Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Watarana ina daki inayin karatun alkur’ani da sassafene, lokacin mustapha yayi kusan wata takwas ahannunmu, yanata rarrafensa atsakar gida yana wasansa. Atika kuma tanata kokarin hada mana abunkari domin fitar wuri nakeyi zuwa gurin aiki, shayi ta sauke atukunya kafin tajuye a flaks, abunka da yaro yana ganin ta ajiye tukunyar ya rarrafa gurin da gudunsa, ina daga daki ina hangoshi banyi tunanin komaiba dannaga atika tana gurin nasan bazata barshi yataba tukunyarba, sunkuyar dakaina nayi nacigaba da karatuna. Ihun da mustapha ya kwallane yasani dagowa dasauri, hangoshi nayi yabude murfin tukunyar yatsoma hannunshi acikin ruwan shayin atika na kallonshi tacigaba da aikinta. dasauri nafito daga daki nadaukeshi cike da tsananin tausayawa, gabadaya ya gigice se kuka yakeyi da dukkan karfinsa. ruwa nadebo nashiga kwara masa ahannunnasa seda nazuba masa ruwan sosai, sannan nadakko gishiri na barbada masa natottofamasa addu’oi. dakyar nasamu bacci yadaukeshi bayan yaci kuka yagode Allah, muryarshi hardashewa tayi, se faman ajiyar zuciya yake saukewa. Har hawaye seda namasa alokacin tsabar tausayawa. bayan naje na kwantar dashi adaki nafito nasamu atika datake ta aikinta hankali kwance nace mata. “Kin kyauta atika, yau nakara tabbatar da imaninki ragaggene kina kallon yaron harya bude tukunya da ruwan zafi aciki amma kigagara daukeshi. Toya kone hankalinki ya kwanta, zanfita idan kintashi duk abunda kikaga dama kimasa kokasheshinema kiyi,amma kisani Allah baze barkiba, Abunda kikashuka shizaki girba kema bakisan ahannun wanda danki ze rayuba nangaba, zaki iya haihuwa kimutu kibar dan, domin babu wanda yasan zeyaru da dansa har abada, itama uwarsa batasan wannan kaddarar zata sametaba aduniya, kuma ki sani zalintar marayan Allah kikeyi,kikiyayi gamuwarki da ubangiji” inagama fada mata haka najuya nafice daga gidan raina a tsananin bace.

Hakadai mukacigaba da rayuwa a garin nijer ina rainon mustapha, yaro me tsananin hakuri idan kaji kukansa tobakaramin abubane, atika tamasa mugunta kala_kala duk abunda zecutar dashi koda tana gani bazata hanaba, yasha zuba yaji a idonsa kokuma yaji ciwo da wani abun. Amma duk da haka yaron Kallon mahaifiya yakewa atika, danyana ganinta sefara wangale mata baki yana mikamata hannu alamun tadaukeshi. Ko yarane suka shigo namakota idan kiwarsa tatashi seyaki zuwa gurinsu yayita binta,ita kuma intaga dama ta daukeshi tana dungure masa kai, idanbatagadamaba kuwa ko kallonsa batayi sedai yayi abinsa shikadai yagama. Mustapha befi shekara dayaba ahannunmu atika tafara laulayin ciki, murna da farincikin danaji bazata misaltuba, duk da ina kallon mustapha amatsayin dana amma nima inason naga dana nacikina, atika tayi murna sosai taita yada habaici ga yaron dabemasan me duniya take Cikiba, dan ita a ganinta danbani da dane yasa nakeson mustapha yanzu kuwa tunda zansamu nakaina sena rage sonsa. batasan abunbahaka bane soyayyar mustapha acikin jinina take, ina kaunarsa sosai gami da matsanancin tausayinsa. Alhamdulillah zuwa wannan lokacin nasamu rufin asirin kaina, natara kudadena. Harna fara tunanin dawowa kasata dazama gabadaya kodan yawan Aiken danakesha daga gurin yan’uwana musammanma Isma’il kanina.

Wataranar juma’a dabazan taba mantawa da itaba arayuwata, bayan ansakko daga masallaci dama ranar juma’a bama fita aiki. Lokacin cikin jikin atika yayi wata hudu, ina zaune adakina ina ware kayana masu amfani damarasa amfani danbanajin zankara sati biyu a nijer. Jakar danake ajiye abubuwa nasauko senajita da nauyi sosai, mamakine yakamani domin ni namamanta da batun jakar da babar mustapha ta bani, tun ranar kuma bankara dakko jakarba. cike da mamaki na ajiye jakar na budeta, tozali nayi da jakar se’alokacin natunata,to jarabar atika kadaima ta isa tasa tamanta da ita. Banyi kasa agwiwaba na dakkota, yarkaramar jakace me gurare ajikinta. Kananun zip din nafara budewa, a wani naga azurfa babba bata danyatasaba ta tsintsiyar hannu, sekuma wani abu kaman tambarin gidan sarauta kona wani abu dai, anyi rubutu da yaren French ajiki, ajiyesu nayi agefe na bude babban zip din jakar, abunda nayi tozali dashi acikin jakarne yakusa zautar dani…………✍️

Ba editing????????

TO MASOYA WANNAN SHINE LAST PAGE DINMU KAFIN AZUMI, SEKUMA IDAN ALLAH YAKAIMU BAYAN SALLAH,ZAMU DORA A PAGE 37 INSHA ALLAH, NAGODE MASOYAN ABUNDA KASHUKA ALKHAIRIN ALLAH YAKAI MUKU ADUK INDA KUKE AFADIN DUNIYA

By
zeey kumurya

ABUNDA KASHUKA….
(shizaka girba)

3️⃣7️⃣

INAWA DAUKACIN AL’UMMAR MUSULMI BARKA DA SALLAH, DAFATAN ANYI SALLAH LAFIYA. ALLAH YA MAIMAITA MANA YA AMSHI IBADUNMU,AMEEN????????

Bismillahirrahmanirrahim

……….Gwalagwalaine a duddunk’ule tamkar duwatsu se daukar ido da kyalli gami da walwali sukeyi. jikina na rawa nasaka hannu nadakko curi daya ina dubawa dannakara tabbatarwa. dan gani nake tamkar idonane kemun gizo,babu tantama gwalagwalaine acikin jakarnan. ahankali nadago ina kallon mustapha dake kwance yana bacci, ina tunanin wanne irin kudine da mahaifiyarsa haka dahar tabani wannan irin kayan dukiya haka, kamar kuma antsikareni sena mike dasauri nafice ina kwadawa atika kira domin tazo tatayani ganin abunda nagani ko idonane yake mun gizo. “Lafiya sulaiman kake kwadamun irin wannan kira haka sekace sabon makaho?” cewar atika tana yamutsa fuska. cikin rudu nace mata, “atika abun mamaki nagani, kema zokiga abunda nagani” banjira amsartaba najuya nakoma dakina tana biye dani abaya, da hannu nanuna mata jakar batare danace mata komaiba. tsugunnawa tayi tadakko gold din daya ahannunta tana dubawa. Zaro ido atika tayi waje cikin gigita tace, “sulaiman wannan ai gold ne ina kasamo su,waya baka,ko satowa kayi?” banbata amsaba se zama danayi agefenta ina kara fito da sauran ina dubawa. kara tambayata atika tayi akaro nabiyu da fadin”sulaiman tambayarkafa nake kamun shuru,kuma kana jina”. Cikin daukewar tunani daga kwanyata nace mata. “Ranar da mahaifiyar mustapha ta bani shi aranar tabani acikin wannan jakar, ninama manta da ita seyau ina duba kaya naganta shine na dakko naga menene aciki senaga wannan abun nida farkoma nadauka nine bangani daidaiba,shiyasa nakiraki kitayani gan….” gani kawai nayi atika ta washe baki tatashi ta rangada guda gami da juyi tana rawa tana waka cikin tsananin farin ciki,batare data bari nakarasa zancenaba. sakin baki nayi kawai ina kallon ikon Allah. Surar mustapha tayi daketa baccinsa tahau yimasa rawa tana fadin. “Yaro ashe da arzikinka kake tafe, Ashe ta sanadinka mafarkina zecika inzama matar attajiri,kai amma Allah yayiwa mahaifiyarka albarka, nikam tagamamun komai arayuwata databawa sulaiman wannan irin dukiya metarin yawa” cikin tsananin mamaki nake dubanta baki bude, dakyar nayi dauriyar cemata, “atika mekikeyi hakane?” Bata kulaniba secigaba da juyi da mustapha datayi, aiko mustapha yace besan zanceba, yaji ana wujijjigashi tuni yafarka da kukansa. zama tayi tana lallashinsa abunda atika bata taba yimasaba tunda nakawoshi gidan. seda yayi shiru ta dubeni tace, “yanzu sulaiman semu dawo da tafiyarmu gida nankusa muje musaida wadannanan gwalagwalan muwataya mu fancakala muyi wadaka da dukiyar datazo mana, tsuntsu daga sama gashashshe” kallon mahaukaciya nayiwa atika sannan nace mata, “haba atika yadaga ganin dukiya hankalinki yabar jikinki gabadaya duk kinbi kin burkice, wannan dukiyar dakike gani bazan taba komai daga cikintaba, dukiyar marayan Allah ce, zan ajiye masa harzuwa sanda ze girma ya juya abarsa,kuma ni bana cire ran bazankara ganin mahaifiyar mustapha ba, ko wani nata, lokaci kawai nake jira dazannemomasa danginsa insha Allahu, kinga kuwa dazarar munhadu dole nabasu dansu da dukiyarsa” gabadaya fara’ar dake fuskar atika daukewa tayi hartana kokarin yarda mustapha dake kan cinyarta. Cikin takaici tace, “lallaikuwa sulaiman daka cika me bakin hali, mu raini yaron sannan kuma kace bazamuci dukiyarsaba salon inya girman yajuya mana baya, bayan mungama cin wahalarsa,wlh baka isaba abunda bazeyiyuba kenan,aka’idama wannan dukiyar tazama tamu tunda yanzu mune uwarsa mune ubansa,mune shansa da suturarsa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button