Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Zannurainne yashigo falon, zama yayi agefen mahaifiyarsa, gaishesa nayi, bayare daya kalleniba ya’amsamun, yau kam naci sa’a ya’amsamun amma duk da haka gwarashi akan haidar. “Mommy yaufa ba’a gyaramun dakiba, yanacan yayi kaca_kaca.” “Meyasa my son, su salame basuzobane?” “Sunzo ina bacci, that is the why” “ohk bari nakirasu yanzu su gyara maka” “no, mommy leave them, wannan yarinyar taje ta gyaramun kawai”. Bansan meyasaba naji gabana yayanke yafadi, duka maganar dasukeyi inajinsu, Allah yasa kar mommy ta yarda naje na gyara masa, nifa harga Allah bansan zuwa dakin maza, sukuma naga hakan bakomai bane agurins…….”maryam kije kigyarawa zannurain dakinshi yanzu” muryar mommy takatsemun tunani. Cikin ladabi na’amsa mata. “Toh mommy, amma bansan inane dakinba” kwatantamun part dinnasu mommy tayi, mikewa nayi zuciyata babu dadi, nafice. Ina kallon fuskar yaya sadiq nagane Sam beji dadin hakanba. Da tafiya daga part din mommy zuwa nasu, suma part dinnasu babbane kuma shima yayi kyau. Sama nahau kamar yadda mommy tacemun, dakin dake left side, nashiga. Banwani tsaya karewa dakin kalloba, saboda burina inyi ingama gyaran. Filallika nasauke kasa nafara karkade zanin gadon, wani abune karami naga yafado daga kan gadon, dauka nayi ina dubawa. Zaro idonayi nayi waje, domin bazantaba mantawa da abunnanba, saboda asanadinsa aka taba zanemu lokacin muna j.s 3, wata kawarmu aka kamashi, ni’a time dinma bansan ko meneba, sedaga baya salimat takemun bayani wai sunansa condom, da kuma dalilin dayasa ake amfani dashi. Ajiyewa nayi zuciyata cike da mamaki, tome zannurain yakeyi dashi shida ba mataba. Ajiyewa nayi tare da Tabe baki, nacigaba da gyaran dakin, nagama gyaran gado ina kokarin share dakin, naji anturo kofar dakin. Dasauri nadago dan ganin meshigowa, zannurain dinne, yana kokarin maida kofar yarufe……..✍️

idan banga ruwan comments ba zamu koma gidan jiya, kuma bansan guntun comment dogon sharhi nakeso

BY
Zeey kumurya

ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

1️⃣5️⃣

……….maida kofar yayi ya rufe,hakan yayi daidai da buguwar da zuciyata tayi, cak na tsaya rike da tsintsiyar ahannuna,ina kallonsa, hade fuskarsa yayi yana bina da wani mugun kallo tamkar yaga kashi, wayar hannunsa ya ajiye akan mudubi,toilet naga ya nufa,becemun komaiba. Wata sassanyar ajiyar zuciya nasauke,bayan ya shiga toilet din. Sunkuyawa nayi nafara sharar,cikin sauri,sonake kafin ya fito nakarasa saboda kasancewarmu a daki daya bedaceba. Ko Rabin dakin banyiba,naji ana knocking kofar dakin,ajiye tsintsiyar hannuna nayi naje na bude,zuciyata nadan bugawa. Yaya sadiq nagani tsaye fuskarsa ahade, kallona yayi na wasu sakanni,sannan yace, “wuce mu tafi” da mamaki nake kallonsa,zanyi magana yadagamun hannu,jiki asanyaye nabiyo bayanshi muka fice. Tafiya mukeyi amma babu Wanda yayiwa dan’uwansa magana,nalura ransa abace yake sosai,danni tunda nazo gidanma bantaba ganinsa cikin irin wannan bacin ranba,domin shi mutum ne ma’abocin fara’a da raha. Har kofar part dinmu yarakani, satar kallonsa nayi naga shima ni yake kallo,duk senaji na tsargu, ahankali na juya na fara tafiya, na shige part dinnamu. Wata sassanyar ajiyar zuciya sadiq yasauke bayan tashige,shima juyawa yayi ya koma part dinnasu……….

Turus zannurain ya tsaya bayan yafito daga toilet din,ganin babu maryam adakin, ga shara ta fara kuma bata karasaba. Cikin dacin rai ya fita domin ganin iskancin daya hanata karasa masa gyaran dakin,ga toilet dinma bata wankeshiba. A falon kasa yaci karo da yaya sadiq,daya shigo part din,zagaye shi yayi yana kokarin fita sadiq ya rukosa. Tsayawa yayi batare daya juyoba, “kama dena wani sauri,kana tafiya fuuu kamar zaka tashi sama,nasan mekake shirinyi,toni nace ta koma,ka gyara dakin da kanka,kokuma Wanda suka saba gyara maka su gyarama,aidama ita banda gyaran dakinku aka dauketa aiki a gidannan,danhaka daga yau karka kara sata gyaran daki,nafada maka,kuma karka kuskura kace zaka mata wani abun!” Yakarasa zancen dadan daga murya, zannurain bashi dadamar musawa sadiq abunda yace,domin duk fitsararsu basayiwa yayyensu,dan daddy bebasu wannan tarbiyyarba,ga kuma oga kwata_kwata mustapha yanajin labarin kayiwa nagaba dakai rashin kunya seya sabarmaka. Juyawa yayi,yakoma sama yana kunkuni aransa amma bece komaiba……..

Seda gabana yafadi danashiga falo,ganin suhailat kwance akan cinyar mommy ita kuma mommy tana waya,ni indai ba tsautsayiba bana kaunar abunda zehadani da suhailat. Sallama nayi batako kalkeniba balle ta amsamun,mommy cema kawai tadagamun hannu tana bina da kallon dabana ganemasa, narasa meyasa indai muna guri daya duk dagowar dazanyi senaga mommy tana bina da wani irin kallo,araina nakance ko dabi’arta kenan kalllon mutane oho,danni kallonnata yafara isata. Dakina nashige.

Mommy bayan tagama wayar datakeyi ta shafa kan suhailat Wanda ko dankwali babu,tana fadin, “yadai daughter naga kamar ranki abace,meke damarmunkene.?” Cikin tabara tace, “mum, yayanefa daga naje part dinsa dazu yayitamun fada yanamun tsawa,karshema koroni yayi wai duk akan kamal yazo gidannan,kuma nafada masa abokin karatunane” murmushi mommy tayi tace, “aidama nasani,toki kwantar da hankalinki kidena damuwa bari nakirasa awaya nabashi hakuri” “yawwa mommy ta thanks” pick mommy tamata agoshi. ta dakko wayarta ta yi diarling number shi, har 2 missed call tamasa amma bedagaba. “Kinga daughter, beyi picking call dinba,amma mubari zuwa later idanma bekiraniba senaje har part dinnasa,natausheshi” “tom shikenan mum,bari naje na kwanta bacci nakeji” suhailat ta fadi haka tana tashi daga jikin mommy. “Ohk daughter sekin tashi”……

Bayan sallar sala’ar ina toilet ina wanke kayan dana cire naji,ana knocking kofar dakina,tsane hannuna nayi na dauraye na fito na bude. Daya daga cikin masu aikin gidan ce, gaisawa mukayi tacemun infito falo hajiya tana nemana. Amsa mata nayi nakoma na dakko hijabina nasaka,ina mamakin mommy,yanda idan tana nemana bazata iya zuwa takiraniba da kanta, dukda muna part daya,sedai ta turo wasu dasukecan da nisa,aganina ai wannan wahalace. Da sallama abakina na karasa falon,ina bin bakin masu kamala dake falon da kallo. Wata dattijuwace,sekuma wata yar budurwa dako zata girmemun kadanne. Tsugunnawa nayi na gaishe da dattijuwar cikin ladabi, ta amsamun fuskarta dauke da fara’a,ita kuwa matashiyar se kallona takeyi. Sannu namata,amsawa tayi ta kara da fadin, “aunty,kinga nasaki baki se kallonta nakeyi,naganta kyakkyawa masha Allah,mommy ina kika samu wannan me aikin kyakkyawa da ita,gata kuma……”kai aliya badai danbanzan surutuba,daga ganin yarmutane zaki fara cikata da surutu.” Wadda sukazo taren ta fadi haka,da alama kuma mahaifiyartace saboda tsananin kamar dasukeyi. Nidai murmushi kawai nayi,mommy ma murmushin tayi tana kallona. “Maryam baki mukayi,kije kihado musu abinci” cewar mommy tana mikewa. Cikin ladabi na amsa mata ina tashi. “Bari inzo intayaki” cewar budurwar itama tana mikewa,Murmushi nakara mata akaro na biyu. Tare muka Shiga kitchen din, muka hado kayan muka jera akan dinning, mamakinta ya cikani,daga ganinta itama daga gidan kudi ta fito,amma jibi yanda takemun babu kyama kokuma nuna banbanci,ashe dai masu kudin akwai masu kirki. dakina na koma,bayan mun kammala. “Gaskiya aunty me aikin gidan daddy menasara,ta burgeni zanso ta zama frnd dita,bari nagama cin abincin nan naje musha hira.” cewar aliya tana kokarin kai abinci baki. Harararta aunty tayi tace, “zadai kije cikata da shegen surutunnan naki, Mara kan gado,to itadai kinga yanda take, daga ganinta bameson hayaniya bace,karkije ki takura mata.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button