Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Direban mommy yakai mata suhailat kamar yadda ta bukata, suhailat tana shiga falon gidan taga mommy zaune ta rafka uban tagumi. dagudu tatafi tafada jikinta ta rungumeta tana kuka. “Cikin takaicin dake nukurkusar mommy tace, “Meyafaru daughter?” “Mom, meyasa kikayi haka, gashi yanzu duk suntafi sunbar gidan, mom dan Allah kiyi hakuri kijanye kudirinki kibawa daddy hakuri kidawo gida, mucigaba da rayuwarmu medadi kamar da.” janye suhailat mommy tayi daga jikinta tana fadin. “Yaro man kaza!”. daga haka bata kara cewa komaiba ta mike tanufi daya daga cikin dakunan dake falon. suhailat kuwa kuka tacigaba tayi, domin ita damuwarta daya a yanzu maganar auranta da mustapha batasan ina maganar ta kwanaba, tana matukar kaunarsa bazataso ta rasashiba. wayarta dake cikin jaka ta dakko saboda kiran da’ake tamata tuntana mota. kamal ne yake kirannata, cillar da wayar tayi akan kujera danbatashi takeba a yanzu. Binta kuwa dama tunda taga mommy ahaka, tamata sallama tayi tafiyarta. Abun duniyafa yataro yayiwa mommy yawa, takasa zaune takasa tsaye, ita burinta a yanzu kawai tasan ina su daddy suke, idan tasan haka to komai zezo mata da sauki aganinta………..

Maryam, tadade tana bacci sosai dantayi fiye da awa uku, sebayan la’asar tatashi. Ahankali ta sakko daga kan gadon aunty ta nufi toilet, alwala ta dauro tadawo tatada sallah ganin har lokacin ta yana kokarin kurewa. bayan ta idar tazauna tana addu’a, Alhamdulillah taji saukin jikinta sosai, zugi da radadin da hannunta shima se kadan yanzu. tunani nashigayi akan abunda yafaru dani jiya, amma nakasa tunawa, gaba daya kaina ya kulle. kawar da tunanin hakan nayi nashiga wanda yazamarmun jiki wato tunanin mahaifina, koyana raye koya mace se Allah. A fili na furta “ya Allah kabayyamun mahaifina,kowani dan’uwansa kafin na mutu.” nima naga dangina kamar kowa. hawayen daban shirya musubane naji sunabin kuncina, koyaushe zandena kukan rashin mahaifi da danginsa se Allah. mikewa nayi naninke dardumar danai sallah akai na ajiye. bakin kofa nanufa na bude nafita. Falon babu kowa bakamar yadda nazataba, kitchen nanufa nanma babu kowa, dakin mommy naje nayi knocking nanma shiru. gabanane naji yafadi kawai senaji ina tsoron zaman kadaicin, danna fuskanci babu kowa asaman. harna nufi dakina sekuma nafasa nasauka kasa. Ajiyar zuciya nasauke saboda ganin asabe me aiki. Cikin jindadi nace. “Aunty asabe, sannu da gida” “yawwa maryama kintashi” “eh” “yajikinnaki” “dasauki, inasu mommy ne da aunty naji gidan tsit” “wlh duk basanan maryam, dan hajiya babbama yaubansata a idonaba, se hajiya karamace tacemun idan kintashi nafada miki sun fita” jikina asanyaye nace, “to aunty asabe nagode, bari nakoma sama” ina tafe ina tunanin ina su aunty da mommy suka tafi, kodai jikin yaya mustapha ne yayi tsamari suka tafi gurin magani.?” bani dame bani amsa, hakan yasa nace. “Allah yasa alkhairi ne fitar tasu” kitchen na shiga nahada tea, nasha sannan nasha maganina da doctor yabani. zama nayi afalo cikin rashin sanin abunyi nahau karanta wasikar jaki……..

Daddy ne zaune agaban gadon da mustapha yake kwance yakura masa ido cikin tausayawa, yaro mejuriya da dauriya akan dukkan abunda yasamesa amma wannan yakasa jure masa, se faman shan wahalar ciwo yakeyi. gaskiya atika ta cutar dashi, amma sakamakonta yanaga ubangiji shiyasan meze mata. Ahankali yabude lumsheshshun idanunsa yana bin saman dakin dayake da kallo. beyi yunkurin koda motsiba face silik din dakin daya kurawa ido kawai yana kallo, daddy yanacan duniyar tunani bemasan yatashiba. aunty dake zaune akan darduma tana lazimi kamar ance tadago takalleshi taga yafarka. mikewa tayi tana fadin, “yaya kaga yatashi” maganar aunty tadawo da daddy daga duniyar tunanin daya tafi. “Masha Allah” daddy yafadi haka cikin farin ciki yana kallon mustapha daya juyo yakura musu ido baya ko kiftawa. “Sannu, son yajikinnaka bari nakira doctor” cewar aunty tana kokarin juyawa tafita. da hannu yamata alama alamun karta fita tazo garesa. aunty bata musaba takarasa gareshi. kama hannunta yayi, cikin tsananin kaunarta dabayajin yanawa kowacce diya mace aduniya bayan mahaifiyarsa se ita. girgiza mata kai yahauyi kafin yayi karfin hali fara mata magana da muryarsa dabata fita sosai saboda ciwo da fadin. “Kada kiwahalar da kanki aunty wajen kiran doctor,domin nasan wannan ciwonnawa bana tashi bane inaji ajikina shine zezama ajalina” yakarashe zancen yana taune lips dinsa,saboda azaba da zugi da zuciyarsa kemasa. kwallace tatararwa aunty a idonta, kokarin maidata tayi tace. “haba Muhammad, kadena irin wannan zancen ba lokacin yinsu bane,insha Allahu zaka samu lafiya kawarke kakoma kamar da” kara damke hannun aunty yayi tare da runtse idanunsa, dago hannun aunty yayi yadora adaidai saitin zuciyarsa yafara magana a wahalce. “Aunty kinjifa yanda zuciyata take bugawa, inajin wani irin radadi acikinta dama dukkan jikina, aunty inaji tamkar ana zarar numfashi nane” bude idonsa yayi yadorashi akan na aunty wadda hawaye keta kwarara akan kuncinta yacigaba da magana. “Aunty nikam gwara mutuwa da wannan”……. hannu aunty tasa tatoshe masa bakinsa da sauri ta hau girgiza masa kai, Cikin kuka tafara magana. “Haba Muhammad, kaifa musulmine kazama me yarda da kaddara aduk yadda tazo maka. kada kazama me butulcewa Allah, duk abunda hakuri bebakaba rashinsama baze bakaba, kayi hakuri insha Allahu duk wannan abunda ze faruwa wataran seya zama tarihi, kaji tamkar ba’ayiba. Very soon zaka koma rayuwar farinciki da jindadi fiye da da.” lumshe idonsa yayi yanajin ninkin kaunar aunty nakara ratsa zuciyarsa. ahankali yakai hannu yana share mata hawayen dake fuskarta batare daya bude idontasaba,dan har cikin ransa yakejin kukannata. murmushi aunty tayi Cikin tsananin kaunarsa ta rike hannunnasa ta sumbata. Ahankali tace, “bakaso kaganni ina kukane son?” daga mata kai yayi alamun eh. “To idan kanaso indena se kamun alkawarin zaka dena damuwa, zaka mikawa Allah dukkan lamuranka, kuma zaka dena tunane_tunane. domin shine yajanyo maka wannan ciwon dakakeyi.” bude idonsa yayi yana murmushi yace, “nadena uwa tagari, kuma alkawari namiki insha Allah zandena tunanin komai, indai zakiji dadi” murmushi aunty tayi Cikin jindadi tace. “Nagode sosai, son,Allah yabaka lafiya.” takarashe zancen dakai hannu tana shafa lallausar sumar kansa. Daddy dake tsaye yana kallonsu cike da bansha’awa da tausayawa, duk dauriyarsa amma seda kwalla tacika masa ido, amma bebarta tazuboba yamaidata. Yana mamakin yanda sauda take kaunar mustapha, fiye da yayan cikinta a yanda take nunawa. itama ayanxu tausayi take bashi, duk hankalinta ba’a kwanceba, tabaro yayanta da mijinta duk dan akan takula da mustapha, gaskiya ya jinjina kaunar datake masa. cike da kauna mustapha ke binta da kallo harta fice domin kiran doctor. sannu daddy yakarayiwa mustapha cike da tsananin kulawa. Aunty tare suka dawo da doctor ya duddubashi bayan yamasa sannu da addu’ar samun sauki. bayan fitar doctor bajimawa su faruq suka dawo dakin, alokacin mustapha yana zaune yajingina bayansa da filo, aunty tana bashi tea a baki. Sunyi matukar farincikin ganinsa ahaka, cike da dunbin farinciki suka karasa garesa suna jera masa sannu. dakai kawai yake amsa musu, yanamejin tarin kaunarsu acikin zuciyarsa. mustapha yatabbatarwa kansa duk duniya bashida kamar daddy da ahalinsa, yanajin koda yayi katarin ganin mahaifiyarsa ko wani nashi, baze iya barin su daddy ba, sedai sucigaba da kasancewa tare. yanda yaga kowa yana nuna jindadinsa da farincikinsa akan yanda sukaga yasamu lafiya, seyaji wani dadi da sanyi yana ratsa zuciyarsa, ahankali damuwar dake cunkushe acikin ruhinsa tafara gushewa, Cikin ransa amabaton sunan Allah kawai yakeyi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button