Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Su ammi suna falo sukaga umaimah ta shigo kamar anjehota, ammi ta dubeta da mamaki tace “lafiya kuwa auta?” girgiza kai kawai umaimah tayi alamun a’a batace komaiba. Mama dake cin abinci tace, “yazakice a’a bayan gakinan kin shigo kamar wata mara lafiya, kuma daga kai wa mutane abinci kinje kin zauna tun dazu, yanzu amminki tagama zancenki tana ko abinci baki ciba zataje ta kirani.” Mikewa umaimah tayi tana faɗin “batajin daɗi ne shine yaya NOOR yasa na gyara musu gidan” zuhura dake bawa Abul tea tace, “gyaran gidan da’aka sakine shine kike bata rai haka?” Umaimah bata bata amsaba ta shige ɗakinta. Ammi kuwa tuni hankalinta yayi kan ƴar surukartata dataji ance bata da lafiya, wayarta ta ɗauka ta lalubo number’n Mustapha tayi dialing dantaji meke damun maryam din. Har Kira uku ta masa amma bedagaba. Fuskarta da alamun damuwa take duban su mama tace, “Allah yasa dai jikinnata ba tsanani yayiba, gashi kuma na kira NOOR ɗinma bedagaba. Cikin son kwantar da hankali mama tace, “karki wani tada hankali ‘yata, kinsan mace me ƙaramin ciki ba’a rabata da dan laulayiba, insha Allahu ciwon ba wani me tsanani bane” cikin sanyin murya ammi tace, “Allah yasa, amma da zuwa zanyi na dubota, dan idan banga yanda jikinnata yakeba hankalina baze kwantaba.” mama tace, “to kije kawai ki dubotan, kice muna mata sannu, idan mungama muma zamu shigo.” mikewa ammi tayi tana amsawa ta fice ta nufi part ɗin su Maryam. Knocking tayi taji shiru hakan yasata tura Kofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama, tayi sallama takai uku amma taji shiru. Ɗakin maryam ta shiga taga wayam ba kowa. fitowa tayi ta nufi ɗakin mustapha, duk da zuciyarta na mata tuni da hakan kamar bedaceba, amma hankalinta baze taɓa kwanciyaba idan bataga yanda jikin Maryam ɗin yakeba. Seda tayi knocking nanma taji shiru sannan ta tura kofar ɗakin a hankali ta shiga bakinta dauke da sallama. Ajiyar zuciya ta sauke ganin su kwance suna bacci, se yanzu hankalinta ya kwanta tasan tunda Maryam ɗin ta samu bacci jikin da sauƙi kenan. fita tayi taja musu ƙofar a hankali, seda ta rufe musu ta falonma yanda sena cikine kawai ze iya buɗewa sannan ta koma part ɗinta……

A hankali na buɗe idona tare da zare jikina daga nasa na tashi zaune ina salati acikin zuciyata, fuskarsa na kalla inajin wani sonsa na ƙara ratsa zuciyata, kusancin damuka samu daga jiya zuwa yau, da kuma kulawar daya bani ba ƙaramin tasiri yayi acikin zuciyataba. Hannuna nakai a hankali na shafi kwantaccen sajensa wanda yake ƙara fito da kyawunsa cikin raina ina faɗin, “Ya Allah kanunamun ranar da wannan bawannaka ze soni, kamar yadda nake tsananin sonsa.” ɗauke hannuna nayi daga kan fuskarsa ina sauke ajiyar zuciya, a hankali cikin lallabawa na zare hannunsa daga jikina dan kar ya farka, sauka nayi daga kan gadon na ɗauki tire ɗin damukaci abinci na fice daga ɗakin. seda na fita falo na duba time naga har 12 na rana ta wuce, lallai mun dade mune shan bacci, amma naji daɗin jikina sosai danayi baccin. Dan ciwon da kaina yakemun ya dena, kawai dai ina jin jikina fayau babu kwari ne. ko ɗakina ban shigaba na fara gyaran gidan, falo na fara sharewa nayi mopping na saka turaren wuta, sannan na nufi kitchen na gyarashi nayi wanke_wanke, sannan na shiga ɗakina shima na gyarashi tass. Bayan na gama na faɗa toilet nayi wanka na ƙara gasa jikina, tare da dauro alwalar sallah azahar. Cikin wata doguwar rigar atamfa na shirya, banyi wata kwalliyaba amma na budade jikina da turaruka masu daɗin kamshi. ganin har 1 ta wuce, sena tada sallah ta……✍️

By
zeey kumurya
ABINDA KASHUKA….!

BY
ZEEY KUMURYA

6️⃣6️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

……….Bayan na idar da sallar na fito da nufin naje na tashi yaya yayi Sallah, knocking din ƙofar falon da’ake shiya tsaidani. Kofar na nufa na buɗe bayan na tambayi waye? Aunty zuhura ce, faɗaɗa fara’a nayi nace, “Aunty zuhura sannu da zuwa” “yawwa Mamana” ta faɗa tana shigowa falon tare yin sallama, amsa mata nayi ina gaba tana bina a baya. Kallon yanda Maryam take tafiya yasa Aunty zuhura ta gane abunda ya faru, duk da maryam ɗin tayi iyakar ƙoƙarinta wajen ganin ta daidaita tafiyar tata yanda baza’a ganeba, amma seda zuhura ta harbo jingin. zama sukayi akan kujera suka ƙara gaisawa, Aunty zuhura ta mata ya jiki. Maryam ta amsa da faɗin “da sauki dannama warke” Aunty zuhura na murmushi tace, Allah ya ƙara sauki” Maryam tatambayeta ina Abul, tace yanacan gurin mama. Aunty zuhura bata wani jimaba tatafi tacewa maryam zataje ta dawo anjima… mustapha yana cikin baccinshi cike da jin daɗi da nishadi, amma tashin Maryam datayi ta barshi duk se yadena jin daɗin baccin. lalube_labule kawai yakeyi da hannunsa a gefensa koze jiyota amma sedai yaji filo, haka dai yacigaba da baccin babu daɗi. A hankali na tura Kofar dakin na shiga, kan gadon na nufa na hau na zauna ina tunanin ta ina zan fara tashinnashi. kyakkyawar fuskarsa me cike da kwarjini na kurawa ido da murmushi ɗauke a fuskata. wani irin farin ciki nakeji mara misaltuwa a cikin zuciyata, jina nake a wata duniya me nishadi da annashuwa, gani nake yau a duniya babu wanda yakaini farin ciki, saboda kasancewata da mutumin da bantaba zaton ze zamto miji a gareniba, amma ikon Allah gashi mun kasance matsayin ma’aurata har mun haɗa shimfida. Lumshe idona nayi saboda kwallar dabansan kota meceba data cikamun ido, tafin hannuna na kai kan cikakkiyar sumar kansa baka sidik me laushi da daɗin shafawa a hannu, na fara shafa masa idona a lumshe cikin tsananin shauki ina sauke ajiyar zuciya. nayi 6 minutes ina shafa kannasa zuwa zajen fuskarsa da bayan kunnensa. Mustapha kuwa duk da bacci yake amma ba ƙaramin jin daɗin abinda take masa yakeba, har wata ajiyar zuciya yake sassaukewa. baccin daya dena masa daɗi ya fara masa yanzu. ƙasa nayi da hannuna ina shafa wuyansa zuwa saman kirjinsa, tunawa danayi lokacin sallah na kurewa yasa nayi ƙoƙarin ɗauke hannuna daga jikinsa domin na tasheshi yayi Sallah, amma naji zaraf ya rikemun hannunnawa, a hankali nake ƙoƙarin zarewa amma ya rike gam da hannunsa. kyale masa nayi senaga ya maida hannun kan kirjinshi ya ɗora nashi akai ya manne. murmushi nayi kawai cikin jin daɗi da farin ciki. A hankali nasa ɗayan hannuna na ɗauke nashi sannan na zare nawa daga kirjinnasa, hakan danayi kuwa kamar tashinshi nayi daga baccin. a hankali ya buɗe lumshashshun idanunsa da suka sirka saboda baccin yayi, ya saukesu akan fuskarta, nima kallon fuskartasa nake hakan yasa idanunmu suka sarke cikin na juna, kasa janye idona nayi daga nasa kamar koyaushe idan ya kalleni, kallon cikin kwayar idonnasa nake zuciyata na tsananta bugu, banfi 30 seconds ina kallonsaba na lumshe idona saboda wata kasala datake lullubeni a sanadiyyar kallon kwayar idansa da nayi, batare dana buɗe idonaba a hankali nace, “ka tashi kayi sallah, kar lokaci ya kure” lumshe ido mustapha yayi cikin rashin jin daɗin rufe idonta datayi ta katse masa wani abu dake bin ilahirin jikinsa a sanadiyyar kallon kwayar idonta dayakeyi gashi ta masa kyau sosai. Tafin hannunsa yasa ya kamo nata a hankali ya haɗesu guri guda yana murzawa, a tare sukaji wani irin shock a jikinsu. batare daya saki hannunnataba ya buɗe idonsa tare da tashi zaune jin abinda tace. zama yayi a daf da ita har jikinsu na gogar na juna, bakinsa yakai daidai kunnenta cikin cool voice dinsa data ƙara sanyi saboda daga bacci ya tashi yace, “haka ake tashin miji a gurinku?” ya ƙarashe zancen yana ɗan matse hannunta dake haɗe da nasa. wayyo Allah, bansan ya misalta muku yanda naji ba a jikina sanadiyyar wannan maganar dayamun, turo bakina nayi gaba bance komaiba. kissing kuncinta yayi sannan yasa ɗayan hannunsa ya kama lips ɗinta da finger dinsa guga biyu ya matse yace, “wannan lips ɗin, nasan mezan masa a dena turomunshi gaba” da sauri na gimtse su, dan ban manta tsotsar dasukasha jiya agurinsaba ta fitar hayyaci har zafi seda sukamun. Tattausan murmushinsa yayi ya cire hannunsa daga bakinta, tare da zare ɗayan daga nata ya sakko daga kan gadon bakinsa ɗauke da salati. ban iya wani yunkuriba duk da yadda naso hakan har ya shige toilet din, duk da ya saki hannuna amma bandenajin wani yarrrr…… ajikinaba gami da kasala. Ajiyar zuciya na sauke na tashi na fara gyara gadon daya yamutse. kafin ya fito harna gyara ɗakin shap_shap na fice falo, zama nayi akan kujera ina sauke numfashi ɗankwalin kaina na cire saboda kan ya ɗan sha iska dan har yanzu da lema a jikin gashin duk da uban man kitson dana shafa kuwa, danma kitsone akan amma datuni na busar da gashin………….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button