Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Watarana dabazan taɓa mantawa da itaba a rayuwata. Ranar juma’a da safe. Nashiga gidansu domin duba mahaifiyarsa a lokacin bata da lafiya tana zazzaɓi, ina shiga gidan naci karo dashi a harabar gidan yana tsaye. seda gabana yafadi dana gansa bansan kuma meyasa ba, kuma seyamun kyau sosai tamkar wani Balarabe, satar kallonsa naitayi harnazo giftawa tagabansa seda na lumshe idona saboda kamshinsa dana shaka me dadin gaske. kaina na kasa nagaisheshi. me mamakon ya amsamun seyace mene ne kallonsa. dasauri na dago nasaci kallonsa senaga yahade rai, tsorone yakamani nafara bashi hakuri, ganin duk na firgice seyayi murmushi kawai ya wuce abinsa, nima jikina ba kwari nakarasa ciki. Ranar agidan na wuni inata aikece aikece, shikuma yazo yazauna yasamun ido yana kallona, duk motsin danayi idansa na kaina. duk se naji na takura. In takaicemuku zancedai a daren ranar yacemun yana sona. nayi matukar mamakinsa danni banyardabama,tun daga ranar nafara wasan buya dashi duk hanyar danasan zata hadamu seda na kauce mata, har gidansuma nadena zuwa. har gida mamansu tazo ta sameni tace kotamun wani lefinne nadauke mata kafa, nace mata wlh babu komai. babu yadda na iya haka naci gaba da zuwa gidansu dankar mahaifiyar sa tayi tunanin wani abu.

Aiko watarana yaritsani yace sena fada masa, shi dodo ne danake gudunsa, nace masa a’a. yace to idannakara gudunsa seya fadawa mahaifiyarsa yana sona. dasauri nace masa a’a karya fada mata nadena insha Allah. Tun daga ranar kullum semunyi tadi, dannima gaskiya inason sa. Dan duk inda ake neman namijin da mace zatayi alfahari dashi MODIBBOnah yakai. tun inajin kunyarsa harna rage. munsaba dashi sosai mun kuma shaku iya shakuwa. Tun munayin soyayyar a boye harta fito fili kowa yasani. mahaifiyarsa tafi kowa murna dajin labarin soyayyar mu, saɓanin mahaifiyarmu dabatayi murnaba, bansan kuma meyasa ba dan alokacin bata fadamunba. munkai kusan shekara muna soyayya dashi sannan akayi zancen aurenmu, aka saka ranar aurentamu. ba’awani saka lokaci me tsahoba na bikin. Tun daga lokacin yan’uwansa suka dora mana karon tsana nida mahaifiyata da kanina, wai kwadayine zesa na auresa badon Allah ba. nikuma ina matukar sonsa shiyasa tsanar dasuke mana ko’ajikina mahaifiyarmucema take damuwa. Rana bata karya, segashi lokacin da’aka saka na bikinmu yazo. Ansha shagali sosai anyi taro lafiya angama lafiya, muka tare a gidanmu dake cikin unguwartamu dai, amma da ɗan tafiya daga gidanmu. munyi rayuwarmu ta farinciki da jindadi da kwanciyar hankali, soyayyar damukasha da megidana ALHASSAN MODIBBO bazata faduba, yasoni ya tattalani kamar kwai, nima kuma ina matukar sonsa. yabani farinciki arayuwata duk abunda nakeso shiyakemun. Nandanan na murje nakara fari nayi haske, ana ganina anga ina cikin kwanciyar hankali Alhamdulillah. Nanfa tsanar da yan’uwansa sukemun ta karo, waina mallake musu dan’uwa se’abunda nace yayi shiyake. Shifa sesuka fara masa zagon kasa, suna masa wayo suna cin dukiyarsa a boye batare da saninsa ba. Aurenmu befi da wata biyar ba, Allah yayiwa mahaifiyarsa rasuwa, alokacin ina dauke da karamin ciki. Munji mutuwarnan sosai, mutuwar tadakeni nayi kuka tamkar raina ze fita, daga karshema shiya komo yana rarrashina. A hankali mutuwar tabi jikinmu muka hakura muka koma yimata addu’a. Tundaga lokacin yan’uwansa suka fara nuna masa wayonsu a fili, suka dinga binsa suna yabasu kadarorinsa. Shima dake yaganesu seya k’,i basu. Mubamu saniba ashe sunacan suna haɗa masa gadar zare. watarana muna zaune a falo da daddare, ranar yadawo daga Dubai yayi sarin gwalagwalai masu yawa, ko inda ake narka masa su a maidasu dankunnaye da sarka bekaiba, ya a jiyesu a gida, yace dasafe zekai dan lokacin yagaji. a lokacin cikina yakai wata 7. Muna zaune naga yakuramun ido yana kallona, tafin hannuna nasa narufe masa idon nace. “Wannan kallonfa” hannuna yacire daga fuskarsa yana bina da wani kallo dayasa jikina duk yayi sanyi yace. “Nasone!” murmusawa nayi cikin jindadi duk da faduwar gaban danakeji amma haka nadaure nace. “Mijina, ina sonka sosai,ina addu’ar Allah yabarmu tare harkarshen rayuwarmu…” kalamai masu dad’i da sanyaya zuciya mukaita fadawa junanmu a wannan daren, a ranar MODIBBO yanunamun soyayyar dabetaba nunamun irintaba, soyayya me tsayawa arai dasanya nishadi a duk sanda aka tunata” shiru ammi tayi tana sauke numfashi, lokaci daya yanayinta yasauya idanunta yakawo ruwa. wani yawu medaci tahadiye sannan ta cigaba da magana. “Amma duk da haka jikina a sanyaye yake kamar wata mara lafiya, shima kuma haka na lura danashi’karfin hali kawai yakeyi. kaina na bisa cinyarsa bacci yasaceni, a falon ya kwantar dani ya tada sallar nafila kamar yadda yakeyi kowanne dare. Bansan mekefaruwaba se farkawa kawai nayi naji suna magana da wasu mutane a falon. bude idona nayi da sauri kokarin mikewa zaune nayi najini rungume ajikinsa. Abunda naji yana fadane ya matukar dagamun hankali. “Kome zakumin kumun,amma karku taɓamun lafiyar matata da abunda ke cikinta” ai bansan sanda na kwace daga rikon dayamunba, ina kallon mutane. Fuskokinsu duk a rufe da wani bakin kyalle. cikin tsorata nace musu. “Suwaye ku,? mekukazoyi gidanmu? mekuke bukata?” Wani me ƙatuwar muryane a cikinsu naji yace. “Ran mijin ki mukazo dauka” cikin zafin rai nace masa, “ƙarya kakeyi, baka isa ka kashe shiba matukar kwanansa bekareba. Ai rannasa ba’a hannunka yake……” kafin na karasa maganata naji daya a cikinsu yadagi yacillar gefe, cikin zafin naka da karfin zuciya namike zankoma gun mijina, suka karayin gefe dani. Intakaice muke zance, ina kallo a gabana, mutanennan marasa imani da tausayi masu zuciyar kafirai suka yankamun mijina, duk da uwar magiyar daya musu akan su kyaleshi karsu maida masa da ɗa/ya Maraya tun kafin suzo duniya, su fadi ko nawa sukeso,kome sukeso zebasu,amma sukace su sam basa bukatar komai. ransa kawai suke da bukata. Inaji ina gani suka masa yankan rago” kuka me karya zuciyar me saurarensa ammi tafashe dashi tamkar a lokacin abun yafaru…….✍️

BY
zeey kumurya
4️⃣7️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

………..Babu wanda bezubar da hawayeba a falon se dady da Mustapha. shikam Mustapha zuciyarsace take tafarfasa tsabar bakin ciki da tausayin mahaifansa, jiyayi dama shima kukan zesamu yazo masa, koyaji sauƙin radadin dake damunsa a zuci. Farararen idanunnan nasa sun kada sunyi jajur, jijiyoyin kansa gaba daya sun mike sunyi rudu_rudu. kasa kawai yayi dakansa yana fesar da zazzzafan huci daga cikin bakinsa. daddy ma dauriyace kawai domin karya kara karyarmusu da zuciya, lallaminsu yafarayi duka da fadin. “Kuka bashine maganiba, duk da nasan tausayine yasaku kukan, amma yakamata kuyi hakuri kuyi shiru, kar kukan yajanyo muku wata matsalar, musammanma ke dakike kukan tun dazu” yakarashe zancen yana kallon ammi. shiru suka masa babu wanda yace masa kala, dakyar dai dady yashawo kan ammi tayi shiru tacigaba da bada labarin cikin raunin murya.

“kafin su kasheshin sunsha dambe dashi a kokarin shi na kwatar ransa, dan har wasu yajiwa ciwo da naushin daya dinga kai musu, to Sarkin yawa yafi Sarkin Karfi. susu biyarne shikuma shi ɗaya, kuma su da makamai a hannunsu. ni kuwa banda ihu babu abunda nakeyi ina neman taimako, ɗaya daga cikinsune yatoshemun baki, da gwabjejen hannunsa. maimaita kalmar shahada yayitayi harsuka yankashi sekace wani dabba. kansa nayi da gudu bayan sun fice ina jijjigashi ina kururuwa ina fadin yatashi karya tafi yabarni. gaba-daya nima nayi dama_dama a cikin jinin dake fita daga jikinsa, tun ina fahimtar menakeyi harna dena. farkawa kawai nayi naga gidan a cike da mutane, ga jami’an tsaro suna jiran na farfaɗo suji karin bayanin abunda yafaru. mahaifiyatace a kaina da kanina Muhammad, gaba-daya ido yadawo kaina, masumun sannu nayi masu kallon tsegumi namun. nidai dakyar na yunkura na tashi zaune saboda nauyin da kaina yamun, ashe nadade a sume dan har anyi masa sutura. Dakin dayake mahaifiyata ta kama hannuna ta kaini, muna shiga na hangoshi a makara da gudu na kwace hannuna daga nata nanufi gurin da makarar take na kwanta akan gawartasa na fashe da kuka, surutai naitayi irin na fitar hayyaci, dakyar aka banbareni daga jikinsa, ina kallo aka fitar dashi zuwa gidansa na gaskiya. Tundaga wannan lokacin nazama ba uhmm ba um’um, saidai naitabin mutane da kallo, banaci banasha kuma bana kukan fili sena zuci, a haka har akayi sadakar uku. Nidai bazance ina cikin hayyacinaba a wannan lokacin, suma kam nayita ba adadi, ga tsohon ciki. Seda na kwanta jinya a asibiti, dannamafi wata a kwance, mahaifiyata kullum cikin kuka take, dan duk sun fitar da rai dani. Kanina Muhammad koyaushe cikin kwantarmun da hankali yake, tare da alƙawarin seya daukarmun fansar mijina akan wadanda suka kasheshi ko su waye. Mahukunta nata aikinsu na binkice akan kisan. kwana biyu da sallamoni daga asibiti yan’uwan MODIBBO sukazo akan rabon gado, nace musu suje surike komai ni banaso. banason komai na dukiyar na bar musu. Muhammad ne, yace hakan bazeyiyuba ai rabon gado Allah ne yace ayi, kuma ko badonniba, abunda ke cikinafa ai dole a fitar masa da hakkinsa. Sukuwa yan’uwansa ba hankali harsun fara hada kan kadarorinnasa suna mallakesu. Muhammad ne yaje yasamu wani yayan abokinsa lauya yafada masa, shikuma yashigar da maganar kotu. segamu har gaban alkali. Alkali yace, ai babu zancen rabon gado yanzu harse na haihu anga menahaifa. dan haka a tattaro duka abunda ya mallaka a damka masa har zuwa lokacin dazan haihu, budar bakinsu secewa sukayi ai anyi scanning anga mace ce, a cikina dan haka ayi raba kawai. mamakinsu bakadanbane ya kamani, dan duk jinyar danasha ko duniya basuzoba, amma wai anmun scanning anga macece. Alkali kuwa fatattakarsu yayi yace dole sena haihu, kar wanda yakara zuwa masa da batun harse na haihu. Ba’afi wata dayin hakaba, na haihu a asibiti bayan uwar wahalar danaci. Nahaifi yaro kyakkyawa me kama da ubansa, lafiya kalau dashi. Nakai kwana 3 bansan waye akainaba, bayan na haihu. saboda damuwa tamun yawa,jinina yahau sosai. Nafi sati a asibiti sannan aka sallamoni. yaro yaci sunan Muhammad nayiwa kanina takwara, saboda soyayyar dake tsakanina dashi, dakuma yanda yake son Muhammad, kodayaushe yana hannunsa, har wanka yake masa sekace mace. kullum cikin fadamun yake, idan yayi aure nabar bishi Muhammad, yarikesa. Haihuwar yaron ita taragemun kaso 50 nadamuwar danake ciki akan mutuwar adalin mijina. soyayyar uwa da danta, daga Allah ne, bansan yazan fasalta muku yanda nakejin kaunar danakewa Muhammad karami ba. Munje kotu alkali yamana rabon gado, tunda namiji aka haifa yan’uwan modibbo basu da komai a cikin gadonsa, komai nasa na yaronsane seni da’aka bawa tumunin takaba. tundaga wannan rana damukaje kotu yan’uwan modibbo suka sakomu a gaba, nida mahaifiyata da kanina. suka takura mana suka tsangwamemu. watarana bayan munyi arba’in, sukazo mun da wata fitinar akan dole sena basu dukiyar Muhammad, tunda sune danginsa na uba, zasu rike masa su juya masa kafin ya girma. harna mike zan tattaro musu kanina Muhammad yashigo gidan, dayaji abunda ke faruwa abakin mahaifiyarmu yace basu isaba baza’abasu komai na dukiyar Muhammad. fada sosai abun yazamarmusu da Muhammad duk da befi ɗan cikinsu ba, daga karshe dai dole suka hakura suka tafi. Yan’uwan mahaifin modibbo danaje musu yawon arba’in sena fada musu abunda yake faruwa, shine sukace natattaro komai nakawo musu aisu basu isa sun kwata ahannunsuba. haka kuwa akayi natattara komai nakai musu. Gwalagwalan da modibbo yasiyo a ranar daya rasu sukadaine ban bayarba. dama a cikin wata jaka yake, sena boye jakar a dakina. Akwai wata a zurfa a hannun modibbo, tunda nasanshi da ita nasanshi da ita, seda ya mutu aka cireta. itama sena jefata a cikin jakarnan dakuma tambarin gidansu modibbo, duk na hada na ajiye. Watarana da daddare muna cikin bacci, wasu mutane suka hauro mana gidanmu. basu tunkari dakin kowaba senawa. Ina rungume da Muhammad a kirjina naji ana ƙoƙarin rabani dashi ta ƙarfi. da sauri na farka, shima Muhammad din farkawa yayi yana tsandara kuka. cikin matukar tsorata naja baya, ina kara kankameshi a kirji na. tare da fadin, “suwaye ku?” wata dariyar rashin imani wani acikin su yakece da ita, sannan yace. “Wadanda suka kashe megidanki ne, yanzu kuma munzo mukashe wannan dannakine, daya hana ruwa gudu.” tsoro metsanani ne yakamani, zanin goyonsa dake kan gadon, na yayiba na mike tsaye na goyeshi, suna tsaye suna kallona basucemun kalaba. cikin kuka nace musu, “wai kudin suwaye, me mijina da yarona suka muku? Kunkashe mun mijinma bazaku barmuba, sekun biyo dannawa guda daya tilo shima kunkasheshi, kuwanne irin marasa imani ne? Wlh Allah bazai barkuba ku…..” Wata uwar tsawa wani a cikin su yadakamun. wadda tasani hadiye maganata, batare dana shiryaba. maganganu yashiga yimun wanda bana fuskantar komai saboda dimuwa da razani, tunanin hanyar dazanbi inkubutar da dana kawai nakeyi. A kalamannasa dai na fahimci yace, turosu akeyi kuma saboda dukiyar modibbo ne. jin haka sena fara neman inda jakarnan take domin na basu, dansu kyalemun dana. seda nagama shan wahala nanemo jakar, nace musu ga dukiya nan, indai dukiyace. Nidai dan Allah subarmun yarona karsu rabani dashi, kokuma ni su kasheni akan sukasheshi. A lokacin senaji gwara ni namutu shiya rayu. wata irin kaunarsa nakeji, tana kara mamaye zuciyata. mutanennan sukace susam Muhammad akace sukashe kuma sesun kasheshi, sannan su tafi da dukiyar. daukar jakar nayi kamar mika musu zanyi, nafaki idonsu nafada toilet na kulle, bubbuga kofar suka hauyi da nufin su ballata. ganin danayi tsaf zasu iya balla kofar su shigo su riskeni sena fara tunanin mafita. shawara zuciyata tabani akan nayi nesa da garin kawai, inda halima nabar kasar gaba daya,ta hakane kawai zan tsira daga sharrin muggan mutanennan. batare da tunanin komaiba na amince da shawarar zuciyata, window din toilet dinmu na kalla naga zan iya fita ta cikinsa, harna bar jakarnan sekumadai nadawo nadauka dannasan zatamun amfani nan gaba, na ratayata, a kafadata, na gyara goyon Muhammad tamau, na fice ta window. da wani irin gudu dabansan ina dashiba nafice daga gidanmu naita falfalashi. Banmasan inda nake jefa kafataba kawai shiga duk layin dana gani yakeyi. nasan balla kofar toilet din sukayi sukaga bananan shine suka biyo bayana, ina cikin guduna kamar ance in juya na hango kyalli fitilarsu daga can nesa. Abunda yasa nagane sune, kuma ni sukebi, duk layin dana shiga nan hasken fitilar yakebi shima. hankalinafa ya kara tashi gashi harna fara gajiya da gudun, ina shan kwanar wani layi nayi kacibus da wani mutum………..(labarin abunda yafaru tsakanin ta da dady ta basu sanna ta cigaba) bayan na bashi yaron senaji hankalina ya kwanta, koda sun cimmun bani da damuwa tunda ɗana ya tsira da yardar Allah, kuma dukiyar da’ake fadan akanta bazasu sametaba. wata mota nagani tazo ta wuce ta gabana ina cikin gudu, can kuma naga motar ta dawo ta tsaya a gabana, kokarin canza hanya nayi cikin tsananin tsorata. mai motar ne yafito da sauri cikin harshen Hausa yacemun. “Baiwar Allah, zoki shiga mota narage miki hanya, naga wasu mutane sunata gudu da muggan makamai karsu suganki suyi miki wata illar, gashi yanzu dare ya tsala” jin kalamansa yasa da sauri na bude bayan motar na shige batare da tunanin komaiba, shima ya koma cikin motar. kafin yakai ga jan motar mutafi azzaluman mutanennan sun karaso layin………✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button