Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Watarana ina zaune a kasuwa bayan anyi sallar la’asar naji ankira sunana,cike da mamaki najuya jin muryar abokina sa’idu,cikin mamaki nace, “sa’idu dama rai kanga rai” danrabona dashi tunda yasamarmun aiki agurin megidana. “Gashi kuwa munhadu sulaiman, tun dazu nashigo kasuwar inata nemanka se nura yace inzonan zansameka” gaisawa mukayi cikin farincikin ganin juna, se kallon sa’idu nakeyi yanda yacanza daga gani kudi sunzauna masa, tambayata yayi menakeyi yanzu nace masa buga_buga ce kawai tunda alh, yarasu har yau bansamu wata kwakkwarar sana’aba. jimantamun sa’idu yayi sosai, yace idan zan iya zuwa NIJER indinga saida takalma zebani jari narasa nadinga kaiwa can, danshima sana’ar dayakeyi kenan acan shiyasama yabarnan, kuma harkar akwai samu sosai acikinta. shiru nayi ina nazari dagacan kuma nace masa, “toyazanyi da iyalina tunda idannace zantafi dasu candinma bani da masauki kuma bani da kudi balle inkama mana haya” murmushi sa’idu yayi yace, “wannan duk ba matsala bace, zakabar iyalinnaka anan gidane, kafara zuwa kaikadai kafin muga abunda Allah zeyi, zuwa lokacin dazaka samu abunda ake fata seka dauketa kukoma can gabadaya, idankatashi sarar kaya sekazo kaikadai kakoma.” godiya nayiwa sa’idu sosai nace masa zanje gida nayi shawara tukunna, yacemun ba matsala idannayi shawarar abunda nayanke zezo gobe mu hadu, seyaji. Koda nakoma gida sena nemi shawarar isma’il akan abunda sa’idu yazomun dashi,aiko isma’il yayi murna sosai, kuma yacemun na amince damace Allah yabani,nanemi albarka abun kawai natafi nafara. banfadawa atikaba seda mukagama magana da sa’idu muka shirya komai yanda abun zekasance, har Lagos mukaje muka saro takalman, nanfa atika tatubure sedai mutafi tare dakyar nasamu na lallabata bayan na cikata da kudi, dannasan mutuniyar tawa akwai son kudi, nakuma ajiye musu komai dazasu bukata itada isma’il ishashshe, alokacin nayi niyyar dakko saudart domin tataya atika zama, amma marikiyartata taki bada ita, dansunsan halin atika ba mutunci garetaba.

Cikin ikon Allah,mukaje nijer lafiya nida sa’idu nakuma fara sana’ata itama da taimakon sa’idu. Naji dadin zama akasar nijer sosai, inda cikin dan kankanin lokaci nasaba da mutane, nakai kusan wata biyu sannan nazo ganin gida, anan na tarar da wani mummunan labari na barewar cikin danabar atika dashi, gashi atika tazama jarababbiya kullum se fada da makota da yawon gantali, isma’il yacemun yana iyakacin yinsa wajen ganin yahanata amma taki hanuwa, banyi kasa a gwiwaba nazaunar da ita namata nasiha takuma nunamun tadauka. Tundaga wannan lokacin nakoma safarar takalma daganan gida Nigeria zuwa kasar nijer, kuma alhamdulillah Allah yadafamun ina samun alkhairi sosai acikin sana’ata. Banfi shekara da fara zuwaba nadauke atika muka komacan Inda nakama mana haya a can din mukacigaba da rayuwarmu, tunda zamana acan yafi yawa gwara ace matata tana kusa dani, yan’uwana kuwa ina musu aiken kudi yanda yakamata. tundaga wannan barin cikin da atika tayi bata kara koda batan wataba, gashi ni kuma Allah ya halicceni mutum ne meson yara, kullum cikin addu’a nake, Allah ya’azurtamu da samun yaya. Atika taso dakko kanwarta jamila tadawo hannunta da zama lokacin dazamu koma nijer,amma kanin mahaifinta yace baze bataba.

Rayuwa tasauyamun sosai nasamu budi da nasara aharkar kasuwancina sosai, nasamu rufin asirina daidai gwargwado. abokina sa’idu shine yasamun sunan menasara daganan sunan yabini wasuma idan kace musu sulaiman bazasu sugane nikake nufiba sekace musu menasara watanmu shida dakomawa nijer dazama nida atika, Allah ya’aiko mana da wani iftila’i, kayana na shago sunkare kaf, natattara kudadena a buhu, zanzo gida nayi siyayya, lokacin account beyi yawaba, dama tafiyar dare mukayi yan fashi da makami suka tare motarmu akan hanya,suka kwace komai namu dagamu se tufafin jikinmu sukabarmu, se juyo damu driven yayi domin dama yawancinmu sare_sare zamu kuma gashi ankwace kudin sarin, dayawa daga cikin wadanda muke a motar kusan zaucewa sukayi,manyan maza magidanta segamu da kuka shabe_shabe da hawaye. wannan fashin da’aka mana bakaramin talautamu akayiba, danseda takai ta kawo naira biyarma gagararmu takeyi, dan abincin da sauran kudin da’akabarwa mata agida duk ancinyesu. Nashiga cikin tsananin tashin hankali bakanba a wannan lokacin narasa ina zantsoma kaina, gashi ko kudin motarma dazan mana mudawo gida Nigeria nida atika kozan samu abunyi anan babu. Alokacinne kuma atika ta fitomun da ainihin halinta na rashin imani da tausayi, kullum cikin yimun tijara da rashin mutunci take, akan rashin da Allah yadoramun, bata ganin nima bayin kaina bane. Kaddarace Allah yadoramun dakuma jarrabawar rayuwa. Watarana da daddare ina zaune a tsakar gidanmu ranar munwuni bamuciba nayi tagumi ina tunanin yanda rayuwa tazomun atika tafito daga daki ta tsayamun aka cikin masifa tafaramun magana, “sulaiman yanaganka anan kazauna, wato bazakaje kasamomun abunda zanciba, mekake nufine, sedai inyi tazama da yunwa ta takasheni” janye tagumin danayi, nayi cikin rarrashi nafara mata magana da fadin, “dan Allah atika kiyi hakuri, kinga yanzu dare yayi bansan inda zannufa insamo miki abunda zakiciba,amma kibari zuwa safiya insha Allahu zannemi koda wankaune domin inbaki abunda zakici” rike kugu atika tayi tace, “wlh baka isaba sulaiman yau bazaka kwana agidannanba seka nemomun abunda zanci, danbazan zauna yunwa tamun lahani abanzaba” cikin takaicin halin atika na rashin tausayi nace, “haba atika amma kinsan nima babuce Allah yadoromun lokacin da ina dashi aina baki abincin” “kaga sulaiman nifa babu ruwana da wani babunka nidai kawai kanemomun abunda zanci, tunda kai kakawoni nan ka’ajiyeni danhaka dole kasamarmin abunda zanci, dankasan shi ciki besan wani babuba ehe” bancemata komaiba namike nafice daga gidan, lokacin goman darema ta kusa. Duk inda nasan zanje insamo wa atika koda biscuit ne amma naje bansamoba, haka nadawo gida jikina asabule lokacin dare yafarayi dan 12 saura, atika harta rufe gida, kwankwasamata nayi ta bude, koda taga hannuna babu komai seta maida kofar gidan tarufe tana fadin wlh bazan shigoba matukar bansamo mata abunda zataciba. wani bakin cikine yaziyarceni nida gidana amma ahanani shiga, meyasa atika bata tausayinane nimafa yunwarnan nakeji amma tunsafe nake yawon nema mata abunda zataji amma bata gani. Wata shawara zuciyata tabani akan naje unguwar masu kudi mana, inrokesu su sanmun koda danyen abincine inkawowa atika tadafa, ko tunanin dare banyiba nakama hanya natafi dukda nisan dake tsakaninmu dasu. ina tafe nakadai tunkis tunkis harna shigo wata unguwa dako sunanta bansaniba amma dai ta masu kudice, kowanne layima da gate dinsa kuma duk an rurrufesu,tsayawa nayi ajikin wata bishiya ina maida numfashin wahala, tunaninma tayanda zan iya komawa gida nakeyi dannagaji likis ga kishirwa dake damuna. ahankali nafarajin taku daga bayana alamar ana gudu, cikin tsoro najuya ina karanta addu’a acikin raina, mutum na hanyo yana gudu da dukkan karfinsa, seda ya matso kusa naga Ashe macece goye da yaro hannunta kuma dauke da wata jaka. Cike da mamaki da tsoro nake kallonta kamar yadda itama ta tsaya cak tana kallona. Cikin karfi hali nace, “baiwar Allah mutum ko aljan?” Cikin hausarta dabata fita sosai tana haki tacemun. “bawan Allah mutum ce ni kamarka” bata jira mezancemataba ta hau kici_kicin kunce dan bayanta bayan ta ajiye jakar hannunta akasa. niko tsayawa nayi kawai ina kallonta cike da mamakin meya fito da ita daga gida cikin darennan, gata yarinya karama danko atika batayiba gata fara jajur kyakkyawa da ita kana ganinta kaga cikakkiyar buzuw….. Katsemun tunani tayi ta hanyar mikomun jaririn hannunta tana kuka tana fadin, “bawan Allah, dan Allah kataimakeni kagudarmun da jaririnnannawa,wlh kashemunshi zasuyi,kuma yanzu suna dubawa basu ganniba zasu biyo bayanane, nikuma dasu kashemun dana gwara ni sukasheni shiya rayu, kataimakeni kagudarmun dashi shikadai Allah yabani, banaso narasashi,wlh dana dan halak ne da ubansa, shima babannasa sun kasheshi shine shima yanzu sukeson kasheshi” takarasa zancen tana fashewa da kuka, tsayawa nayi kawai ina kallonta zuciyata namun wasi_wasi akan abunda tace. “Kataimakeni, sunkusa karasowa, karikemun dana da amana dan Allah,kagudarmun dashi karsu karaso su kashemunshiiiiiiii!…………..✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button