Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da yamma bayan sallar la’asar mustapha da daddy ne suka fito cikin shirinsu zasu gidan gwaggo domin gaisheta, da mustapha yacewa daddy ze jene, shine daddy’n yace suje tare shima ya gaishenta ya kuma duba jikinta, seda suka kira Aunty tayiwa driver’n Daddy kwatance gidan sannan suka tafi. basusha wahalar gane kwatancen layinba tunda babu nisa da titi kuma wajen firamare ne, direban yasan gurin, gidannedai seda suka tambaya aka nuna musu. A Kofar gidan gwaggo direban ya faka motar kasancewar motar tana shiga har layin. fitowa sukayi daga motar mustapha ya shiga bin layin da kallo, dan wannan shine karo na farko daya zuwa irin wannan unguwar a rayuwarsa, abokinsa lukmanne ya fado masa rai, ya manta rabon da suyi waya dashi gashi yanzu yayi aure baya unguwar gandun sarki, daya biya ta gidansu sun gaisa. yaro Daddy ya samu ya turashi gidan gwaggo dan a sanarmata da zuwansu, gwaggo na zaune a tsakar gida akan tabarma ita da asabe wadda take zaune a gurinta yaron ya shigo yayi sallama, su gwaggo suka amsa masa. Yaron yace “wai ana sallama da gwaggo” gwaggo tace, “Ni kuma dannan suwaye?” Yace “wasu ne a mota me kyau su biyu suma masu kyau” gwaggo tace, “jeka tambayo kace suwaye” yaron ya fita bajimawa yadawo yace, “wai yace Alhaji mainasara ne da..” gwaggo ta kwalalo ido waje ta katse yaron da sauri tace, “wakace yaro?” Yaron ya kuma cewa “Alhaji mainasa” gwaggo ta dubi asabe da dunbin mamaki a fuskarta tace “asabe! Kinji wa akace yana sallama, wai Alhaji mainasara ko kunnenane beji daidaiba?” Asabe tace, “a’a gwaggo shi akace” gwaggo ta dubi yaro tace, “jeka maza kace ya shigo” ta juyo ga asabe tace, “dakko musu wannan ƙatuwar daddumarnan sabuwa ki shimfida musu” asabe ta mike da sauri ta dakko dardumar ta shinfida, daidai lokacin su Daddy sukayi sallama. gwaggo ta amsa musu tana washe gajiyayyun haƙoranta tana binsu da kallo cikin tsananin farin ciki tace “sannunku da zuwa Alhaji, dafatan kunzo lafiya?” Daddy ya zauna da fara’a yace “lafiya kalau baaba ina wuni” gwaggo kamar zata ɗauki Daddy ta ɗora a cinya yanda take acting tace “lafiya kalau Alhaji, ya iyali?” Mustapha dai kawai kallonta yake ta ƙasan ido, a ganin farko daya mata a rayuwarsa yaji sam matar bata masaba” bayan sun gama gaisawa da daddy kamar wanday akaiwa dole yace “ina yini” gwaggo ta kalleshi da Fara’a tace “lafiya kalau dannan” daga haka be ƙara cewa komaiba, asabe ta gaishe da daddy da mustapha suka amsa mata. gwaggo ta dubeta tana kunce hannun zaninta tace “ungo ɗari biyu nan kisiyo musu lemo da ruwa, bari in kawo muku abinci” Daddy ya dakatar da ita da faɗin, “A’a baaba ki barshi, a koshe muke mukam” gwaggo tace “to ai ko ruwa kwasha Alhaji” Daddy yace “ki barshi baaba mungode, ya jikinnaki kuwa” gwaggo tana maida 200 ɗinta cikin zani tace, “jiki ai yayi sauƙi Alhamdulillah” Daddy yace “Masha Allah, Allah yakara lafiya, ai naso zuwa tun wancan lokacin to sai kuma wani uzuri ya tsaidani” gwaggo tace “bakomai ai Alhaji, a hakanma Nagode ai naga saƙo gurin Hajiya(Aunty) nagode” Daddy yace “babu komai, sai kuma maganar yarinya Maryam dana aurar da ita batare da neman izni ko yardarku ba, da…..” Gwaggo ta katseshi da sauri da faɗin “haba alhaji, babu komai ai, kaima uban Maryam ne kana da iko akanta, ka kai da zartar da duk wani hukunci dakaso, mune da godiya ai dabaka kyamacemuba ha haɗa zuri’a damu” Daddy yayi murmushi ya mata Godiya, shidai mustapha yayi tsit kamar babu shi a gurin. Gwaggo se sakarwa daddy zantuka takeyi, shi kuma kawai sedai ya bita da murmushi da eh’ko A’a, ganin ƙarfe shida ta gabato Daddy yacewa gwaggo su zasu wuce, nuna mata Mustapha yayi yace “ga sirikinnakifa, shine mijin Maryam ɗin” gwaggo ta gwalalo ido waje tana kallon Mustapha, aranta tace “yanzu wannan mutumin me kama da Balarabe shine mijin maryam” jinjina kai tayi tace, “Masha Allah, ɗana ashema kaine sirikinnawa to Allah ya baku zaman lafiya, dafatan dai baka fuskantar wata matsala daga gurinta?” Mustapha ya gyada mata kai kawai. Tace “aidama nasan Maryama yarinyar kirki ce gata da biyayya da hankali, bata da wata matsala ko….” maganar gwaggo ta makale lokacin dataga uban kuɗin da Daddy ya fito dasu daga alhajinsa ya ajiye a gabanta.Gwaggo ta wangale bakinta tana duban Daddy dake cewa, “bamu samu mun taho da komai ba ga wannan a sai goro” gwaggo ta haɗiye wani yawu tace, “Alhaji angode Allah yasaka da Alkhairi, ya raya zuri’a yajikan mahaifa, Allah ya ƙara buɗi” Daddy ya amsa da “Amin” yana bin bayan mustapha wanda tuni yayi gaba, gwaggo har ƙofar gida ta bisu babu ko lullubin kai se ɗan kwali tana zuba musu Godiya, mustapha yana jingine jikin motar yana latsa wayarsa, saleemat ce ta fito daga gidansu hannunta riƙe da leda zata kaiwa wata kawarta a tamfar anko, kallon su Daddy take cike da mamaki ganinsu a ƙofar gidansu, gasu ƴan gayu dasu wanda kallo ɗaya zaka musu kasan Naira ta zauna a gurin su, bata lura da gwaggo sai daga baya anan ta gane ashe gurinta sukazo, gaishe da Daddy tayi cikin girmamawa duk da batasanshiba, amma tana ganin kamar tasan fuskarsa, amma ta kasa tuno inda tasan sa, Daddy ya amsa mata da fara’a, shima Mustapha gaisheshi tayi a ranta tana yaba kyawun da Allah yayi masa kamar ba ɗan ƙasar nan ba, ya amsa ba yabo ba fallasa, ta gaida gwaggo ma ta wuce, seda gwaggo taga barin motar su daddy layin, Sannan ta dogara sandarta ta koma cikin gida da ƙyar kamar wadda zata bisu. Zama tayi akan dardumar dasu daddy suka tashi ta ɗauki kuɗin tana jujjuyashi a hannunta kafin ta dubi asabe tace “Asabe kinga ikon Allah ko, nida na ɗauki Maryam na kaita aikatau danta wulakanta se gashi ita aikatau ɗin ma ya zamar mata Alkhairi, jibi fa wanda akace shine mijinnata kamar shi yayi kansa dan kyau, anya kuwa wannan ma bahaushe ne kuwa?” Asabe tace “ikon Allah kenan gwaggo yafi gaban komai, amma dai Maryam tayi sa’ar miji” gwaggo tace “Ni duk ba ma wannan ba, wai yau Ni Ladi nice Alhaji mainasara yazo har cikin gidana da sunan ya gaisheni, wayyo daɗi kasheni wlh jinake kamar mafarki nake asabe…” Haka gwaggo taita zubarta cikin tsananin farin cikin yau Alhaji Mainasara ya zo gidanta, asabe dai se dariya take mata, Maryam kam tasha addu’oi kala_kala, kamar ba ita ce da gwaggo take tsine mata ba gami da aiba tataba……..✍️

Na so page ɗin ya fi haka amma abubuwa sun shamun kai yau ɗinnan, mu haɗu bayan sallah idan Allah yakaimu inda za mu ƙare book ɗin gaba-daya cikin kwanaki ƙalilan da yardar Allah, AYI SALLAH LAFIYA MASOYA.

By
Zeey kumurya
ABIN DA KA SHUKA….!

BY
ZEEY KUMURYA

Bismillahirrahmanirrahim

7️⃣3️⃣

………..Se azhar na baro part din aunty zuhura, acan na wanke kannawa, na busar dashi Bayan mun gama tsifar, part din ammi na koma nayi Sallah sannan na shiga kitchen muka ƙarasa girki Ni da umaimah, har lokacin baƙin ammi sunanan, muna gama girkin ko tsayawa cin abincin banba na koma part ɗinmu, sosai kewar yaya ta cikamun zuciya kamar mara lafiya haka nake jina, komai ina yinsane cikin dauriya da ƙarfin hali, amma idan na tuna yau ze dawo se inji farin ciki ya lullubeni, gyaran part ɗinmu na shiga yi bakama ƙafar yaro cikin zumuɗi, ko ina na shareshi nayi mopping na sauya zanin gadon ɗakina dana ɗakinshi bayan na feshesu da turare, gidanma gaba-daya na buɗade shi da turaren wuta me daɗin gaske, se wajen ƙarfe shida na gama gyaran gidan, wanka na faɗa toilet na tsalo na shirya cikin wata atamfa super ɗinkin riga da zani, ɗinkin rigar yayi matuƙar kyau yamun dass a jikina, gashin kaina na faka a ƙeya, ya sauka har gadon bayana, nannade gashin nayi a jikin ribbom ɗin kaina na kafa daurin ture kaga arziki(ba ture kaga tsiyaba????), dankunne da sarka masu kyau na saka, harda agogo da abun hannu duk na saka, ba wata kwalliya nayiba amma Ni kaina nasan ba ƙaramin kyau nayiba, powder kawai nasawa fuskata kalar fatata, se kuma kwalli da white lipstick me ɗan ɗanko se cikakkiyar girata dana taje da brush ɗin tajeta, humra na me sanyi da daɗin kamshi na buɗaɗe jikina da ita, tare da turaren fesawa shima me sanyin kamshi da daɗi, se kamshin ya haɗu ya bada wani kamshi me daɗin gaske, kallon kaina nayi a madubi na ƙara kallo a fili nace, “ALHAMDULILLAHILLAZI, AHSANIL KALK’I WA KALK’IHI” jin cikina ya fara kiran ciroma saboda yunwa, na dakko mayafina daya shiga da a tamfar na yafa a saman kaina, na fito na nufi part din ammi danna ci abinci. Fitowar Maryam daga part ɗinta yayi dai_dai da zuwan fareedah gidan, tazo ne dantaga Mustapha ta fara nuna masa kudirinta a kansa, amma ita da kissa zata masa bada hauka irin na umaimah, tana sanye da zunbulelen hijab har ƙasa, a matsayin ita mutuniyar kirki ce. Maryam na gaba batama lura da itaba ita kuma tana binta a baya, ƙurawa bayan Maryam ido tayi tana kallon yanda jikinta yake juyawa duk da mayafi, zanin data daura ya fito mata da shap ɗin jikinta sosai, ta taka step ɗin bakin part din ammi mayafinta ya zame daga kanta, bata tsaya gyarashi ba tunda tana ganin ta ƙaraso part ɗin, kallon gashin Maryam daya fito ta ƙasan daurinta kawai fareedah takeyi, ƙara sauri tayi domin zuciyarta cike take da son ganin fuskar me wannan dirarren jikin da kuma uban gashi haka baƙi sidik se sheki yakeyi yaji man kitso. da sallama na shiga falon, suna zaune dukansu da ammi da Aunty zuhura da umaimah, suka amsamun a tare har umaiman tunda taga ammi tana falon, amma batare data ɗagoba, zuhura data saki baki tana kallon Maryam tace, “wow Masha Allah, gaskiya Mamana kinyi kyau sosai, kin fito zam a amaryarki, sedai kash ɗan’uwana bayanan” murmushi kawai nayi na zauna a gefenta, araina nace ai danshi nayi kwalliyar umaimah ta dago da kanta da sauri, jin bayanin zuhura ta kalli Maryam, sosai itama Maryam ɗin ta mata kyau, cikin kyashi da hassada tace, aranta, ” shegiyar yarinya se kyan tsiya kamar aljana” ta tabe ta maida kanta kan wayarta, ammi na murmushi tace “ai dama ɗiyata akwai kyau Masha Alla..” shigowar fareeda ta katse mata zancenta, gaba-daya muka kalleta muna amsa mata sallamar datayi. idon fareedah na kan Maryam ta tsugunna ta gaida ammi da zuhura. suka amsa mata cikin fara’a, gaisheta nayi nima tunda daga gani ta girmeni, ta amsamun tana ƙara ƙuramun ido, umaimah ta tabe baki ganin kallon da fareedah takewa Maryam ta mike tana faɗin shigo mana kika zauna a nan, fareedah tana tafe tana satar kallon Maryam ta bi bayan umaimah zuwa ɗakinta, Aunty zuhura ta ajiye Abul dake hannunta ta tashi ta ɗauki wayar ammi tace, “na baro wayata a wajena, bari na miki hoto a wayar ammi” ammi ta mike ta shiga kitchen tana murmushi, gyara mayafina nayi Aunty zuhura ta fara mun hoton, tayi kusan kala biyar nace, “Aunty zuhura a barshi haka” zuhura tace, “Tom shikenan, amma bakiga yadda kikayi kyau ba, tasowa nayi na karba wayar na duba, hotunan na duba sunyi kyau sosai, bata wayar nayi nace, “yayi kyau gaskiya sosai” zuhura tace, “hmmmm, ainaso kanina yananan yaga wankannan, amma duk da haka bazan bari yayi missing ba seya gani a hoto” dariya kawai nayi na nufi kitchen dannaci abinci. ammi na ƙoƙarin fita da plate a hannunta na shiga kitchen din, nace “sannu ammi” tace “yawwa ya jikinnaki” nace “na warware” ammi tace, “Masha Allah, aina gani gakinan kinyi shar dake” murmushi nayi cikin jin kunya. ammi ta ƙara cewa, “jiya da daddare NOOR yakira kinyi bacci, dazuma ya kira kina part din zuhura” lumshe idona nayi bugun zuciyata na sauyawa jin ambaton farin cikinta da ammi tayi, ammi bata jira amsataba tace “idan kin gama cin abincin seki kirashi” nace “Toh” a hankali ina ƙarasawa cikin kitchen din, ammi kuma ta fice. A ɗakin umaimah kuwa bayan sun shiga, umaimah ta zauna a bakin gado tana bata rai batare da tacewa fareedah komai ba, Fareedah bata damu da yanda ta mata ba ta zauna a gefen ta tace, “kawata wace waccan dana ganta a falo kyakkyawa da ita, amma dai yar’uwar ammi ce ko?” Umaimah ta kebe baki tace “to uwar gane_gane, aidama naga tunda kika shigo kallonta kawai kikeyi” fareedah tace “ba dole na kalleta ba, naga mace ga kyau ga diri ga gashi ga daɗin murya, ga iya tafiya, ga wani kamshi datake zubawa me daɗi da sanyi ga….” Umaimah ta katseta cikin tsananin baƙin ciki, da fareeda tasan yanda yabon Maryam yake tafarfasa mata zuciya da bata yi a gabanta, tana hararar fareedan tace “to itace matar yaya NOOR ɗin” fareedah ta gwalalo idonta waje tace, “wanne yaya NOOR ɗin? ba dai wanda kike so ba?” Umaimah ta gyada mata kai tana haɗiyar wani yawu me ɗaci. Fareedah taja wani uban numfashi tace “wannan ƴar yarinya ɗanya shagab itace matar tasa?” Umaimah tace “,se kuma kiyi” fareedah ta jinjina kai a ranta tace “dama yana da wannan tsaleliyar yarinyar me zeyi dake?” amma a fili se tace “ya maganar abunda nace miki kiyi dafatan dai kinyin?” Kafin umaimah ta bata amsa ammi ta shigo ɗakin da sallama, plate din hannunta ta ajiye a ƙasan gadon tana faɗin “fareedah ga abinci” bata jira amsartaba ta dubi umaimah tace, “ki kawo mata ruwa auta” umaimah tace “toh” fareedah na murmushi tace “Nagode ammi” bayan umaimah ta kawo mata ruwan ta ƙara dubanta tace “baki bani amsar tambayar dana miki ba” Umaimah ta kalleta cike da tsananin takaici tace “babu amsarne shiyasa banbakiba” “kamar ya? Ko baki gane akan me nake magana ba” cewar fareedah tana cire hijabin jikinta danya fara takura mata, umaimah tace “nagane mana, akan gurguwar shawarar dakika bani mana” fareedah ta haɗe rai ganin yanda umaimah take mata tunda tazo tace “wai mene hakane ina miki magana kina wani amsamun kamar ana miki dole, se wani babbata rai kike, idan dannazo gidankune sena tashi na tafi” ganin yanda fareedah tayi se umaimah ta ɗan saki fuska tace “ina cikin haushin abunda shawarar da kika bani ta haifarmunne, kin takuramun nayi harda kirana a waya kina ƙara jaddadamun, duk da banaso amma haka na daure na aikata ƙarshe ba’ayi nasaraba se uban mari dana sha” fareedah tayi ƙoƙari ta danne dariyar dake neman kufce mata tace “bangane me kike nufi ba? Shi yaya NOOR ɗinne ya mareki?” umaimah ta sauke wani numfashi tabawa fareedah labarin abunda ya faru, ta ƙara da faɗin, “tun daga ranar ban ƙara bari mun haɗu da shi ba, saboda bansan matakin daze dauka a kainaba, ga wata irin kunyarsa danake ji” fareedah zuciyarta fari ƙal kamar takarda, a ranta tace “wawiya, haka zanta sakaki kina yin abunda ze kara tsanarki” afili kuwa setace “to mene danya miki haka, ai wannan shine alamun nasara” umaimah ta mata wani kallo na baki da hankali amma batace komaiba, fareedah ta ƙara gyara zama tace “mantawa nayi ban faɗa miki ba, ai dama su maza haka suke, dazarar ke kika fara nuna musu kuyi irin wannan harkar sai sun miki haka, karki wani damu danya miki haka, burga ce kawai ya miki da kuma ya nunu miki irin shidin na Allah ne, amma idan kika cigaba da masa zakiga ya dawo shima yana biye miki, wataranma shi ze nemeki da kanshi” umaimah jitayi kamar ta rufe fareedan da duka saboda haushin maganganunta, amma ta danne bacin ranta tace “kinga kibar fa wani dagon jawabi, aini anyi na farko anyi ƙarshe bazan kuma ƙara masa irin abinda na masa ba” fareedan ta kebe baki tace, “kin haƙura dashi kenan, duk da irin tarin soyayyar da kike masa?” umaimah tace “ban haƙura ba, amma na yanke shawarar danake ganin ita kaɗai zata fishsheni” fareedan tace “wacce shawara kika yanke?” Tace “na yanke shawarar zan faɗa wa ammi kawai ina sonsa, nasan….” Fareedah dataji tamkar ta caka mata mashi a kahon zuciya takatseta da faɗin, “lallaima umaimah, aiko wannan shine babban kuskuren dazaki tafka a arayuwarki, ki faɗawa ammi ta tursasashi ya aureki, kije a matsayin matar tushe mara daraja a idon namiji, ya samu damar wulakantaki kenan son ransa” umaimah da jikinta ya fara ɗan yin sanyi jin abunda fareedah ta faɗa tace, “kuma fa hakane fareedah nima da nace bazan faɗa mataba, amma nayi tunanin,nayi tunanin naga bani da wata mafita se hakan” fareedah tace “to karma ki soma faɗa mata wlh, indai zaki ɗauki shawarata, amma kiyi tunani sosai akan hakan” shiru umaimah tayi, ta rafka tagumi, fareedah kuwa se harararta take a fakaice, aranta tana cewa “senayi duk yanda zanyi banbarki ki faɗawa ammi wannan maganar ba, dannasan dazarar kin faɗa mata magana ta ƙare, yanda ammi ta matsu kiyi aurennan zashi zatayi ya aureki, Ni kuma bazan taɓa bari kiyi aure kibarniba, balle kuma har ki auri wanda zuciyata takeso…” umaimah ta katse mata tunaninta da faɗin “ki sakko kici abincin karyayi sanyi” fareedah bata musa ba ta sakko daga kan gadon ta fara cin abinci….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button