Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kuyi manage da wannan Please, gobe insha Allahu zan baku new update, Ku ƙara hakuri dani dai.????????

By
Zeey kumurya
ABINDA KASHUKA….!

BY
ZEEY KUMURYA

6️⃣7️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

………..Binta da kallo Mustapha yayi harta shige kitchen din cike da tausayawa yasan dauriya kawai amma bata jin daɗin jikinta. cire kansa yayi daga kafadar ammi batare dayace mata komaiba ya mike yabi bayan maryam. Itama ammin tausayin maryam takeji matsananci, tarasa meyasa kuma, tun ranar data fara ganinta taji tausayinta me tsanani ya zirga mata, kuma a duk lokacin data ganta setaji wani abu acikin zuciyarta dabatasan meneneba, tanason ta tambayeta ina mamanta da babanta suke? Suna raye ko sun mutu? Tunda ita dai bata taɓa jin tayi zancensuba ko wani ɗan’uwanta bata taɓa ji tayi zancensaba, sedai gwaggonta kawai. kuma ammi ta fuskanci tamkar maryam ɗin tana da wata damuwa a tattare da ita. Numfashi ammi ta sauke a ranta tana faɗin, “yau kam insha Allahu bazatayi ƙasa a gwiwaba zata tambayi Maryam tarihin rayuwarta”……Maryam tana cikin dauraye flate ɗin dazata zuba masa abinci ya shigo kitchen din, tsayawa yayi daga bakin kofa yana kallonta, bansan ya shigoba se kamshin turarensa kawai naji gami da jin wani abu na yawo ajikina kuma bugun zuciyata ya sauya, juyowa nayi naganshi tsaye ya harde hannunsa a kirji, kasa ɗauke idona nayi daga kallonsa amma ba directly ido da ido ba, saboda tsananin kyawun daya ƙaramun, kayan jikinnasa sun masa matuƙar kyau sosai, fuskarsa se annuri take, kamar na dawwama ina kallonsa haka naji. Takowa yayi a hankali ya ƙarasa inda take ya tsaya daf da ita yana kallon fuskarta, shafa saman idonta yayi cikin wani salo yace, “wannan kallon fa, kamar yau kika fara gani na?” Lumshe idona nayi ina sauke numfashi bance komaiba. Rungumeta yayi ta baya a jikinsa tare kai hannunsa ya shafa cikinta yana murmushi yace, “bari inji lafiyar baby nah” buɗe idona nayi da sauri na ɗan waro shi waje cikin mamakin Abunda yace, amma bance komaiba. Seda yagama shafemun cikin son ransa yana shishshina wuyana sannan ya sakeni ya fita, ina sassauke numfashi na ɗauki plate din da cokali da saving spoon na fice daga kitchen din. Kan dinning na koma na zuba masa abincin a cikin plate danni bana tunanin zan iya cin wani abu a yanda nake jin jikina. Rufewa nayi da wani plate din na dora spoon akai na nufi cikin falon, akan Centre table na ajiye. Ammi ta dubeni tana murmushi tace, “sannu ɗiyata” murmushi nayi nace, “yawwa” sannan na koma na dakko masa ruwa da cup na kawo na ajiye. Ammi se sannu takemun kamar wadda nayi wani babban aikin, ga wani kallo datake bina dashi dana kasa gane masa. zama nayi a ƙasan kujerar da suke na dubi yaya dake latsa wayarsa nace, “yaya ga abincin” gyada mun kai kawai yayi. Ammi da kanta ta sakko ƙasa ta zauna kusa dani, nuni tamun da hannu na miko mata abincin, tashi nayi na dakko mata na ajiye mata a gabanta. kallon Mustapha tayi tace, “NOOR sakko kaci abincin mana kar yayi sanyi” batare daya dagoba daga latsar wayar da yakeyiba yace, “ammi taci kawai, Ni naci later” ammi tace, “A’a, nasan halinka anjiman baci zaka yiba ka sakko kawai” ajiye wayar tasa yayi yana murmushi ya sakko ya zauna a ɗayan gefen ammin, muka sata a tsakiya kenan. Buɗe plate ɗin saman tayi ta saka spoon a cikin hadaddiyar pride rice din dataji kayan hadi se tashin kamshi take, ta debo abincin ta kai bakin mustapha, buɗe bakinsa yayi a hankali ta zuba masa. ƙara debowa tayi ta kai bakin Maryam, duk da banajin cin abincin amma haka na buɗe bakina a kunyace nima ta zubamun…..haka ammi taita bamu abincin a baki cike da kulawa da kauna gami da tattali, harseda muka cinye duka na cikin plate din, ruwa ma da kanta ta tsiyaya a cup ta bamu, duk ni naso karba nasha da kaina amma tace ita zata bani ta cikashe ladanta. Plates din da mukaci abincin na ɗauka na kai kitchen na tsaya dauresu. Mustapha bayan yagoge bakinsa da tissue ya kama hannun ammi ya haɗe da nasa yana murmushin yace, “nagode Ammi nah, Allah yasaka Miki da gidan Aljannah” murmushi ammi tayi ta tsare shi da ido tace, “Ameen, amma NOOR, meyafaru ne yau, naga kana cikin farinciki wanda yakasa boyuwa a fuskarka” murmushi yayi a karo na ba’a daɗi daga daren jiya zuwa yau yace, “babu komai ammi nah” ammi ta masa wani kallo tace, “akwai mana NOOR duk wannan murmushin dakake fa nasan bana kawai bane” murmushin ya kumayi me sauti sannan yace, “au da bana murmushin?” Ammi ta hararesa tace, “kafi kowa sani ai, bama murmushi kawai ba, komai naka ya canza a yau har maganarka ta yawaita akan da, yau ko ɗan miskilancinnan babu” wannan karon dariya yayi saboda yanda ammin tayi maganar, shi kanshi yasan yau ɗin rana ce ta dabance a cikin rayuwarsa kuma kamar yadda ammi ta faɗa yana cikin tsananin farin cikin, a yanda yake jin kansa ma yanaji tamkar babu wanda ya kaishi farin ciki a yau. Itama ammi murmushi tayi bata ƙara cewa komaiba. A haka Maryam ta fito ta samesu, itama Maryam ɗin ammi ta lura tana cikin farin cikin, hakan yasa ta fasa yiwa Maryam tambayar data kudiri niyyar yimata akan rayuwarta dan karta yi sanadin tadawa Maryam ɗin da damuwarta. Ammi ta daɗe a part ɗinmu muna hira cikin nishadi, tanata bamu labarin yan’uwanta da dangin mahaifin yaya, senaji dama nice nake da dangin mahaifin kamar haka. Takuma ce bayan sallah insha Allahu zamuje Niger ɗin mu zazzaga yan’uwa, dan har yau bata sanar musu da bayyanar mustapha’n ba, tafiso ta kaishi su ganshi da idanunsu. Mustapha dama yana da kudirin ya tambayi ammi yanason ta kaishi yaga danginsa se gashi tamasa zancen da kanta.

Bayan sallar magriba muna zaune a falon ammi, dazata dawo daga part dinmu na biyota muka taho tare. Umaimah datake kwance a ɗaki tun safe tana kunci ta fito falon cikin shirinta da alama fita zatayi. Ina kwance akan doguwar kujera, ina yin game a wayar ammi, banko motsaba balle na dago na kalleta. umaimah ta harari maryam taja wani uban tsaki ta shige ɗakin ammi ganin bata falon, ina jinta amma duk da haka nayi kamar bansan da halittarta a cikin falonba. Ammi na ninke wasu abayoyi dazata bawa direbanta ya kaiwa wata mata da zata siya umaimah ta shigo dakin, ammi ya dubeta tace, “ke kuma lafiya kike kuwa yau” tana zama a gefen ammi tace, “lafiya kalau nake” ammi tace, “to mene kuma kike ta ɓata rai, tun safe kin kule a ɗaki ko abincima bance kinciba” umaimah ta zunburo baki gaba tace, “babu komai fa ammi dagaske, kainane ke mun ciwo amma yanzu ya dena nasha magani” ammi ta mata wani kallo tace, “Allah ya ƙara sauƙi” taci gaba da ninkinta. Umaimah tace, “Ammi zani gidansu Farda ne, na shigo na faɗa miki” ammi tace, “gidansu Farida kuma a darennan? mezakiyo?” Umaimah tace, “ammi abu kawai zangani, yanzu zan dawo” “mene abun da zaki gani, baza ki bari se Allah yakaimu safiyaba kije” umaimah ta marairaice tace “Please ammi nah, dan Allah kedai ki barni yanzu zandawo wlh ba jimawa zanyi ba” ammi ta mata wani kallo kamar tanason ta gano wani abu tace, “shikenan yanzu dama zan aiki driver gidan Hajiya zulai, seki bisa ya saukeki, idan ya kaimata seya dawo ya ɗauke ki” umaimah tana murmushin jin daɗi tace. “Yawwa amminah nagode” “saura kuma ki daɗe” ammi ta fadi haka tana saka abayoyin a cikin wata jaka. “Insha Allahu Ammi bazan dadeba” ammi ta bata jakar kayan ta fice. ko da ta fito ma seda ta ƙara hararata da tsakin sannan ta fice, ni batasan ba ta ita nakeba dan bana jin daɗin jikina.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button