Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Fitowarta kenan Daga toilet,ta hango wayarta tana ringing.batabi ta kantaba,kararasawa gaban mudubi tayi ta fara mulke jikinta da tsadaddun lotions dinta,tafi 20 minutes agaban mudubin,kafin,ta koma ta bude ward rope din kayanta dake cike makil da kaya,ta dakko wata red gawn me adon black,pant kawai tasaka da bra,ta zirata ta matukar kamata,kasancewar rigar robace.gashin kanta wanda bashi da cika da tsayi sosai ta kamashi da wani red ribbon.gaban mudubi ta koma tana karewa kanta kallo,ita kanta tasan tayi kyau,duk da ba wata kwalliya tayiba.perfumes dinta ta fesa sannan ta koma ta dakko,wayarta.missed call din kamal, ta gani.murmushin tayi,tare da bin bayan kirannashi. “Hello kamal!” ta furta, bayan ya ɗaga wayar. cikin wata wahalalliyar murya yace.”aini fushi nakeyi baby,yau kwata-kwata koki nemeni,kuma kinsan banajin dadi idan banjiki ajikina ina kuguigwitakiba”.ya karashe zancen tare da busa mata wani numfashi cikin son yarikitata. Wani dogon numfashi taja saboda sakonsa ya isa inda yakeso.”am sorry my kamal,nima nayi missing dinka,but don’t worry,gobe bani da lecture throughout muna tare.wani ihun murna kamal yasaka wanda yasa da sauri suhailat ta kashe wayarta.karya kashe mata dodon kunne. Number,habibinta tayi dialing tayi ringing harta gama be daukaba.tana shirin tashi kuma yakirata,da sauri ta picking cikin,zumuɗinta.shagwaɓarta kawai taita zuba masa,tana faɗa masa yanda tayi missing ɗinsa.Da kuma,korafin,ya tafi basuyi sallama.samu yayi,ya lallabata.kusan 20 minutes suna wanda,wanda gaba daya suhailat ce take ta surutunta. Cike da murna ta fito,daga dakinta zuwa falo domin yin dinner……

Dare ya tsala, amma babu digon bacci a idona.ina zaune na zabga uban tagumi,se kuncewa da sakawa nakeyi amma babu mafita,gashi nayiwa baaba,talatu alƙawarin,bazan gudu daga wannan baƙin gidanba shawarar zuciyata nabi nafada toilet na watsa ruwa,tare da dauro alwala,na fara jero nafilfili ina kaiwa Allah kukana.bansan adadin raka’ar danayiba nasan dai na dade ina sallar.Ina zaune akan daddumar ina lazimi hannuna naɗaga nafara rokon Allah. ya Allah ina roƙonka da tsarkakan sunayenka,kakareni da karewarka,ka tallafi rayuwata,ya Allah kaine gatana bani da wani gata senaka.Allah kakawomun ɗauki arayuwata,ka nisantani da duk wani abunda ze cutar dani,ka bayyanamun mahaifina da gaggawa idan har yana Raye, alfarmar darajar annabinka. shafa addu’ar nayi,inajin wata nutsuwa tana zagaye dukkan jikina,kunci da damuwar danake ciki gaba daya,ya fara yayewa.mikawa Allah komai nayi,tare da kudirin fuskantar kowacce irin kaddara ta rayuwa ta.nasan Allah baya bacci kuma yanaji yana gani. Da wannan tunanin na mike na ninke sallàyar da nayi sallah,abincin da’aka kawomun na tsakura naci kadan,bayan nagama na hau kan gado na kwanta,na lulluba da bargon Dana gani a ninke a gefen gadon.zuciyata cike da kewar umma,da saleemat harma da gwaggo,cikin mintuna kadan wani bacci me nauyi yadaukeni…….

Kiran assalatune ya tasheni daga baccina,dakyar na yunkura na tashi nayi sallah,saboda wani bacci danakeji,ina idarwa kuwa nakara Jan bargo na koma baccina.

Ina cikin daddadan baccina, Wanda na manta rabon danayishi naji ana tashina.ahankali na bude shanyayyun idanuwana, baaba talatu nagani tsaye akaina.yunkurawa nayi na tashi zaune,gaisheta nayi.amsamun tayi tare da zama agefena. “Da’alamudai maryam jiya baki samu kinyi bacciba,tunda gashi har rana tafito baki saniba.murje idona nayi nace. “Eh baaba,bansamu nayi bacci da wuriba. Amma duk da haka nayi mamakin dadewar da nayi ina bacci.” “Kitashi ki watsa ruwa,kishirya nafara nuna miki abubuwan,saboda yau zaki fara aikinki”. ” tom baaba,na amsa mata ina sauka Daga kan gadon. “Akwai komai na amfani dazaki bukata adakinnan,harda kayan sawa idan kin shirya kisameni a falo. Dakai na amsa mata na nufi toilet. Sabon burush din danagani da MacLean nayi amfani dasu,wajen wanke bakina.kamar yadda baaba talatu,ta fada akwai komai na amfani adakin, kayan shafene kawai babu sosai,kayan sawama gasunan burjik a wardrobe din dakin,abunda ya matukar dauremun kai kenan.banyi gigin saka kowanne kayaba,kayana na saka.na nufi falo gurin baaba talatu.

Tundaga kan toilet ta fara koyamun yadda zanyi amfani da komai,se kuma kitchen shima ta nunamun komai yadda zanyi amfani dashi,Alhamdulillah kuma na gane sosai,sedai dan abunda baza’arasaba Wanda se ahankali,tana nunamun take fadamun sunan kowa nagidan,da kuma yadda zan tafiyar da aikina. Dakina muka koma bayan ta debo mana kayan breakfast,tare mukaci abinci da baaba,tanata bani labaran ban dariya, duk akokarinta nasan ganin ta kwantar mun da hankali. Bayan mungama na tambayeta nace.”waini baaba,wannan kayan Dana gani nasawa na waye”?. Murmushi baaba talatu tayi tace”nakine maryama.cike da mamaki nadago na kalleta “nawa kuma baba”? “Eh maryam,kidauki dukkayan dakika gani adakinnan kisaka mallakinkine,kafin kizo nawatane amma yanzu ya zama naki,idan za’akawo me aiki gidannan kafin tazo komai dazatayi amfani dashi se’an tanadar mata.yanzu ni zanje nafara aikina,naga goma ta kusa idan nagama komai anjima zanzo nakarasa miki bayanin gidannan.kekuma Daga yanzu zaki fara aikinki.

Kayan da mukaci abinci,na tattara na kai kitchen seda na fara gyara dakina na wanke toilet sannan na gyara falon gidan, nayi mopping dinsa,amma abunda ya bani mamaki har lokacin babu Wanda yafito na gidan.araina nace wannan wanne irin baccine.kukune ya fito Daga kitchen yafara jera abinci akan dinning,gaisawa mukayi cikin rubabbiyar hausarsa,sejana yakeyi da surutu.ni kuwa dariya hausarsama take bani.hakan yasa nabiye masa,tamkar munsaba da juna munata hira.fitowar hajiya ya katse mana hirarmu,ta fito cikin takunta na ishashshiyar mace,taci kwalliya kuma tayi kyau sosai.fuskarta ba yabo ba fallasa.tsugunnawa nayi har kasa ina gaisheta amsawa tayi tana bina da wani irin kallo.nidai ina tsugunne kaina akasa,ina jiran umarni.kusan mintuna 10 muna haka,yayantane suka shigo gaba dayansu falon.

Daya bayan daya naga suna hugging dinta,ita kuma sefara’a take saki.babu Wanda ya kulani acikinsu da gaisuwar danake musu. Se guda dayannan.gaba dayansu suka nufi dinning har hajiya.gajiya nayi da tsugunno na koma gefe na rakube,ina kallonsu kawai. “Haidar yakaji yau,munsha baccinmu mun more, saboda big bro bayanan dayanan da tuni muntashi tun dazu” dariya haydar din yayi “kaidai bari ai big bro akwai takura” harararsu mommy,tayi batace komaiba.kamshinta yarigata karasowa falon,rasss gabana yayanke ya fadi,haka kawai Allah yadoramun wani matsanancin tsoronta a kallo daya Dana mata,arayuwata.tana sanye cikin wani Riga da wandon jeans,rigar iya gwaiwace,kanta sanye da wata hula me matukar kyau. Dagudu ta karasa ga yan uwanta tayi hugging kowanne,sakin baki nayi ina kallonsu araina nace sukuma haka al’adarsu take,sekace ba musulmaiba,domin ni aganina,wannan badaidai bane, mu’aro al’adar daba tamuba……..maganar suhailat ce ta dawo dani hankalina cikin tsawa takemun magana. “Dalla malama me kike jira,ko zuwa kikayi kisamu agaba kina kallonmu da kwalakwalan idanuwanki,kamar mujiya” dasauri na mike jikina har rawa yakeyi na karasa dinning din,batare da nace komaiba.kamar yadda baaba talatu tacemun sena tambayi kowa abunda yakeso,takan Wanda naji ankira da haydar na fara. “Yaya haidar me kake bukata?” Na tambayesa kaina akasa. Wani banzan kallo ya watsomun yana karemun kallo tundaga sama har kasa. Dagowa nayi ina kallonsa jin yayi shiru,kamar yadda kowa na falon yayi,wata uwar harara ya wurgomun,yace “dawannan dattin hannunaki zaki zubamun abinci.” da sauri na kalli hannuna fess yake babu dattin komai,kawai tsabar son ya bakantamun raine,kuma yayi nasara. Seda yagama mun shakiyancinsa,sannan ya fadamun abunda yakeso. Tsabar kasaitama da hannu yanunamun abunda yakeso din.zuba masa nayi nacigaba da tambayarsu ina zubawa kowa. Suhailat ce ta karshe,tambayarta nayi amma memakon ta bani amsa senaji ta tsinkamun mari. “Ke wacce irin dabbace,mahaukaciya jahila” dafe kuncina nayi idona ya fara kawo ruwa. “Kiyi hakuri aunty suhailat”,duk da bansan mena mataba,amma na bata hakuri. Tsaki taja tare da tabe baki,ta fadamun abunda takeso na zuba mata.babu Wanda yayi magana akan abunda tamun,cin abincin su kawai suke hankali kwance.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button