Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

By
Zeey kumurya
ABINDA KASHUKA….!

BY
ZEEY KUMURYA

6️⃣5️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

……….Batare datayi knocking ba ta murda handle din ɗakin ta shiga babu ko sallama. Maryam tana kwance akan gado tayi rigingine idanunta a lumshe, mustapha kuma ya zaune ta wajen kafafunta ya ɗora su akan cinyarsa yana mammatsa mata a hankali, daya shigo ne take masa complain din har yanzu bata jin daɗin kafartata shine yace bari ya mata tausa. Umaimah da bata taɓa tunanin ganin Maryam a ɗakin ba ba ƙaramin shock ta shigaba data ganta harta kusa yarda tire ɗin hannunta, Allah dai ya taimaka be faɗin ba ta ajiyeshi. Ita duk a tunaninta Maryam tanacan ɗakinta tana bacci shiyasa ma Mustapha’n yace ta kawo masa daki. “ashe tananan kwance ita hamshakiya yana mata tausa kamar wani bawa da uwargijiyarsa” umaimah ta faɗi haka aranta ranta na ɓaci. Wani irin ɗaci ne ya ziyarci zuciyarta ƙasa kawai tayi kanta zuciyarta na wani irin bugu saboda kunci batare datace ƙalaba ta mike da niyyar tafiya. Mustapha dake kallonta yace, “jirani” buɗe idona nayi a hankali mukayi ido huɗu da umaimah, kallonta nake cike da mamaki dan banmasan sanda ta shigo ba, maida kallona nayi garesa da’alamun tambaya, dagemun gira yayi tare da mun wani lallausan murmushi, nima martanin murmushin na maida masa. A hankali mustapha ya sauke kafar Maryam daga jikinsa yana faɗin “my one kinji daɗin kafar yanzu ko?” Gyada masa kai nayi ina yunkurin tashi zaune. ƙara kallon Umaimah nayi nace mata. “Sannu fa” umaimah dake tsaye kamar dogari ta haɗiye wani yawu me ɗaci makut tace, “yawwa” kamar an mata dole tana kau da kai gefe. Sakkowa mustapha yayi daga kan gadon yana duban umaimah ya mata nuni da hannu alamar ta kawo masa kayan abincin kusa dashi, ɗauka tayi cikin sauri ta kai masa tana tunanin zece ta tafi karta ƙara ganin abunda ze ɓata mata rai, amma setaga ya ƙara tsaida ita, badan tasoba ta tsugunna ɗan nesa dashi kaɗan tana hararar Maryam ta gefen ido. Juyawa yayi ya kalli Maryam cikin wata irin murya me daɗin saurare da tsumar da zuciya yace, “luv sakko kiyi break” dan ɓata rai nayi na girgiza kaina tare da faɗin, “na koshi fa” wani kallo yamun wanda na kasa gane masa sannan ya lumshe idonsa ya buɗe cikin wani irin salo me narkar da zuciya. hannunsa ya mikomun yace, “to zo kiji” batare dana kama hannunnasaba na sakko daga kan gadon ina ƙoƙarin zama a gefensa bazantaba kawai naji na janyoni na faɗa kan cinyarshi. Cikin shagwaba nace, “washhh….ka kusa ballanibafa” gefen fuskata ya shafa yana murmushi cikin rada yace mun, “idan na karyaki dawa zan dinga…..” (???? nidai zeey musty be barni naji ƙarshen zancennashiba) Fuskata na rufe cikin jin kunyar abunda ya faɗa ina murmushi. Kissing gefen wuyana yayi ya ƙara gyaramun zamana ajikinshi, tire din ya ƙara janyowa gabanmu ya shiga bubbɗewa. kamshin stew ne ya daki hancina lumshe idona nayi yawuna na tsinkewa. Soyayyayiyar doya da kwai ya dakko yanka ɗaya ya kai bakina yana faɗin “haa” make kafada nayi ina turo baki gaba nace, “nace maka na koshifa” marairaice fuska yayi cikin lallashi yace, “haba tawan ki daure kici ko kaɗan ne, banason yunwa ta illatamun ke” ƙara shagwabewa nayi na kwantar da kaina a kirjinsa nace, “nifa bakina babu daɗi, kabarni kawai kaikaci” hannunsa yasa yazagaye jikina yace, “ki daure kici ko kaɗanne Please, kinsan idan bakiciba bazan iya ciba nima, Please dear eat” ya ƙarashe zancen yana kuma marairaicewa. a hankali nace, “to bani zanci” kiss ya sakamur a gefen kuncina yace, “yawwa matar Aljannah ta.” murmushi nayi cikin jin daɗin yanda yakemun. Doyar ya ƙara mikomun bakina a hankali na buɗe bakinnawa ina jiran ya samun kawai se kai bakinsa yana dariya ƙasa_ƙasa wadda ta ƙara fito da tsananin kyawunsa dimples ɗinsa na kunci biyu suka ƙara lomawa abun sha’awa. bata rai nayi na turo bakina gaba kamar zanyi kuka. a hankali cikin nutsuwa ya fara taunawa yana jifana da wani irin kallo ƙasa_ƙasa yana wani munafukin Murmushi. seda ya cinye sannan yaja karan hancina yace, “yadai Madam” cire hannunshi nayi daga fuskata na yunkura da nufin na tashi ina faɗin, “kuma ba ruwana dakai” maidani yayi jikinshi yace, “am sorry zo in baki” kawar da kaina nayi nace, “bazanciba kuma” batare da yayi maganaba ya ƙara dakko yankan doyar guda ɗaya ya saka a bakinsa amma ba dukaba dan gefe kaɗan, Juyo da fuskata yayi daf da tasa har muna jiyo hucin numfashin juna, ‘yan yatsunsa guda biyu yasa ya buɗe bakina banzataba kawai naji ya haɗe bakina da nashi ya sakamun doyar bakinshi acikin bakina. umaimah dake tsugunne a gefe tamkar almajira tana kallonsu tamkar ta samu TV, wani irin zafi zuciyarta take mata, takaici da baƙinciki duk sun lullubeta abunda yafi kona mata rai yanda mustapha ya tsayar da ita, kuma tamkar ya manta da ita se sha’aninsu sukesha wanda ke ƙoƙarin tarwatsa mata zuciya, gashi bazata iya tafiyaba batare da mustapha ya bata umarniba dan gudun karta saɓa masa. Lumshe idona nayi ganin yadda yake kallona kuma yaƙi sakin bakinnawa, wani irin yammm..nakeji ajikina saboda lips dinsa dake gogar nawa, a hankali nake taune doyar harna cinye, ƙoƙarin janye bakina nayi daga nasa amma yaƙi bani damar hakan sema ƙara mamular lips ɗina da yake yana tsotsa, seda ya tsotsa san ransa sannan ya sakarmun bakin yana sauke numfashi, nima sauke numfashin nake cikin wani irin baƙon yanayi daya riskeni. Harga Allah na manta da wata umaimah a ɗakin, seda naji yana mata magana da faɗin. “Sorry na barki kina jirana ko? dama gyaran falo zaki ɗan gyara mana idan babu damuwa” yanda yayi maganar zaka gane da tsantsar rainin hankali yayita. Umaimah datake jin kamar ta fasa ihu, ta tattaro duk wata dauriyarta tace. “Ok babu damuwa” buɗe idona nayi da sauri na kallesa nace, “data barshi nima zan iya fa” lakacemun kumatu yayi yace, “no kibarta tayi kawai keda baki da lafiya ina ke ina wani aiki” zanyi magana ya ɗora finger dinsa aka lips ɗina yace “shiiiiii, kinsan banaso kina wahala ki barta tayi kawai” maida kallonsa yayi ga umaimah yace, “you can go” mikewa umaimah tayi cikin wani irin mummunan yanayi, har wani jiri_jiri takeji tsabar baƙin_ciki, tana fita falo ta saki kukan datake ta dannewa, durkushewa tayi a ƙasa, mustapha da Maryam kawai take hangowa a idonta manne da juna suna zuba love. datasan wannan baƙincikin zatazo tatarar da wlh bazata kawo musu breakfast dinba, gashi abunda yafi bata mata rai wai ta gyara musu falo, wato bayason matarsa ta wahala itace baiwa kenan ita zata wahala. Kwafa taja ta share hawayenta ta mike ta fice batare data gyara falonba. Ni kuwa bayan fitar umaimah na dubeshi srioustly nace, “Allah yaya daka barta tatafi zan iya gyara gidan da kaina” hararata yayi yace, “baki da lafiyar zan barki kiyi wani gyaran gida.” ina tashi daga jikinshi nace, “nafa warke Ni, dama kuma ba cuta nakeba.” Be ƙara mun magana se abincin daya cigaba da ci hankali kwance cikin nutsuwa. Seda ya gama ya dubeni fuska babu wasa yace, “zo” ganin yanda yayi yasa na matso kusa dashi, abincin ya dinga ɗiba yana bani a baki fuskarsa babu walwala kamar bashi yagama yintaba ɗazu. seda ya tabbatar data koshi sannan ya rufe sauran. Tashi yayi ya dakko magani da ruwa yazo ya ɓalle ya mikomun, nida banason shan magani harda zanyi musu naga yamun wani kallo, ba shiri na karba na sha ina yatsina fuska. ganin yanda ta tsorata dashi seya ɗan saki fuskarshi, ɗaukarta yayi cak suka kwanta akan gado, bargo yaja ya lullubesu cikin tsokana yace, “tunda kin warke bari na ƙara” “Ni ban warkeba” na fadi haka kamar zan fashe da kuka danna ɗauka dagaske yake ze ƙara yi ɗin. daga kafadarsa yayi yana tabe baki yace, “ke kika faɗa da bakinki, Ni baruwana ƙarawa zanyi” kuka tasa wanda kana gani kasan na taɓara ne tace, “nidai A’a kuma sena faɗawa Aunty idan ka ƙara” murmushi yayi yasa hannunsa yana ƙara rungumeta ajikinsa ganin tana ƙoƙarin tashi. Kuka Maryam take bilhakki, shafa kanta ya hauyi cikin lallashi tare da hura mata iska daga bakinsa a cikin kunnenta. amma bece mata komaiba, ganin kukannata bana ƙare bane, seya dago fuskarta, idanunta a rufe suke baccima ya fara ɗaukarta amma tsabar rigima batabar kukanba, a hankali ya zira mata lips dinsa na ƙasa acikin bakinta, dif ta dauke kukan ta fara mamular lips dinnasa kamar jaririn daya kama nonon uwarsa tana sakin ajiyar zuciya. seda ya tabbatar bacci ya ɗauketa sosai sannan ya zare lips dinnasa a hankali daga cikin bakinta. Kwabe fuska tayi ta turo baki gaba alamun bataso hakanba. lips dinta ya shafa a fili yace, “rigima girl” yana aikin kallonta besan sanda shima bacci me daɗi ya ɗaukeshiba…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button