Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Doctor yazo yaduba hannun maryam yasa mata maganin,yakuma bata wasu dazata dinga sha. har Aunty tagama hada yan abubuwan datasan zasu bukata atafiyarsu sukayi sallar azhar amma daddy shiru_shiru bedawoba bekuma kirataba. part din mustapha takoma domin tagano halin dayake ciki, tana zuwa tatarar dashi cikin mummunan yanayi. cikin kidima mommy takira daddy danta sanar masa. “Hello, yaya ina katsayane?” numfashi daddy yasauke yace, “saudart ina hanyata tatafiya na bugi wata motane, yanzu haka muna asibiti” “innalillahi’wa’inna’ilaihirraji’un, subhanallah Allah yasadai babu wanda yayi mummunan rauni” “to, su biyune dai acikin motar, da driver da wata mata, direban yar buguwa yayi, sunma samasa ruwa, matar cedai kwance haryanzu likitoci nakanta” “ya Allah, Allah katakaitamana” “ameen” “yanzu kuna wanne asibitinne” “Aminu kano” “OK, bari muzo nida su faruq, Allah yakiyaye gaba” bayan sunyi sallama mommy takira faruq tace yadakko mota yazo bakin part din mustapha. taboyewa daddy halin da mustapha yake cikine saboda kar abun yamasa yawa,wannan tashin hankali har ina, dama haka rayuwatake,watarana dole se Allah ya jarrabeka. koda faruq yazo yaga halin da mustapha yake ciki hankalinshi yatashi sosai shima, batare da bata lokaciba yakira su haidar suka kamashi sukasashi a mota suka nufi asibiti dashi. aunty ce, tafadawa asabe me aiki sunfita, idan maryam tatashi tasanar mata, dantunda tasha maganin da doctor yabata sekuma bacci yadauketa. Asibiti mafi kusa dasu suka kaishi wanda yakasance private ne, suna zuwa aka karbeshi likitoci suka rufa akansa,domin ceto rayuwarsa……..

mommy cikin mintuna kalilan takarasa gidanta dake lamido, wanda babu kowa aciki se megadi. horn tahau dannawa ba kakkautawa megadi dake kwance adakinsa yana bacci yaji horn din tamkar a mafarki. ahankali yabude idonsa yajidai azahiri yakejin horn din, dasauri yatashi yasuri rigarsa yasaka yafito danyaga waye a wannan lokacin yakatse masa baccinsa. karamar kofar gidan yabude ya leka, ganin motar mommy ce yasashi komawa da sauri ya bude mata get din, zuciyarsa cike da mamakin ganinnata domin tunda yazo gadi gidan bata taba zuwa a irin wannan lokacin ba, tafi zuwa da yamma koda daddare. A fili ya furta “banda abuna,ita da gidanta mene nawa aciki.” gudu_gudu, sauri_sauri, yakarasa inda mommy take bayan yarufe gida. “Hajiya sannu da zuwa dafatan kin iso lafiya” yafadi haka yana kokarin karbar jakar hannunta kamar yadda yasaba a kodayaushe idan tazo yakai mata har cikin falo. Amma yau ga mamakinsa seyaga tadaga masa hannu bata bashi jakarba, bakuma ta amsa masa sannun dayake mataba tayi wucewarta ciki. kallonta kawai yatsaya yanayi harta bacewa ganinsa, zuciyarsa cike da mamakin ta, dan duk da bata da sakin fuska amma yau yaga abun yafi na kullum, yana tunanindai akwai matsala tunda gashima ita kadai tazo, sabanin da datake zuwa da driver wani lokacin ma, harda danta. komawa dakinsa yayi domin cigaba da baccinsa.

Momy tana shiga falo ta ajiye jakarta gami da mayafinta akan kujera, zuciyarta sam babu dadi, zarya tafarayi afalon cike da tsananin damuwa, se’alokacin wani gumi yafara keto mata. tanunawa su daddy warkewar mustapha bedaga mata hankalibane dankarsuga gazawarta da wuri. Amma bakaramin dimuwa gami da tashin hankali tashigaba, musamman datasan boka yace, idan aiki ya lalace komai zekoma kan sadiq ne. Tarasa meyasa tun mustapha yana karami kome tamasa na sharri sedai taganshi akan yayanta, taso mustapha ya lalace yazama mebin mata kuma takadirin dan shaye_shaye amma kuma sebezamaba, seyayantane sukeyi. lokacin da mustapha suka fara soyayya da suhailat agabanta suhailat zata dane kan cinyarsa kotayi huging dinsa amma bata hanata, duk dan mustaphan yalalace amma kuma belalace dinba. “tabbas! yazama dole natafi Neman mafita ayau ba gobeba, yanzu_yanzu ma kuwa!” mommy ta fadi haka a fili,tana cizon yatsa. (Hmmm, momy kenan, aishi sharri dan aikene.) wayarta dake cikin jaka ta dakko ta lalubo number wata kawarta takirata. tayi sa’a wayar tashiga amma harta katse bata dagaba,kara kira tayi nanma bata dagaba. Tsaki mommy taja afili ta furta. “ko’ina binta tashiga tabar wayartata oho,Inata kiranta amma taki dagawa” kara kiranta tayi akaro na uku, harta kusa katsewa sekuma ta daga. “Hello kawata, uwargida agidan alh mai nas”………. “kinga dalla ni badogon zance nanemaba, ina kika shiga inata kiranki baki dagaba” mommy ta katseta da fadin haka. “ina falone ina hutawa wayar kuma na daki” “ohk, idan babu damuwa inason ganinki yanzu domin akwai wata matsala babba” “matsala kuma atika, tame?” binta tatambayeta cikin kidima. “Kedai kawai idan da hali kizo, maganar bazata yiyu a wayaba, amma bana gida zanturo miki address din inda nake sekizo kisameni.” “Tom, shikenan ba matsala ganinan zuwa yanzunnan” “yawwa binta sekin karaso” mommy nagama fadar haka ta katse wayar, address din inda take ta turawa binta kawarta. jefar da wayar tayi akan kujera bayan text din yaje, zama tayi itama akan kujerar ta rafka uban tagumi da hannu biyu tana tunane_tunane.

Bayan 40 minutes binta ta karaso gidan da mommy take, bayan tafito daga motarta sungaisa da megadi take tambayarsa ina mommy, dantaga gidan part 2 ne. jagora megadi yamata har bakin part din da mommy take, godiya ta masa ta karasa bakin falon tayi knocking. Ajiyar zuciya mommy ta sauke jin ana knocking, dantasan bintace ta karaso. “A shigo” tafada atakaice domin kofar abude take. turowa binta tayi tashigo taname bin falon da kallo, kafin tace, “atika wannan gidanfa,gidan waye?” mikewa tsaye mommy tayi tace, “bashine abun damuwaba binta ahalin yanzu. Ina cikin matsala kikaraso muyi magana ina bukatar shawararki.” binta batayi musuba ta karasa cikin falon tazauna akan kujera ta fuskanci mommy tace, “Atika inajinki wacce irin matsalace gareki, kinsa hankalina gabadaya ya tashi” shiru mommy tayi nakusan mintuna uku kafin tafara magana kamar haka.”binta inason ganin bayan mustaphanah, da sulaiman mijina, inason ayau ba gobebe nashafe labarinsu a doron duniya, ke atakaicedai inason nakashesune.!”
cikin tsananin mamaki binta take duban mommy baki bude, kafin tayi karfin halin fadin, “atika! Kinsan mekike fada kuwa, kokinfara haukane, danki da mijinki kikeson ganin bayansu,kikeson kashesu kuma akanme to?” “Akan kudi” mommy tabata amsa agadarance. “Kudi kuma atika, kudinme to?” gyara zama mommy tayi tace, “labarine me tsaho amma zantakaita miki shi nabaki” ……….. Labari mommy tabawa binta tundaga ranar dasuka samu mustapha har kawo yau. baki hangame binta take kallon mommy, tama kasa magana saboda dinbun mamaki, gani takeyi tamkar mommy kirkirar labarin tayi kawai tabata, yaron datake matukar sonsa fiye da komai a duniya amma ita take fadin ta masa mugayen abubuwa irinka,gaskiya ta jinjinawa hali irinna mommy, domin duk shedanancinta bazata iya abunda mommy tayiba. Jikinta a sanyaye tace, “Atika!, dagaske kike wannan labarinnaki,nifa kwanyata ta kasa dauka,amma tayaya kika gudanar da duk wadannan ayyuka batare da sanin kowaba tsahon shekaru?” taune lips mommy tayi tace, “kinga alamar wasa akan fuskata dazan miki karya. dagaske nake mustapha badana bane nacikina, kuma ina gudanar da aikinane cikin sirri a wannan gidan nida sadiq, abunda yasa babu wanda ya’ankare tsawon lokacin dana dauka inayi, saboda sadiq nake aikawa gurin boka tsidau, ninayi shekaru banje gurinsaba sedai idan sadiq yaje ya hadamu a waya. ko zuwa gidannan damukeyi babu wanda yasani, danse yamma lis nake zuwa kuma ta get din baya muke fita. Abundai da kawai yarana da megidana suka sani inada wannan gidan kuma ina zuwa lokaci zuwa lokaci ina dubashi.” wani dogon numfashi binta taja sannan tace, “yanzu ke Atika duk daular dakike ciki, gamida kudaden da kike juyawa wanda har karshen rayuwarki zasu isheki, amma shine kika aikata haka, gashi yanzu asirinki yatonu, batare da kincinma kudirinkiba. mene amfanin hakan, gaskiya Atika duk tsagerancina gamida son duniyata da shu’umancina amma nasara miki gami da jinjina miki” wani murmushi mommy tayi tace. “Lallai binta haryanzu bakigama sanin Atikaba, tokisani nawuce duk yanda kike tunani indai akan cikar burinane babu abunda bazanyiba arayuwarnan. Dakike maganar kuma duk dukiyar danake ciki, amma senayi hankorin wata. Namiki uzuri, bakisan tarin dukiyar da golds din mustapha sukayibane shiyasa zakice haka”…… “Amm”…..”dakata binta” mommy ta katse binta ta hanyar daga mata hannu kamar yadda itama ta katseta. “Bana kirakibane muyita ja’inja kokuma jan maganaba, nakirakine kawai kibani shawara domin kaina gabadaya ya kulle, narasa mafita. gashi kuma boka yamana gargadin dazarar aiki ya lalace karmu koma gurinsa” Ajiyar zuciya binta tasauke tace, “yanzu yakikeso ayi?” mikewa mommy tayi tsaye tadanyi taku sannan ta tsaya tace, “sonake mustapha, menasara da wannan tsinanniyar yarinyar maryam su mutu ayau. Shiru binta tayi kafin yadago kai ta dubi mommy dake kallonta tace. “Kidawo kizauna sena fada miki yanda za’ayi” babu musu mommy tadawo tazauna suka fuskanci juna binta tafara bata shawara…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button