Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

KANO

Yau suhailat da wani matsananci ciwon kai da zazzaɓi tatashi. jikinta gaba-daya rawar dari kawai yakeyi. misalin ƙarfe 11 na safe mommy tashigo dakin datake tana fadin. “kinanan kina wannan shegen baccinnaki na jaraba ko? kinsandai nan bagida bane babu masu aiki, kitashi kifito kimun shara.” Wasu hawayene masu zafi suka zubowa suhailat, ita kadai tasan azabar datakeji ajikinta amma mommy tashigo tana mata masifa, duk mommy tabi ta canza mata yanzu kullum se fada da masifa, kamar ita tadora mata damuwar dake damunta. kan gadon datake mommy ta karasa da nufin tatasheta. tana dora hannu ajikinta taji zafi zau. “suhailat bakida da lafiya ne?” suhailat bata bata amsaba, hawa gadon mommy tayi ta janyota jikinta. da sauri suhailat ta janye jikinta daga na mommy, saboda kamshin turarenta data shaka bemata dadiba. kafin tayi wani yunkuri tuni wani amai yataho mata, kokarin sakkowa tayi daga kan gadon kafafuwanta kawai ta zuru aman ya kufce mata, ta fara kelayashi a nan bakin gadon, tamkar zata amayar da kayan cikinta saboda azabar aman, se haki takeyi tana kelayashi. kallonta mommy tayi cikin wani irin yanayi na alamar tambaya. gaba-daya suhailat din ta canza mata, jikinta har wani yalo yakeyi tsabar fari, ga cika data kara sekace wata matar aure, seyanzu ta lura da hakan. jan jiki tayi takoma kan gadon ta kwanta tana sauke numfashi,bayan aman ya tsaya mata. “Sannu” mommy tace mata adakile. dole ta mike tahau gyara gurin tanayi tana tsaki, bayan tagama gyara dakin ta gogeshi tass. ta dakko room freshener ta hau fesawa. suhailat na shaka wani aman yakara taso mata, da gudu tatashi tanufi toilet ta fara kakari. tsayawa mommy tayi cak tana kallonta zuciyarta cike da fargaba gami da wasiwasin meke damun suhailat din take ta kwara amai haka. wani tunani tayi dasauri tafice daga dakin taje dakin datake taɗauki wayarta takira likitanta ta mata bayani atakaice. Address din gidannata ta tura mata. da rarrafe suhailat ta fito daga toilet din, jikinta gabadaya ya mutu babu kwari kokadan a bakin toilet din ta kwanta, domin ko kan gadon bazata iya karasawaba. mommy data shigo taganka a haka tana numfarfashi se tausayinta ya tsirga mata. dagata tayi ta kaita kan gado ta kwantar, suhailat kam se toshe hanci take dan batason turaren mommy kokadan daga mata hankali yakeyi bakadanba. yanda jikinta yayi zafi zau se mommy ta rage mata kayan jikinta, towel ta dakko da ruwa ta daddanna mata ajikinta, se zafin jikinnata yaragu,amma se rawar sanyi take. lulluba mata blanket mommy tayi bajimawa bacci yadauketa. fita mommy tayi tafara rage ayyukan gidan. wajen 12/30 doctor din tazo. Bayan sungaisa mommy tamata jagora zuwa dakin, har lokacin suhailat baccinta takesha. duddubata ta shigayi, tanayi tana tambayar mommy yanayin yanda taga jikinnata. jininta ta diba tace, zataje asibiti ta auna seta dawowa da mommy da result din. godiya mommy ta mata, sukayi sallama ta tafi………..✍️

By
zeey kumurya
ABINDA KASHUKA….

5️⃣0️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

………A ɓangaren Sadik kuwa yau da wani matsanancin ciwon kai yatashi wanda ko idansa yakasa budewa saboda azabar ciwon kan, hakanne yasa besamu yafito ganin Maryam ba, kamar yadda yaci alwashi jiya. daga ciwon kai jikinshi gaba-daya yaɗauki wani irin zafi, da kyarma. tun yana iya sanin duniyar dayake ciki harya fice daga hayyacinsa……..

        ********************

DARMANAWA

Saleemat ce zaune adakinta da waya a hannunta yau wurin sati guda kenan tana trying number’n Maryam amma a kashe. cikin takaici tafito daga dakinnata ta nufi dakin umma. ”umma wlh haryanzu wayartata a kashe, kuma su ba matsalar NEPA ba, bare nace caji ne babu a wayartata.” saleemat ta fadi haka bayan ta daga labulen dakin. umma tana dubanta tace, “toko matsalar network ne, saleema?” “gaskiya umma bana jin network ne, wayarce dai a kashe” “to Allah yasa dai lafiya” “lafiya kalauma insha Allah, nafi tunanin wayarce ta samu matsala” “to Allah yasa muji Alkhairi” “Ameen, umma bari nakarasa ninkin danakeyi naje gidan gwaggo nasanar mata dakaina” murmushi umma tayi tace, “saleemat ba kunya, kawo kayan lefennaki zaki fada mata da kanki” dariya saleemat tayi tace, “Aiso nake na kunnota kwana biyu shiruma banjitaba” umma tace, “nimun hadu da ita jiya, dana fita, naga tanata sauri ne, shiyasa banfada mata kawo kayan ba.”….

Gwaggo tana zaune adakinta tanata lissafe kudinta na adashi dana aikatau din Maryam. tanayi tana mitar sabon wata yashiga amma shiru bataji alert na aikatau din Maryam ba, gashi tanata kiran number’n lami bata shiga. sabuwar me aikin datayi me suna laure ce tashigo dakin ko sallama babu. zabura gwaggo tayi tashiga boye kudin akasanta. tana fadin, “ubanme yashigo dake dakina babu sallama, kinga laure kikiyayeni” tabe baki lauren tayi tana jijjiga kafa tana jifan gwaggo da kallon raini tace. “Kekika sani dai, uwar mako da rowa, wannan uban tumulin kudin ina kikasamoshi gwaggo?” cikin harzuka gwaggo tace, “bansaniba uwata, nace bansaniba, kujimun yarinya da fitsara haifata kikayi dazakizo ki titsiyeni da tambaya, to a gidan uwarki nasamo” “badai uwataba gaskiya” laure ta fada tana kauda kai gefe. “bazan kulakiba dannasan uwarki bata baki cikakkiyar tarbiyyaba, ina fatan kingamamun ayyukana. “Cabb, wannan uban ayyukan sekace wata jaka, nayidai iya abinda zan iya” rike haba gwaggo tayi tace, “aa..lallai laure rashin kunyartaki kullum kara gaba take to wlh baki isaba sekinmun duka ayyukan gidannan, zandinga biyanki kudin aikine a banza bakyamun aiki yanda Yakamata. wani kallon banza laure tayiwa gwaggo sannan tace. “Nawane kudinnaki da har kikemun iko akansa, akan 20,000 din dako kayan kwalliya bata isata na siya” “kinsan da haka meyasa kikazo mun aikin, Ai da sekiyi zamanki uwarki ta dinga baki” laure zatayi magana wayarta dake kan cinyarta tayi kara, fita tayi domin ta daga wayar. gwaggo ta bita da harara. kullum sesunyi sa’insa da laure, yarinyar da inda ta haihu setayi jika da ita. amma ta rainata laure bata da tarbiyya kokadan, duk fadan gwaggo da masifarta laure tafi karfinta, duk iskancin dataga dama shitakeyi kuma gwaggo bata isa ta hanataba sedai kallo da ido. kullum se gwaggo tashiwa Maryam albarka tana cewa, “yarinya me biyayya da hakuri bakamarkiba laure” a duk sanda gwaggo ta fadi haka se laure tatabe baki tace da gwaggo. “To kinsan da itan kika daukeni, kije ki dawo da ita mana” a kauye lami tasamowa gwaggo laure, dududu batafi wata da zuwaba amma ta gallabi gwaggo, ga yawon bin samari. gwaggo tanata cigaba da lissafinta na kudadenta, zuciyarta fari kal kamar takadda tatara kudin komawa Saudiyya. Ashe fitar da laure tayi tana waya, wani saurayinta ɗan daba ne yakirata wanda sukayi magana tun jiya zasuzo da abokansa suyiwa gwaggo fashi. tunda ta kyallara ido taga kudin gwaggon takirasa ta fada masa, amma da sharadin bayan sun kwaci kudin itama zebata nata kason. Bayan befi 40 minutes ba, suka karaso unguwar. Laure ce tafita dakanta ta tarosu ta musu jagora har kofar dakin gwaggo.(fashi da ranar Allah????)

Gwaggo kawai jitayi an banko mata daki anfado babu ko neman izni, susu biyarne. suka tsaya mata cirko_cirko ai. zabura tayi, ta mike tsaye tare fadin. “Subhanallahi suwaye ku, wadannan samudawa daku zaku shigomun gida har daki. lafiya?” daya daga cikinsune yace, “lafiyar ce takawo haka” wuka da yafito da ita daga aljihunsa tare da karbar wani mulmulallen karfe a hannu wani yana muzurai yacewa gwaggo. “Ki bamu kudin dake cikin gidannan ta lallami kokuma na fardeki na kwata” “wanne kudi kuma, uwarku ta bani ajiyan….” “Ke!” wani daga cikinsu yadaka mata da tsawa yana zaro wuka shima daga aljihunsa yana nuna gwaggo da ita. duk da gwaggo ta tsorata amma bakinta be mutu ba, kuma tace kome zesu mata bazata basu dukinba. ganin tana bata musu lokaci, wanda ya mata magana da farko ya kwada mata ƙarfen hannunsa akafa sau biyu, gwaggo ta hau ihu tana neman taimako. Toshe mata baki sukayi sannan suka datsa mata wuka agefen kafadarta, ga azabar yanka gata rufe mata baki da hanci da sukaimata, nanfa numfashinta yafara sarkewa daga karshema se numfashin ya dauke dif. Kasan gadonta kawai suka daga sukaga kuɗin acikin leda babba sekuma wani a cikin tarkacen kwanukanta, seda suka kwace kuɗin gwaggo kaf, ko sisi basu barmataba sannan suka tsallaketa suka fice. suna fita laure tabi bayansu da kunshin kayanta dama tagama hada komai nata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button