Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

_____
HAJ.GWAGGO
_____

Tun tafiyar maryam, haryau datafi sati ba’asamomata me aikinba, ansamo mata wata yarinya dai, tana zuwa taji lissafin ayyukan gwaggo tace bazata iya jaki work ba, aiki babu hutu. gwaggo taita mata masifa tace karta iya din, aikin da’ake nemansa ido rufe danma ita tasamu za’a dauketa, taje dubunta zasuzo. Kamar kodayaushe yauma se rana tatashi daga asararren barcinta, bakinta kawai ta kuskuro ta dawo ta hada tea tahau sha, tana Karin kumallon tana mitar maryam taki zuwa, balle ta kawo mata abun duniya, dan bakin hali irinnata. Sallama taji ana kwadawa abakin kofar gidanta, banza tayi tacigaba da cin abincin ta, cigaba akayi da kwada sallamar, hakura tayi ta mike ta zari mayafinta,ta nufi kofar gidan tana fadin, “jaraba da masifar duniya, ko ubanwaye zezo mata gida wannan farar safiyar ya takura mata oho, itadai tasan ba bashin uban wanda take ci…..

Tsayawa tayi cak, bayan ta karaso kofar gidannata cike da mamakin ganin Wanda batayi zaton ganinsaba. “Malam audu!” Gwaggo ta ambata cikin mamaki. “Na’am ladi, kinyi mamakin ganina ko?” “Sosaima malam audu, Ashe rai kanga rai, shigo_shigo maraba lale marhabun” gwaggo tayi gaba yana binta abaya, se kallon gidan yake, yana mamakin yanda gidan duk yabi ya mutu, ga tarin ledodi da abubuwa na rashin shara. Rabonsa da gidan tun mutuwar inna. (Malam audu, dan’uwan mijin innane, wato kakan maryam, kani yake agurinsa, inafatan kun gane) atsakar gida cikin datti gwaggo ta masa shimfidar tabarma, zama yayi adarare. Gwaggo ta dakko kujerar tsuguno ta zauna,ko tunanin kawo masa ruwa batayiba. Suka gaisa, gwaggo se washe masa baki takeyi, saboda tasan malam audu, shime alkhairi ne, ko lokacin da inna take raye shikadai yake waiwayarta ayan uwan mijinta. Gyara zama malam audu yayi yace, “ladi ina jikartawane, banga gilmawartaba kotana makarantane.” Cikin kaudi inna tace, “eh, tana makaranta aidayake bata wasa da karatu akwaita da himma” “ai hakan yanada kyau, Dama zuwa nayi ince tashirya ta hada kayanta, idan zan koma gobe Lagos dim, mutafi tare ta koma hannuna da zama, tunda kinga ke macece, ita kuma yarinyarnan…….. “Malam Audu, mekake nufi maryam din zaka rabani da ita?” Gwaggo ta katsesa cikin karaji, fara’ar dake fuskata gaba daya ta dauke. Batajira amsarsaba, cikin makirci ta fashe da kukan munafurci, tana fadin. “Yanzu maryam din danake gani inji dadima, ita kake kokarin rabani da ita, ko tausayina bakaji, tunda ni Allah bebani haihuwaba, ita kadai nake kalla inji dadi,shine kake kokarin rabani da ita” Tausasa murya malam audu yayi yace, “bahaka bane ladi, rayuwafa yanzu ta sauya, rikon maryam da namiji yadace ba maceba, yarinyarnan yanzu koda aurantane ya tashi a misali, bata da kowa wani namiji tsayayye daze tsaya mata, nikuma kinga kafinnazo garinnanma senadauki shekaru,shiyasa naga gwara ace tana hannuna” kafewa gwaggo tayi ita bazata bada maryamba, shikuma malam audu yasan halin gwaggo sarai, babu Allah aranta, shiyasa yakeson yadauke maryam daga hannunta, dan yarinyar tana matukar bashi tausayi.

Ganin inna ta kafe se malam audu yace, “shikenan ladi tunda kinkafe bazakibada maryam ba, insha Allah zandinga kokarin wajen ganin ina ziyartarku akai_akai, yanzu bari najira tadawo daga makarantar naganta sena wuce.” Cike da rashin gaskiya, inna tace, “ai ba makarantar jeka kadawo takeba, makarantar kwana takeyi” “haba ladi, kanki daya kuwa zakidau yarinya marainiyar Allah, kikaita wata makarantar kwana?” Malam audu yafadi haka cikin dan fada. “To, malam audu itafa yarinyarnan ita tace tanason makarantarnan” “to kuma dantace tanaso seki biye mata kikaita, ai ita yarinyace kuriciya nadamunta, ke kuma……”Haba malam audu, kazo se masifa kakemun, nimafa maryam dinnan jininace bazan cutar da itaba, kuma makarantar ba ita kadai tatafiba, harda kawarta tanan gidan saleemat, kuma shi alh. Adon shiya kaisu da kansa” ajiyar zuciya malam audu, yasauke domin yasan mahaifin saleemat, mutumin kirkine. “Shikenan ladi, wacce makarantarce sena biya naga maryam din” sosa kai gwaggo tahauyi cikin in’ina tace, “um..um, kajima sunan makarantar ya kwantamun, kasanni dake ba bokonnayiba barikewa nakeba” cikin takaici malam audu, yafarawa gwaggo fada, danta fara kaishi bango, ganin sakacinnata yayi yawa, banda haka kadauki yarinya kakaita makaranta,amma kace kamanta sunan makarantar. Gwaggo datasan bata da gaskiya anan, kuma tana tsoron yaganota setahau bashi hakuri, tace masa bari taje gidansu saleeman tatambayo…..

Saleemat yau bataje school ba saboda ciwon marar daya addaba mata tun cikin dare, seyanzu datasha magani tasamu ya sarara mata. Fitowa tsakar gida tayi, ta kama shara, umma nahanata, amma tace ta barshi zata iya taji sauki. “Suwaiba, suwaiba!” Abunda gwaggo tashigo gidan tana fada kenan ko sallama babu. Umma dake hura wuta tafito daga kitchen din tana fadin. “Na’am gwaggo lafiya?” “Inafa lafiya suwaiba, wannan jarababben dan ka’idar yazomun,zedaga mun hankali” “wakenan gwaggo?” “Malam audu na Lagos mana…labarin abunda yafaru tsakaninsu gwaggo ta bata atakaice, ta kara da fadin, “suwaiba kitaimakeni kifadamun sunan wata makarantar kwana ta gwamnati da kika sani, infada masa. Idanyaje yagama bulayinsa ba’asametaba,aiya hakura.” Cike da mamakin halin gwaggo umma take kallonta, cikin sauke numfashi tace mata, “kice masa nannan shekara take” “yawwa suwaiba nagode” gwaggo ta fadi haka, tare da juyawa ta fice.” Saleemat dake tsaye rike da tsintsiya tace, “haba umma, yazaki fada mata, kenan kina goyon bayan karyar datayi?” “Bagoyon bayan karyar gwaggo nakeba, saleemat, kinsan halin gwaggo yanzu idan banfada mataba, seta hauni da tsinuwa ta tataramun jama’a, kibarta kawai kome tayi ita da Allah, insha Allahu aikatau din data tura maryam, seya zamo mata alkhairi.” “Shikenan umma, Allah yasa” cike da kewa da begen kawar kirki, kuma yar’uwa, saleemat tacigaba da shararta. Itama umma, komawa kitchen tayi tacigaba da aikinta. Malam audu, bejira komaiba yashuri takalminsa bayan gwaggo ta fada masa sunan makarantar, yafice domin zuwa dubata,gwaggo tana ala raka taki a zuciyarta………

_______________
ALH. MENASARA HOUSE
________________

Bayan sallar magriba mommy ta aiko kirana, danaje setacemun induba kitchen ta hadawa son dinta abinci, inkaimasa,amsa mata nayi nafito. Dakina nadawo,domin neman rakiyar aliya zuciyata cike da tsoro. Amma senaga bata dakin, dakin aunty na nufa, tanacan kuwa. Dubanta nayi bayan nayi sallama sun amsa nace, “Aliya dan Allah zokirakani nakaiwa yaya mustapha abinci part dinsa” zaro ido waje aliya tayi tace, “cabdijan, rufamun asiri, inkin ganni a lahira kaini akai, aini nan dakika ganni bana kaunar abunda zehadani da yaya, kinga dadin danakeji kuwa,dabaya zama a part dinnan sosai” “haba aliyata dan Allah kizo kirakani kinga darene tsoron hanya nakeji” “mene hakane aliya, kitashi ki rakata mana” cewar aunty. “Nifa yanzu ina zuwa, zefara hararata yanacemun parrot ko turkartive.” “To karya yayi, bahaka kikeba, kitashi kuje,aidama ba tsari tatafi ita kadai,part dinnasa.” gwalo nayiwa aliya, ina kunshe dariya nafice, tashi tayi tana babbata rai ta biyoni abaya. Dundu tadakamun abaya, bayan munfito. Dariya na mata nashige kitchen nadakko basket din da’aka hada masa abincin. Tunkafin musauka kasama muka shirya da aliya, tafaramun surutu. Tunda muka tunkaro part din gabana yake dukan tara_tara, nikam narasa wannan bawan Allah, meyaymun nake tsoronsa haka. Aliyama tsit tayi daga hirar datakemun, dataga munhau falon sama. Ahankali na murda handle din kofar falon, dama nice agaba, dan aliyama dacewa tayi bazata shigaba a waje zata tsaya,seda naroketa sannan ta yarda zata bini har ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button