Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari su Aunty suka tafi tun safe, kamar na bisu haka naji. su ammi ma sunso su Aunty su ƙara kwanaki amma Aunty tace tafiya zasuyi saboda makarantar Aliya, wani satin zasu koma kuma zataje dangin babanta kafin su koma. Suhailat ma kamar tayi kuka, se botsare_botsare take tana bata rai, Aunty dai ko kulata batayiba tafiyace dai dole seta yita. Direban ammi ne ze kaisu gida, dan direban su Aunty tun a ranar daya kawosu ya juya ya koma. Wunin yau gabaɗaya cikin rashin walwala nayishi saboda tafiyar su Aunty. Danma munyi waya dasu saleemat ne da gwaggo, shiya ragemun kewar su antin…..

Har bayan sallar magriba ina part din ammi, bayan na idar da Sallah naji babu abunda nakeson ci se wainar fulawa. kitchen din ammi na shiga na hado kayan hadi na fara kwabawa, Aunty zuhura tazo diban abinci ta tarar ina kwabawa, tsokanata ta shigayi wai yau kuma babynnasu waina zeci, dariya nayi kawai bance mata komaiba. Na fara soyawa ammi ta shigo kitchen din tana faɗin, “Maryam dakanki kikeyi, kinsan ita waina idan mutum ne ya soya da kansa baya iyaci, dakin fadamun dana soya Miki da kaina ai, kokuma nasa umaimah ta soya Miki” cikin ladabi nace mata, “Ammi ai zan iyaci, agidama idan inaso ni nake soyawa da kaina” murmushi ammi tayi tace, “To ai yanzu da da ba ɗaya bane Maryam, sekiga yanzu kin soya kuma kinkasa ci.” nace, “ammi fa zan iya da gaske” ammi tace, “toh shikenan ɗiyata sekin gama.” Se bayan isha’i nagama soya wainar. Yawuna har tsinkewa yake tun kafin nagama, dibar tawa nayi acikin flaks sauran kuma na barwa su ammi. Part dinmu na wuce, akan dinning na aje flaks din sannan na nufi ɗakina, toilet na faɗa cikin sauri nayi wanka tare da dauro alwala. Shap_shap na shirya cikin wata doguwar rigar mara nauyi Black colour, wadda na turarata da turaren da Aunty ta bani, tun bayan sallar azhar nayi kabbasunta amma haryanzu kamshin yananan ajikin rigar. wanda ta bani na shafawa a jiki na shafe jikina dashi lungo da sako, turaren yanada daɗin kamshi sosai shiyasa naita mulkashi ajikina. Hijabi na zira na tada sallah, bayan na idar na fito falo batare dana cire hijabin jikinaba, flate na dakko a kitchen da robar yaji na dawo kan dinning na zuba wainata na faraci, ina tunanin har yanzu yaya bedawo ba…

Tare suka shigo gidan shida yaya Saddam, bayan sunyi sallah ne suka tsaya tattaunawa akan kasuwancinsu. sallama sukayi kowa ya nufi part ɗinsa. Key din hannunsa yayi amfani dashi ya buɗe Kofar palon domin beyi zaton ta dawo daga part ɗin ammi ba. A hankali ya tura Kofar ya shiga bakinsa dauke da sallama. na gutsuro wainata zankai baki na ganshi kamar daga sama ya shigo, kasa kai wainar nayi cikin bakina na maidata cikin plate, na tsaya ina kallonsa, bugun zuciyata na sauyawa. shima tsayawa yayi yana kallonta, kurawa juna ido sukayi daga ɗan nesa batare da sun shirya hakanba, kowa zuciyarsa cike da kewar ɗan’uwansa. Tun safe a gurin rakiyar su Aunty basu ƙara haɗuwa ba se yanzu. Nina fara janye ido daga kansa ina sauke ajiyar zuciya. A hankali na amsa masa sallamar da yayi. a hankali yafara takowa har gurin dinning din, kujerar dake fuskantar tawa yaja ya zauna. kaina na ƙasa nace, “sannu da zuwa” gyada mata kai yayi idanunsa na kan guntuwar wainar dake cikin plate din. kasa cigaba da cin wainar nayi se jujjuya hannuna kawai nake a ciki saboda zamansa a gurin, ga idanunsa danakeji suna yawo a jikina. Wani tunani ne yazomun cikin zuciyata, mikewa nayi na nufi kitchen, binta yayi da kallo harta shige, Ajiyar zuciya ya sauke ya maida kallonsa kan wayarsa dake hannunsa. plate na dakko na dawo, ragowar wainar dake cikin flaks na zuba na tura masa gabansa. kallon wainar yayi ya kalleta da alamun tambaya akan fuskarsa. yaji na miko masa nace, “yaya ga waina” kallonta yayi da murmushi dauke akan fuskarsa yace, “ai wannan abincin matane bana maza ba” ina zama a kujerar dana tashi nace, “maza ma sunaci sosaima” yana kallonta yace, “to nidai bazan ciba, Nagode” shiru nayi ban ƙara cewa komaiba. Ganin yanda fuskarta tayi kamar bataji daɗi ba dan yace baze ciba seya mike yana faɗin, “ki kawo mun coffe ɗakina” amsa masa nayi da “toh” dakinsa ya nufa zuciyarsa na basa kwarin gwiwa akan kudirinsa akan Maryam, domin yagaji da yanda yake abzatuwa akan abunda yake halalinsane, yau kam ya shirya tsaf domin angoncewa. (????musty an ajiye miskilancin kenan, to mairon mudai yarinyace.????)……✍️

By
zeey kumurya
ABINDA KASHUKA….!

BY
ZEEY KUMURYA

6️⃣3️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

………Binsa nayi da kallo harya shige dakinsa, ajiyar zuciya na sauke me ƙarfi ina lumshe idona, sonsa da shaukinsa na ƙara yawaita a cikin zuciyata. Yaya Sadiq ne ya fadomun arai, gabana ne ya yanke ya faɗi, da sauri na buɗe idona na kalli yatsun hannuna, azurfar da ya bani har yanzu tana hannuna. A fili na furta “ko wanne hali yake ciki yanzu? ko yaji sauƙi daga cutar dayake? Ko yaya yaji da yaji labarin na auri ɗan’uwansa? Se Allah.” mikewa nayi jikina a sanyaye na shige dakina, toilet na shiga nayi brush saboda manjan danaci a waina dayake mun makaki a makogoro, duk da nayi brush ɗinma amma banji daidaiba, alawar danake sha kullum na dakko na saka abakina sannan na fito daga ɗakin na nufi kitchen din. Jikina a sanyaye na haɗa masa coffee din, sosai nakejin ba daɗi ajikina saboda tuno yaya sadiq danayi, bawai dan soyayyar da muka yiba, se dan tsananin tausayinsa. juye masa coffe ɗin nayi a cikin tea flaks ƙarami na ɗauki cup na nufi dakinnashi bugun zuciyata na sauyawa. Knocking nayi a hankali, nayi 3 minutes a tsaye sannan yazo ya buɗe mun, a niyyata in mika masa kawai in juyo amma senaga ya juya ya koma ciki batare daya karbaba, binsa nayi badan nasoba na ajiye masa akan bedside locker, rigar wanka ce ajikinsa ga kuma jikinnasa da ruwa alamun daga wanka ya fito. bance masa komaiba ina ajiyewa na juyo na nufi kofa da niyyar fita se naji yace, “ki dafomun indomie guda ɗaya” juyowa nayi na kallesa yana tsaye a gaban madubi yana shafa mai, kamar zanyi kuka na amsa masa sannan na fita. wani munafukin Murmushi mustapha yayi yacigaba da shafe_shafensa. Cikin mintuna ƙalilan na dafa masa indomie’n guda biyu dan a ganina ɗaya bazata ishesaba. Juye masa nayi a cikin plate na ɗauki fork guda ɗaya na nufi dakinnashi.

Harya gama shiryawa,yana zaune akan carpet a kasa yana operating system, a hankali lokaci zuwa lokaci yana kurbar coffee din dana kawo masa. Da sallama na shiga ɗakin, batare daya dagoba ya amsamun, a gabansa na ajiye masa plate ɗin, na mike da niyyar fita. Alama yamun hannunsa alamun najirashi. Komawa nayi na zauna a ɗan nesa dashi akan carpet din, lumshe idona nayi ina shaƙar kamshinsa daya ƙara yawaita a ɗakin fiye da dazu dana shigo. wani iri nakejin jikina kamar wata mara lafiya. Ko minti biyar banyi da zamaba naji yana faɗin, “wakika dafawa wannan indomie’n?” buɗe idona nayi da sauri na sauke su akan fuskarsa, haɗa ido mukayi na ɗauke idona da sauri nace masa. “Kai mana” still idanunsa na kanta yace, “da yawa haka nace miki?” Yamutsa fuska nayi kaɗan nace, “wannan ɗin ce me yawa, guda biyu cefa kawai” “amma ai ɗaya nace miki” ya faɗi haka cikin wata irin murya kamar me rada. Ya tsareni da tsumammun idanunsa. “To ainaga ɗayar bazata ishekaba shiyasa” na faɗi haka cikin shagwaba. be ƙara cemun komaiba, ya sa cokali ya fara cin indomie’n sa hankali kwance cikin nutsuwa. kaɗan yaci ya tashi yana faɗin, “ki cinye kafin na fito” waro ido na nayi waje nace, “nifa na koshi cikina kamar ze fashe” becemun komai ba, se toilet daya shiga abunsa. Rufe flate ɗin indomie’n nayi na matsar gefe, ban kawo komaiba akan zaunar dani ɗin da yayiba, tunanina wani aikin ze sakani. jingina bayana nayi ajikin gado, sosai bugun zuciyata yake karuwa. Na rasa meyasa a ƴan kwanakinnan nakejin hakan a tattare dani. fitowa yayi daga toilet din yana faɗin, “kije kiyi alwala” “alwala kuma?” na tambayeshi da mamaki ɗauke akan fuskata” yana dakko dadduma yace mun, “ehhh karatu zamuyi.” “Karatu kuma?” na maimaita a zuciyata, amma a zahiri mikewa nayi na nufi toilet din, sanin danayi baya son musu ko jayayya. Toilet din nashi, fess dashi babu ko digon ruwa a ƙasa, kamshi sabulu me daɗi ne yake tashi a toilet din. Sink na nufa nayi alwalar na fito. Yana zaune akan dadduma ya fuskanci alkibla, yana ganin na fito ya mike yana faɗin, “zo mu fara sallah tukunna” a hankali nace “nayi Sallah tafa” “eh nasani” ya faɗi haka yana bina da wani kallo. ban ƙara cewa komaiba, na ƙarasa na tsaya a bayansa. Tada sallar yayi nima nabi bayansa, raka’a biyu mukayi. Muka sallame, tambayoyin yafaramun akan addini, tsabar rashin wayona har yanzu na kasa harbo jirginsa, Ni harga Allah na ɗauka karatun zamuyi da gaske. duk da yadda yake tsareni da ido da kuma baccin da nakeji haka na daure nake bashi amsar duk abunda ya tambayeni daidai gwargwado, nayi mamakin iliminsa a kan fannin addinin musulunci, dan tambayoyinma se mutum nada ilimin ze iya yinsu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button