Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ina gunjin kuka,na zare sakatar gidanmu,na nufi gidansu saleemat.gidan abude yake,idan babansu yaje masallaci baya kara rufewa.ko sallama banyiba saboda rudewa kafata ko takalmi babu,umma tana kokarin hura gawayi saboda yan makaranta ta hangoni nashigo a hargitse. “Maryam lafiya dasassafennan? “Umma kitaimakamun mukai inna asibiti ta suma,kuma babu inda yake motsi ajikint…ai umma bata bari na karasaba tayi hanyar fita,dama da hijabinta ajikinta.bin bayanta nayi.muna zuwa naga ta kara kunnanta akan hancin inna, duddubata naga tanayi.batacemun komaiba,kawai gani nayi taja bargo ta lullube inna har fuskarta.

Janyoni tayi jikinta idanuwanta na zubar da hawaye,sonake nayi magana amma na kasa,saboda nidai nasan Wanda ya mutu kadai ake lullubewa.dakyar na iya tambayar umma cikin rawar murya.”umma,bangane me hakan yake nufiba,umma dan Allah kada kicemun innata ta mutu,wlh nima mutuwa zanyi.cikin San kwantarmun da hankali,umma tace”innarki bata mutuba,bari na fadawa baban salermah,yasamo mota mukaita asibiti. Ajiyar zuciya na sauke.umma ta rabani da jikinta ta fice daga dakin.intakaice miki zance,baban saleemah yazo,da wani likita har dakin inna,karshe dai likitan ya tabbarmana,Allah ya karbi baiwarsa inna,ya mata rasuwa.

Cakumar likinta nayi,ina kuka nace.”karyane innta bata mutuba,innata bazata taba mutuwa tabarniba.janyeni umma tayi daga jikinsa,itama tana kuka tace.”haba maryam, kefa musulmace,kuma kinsan dukkan merai mamacine,ki yarda da kaddara,yanzu inna bata bukatar kukanki addu’arki kawai take bukata. “Yanzu umma kema kinyarda inna ta mutu,wlh bata mutuba suma tayi,damafa bata da lafiya mukaita asibiti,wancan karanma haka tayi,umma kitaimakeni mukaita asibiti,nasan zata tashi,inna bazata mutu ta barniba.kuka kawai nakeyi na fitar hankali,ina maganganu marasa kan gado.hannuna umma ta kama muka fice daga dakin. Duk wannan abun da akeyi gwaggo tana daki tana barci,har lokacin bata fitoba.

Kafin karfe 7 na safe,gidanmu ya cika da mutane anata koke koke,makuta da abokanan arziki domin inna ta kowace,kowa seyabonta yakeyi.se’alokacin gwaggo ta fito ta kama kukan munafurcinta,babu Wanda yabi ta kanta. Nidai ina zaune nayi jigum,kukanma babu ya dauke,zuciyata ta kekeshe.duk da ni yarinyace a lokacin amma nasan dacin mutuwa.bin kowa nake da kallo,domin ni banyarda inna ta rasuba,nasan suma tayi kuma zata farfado. Seda ‘yan kauyenmu suka karaso sannan,aka mata sutura.nidai ina daki umma ta rikeni gam taki sakina.wata ‘yar uwarsu innace,dasukazo daga kauye tazo ta kama hannuna,ta kaini dakin inna.wata irin harbawa zuciyata tayi saboda ganin inna,kwance a cikin makara,kwace hannuna nayi na fada kan makarar ina sakin kuka.”wayyo innata,dan Allah kitashi,karki tafi ki barni,kitashi kice musu baki mutuba,inna bani da kowa seke,meyasa zaki tafi kibarni,kece uwata,kece ubana,kekadai nake gani inji dadi araina,innaaaa!!!….. Kuka yaci karfina. Janyeni akayi,su baban saleemah da wasu ‘yan uwan inna,suka kinkimi makarar. Wani karfine yazomun na tashi da sauri, na kankame makarar,ina ihu ina fadin baza’a fitarmun da innataba,amma inaji ina gani aka janyeni aka ficemun,da sanyin idaniyata,me tallafar rayuwata.

Bankara sanin meyafaruba,se farkawa nayi na ganni akan cinyar umma,tanamun firfita,idanta yayi luhu_luhu alamun taci kuka ta koshi.yunkurawa nayi dakyar,na tashi zaune.sannu mutanen dake dakin suka kama yimun,kaina kawai na iya daga musu.saboda wata muguwar sarawa da kaina yakemun.dole na hakura nadau dangana,akan tabbas inna ta rasu.amma tashin hankalin da rudanin da zuciyata ta shiga baze misaltuba.kowa yazo ya ganni seya zubarmun da hawaye.nasiha sosai umma tamun.akan yadda da kaddara.nayi kukan fili Dana zuciya.Mara adadi akan rashin inna.haka akayi sadakar uku aka watse,a lokacin mutuwar inna tadawomun sabuwa.bana ci bana sha,se aikin kuka.dakyar umma take sani nakecin kwayoyin abinci,suma jinsu nakeyi tamkar madaci.komai ya tsayamun cak.kunci da damuwa sun taru sun mun yawa.hakan ya haifarmun da matsanancin ciwon kai,Wanda ko idona dakyar nake motsawa.karshedai har kwanciya nayi a gadon asibiti saboda ciwo,mutuwar gwaggo ta dakeni sosai,kuma har yau bata bar dukanaba,idannatunota inajin tamkar yau abunyafaru.

Ahankali ahankali komai yake wucewa na duniya,haka innata ta shude ta zama sedai tarihinta,ahankali rashinta yafara bin jikina,nabawa zuciyata hakuri da dangana akan rashin innata.addu’a kawai nake mata nasan shine abunda tafi bukata.’yan uwan inna,sunso tafiya dani kauye amma gwaggo tace”zata rikeni anan,saboda makaranta ta,badan sunsoba,suka hakura suka barni,awajenta.

Gwaggo ta gaje,gidan innata,tagaje komai nata.ta koma dakinta ma da zama ni kuma ta koroni dayan dakin.gwaggo bata bani abinci,babu ruwanta da cina balle shana.shargoriyarta kawai takeyi.tatara kawayenta su cika gidan,su kunna kida suyita rawa wataranma har maza take kawowa.mutuwar inna ko’ajikinta.umma ce,take bani abinci da duk wani Abu danake bukata.kudin makaranta kuma babansu saleemat ne yake bamu tare.ahaka rayuwa taita tafiyarmun babu dadi kokadan.cikin ikon Allah muka zana jarrabawa,kuma duk munci nida saleemat.nayi farin ciki sosai,danaci, kuma naji dadi.shine Abu na farko daya sanyayamun rai bayan mutuwar inna.amma naso inna tananan tatayani murna. Babansu salermat ne yamana,komai tun daga uniform,littattafai da duk abubuwan da’ake bukata.duk da shima bawani karfine dashiba,sedai rufin asirin Allah.

Nafara makaranta,kuma inajin dadinta sosai,tana debemun kewa.amma term 2 kawai naje,gwaggo ta hana.tacemun tagaji da zama ba Sana’a dole inzauna,indinga mata Sana’a agida.nayi kuka,na roki gwaggo,amma gwaggo taki hakura.akan haka har fada sukayi da umma.baban saleemat yace”umma ta kyaleta saboda shi bayason fitina.tun daga lokacin gwaggo ta maidani tamkar jaka,ko wata baiwa.nice,wankinta,shara,wanke_wanke,girkin gida dana kayan sana’arta.baruwanta da kankantar shekaruna haka take tulamun uban aiki.bani da Hutu kwata_kwata se cikin dare.Tun inayi ina kuka saboda rashin sabo da gajiya,harna saba.mugunta kala_kala nashata a wajen gwaggo,ta rabani da kowa,har umma ta hanani zuwa wajen ta,sedai na saci hanya naje,bata saniba.naci wahala bakadanba,awajen gwaggo.duk abunda zan mata,bata gani sedai ta sakamun,da duka koda zagi,ko mugun alkaba’i.gwaggo bata da imani,kokadan muguwace ta karshe,kanta kawai tasani arayuwarta.indai zata samu kudi ko menene zatayi,makota kowa kuka yakeyi da ita.saboda munanan dabi’unta.

Ajiyar zuciya,nasauke ina duban baaba talatu,data kuramun ido kawai tana saurarona,idanuwanta na zubar da hawaye.nima hawayen fuskata na share,nace”wannan shine takaitaccen labarina.naso fayyace miki komai,amma lokaci baze barmuba,kuma banason tuno wasu abubuwan da suka faru dani.

“Gaskiya,maryam kinga rayuwa tunkina yar karamarki,labarinki akwai abun tausayi,Allah yajikan innarki da mahaifiyarki.mahaifinki kuma idan har yana raye Allah ya bayyana miki shi,da gaggawa. “Ameen baaba,nagode. “to,amma maryam wayakawoki gidannan aikatau?. “Wata kawar gwaggoce lami,ta dakkoni daga gida,amma ba ita ta kawoniba wata hajiya lamice daban. Jinjina kai talatu tayi,tabbas nasan hajiya lamin,mutuniyar hajiyace sosai.Mikewa baaba,talatu tayi tana fadin,”muje muyi sallah kinga har anyi isha’i.sena fada miki aikinki a gidannan,da kuma takaitaccen tarihin gidan,kafin masu gidan su fito cin abincin dare.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button