo Allah yakaimu jibin” “ameen” gyara zama nayi natambayi aunty abunda yake damuna arai dafadin”aunty yame jikin kuwa” “jiki da sauki maryam, daga gurinshi nakema nabiyo tanan,yau jikinnashi yayi kyau sosai” gyada kai nayi nace, “Allah ubangiji yakaro sauki,amma aunty meyasa ba’abashi rubutu kokuma adinga masa tofi aruwa ana shafa masa ajiki” “nima dafarko nayi wannan tunanin maryam,amma ganin malam yabashi na shafawa ajikin yasa banmaida hankali akan adinga masa hakaba, kuma shima yabada tofin ana diga masa abaki” “hakane aunty, amma ni aganina addu’a bata yawa, malaminmu na islamiyya ya turamun ayayoyin da ake karantawa na rokiyya a wayata wanda SUDAIS ne yake karantawa,kullum kafin nayi bacci sena kunna naji harna haddacema yanzu, meze hana adinga kunnamasa shima yanaji, nikuma zantofa aruwa se’abashi yasha kokuma ashafa masa ajiki.” Cikin gamsuwa da bayanan maryam aunty tace,gaskiya maryam kinkawo abu me kyau,aidamu bamuyi tunanin koda karatunne adinga kunnamasaba, wannan shawarartaki tayi sosai maryam, mungode Allah yasaka da alkhairi, anjima bayan la’asar idan zani semuje tare a fara masa.” “Bakomai aunty fatanmu kawai,Allah yabashi lafiya” hira mukacigaba dayi da aunty, zuciyata fess da farinciki zandinga ganin heartbeat kullum, kuma da izinin Allah seya samu rangawame aciwon dake damunsa dan ayar Allah bakarya bace,kuma alkur’ani warakace ga dukkan kowanne ciwo.

Kamar yadda aunty tace, dayamma mukaje na kunnamasa karatun adakinsa ita kuma takawomun ruwa a cup na tofa aka shafe masa jikinsa dashi. mommy da aunty tafada mata abunda za’adinga yiwa mustapha batace komaiba, daddy kam yayi farinciki sosai yayta sawa maryam albarka. Tundaga ranar kullum senaje namasa safe da dare,wataranma aunty tana falo nikadai take bari adakin inyi ta kallonsa. Kuma alhamdulillah jikinnasa yanasamun sassauci, dan wannan kumburin jikinnan nasa duka babu yanzu, saidaifa wani abun mamaki, duk sanda nazo nakunna masa karatun kuma akashafa masa ruwan tofin ajikinsa sejikinsa yayi sanyi kamar nakowa, amma washegari, ina kara zuwa za’a masa se’aji zafin jikinnasa yadawo zafi zau se ankuma masa yake tafiya. Su aliya sunzu sunyi kwana biyu ita da yan’uwan abbansu da yayanta,umma da saleemat ma sunzu harda gwaggo, duk sunzo dubiya, muna waya da saleemat ne nakefada mata ciwon yaya mustaphan, shine tafadawa umma, umman tace kodan kirkin sadiq zasuzo suduba yayansa,shine tayiwa gwaggo magana sukazo tare. Gwaggo anzo gidan alh.menasara hankali ya kwanta, mommy kam bata wani kulasuba daga gaisuwa shikenan, danma aunty tananan itakam ta karbesu hannu bibbiyu faran_faran.

Yau asabar wanda yakama daidai da saura kwana 2 mukoma school, bayan nadawo daga islamiyya karfe 11/30 muka nufi part dinnasa nida aunty, dama a irin wannan lokacin kullum muke zuwa, kafin muje yaya sadiq yagama masa na malamin da’ake masa. A bakin kofa muka tarar da yaya sadiq ze fita, gaisawa mukayi aunty tayi gaba tabarni dashi. “Malamata” yaya sadiq yafada cikin sigar tsokana, batarai nayi nace, “kaganga ko, zaka kafara kenan” murmushi yayi yace, “to ba malamar bace, karya nayi” “a’a niba malama bace dalibace me koyo” “toh shikenan na yarda, gobefa zanwuce me’aza bani dazan dinga tunawa dake kullum da kullum inji kamar muna tare.” “Mekakeso kafada mana se’inbaka” “kinyarda infadi koma mene zakiban” “insha Allah indai ina dashi zanbaka” “tom shikenan kibari segoben idan zamuyi sallama zanfada miki, danse yamma zan tafi,” “Allah yakaimu goben lafiya” “ameen, malama sekin fito” yafadi haka yana dariya. kin kulasa nayi nayi tafiyata, inajinsa yana cigaba da dariyarsa. A falon saman na tarar da mommy, hakimce akan kujera tanata latsa waya hankalinta kwance, gaishenayi tare da mata yame jiki nashige daki. Aunty tana gaban gadon ta rafka tagumi tana kallonsa nashiga dakin da sallama,amsamun tayi batare data dauke idonta daga kallonsaba. wayata dake hannuna na kunna, nasaka karatun, dai_dai saitin kunnensa anan ake ajiyemasa nannaje nasamasa, nadawo nabude fridge din dake dakinsa na dakko ruwa nazuba a cup, nazauna inabin karatun azuciyata ina tofawa acikin ruwan, aunty ma bin karatun takeyi, karatun yanada dan yawa, munfi rabi munma kusa gamawa aunty tafita zata amsa waya, harna gama tofawa karatun yakare aunty bata dawoba, karambani nayi nadau cup din zanshafa masa ruwan ajiki, dama aunty ce take shafa masa kullum. ahankali nazauna abakin gadon bayan na ajiye cup din agabana akasa, kura masa ido nayi cikin tsananin kaunarsa, wani shaukin sansa da tausayinsa na mamaye dukkan jini da tsoka najikina, ahankali natsiyayo ruwan ahannuna nafara shafa masa a fuskarsa, zuciyata na luguden bugu tamkar zata faso kirjina tafito, wani irin bakon yanayi naji ya bakunci dukkan gabban jikina wanda bansan yazan misalta muku shiba, lumshe idona nayi lokacin danake shafa masa ruwan a wuyansa zuwa saman kirjinsa, wani irin laushine da fatarshi gata da santsi, hannayensa duka biyun nashafa masa tare da kafafunsa, dama iya inda ake shafa masa kenan. wayata dake gefensa na dauka na tsaya kawai ina kallonsa, zancen zuci nakeyi nikadai akan koyaushe bawan Allah zetashi yacigaba da rayuwa kamar kowa se Allah. hannun haguna dake rike da wayata nadafa fuskar gado dashi, hannun damana kuma nasashi asaman goshinsa ina shafe masa ruwan dayake gurin, ban’auneba kawai naji wayata tafada ta bayan fuskar gadon. da sauri na dago cikin takaicin fadawar wayar, “yanzu ni tayaya zan iya dakko wayata ana gurin.” nafadi haka a fili cikin rashin sanin abunyi, niba’abun infadawa aunty wayata tafadaba tacemun meyakaini gurin, balle kuma mommy. shiru nayi inatunanin mafita, can wata dabara ta fadomun nakoma karshen fuskar gadon na leka sena hango dan kyalli kwabar wayata amma tayimun nesa bazan iya dakkowa tananba, dawowa nayi nahau kan gadon ina kallon fuskar yaya mustapha, ahankali nakai hannuna duka biyu na matsar dakansa gefe yakoma karshen filon dayake inda nacire kannasa nanna dora gwiwata na leka fuskar gadon, adaidai nan kuwa na hango kyallin wayartawa amma bazan iya daukowaba, hakura nayi nabar leken, nazo zandaga gwiwata kawai naji wani abu metudu acikin filonnasa, cike da mamaki nazare kafata duka nasaka hannuna atsakiyar filon ina ta bawa, wani abu naji nariko ahannuna ta cikin rigar filon kamar dutse. mamakine yakamani na mene kuma zekawo dutse cikin filo, Allah sarki bawan Allah yana kwance abu yanata damunsa aka amma saboda babu bakin magana baze iya fadaba. ahankali cikin lallabawa nakara saukar dakansa kasa daga kan filon gabadaya, na juya filon tabaya nazuge zip din rigar filon nazira hannu na dakko abun. ajiye abunnayi akan gadon nazuge zip din namaida filon daidai nakara kamo kannasa nadora akai ahankali. Abunda nadakko nakurawa ido, abun kamar kaskon turaren wuta yanayin shape dinshi,amma karamine sosai harda murfinsa kamar tukunyar dandankuwa da yara sukeyi da kasa. sakkowa nayi daga kan gadon nadauki abun ahannuna, wani dogon numfashi naji yaya mustapha yasauke harya kusa tsoratar dani, dasauri na kallesa naji yanata sauke ajiyar zuciya tare da numfarfashi. ahankali kuma naga fatar saman idonsa tana motsi kamar ze bude ido, dasauri nafita da gudu zuwa falo ina kwalawa aunty kira, aunty dake waya da abbansu aliya takatse wayar dasauri jin kiran da maryam take kwala mata, “lafiya maryam” aunty tatambayi maryam tana mikewa tsaye gabanta yana faduwa. cikin haki nace, “aunty zokigani naga idonsa yana motsi” ai aunty bata jira maryam takarasa abunda zatajeba tanufi dakin dasaurinta, ilaikuwa seta tararda abunda maryam tafada mata, cikin tsananin jin dadi aunty tace, “Alhamdulillah maryam, sauki yafara samuwa da yardar Allah, tunda har wani abu najikinsa yafara motsi” nima cikin tsananin farin ciki nace, “insha Allah, aunty dama naji yanata sauke ajiyar zuciya” shafa kansa aunty tayi tace, “Allah yakara baka lafiya Muhammad, Allah yasa warakarkace tazo,dakuma karshen ciwonka” “ameen aunty” “kinshafa masa tofinne” aunty tafadi haka bayan tadago tana dubana. “Eh aunty” “yawwa dama Inata addu’ar, Allah yasa kinshafa masa abban aliyane yatsaidani awaya shiyasa.” “Tom aunty bakomai bari nakoma” “ohk, maryam,mungode sosai Allah yayi albarka” “ameen” nafadi haka ina juyawa nafita, haryanzu abunnan yana hannuna na damkeshi, tare da boye hannunnawa acikin hijabi. bayan fitar maryam aunty ta dauki guntun ruwan tofin tasa acikin fridge, tazauna agefen gadon tabi bayan kiranda abbansu aliya yaketa mata bayan katse kiran datayi. Cikin sauri nake tafiya saboda Allah,Allah nake nakarasa part dinmu nabude abun hannuna naga menene, Allah yasoni babu kowa a falo nayi sauri nashige dakina. ajiye abunnayi akan madubi, nafara kokarin budewa amma abun yaki buduwa tamkar ansaka gam amanne, hakura nayi ganin nayi_nayi yaki buduwa nabarshi a gurin nakama sabgar gabana,danbanyi tunanin wani abune me mahimmanciba. Se bayan sallar azahar aunty tadawo daga part din mustapha, ta baro mommy da haidar agurinsa. Bayan sallar lasa’ar nafito falo nahadu da yaya sadiq yana kokarin fita da sauri yatsaya yace, “maryam, ina kika ajiye wayarki inata kiranki akashe” “yayana ta mutune ba caji” “haba maryam duk wutarnan amma kika bari wayarki ta mutu kuma tundazu bakisa cajiba” “baccine yadaukeni kuma namanta bansaka cajinba seyanzu dana tashi” “ohk,tafiyar danace miki zanyi gobe tadawo yau” da mamaki nake kallon sa nace, “yaya yau kuma ai yamma tayi kabaridai goben” “wlh maryam, kiran gaggawane yasameni daga kamfanin daddy na abuja” cikin sanyin jiki nace, “shikenan yayana Allah yakiyaye hanya” “to mene kuma, ko bakyason natafi naga dukkinyi wani iri” kaina nagyada masa alamun eh, haka kawai naji banason yatafi jikina duk yayi sanyi. “Kiyi hakuri kinji maryam dita, aiba dadewa zanyiba zandawo befi nayi sati dayaba ki saki jikinki kinji, karki karyamun gwiwa” danne damuwata nayi ina murmushi nace, “shikenan yayana, Adawo lafiya Allah yakiyaye, ya kare hanya kakuma kulamun da kanka” murmushi sadiq yayi cikin jin kalaman maryam yace, “kokefa yar matata, nagode sosai, kikulamun dakanki kema sosai I will miss u” “miss u too dear” nafadi haka kaina akasa, cikin fadada fara’a sadiq yace. “Byeeer I love you” hannu nadaga masa alamar bye_bye nace, “love u too” sekuma najuya da sauri nakoma dakina. Murmushi sadiq yayi yanabin maryam da kallo cike bansha’awa da tsananin kaunarta, harta shige daki sannan ya juya yatafi. Wuraren karfe 5:30 muna zaune nida aunty a falo aunty suhailat tashigo falon, da alama daga unguwa take, dan taci kwalliyarta hannunta kuma nadauke da jaka. seda tazo tsakiyar falon tayi sallama shima dantaga aunty ne dabaza tayiba. “Suhailat daga ina haka dannasan yau ba school” aunty tafadi haka bayan mun amsa mata sallamar tata. “Naje gidan wata friend ditane” itama suhailat din ta bata amsa da haka. Kallon suhailat aunty takeyi cike da tuhuma ganin yanda taga gabadaya ta canza sannan tace, “wakika tambaya” cike da kosawa suhailat tace, “mom” atakaice. aunty bata kara cewa komaiba, ita kuma suhailat tashige daki tana tutturo baki gami da kunkuni. Daga gurin kamal take, yanzu kullum ta Allah sesun hadu sun sheke ayarsu, ko duba mustapha ma saudaya take zuwa a rana, yanzu tazama yar hannu, idan bataje tayi sex da kamal ba kullum bata samun nutsuwa. Aunty takanas taje har dakin mommy bayan sallar magriba tayi mata magana akan fitar suhailat, se mommy tace ita batason haka mene nadamuwa akan yawan fitar suhailat din, yar marainiyar Allah ma se’ansa mata ido,adai dinga kyautata zato. Ran aunty yayi matukar baci dajin kalaman aunty, amma ta daure batace mata komaiba tatashi tafito ta bata guri,ita bada wata manufa tafada mataba,tafada matane kawai akan amata fada ganin yawonnata yayi yawa, alhalin kuma ga wanda ake saran yazama mijinta kwance babu lafiya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button