Bayan 5 minutes yaya ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, muka amsa masa, gwaggo ta tashi ta leka tace “shigo ciki mana, kamar wani bak’o” baice komai ba yashigo ya zauna, cikin miskilancinsa ya gaida gwaggo, gwaggo ta amsa masa da fara’a, daga gaisuwar bai ƙara cewa komai ba ya mike yayiwa gwaggo sallama ya fice, gwaggo ta dube ni tace “to kije kuyi sallama mana” na tashi nabi bayanshi, har ya shige motar dana fita kofar gidan, buɗewa murfin nayi na shiga nima da sallama, ya amsa mata cikin sanyin murya nace “yaya” yace “uhm” tare kallonta yana ƙoƙarin boye damuwarsa, na matsa kusa dashi ina shafa sajen fuskarshi nace “meke damunka?” numfashi yaja ya fesar ya juyo ya fuskanceta yana k’ak’alo murmushi yace “nothing” na kwantar da kaina a kirjinshi ina kallon fuskarsa, handbag ɗita ya mikomun yana faɗin “Take your bag, saboda zumuɗi kin manta da ita” ban karb’a ba, sai ƙara lafewa danayi a jikinsa, kwalla na zubomun, wata irin kewarsa na fara ji tun kafin mu rabu, haska fuskarta yayi da wayar hannunsa jin tayi shiru, abun da yayi tunani kuwa shi takeyi, taune lips d’insa yayi bece komai ba, dan shima ji yake kamar yayi kukan saboda yanda yakeji a ransa, murya ƙasa ƙasa yace “kukan na mene?” na turo baki gaba nace “yaya tafiya zakayi ka barni ko?” yace “Ehh, amma ai zan dawo na ɗauke ki mu koma gida” nace “yaushe?” Yace “idan kun gama biki mana” nace “a’a nidai kazo gobe?” ya shafi gefen fuskarta yace “gobe ba time, Daddy yace zani Abuja in the early morning” nasa kuka nace “to ni zan bika Abujan” runtse idonsa yayi kukanta na taɓa masa zuciya, ita kuwa kukanta take bil haqqi, bubbuga bayanta ya shiga yi cikin rarrashi yana hura mata iska a cikin kunnenta, shiru nayi ina sauke numfashi tare da ƙara kankameshi kamar zan koma cikinsa, nace “kaji yaya zan bika, ni banason kayi nesa dani” yace “Ummu bikinnaku fa?” cikin shagwaba nace “na fasa, binka zanyi” yayi murmushi yace “um’um, in tafi dake kitamun kukannannaki, kice sai na dawo dake” nace “Allah bazan maka ba” yace “baza fa ki bini ba, ba kincemun best freind ɗinki bace amaryar?” nace “eh” yace “to ai ba za taji daɗi ba, idan bakiyi attending bikin ba” nayi shiru bance komai ba, yayi murmushi jin yadda take ta kankameshi, dagota yayi daga jikinsa ya ɗora mata jakarta akan cinyarta, kuɗaɗe ya ɗauko bandir ɗin 1k, ya buɗe jakar ya saka a ciki yace “gashi ki bawa gwaggo” ya ƙara ɗauko wani yasa yace “wannan kuma ki bawa amarya” ya ɗakko bandir ɗin #200 guda biyu yasa yace “wannan kuma kiyi lik’i” kallonsa kawai na tsaya ina yi, ya ƙara ɗakko wani kuɗin yasa yace “wannan kuma na sweet ɗinki ne” cikin sanyin murya nace “yaya kuɗin sunyi yaw….” ya ɗora ɗan yatsanshi akan lips ɗina yana faɗin “shiiiiii” nayi murmushi ganin yanda yayi da fuska nace “Nagode sosai yaya, Allah yasaka da Alkhairi ya ƙara buɗi” yace “ameen” yana zugemun jakar, ya dago ya kalleni yace “sai yaushe?” ɓata fuska nayi sosai tare da turo baki gaba nace “yaushe zaka dawo daga Abujan?” yace “may be next tomorrow or Sunday” na waro ido waje nace “har Sunday, nidai ban yarda ba, yamun nisa” ya janyoni jikinsa yace “to yaushe kike so?” nace “jibi” yayi shiru na wasu sakanni, yasan aikin da zai yi a Abuja baze yiyu yayi shi a 1 day ba, amma saboda ya kwantar mata da hankali yace “Allah yakaimu” nace “ameen” yana dagoni daga jikinsa yace “kije gida, gwaggo na jiranki kuyi hira” na kwabe fuska nace “kora tama kake” yace “Ni na isa” na koma jikinsa na kwanta ina shaƙar kamshinsa nace “kasamun turarennaka a cikin kayana?” yace “ehh, nasa miki duka wanda nake amfani dasu” ya ƙarashe zancen yana kunna light din motar, wayarsa ya zaro daga aljihunsa gaban rigarsa ya latsa ya ɗauke mu a hoto, nayi dariya ya ƙara mana wani, ya mana da yawa sannan ya mun ni kaɗai, na karbi wayar ina dubawa nace “kaima bari na maka” yace “ai bazanyi kyauba” nace “nidai sai na maka” yayi murmushi har dimples ɗinsa suka loma sosai na masa hoton, na nuna masa nace “ka gani kayi kyau sosai, katuramun duka, ya turamun ta whatsApp, na ɗauko wayata na kunna data suka shigo, duba tsadadden agogon hannunsa yayi yace “zan wuce, Daddy na jirana” nayi shiru ina kebe fuska, fuskarsa ya matsar daf da tata a hankali yace “Please don’t cry, ko bananan karkiyi kuka kinji” nace “bazan ba” yace “promise” nace “i promised” ya haɗe bakinsu guri guda ya fara kissing ɗinta, yayi 4 minutes yana kissing ɗinta, kafin ya zare bakinsa a hankali yana sauke numfashi ya kalli cikin idonta yace “i love You so much Habibty, and am gonna miss you” lumshe idona nayi cikin jin daɗin kalamansa bance komai ba, yayi kissing saman idona yace “ba reply” na turo masa kawai, yayi murmushi tare kissing lips ɗinta, ya kama hannunta yana messaging yace “byee” na buɗe idona na saukesu akan fuskarsa, tattausan murmushi yamun na mayar masa tare da zare hannuna daga nasa, cikin sanyin murya nace “bye bye” jikina a matuƙar sanyaye na buɗe murfin motar na fita ina jin kamar na fashe da kuka, ya bita da kallo kawai kamar yace ta dawo, hannu na d’aga masa bayan na rufe motar, shima ya dagomun hannu, nayi murmushin ƙarfin hali na juya na tafi, gidansu saleemat na nufa, sai da yaga shigewarta sannan yaja ajiyar zuciya ya kunna motar yayi reverse ya tafi zuciyarsa cike da shauk’in ta da kewarta. ina shiga gidan su saleemat ana fara kiran sallar isha’i, da umma na fara cin karo tana jan ruwa a Rijiya, umma ta amsa sallamar da nayi ta ƙara da faɗin “Maryam!” Ina murmushi nace “na’am umma” umma tace “maraba lale, sannunki da zuwa, saukar yaushe?” nace “yau ɗinnan nazo umma” saleemat dake banɗaki ta fito da sauri tazo ta rungumeni, nace “amarya bakya lefi” ta sakeni tana haskani da fitilar hannunta tace “ai kece amaryar, irin wannan kyau haka, ni ai badaban naji muryarki ba, bazance ke bace, zata zan wata balarabiyar ce” nayi murmushi kawai, tajani muka nufi ɗakinta, bayan na zauna ta ƙara haskani, nace “ke mene haka ne?” tace “wlh Maryam bakiga yanda kika canza ba, aurennan ya karbe ki” ina cire mayafin abayar danayi rolling nace “ya ranki” tace “fari tass” nace “ina angonki?” tace “hubbynah yananan kalau” muka shiga hira akan sha’anin bikinta, umma ta shigo ta kawomun ruwa muka ƙara gaisawa, anan nayi Sallah isha’i, ina cikin cin tuwon da umma data kawomun na dubi saleemat nace “ina autan umma ne, banji shiba” saleemat tace “bai shigo ba” nace “inason ya siyomun IBON ne, kar dare yayi” saleemat tace “alawa a darennan, ke kuma cikin da shan Zaki yazo miki?” nace “bani da wani ciki ni, sadaka zanyi da alawar” tace “ok, gogemun hadda, ai ana ganinki anga me ciki” nace “sai kuma kiyi” banbar gidansu saleemat ba, sai tara da rabi shima sai da gwaggo ta turo Asabe kirana, Sani k’anin saleemat ya siyomun IBON ɗita da yawa na juyeta a jaka bayan na basu tasu, kuɗin da yaya ya bani da 20k ɗin da ammi tabani na bawa saleemat na bata, sukai taimun godiya ita da umma, gwaggo ma ina zuwa na bata nata, asabe ma, na bata a cikin kuɗi na, tun kafin nayi wanka na kira yaya be d’aga ba, har nayi wanka na kwanta bai kira ba, na ƙara kiransa bai d’aga ba. har dare yayi sosai be kirani ba, Ni kuma na kasa bacci sai juyi nake akan gadon gwaggo, har gwaggo ta gaji tamun magana da faɗin “Maryam ko sauro ne, ya dameki?” nace “um,um” da ƙyar na samu bacci ya ɗaukeni, dan sosai nayi kewar yaya. Mustapha kuwa yana can suna tattaunawa da Daddy akan harkar kasuwanci, sai da yazo bacci yaga missed call ɗin Maryam, yasan zuwa lokacin kuma tayi bacci, shiyasa bai kirata ba, ya bari sai da safe……..
Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page