Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Thank you so much my FAN’S for your wishes and du’a. Allah yabar kauna da zumunci me ɗorewa.❤️????

By
Zeey kumurya
ABINDA KASHUKA…..

BY
ZEEY KUMURYA

6️⃣2️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

……….. Har na ƙaraso bakin kofar dakinnasa sena tuna ban dauko cup ba, juyawa nayi na koma kitchen na dakko na dawo. A hankali kamar mara gaskiya na murda handle din dakin tare da turawa. kwance na hangoshi yayi ruf da ciki idanunshi a lumshe, hannunsa ɗaya dafe da kansa. Tausayinsane ya ƙara lullubeni, a hankali nake takawa har na ƙarasa gaban gadon idanuna akansa. Tunda ta shigo dakin yaji alamun anshigo, amma ya kasa buɗe idonsa yaga ko waye, seda ta ƙaraso ya gane itace ta hanyar sassanyan kamshinta daya ziyarci hancinsa. Farin ciki mara misaltuwa ne ya lullube zuciyarsa gami da mamakin abunda yakawota dakinsa adaidai wannan lokacin, dan be taɓa zatoba, ko motsawa beyiba duk da yanda zuciyarsa take azalzalarsa akan ya buɗe ido koda kallontane yayi koyaji sauƙi aransa. Ajiyar zuciya na sauke ina tunanin ta ina zanfara, dan atunanina bacci yake. A jiye ruwan da cup din gami da maganin nayi akan bedside, a hankali na hau kan gado na zauna daf dashi zuciyata na ƙara tsananta bugu, tafin hannuna na dora akan forehead dinsa, bayan na zame hannunsa a hankali daga kannasa, zafi naji akannasa ga jijiyoyin kansa duk sun fito rada_rada se gumine dake ɗan tsatstsafowa kadan_kadan a goshinsa, daga gani kan bakaramin ciwo yake masaba. Ƙasan hijabina nasa na fara goge masa gumin. Ajiyar zuciya ya sauke sassanya yana ƙara lumshe ido lokacin dayaji tattausan tafin hannunta akan goshinsa. seda na goge masa gumin tass sannan a hankali na fara kiran sunansa domin na tasheshi na bashi maganin yasha, dan banga alamun yasha maganinba. “Yaya..yaya!” Buɗe idansa yayi a hankali ya saukesu akan kyakkyawar fuskarta. cikin tausayawa nace, “sannu ya jikinnaka?” Daga mata kai kawai yayi still idanunsa na kan fuskarta. “Allah ya ƙara sauƙi” na faɗa a hankali ina tashi na sauka daga kan gadon. Robar ruwan na ɗauka na tsiyaya a cup na ballo maganin guda biyu, kan gadon na dawo na taimaka masa ya tashi zaune, filo nasa masa ya jingina bayansa, sannan na dakko maganin na bashi, karba yayi ya sha ya kora da ruwan, sannan ya mikomun sauran maganin yana sauke ajiyar zuciya, Ni Ko se jera masa sannu nake cikin tausayawa. Zamewa yayi ya koma ya kwanta tare da lumshe idanunsa. kamar kar na tafi na barshi haka nakeji, zuciyata ta cika da tausayinsa yanda yake taune lips dinsa nasan ba ƙaramin jin jiki yakeba. jiki a sanyaye na tashi na fice bayan na kashe masa light din dakin, ina masa addu’ar samun sauƙi a cikin raina. Yana jinta harta fice amma yakasa tabuka komai, murnarsa duk ta koma ciki na zuwanta, ya rasa meyasa daya ganta yakasa aiwatar da komai akanta, duk da yanda yake cikin tsananin bukatarta a yanzu. hangota yakeyi a idanuwansa yanda takeyin komai cikin nutsuwa da sanyinta lokacin datake bashi magani, yaga tsananin tausayasinsa a cikin idanunta. ciza lips ɗinsa yayi cikin takaici. besamu bacci ya daukeshiba se can dare……..

Washegari kamar kullum danayi sallar asuba ban koma bacciba, karatun Alkur’ani mai girma nayi, seda gari ya fara haske sannan na tashi na fara gyara gidan. Har yau bana girki a part ɗina, sedai mu haɗu muyi a part ɗin ammi, na safe Kuma kafinma nagama aikina ammi ta aiko ankawo mana….. suhailat tunda Aunty ta tasheta tayi sallah da ƙyar take ta tambayar “ina yaya, ko ba’agidan yake kwana bane.?” Aunty da aliya banza suka mata suka cigaba da sabgarsu ko tanka mata basuyiba. Kafin su fito, ammi ta shigo dakin da kanta sun gaisa, bayan sungama gaisawa ta dubi suhailat dake ta kallonta tace. “Wannan ƴar gidan Alhaji mainasara ce?” Aunty tace, “A’a mahaifinta kanine a gurinsa Ni kuma yayanane, amma Allah ya masa rasuwa tun tana yarinya shida mahaifiyarta, se rukunta ya koma hannunsa.” cikin tausayawa ammi tace, “Allah sarki, Allah yajikansu ya gafarta musu” suka amsa baki ɗaya da “Ammeen” ammi ta ƙara cewa, “yaranshi nawa ne? har yau be kawo mana suba” murmushi Aunty tayi tace, “su huɗu ne, kuma duk mazane. Abunda yasa basu zoba saboda harkar kasuwancinsa duk sune akai, babban kuma kinsan suna saudiyya mabiyanshi kuma tare suke jinyarsa da yayah, suma su haidar ɗin kullum mukayi waya zancensu yaushe yayansu ze dawo Kano sunyi missing ɗinsa.” Ammi na murmushi itama tace, “su a tsammaninsu Muhammad ze koma Kano da zamane?” Aunty tace, “ehhh mana ko kinfiso ya zauna anan?” Ammi tace, “ehhh gaskiya inda so samune nafiso ya zauna anan, amma shima naga yafison ya koma Kanon” Aunty tace, “to ai kinga can ya taso, a can komai nasa yake, kuma harkar kasuwancinsama duk yana can, zeyi wuya mutum yayi rayuwar Kano yazonan yaji daɗin rayuwa, kinsan nan da can da banbanci.” Ammi tace “hakane kam to idan Allah yakaimu bayan babbar Sallah sesu koma Kanon da gabaɗaya” suhailat dake sauraren hirar tasu ta dubi Aunty tayi farat tace, “Aunty nima Dan Allah kibarni anan, idan yayan ze koma semu koma tare” wani kallo Aunty ta wurga mata sannan tace, “A’a, gobe zamu tafi tare” suhailat ta marairaice tace, “Please Aunty I want…..” Aunty ta katseta cikin faɗa, “nace fa bazaki zaunaba gobe zamu tafi” ammi ta tari Aunty da faɗin, “haba Hajiya sauda kibarta mana ta ɗan kwana 2 tunda tanaso” Aunty tace, “Tana zuwa makaranta shiyasa” ammi na duban suhailat tace, “To kinji ɗiyata ashe da makarantarki, kiyi hakuri ki bitan ku tafi, idan kukayi hutu sekizo mana” suhailat batace komaiba, amma bataso hakaba, taso Aunty ta barta ta zauna anan ɗin kusa da yayanta, duk da batasan alaƙarsu da mutanen gidanba, amma ita wannan ba damuwarta bace, Ita dai tunda zata dinga ganin yayanta kullum zata zauna. Tun jiya da yamma ta kashe wayarta saboda kar mommy ta addabeta da kira, dan tunda taga Mustapha a gidannan tasa aranta ta samu gidan zama. (Suhailat badai hankaliba ????) hirar duniya ammi da Aunty suka shigayi. Aliya kuwa dama tana kitchen aunty ta turata suna aiki ita da umaimah da Aunty zuhura….

Se kusan ƙarfe goma nagama aikina, duk da ba wani aiki bane a gidan amma kullum haka nake, sena wanke komai nayi goge_goge, har kayan dana cire duk se na wankesu shiyasa bana kammala aikina da wuri. ina toilet ina wanka Aliya ta shigo part ɗin, fitowa kawai nayi daga wanka naganta zaune a bakin gado tana danna waya. Da mamaki nace mata, “ke yaushe kika shigo ko motsinki Banji ba” Aliya ta ajiye wayar hannunta tace, “yanzu na shigo na kawo muku kayan break, se yanzuma kika tashi kenan?” Ina karasawa gaban mudubi nace, “sekace wata ke, zanta bacci har safiya haka” cike da shaƙiyanci Aliya tace “nasani ko yanzu kin koya, tunda yanzu kina lole mana jikin yaya” ban kulataba nacigaba da shafa maina. Bayan mun shirya muka fito falo na haɗa tea nasha da soyayyiyar wainar kwai da dankali, ina ci ina yamutsa fuska ina babu daɗi tunda aliya tacemun ita tayi. Itama da bakinta baya shiru ba kyaleni tayiba, mayarmun take. Cin abincin nake amma hankalina yana kan kofar dakin yaya, so nake na ƙarasa cin abincin naje na dubo jikinnasa. ina gama karyawa na nufi dakinnashi, Aliya kuma na kitchen tana wanke kwanukan danayi amfani dasu. Amma abun mamaki Koda na buɗe Kofar dakinnasa senaga wayam bayananan, amma dakinnasa fess dashi se tashin kamshinsa yake dana room freshener. A part din ammi na tarar dashi suna hira da Aunty, cikin shirinsa da alamama fita zeyi. Naji daɗin yanda nagansa da alamun yaji sauƙi kenan. ban wani jima da zuwaba ya fita. Suhailat yauma taso ta shishshige masa amma be bata fuskar hakanba, daga gaisuwarta daya amsa be ƙara kallon koda inda takeba. Ita batason bayason ganintaba, saboda indai ya kalleta seya tuno da mommy, shikuma bayason ya dinga tuna mommy so yake yayi deleting ɗinta gabadaya daga cikin rayuwarsa ko tunata bayason ya dingayi. Yauma haka na wuni a part din ammi, munashan hira cikin nishadi, sosai zuwansu Aunty yaymun dadi. Aunty ta kirani daki ta tambayeni, ko akwai wata matsala a zamanmu da yaya, nace mata babu matsalar komai. nasiha ta ƙaramun akan zamantakewar aure, ta kuma bani wasu turaruka masu kamshi tace kullum kafin na kwanta na dinga tsugunno dashi, wani kuma na turara jikine dana shafawa harda na turare kaya duk ta bani. Cike da kunya na karba na mata Godiya. Yauma se dare na koma part dinmu, tun safe dana ganshi a part din ammi ban ƙara sakashi a idonaba dana dawo kuma banganshi a falo ba kamar yadda na zataba, haka na wuce ɗakina zuciyata babu daɗi, kewarsa duk ta cika mun zuciya kamar naje naganshi haka nakeji, amma bazan iyaba, tunda innaje bansan mezan ce masa yakawoniba…. Abangaren mustapha ma, zuciyarsa cike ta wuni da tunanin maryam har mamakin kansa yake akan yanda tunaninta ya yawaita acikin zuciyarsa. duk abunda zeyi tunaninta na makale a cikin zuciyarsa. yau kam yaji sauƙin jikinsa sosai, dan tunda ya tashi ciwon kan da ciwon marar yasarara masa, yayi zaton yauma zatazo ta ƙara dubasa amma yaji tsit, ya gama budget dinshi akanta yau idan tazo, amma ta bata masa shiri. zuciyarsa babu daɗi shima ya kwanta cike da takaici. (???? kai kaje mana, wannan miskilancin naka ya ishemu fa????????)…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button