Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kwanci tashi asarar mai rai. Yau 23 ga watan Ramadan yau kuma muka gama exam dinmu ta NECO, dayake babu wani interval sosai. A ‘yan kwanakinnan wata shakuwace ta shiga tsakanin Maryam da Mustapha, wanda su kansu basu gane hakanba. Mustapha matukar da umaimah a guri ze nunawa Maryam kulawa da tattali koda a gaban ammi ne kuwa. Hakan kuwa bakaramin kona ran umaimah yakeba. gashi kullum son mustapha karuwa yake a ranta tarasa yadda zatayi, zuciyarta nabata shawarar ta sanar masa kawai koze amshi tayinta, amma kawarta ta hanata tace ta bari a gama azumi tasan mezasuyi dole mustapha yasota. Maryam kam ta fara gwada abubuwan da taji zuhura na fadawa kawarta a waya, ta kuma dage da addu’a akan Allah ya waiwayo mata da hankalin mustapha gareta. Mustapha kuwa yanzun baya gane kansa dan kwata_kwata bayajin daɗin jikinsa, yakuma rasa meke damunsa. Gashi yanzu babu abunda yaji yanaso sama daya dinga jin Maryam ajikinsa yana shaƙar daddaɗan kamshinta, yanason kamshin jikinta sosai. kullum seya ayyana ya rungumeta ba’adadi amma seya kasa. saboda yana ganin Maryam zata rainashi gata yarinya ƙarama ai girmansa seya zube. Ya lura kuma yarinyar itama miskikar kantace.

Yau exam din rana sukayi 2_4 daya dakkota be koma kasuwaba ya kwanta a dakinsa. ita kuma Maryam tana part din ammi sunata aikin girki. tunani yakeyi kawai ta yanda za’ayi su kwana tare, badan ya mata komaiba sedan kawai soyake yajita a jikinsa suna bacci tare. mikewa yayi ya fice bayan yasamo mafita. yau nasha wahalar azumi sosai, dama gashi har yau bansha a zumiba. kafin asha ruwa kamar kullum zandebo abincinsa in ajiye masa akan dinning, mukuma dama a part din ammi muke shanruwa. Bayan na jera masa komai akan dinning na koma part din ammi na sheme akan carpet kafin akira sallah. Aunty zuhura se tsokanata take. Ammi kuwa se sannu takemun tana faɗin, “wannan megidannawa yana wahalarmun dake ɗiyata” duk a zaton ammi karamin ciki ne dani, kullum seta dinga cemun Yakamata insha azumi in dan huta saboda lafiyarmu. Idan ta fadi haka senaita mamaki araina ince. “Dududu yaushe muka tare da har suke tunanin inada ciki, inma ha hakaba nida ko wata mu’amalar aure bata taɓa shiga tsakaninmuba ta ina za’a samu cikin.” Da’aka sha ruwa kunun aya kawai nasha yacikamun ciki. Aiko jikina ya mutu murus kamar anmun shegen duka, dakyar na lallaba na koma part dinmu nayi Sallah, ina idarwa na baje akan gado se bacci. Ban tashi farkawaba se wajen 9:30. sallar isha’i nayi na fito falo domin na samarwa kaina abunda zanci. yana zaune a falo yana kallon labarai. “Sannu da zuwa” na masa ya amsamun dakai. kan dinning na nufa na dibi sauran abincin daya rage naci na koshi sannan na koma daki. Mustapha daketa satar kallon Maryam harta gama ta koma daki. Bayan kamar 10 minutes da shigarta dakin, ya dauki wata leda dake gefenshi yabi bayanta. A hankali ya taɓa handle din dakin yaji kofar a buɗe take, ajiyar zuciya yasauke ya tura kofar a hankali. kamar yadda yazata Maryam tana toilet tana wanka, murmushin mugunta yayi ya aiwatar da abunda zeyi ya fice. Yana fita ba jimawa Maryam ta fito daga toilet tana daure da towel. gaban mudubi na nufa na zauna akan stool nafara shafa tsadaddadun lotions masu kamshi ajikina. seda na mulke jikina tass dasu sannan nabi kowanne lungu da sako na jikina na shafeshi da daddaɗar humrar da Aunty zuhura ta bani gami da body spray me sanyin kamshi. lokar mudubi na janyo na dakko alawata da kullum senasha kafin na kwanta, itama Aunty zuhura ce ta bani tace nadinga sha kafin na kwanta bacci. kokaɗan banajin bacci a idona tunda banjima da tashiba. Addu’a nafarayi Allah yasa kafin nagama shiryawa yabar falon, intafi part ɗin ammi musha hira, dan wataran hanani zuwa yake yace dare yayi, shiyasa kafin yadawo nake guduwa harse yagaji da kansa yazo yakirani. white lipstick na shafa kawai a lips ɗina na Mike da nufin na dakko kaya. Abunda nagani a kan gadone yasani kwalla wata gigiciyar ƙara a matuƙar firgice nayi baya na manne da bango ina runtse ido tare da karanto duk addu’ar datazo bakina. A hankali na buɗe idona kaɗan cikin tsoro na ƙara kallon kan gadon. abunda nagani dai shi nakara gani, kadangarene jangwala gwada katoto kamar ma yana motsi yanzu. da gudu na nufi kofa na buɗe nafice daga dakin nama manta babu kaya a jikina se ɗan guntun towel……..✍️

By
zeey kumurya
ABINDA KASHUKA…

BY
ZEEY KUMURYA

5️⃣8️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

……….. Mustapha dake zauna a falo yana kallonsa hankali kwance tamkar beji ƙarar da Maryam ta kwallaba. A matukar tsorace na fito falon jikina na wata irin kyarma karasawa nayi na faɗa jikinshi cikin fitar hayyaci sosai na tsorata saboda arayuwata ina bala’in tsoron kadangare. lumshe idonsa yayi jinta ajikinshi yana sakin boyayyiyar ajiyar zuciya, Maryam kam ta kankameshi rawa kawai jikinta yakeyi idanunta a runtse. A hankali yasa hannunsa yana ƙoƙarin rabata da jikinsa, cikin basarwa yace, “mene haka?” hannunta na rawa ta nuna masa Kofar dakinta. Lips dinshi na kasa ya lasa wannan yace, “what happened?” Maryam da idanunta babu abunda yake hangomata se kadangarennan ta kasa masa bayani, tsigar jikinta se tashi take tanajin tamkar kadangarenne a jikinta. rikeshi tayi sosai tana sakin kuka tama kasa masa bayani. Lumshe idonsa ya kumayi cikin jin bakon yanayi na ziyartarsa saboda yanda sulbin fatar jikinta yake goguwa ajikinsa. yanajin kukan datake har cikin ransa bakuma ya tunanin ze iya jurar cigaba dajin kukannata. Tausayintane ya tsirga masa ganin yadda duk tabi ta tsorata jikinta se ɓari yake, beyi tunanin zata tsorata hakaba. a hankali ya ƙara saka hannunsa ya dago fuskarta daga jikinshi zuciyarsa na ɗan bugawa ya kura mata tsumammun idanunsa. Maryam da har yanzu ta kasa buɗe idonta se ƙara runtse idanta take, ta kudundune jikinta tanajin yanda idanuwansa ke yawo ajikinta. cikin kasalalliyar murya ya ƙara tambayarta. “Meyafaru a dakinnaki” “lizard????” ta bashi amsa hawaye na zubo mata. Yana nuna so surprise yace, “lizard?” Gyada masa kai tayi har lokacin idonta a rufe yake. ƙoƙarin sauke yayi daga jikinsa yana faɗin, “bari na duba dakin” kuka Maryam ta saka tana ƙara kankameshi gani takeyi yana barinta kadangaren ze kara biyota. lips dinsa ya lasa tare da fesar da numfashi yace, “zan cire miki ne daga dakin” girgiza kai Maryam ta hauyi cikin kuka tace “Ni kar katafi ka barni tsoro nakeji” cikin sanyin murya yace, “to muje tare, seki nunamun inda yake” nanma Maryam kin yarda tayi domin kome za’a mata bazata ƙara komawa dakinta a yauba. Be kuma cewa komaiba, jikinta yabi da kallo, musamman ma gashin kanta daya bazu a gadon bayanta. a hankali yakai hannunsa yana tattare mata gashin ya haɗe shi guri guda shafashi ya shiga a hankali yana lumshe ido. ƙara cusa kanta tayi cikin kirjinsa tana shaƙar daddaɗan kamshinsa gami da sassauke ajiyar zuciya, ta rike shi gam ga dukkan alamu har lokacin a matukar tsorace take. A hankali yayi ƙasa da hannunsa yafara shafa wuyanta zuwa bayanta cikin wani sabon yanayi dayake fizgarsa. wani abu naji ya tsirgamun a gabadayan jikina lokacin danaji lallausan tafin hannunsa akan fatar bayana, wani irin tsorone ya ƙara dirarmun, zuciyata ta fara bugawa. mutsu_mutsu na farayi ajikinsa hawaye na zubomun wanda bansan dalilinsuba. jin tana mutsu_mutsu mustapha ya fara bubbuga bayanta a hankali irin yanda akewa yara, bakinsa yakai saitin kunnenta yafara hura mata iskar bakinsa. tsit nayi nadena mutsu_mutsun cikin jin daɗin abinda yakemun, a hankali wani bacci me daɗi yafara fizgata bansan sanda baccin ya ɗaukeni ba gaba-daya. Jikintane yaji ya saki rigon data masama ta cika, hakan ya tabbatar masa da bacci ne ya ɗauketa, ya fuskanci tana da saurin bacci. a hankali ya dago da fuskarta daga jikinsa ya kura mata ido, a duk lokacin daya kalleta yana ganin wani abu dayake daure masa kai a tattare da ita. ɗan karamin bakinta ya kalla data ɗan turoshi gaba, pink lips dinnan nata se kyalli suke, ajiyar zuciya ya sauke yayi ƙasa da idonsa, towel jin jikinta ya kunce yanda ta kudundune jikinta ne yasa be zameba daga jikinnata, amma gaba-daya rabin kirjinta a waje yake. “jikinta me kyau ko ina bul_bul” ya furta hakan a ransa batare daya saniba. sosai jikinsa ya sauya masa ganin maryam a haka, kasalace take ƙara lullubeshi,wani irin sanyi jikinsa yayi. duk yanda zuciyarsa ke tunzurashi yayiwa Maryam wani abu amma yakasa, lips dinta yabashi burgeshi yanaso yamata koda kiss ne amma yakasa aiwatar da komai, daya daga hannunsa da nufin ya shafa kirjinta seyaji jikinsa ya kama rawa, kansa na sara masa. Rungumeta kawai yayi tsam ajikinsa cikin wani irin yanayi yana shaƙar kamshinta dayake ƙara saukar masa da kasala. kusan 30 minutes suna haka, Maryam tanata baccinta cikin kwanciyar hankali, saɓanin mustapha dayake cikin wani irin yanayi na rashin jin dadi me wuyar fassaruwa, duk da yanajin wata nutsuwa nabin jikinshi amma yarasa meyake masa daɗi ga mararsa data daure masa. da kyar ya iya ƙoƙartawa ya kashe TV ya dauki maryam sukayi dakinsa, dakyar yake iya taka kafarshi danma maryam ɗin bata da wani nauyi. a hankali yake ƙoƙarin shinfideta akan makeken gadonsa, kamar wata jaririya haka ya lallaba ya a jiyeta yana cize lips dinsa. yana ƙoƙarin zame hannunsa daga jikinta ta zabura a tsorace ta kankameshi ajiyar zuciya ta sauke tana ƙara lafewa ajikinsa. runtse idonsa yayi tsigar jikinsa na tashi, wani yarrrr yakeji ajikinsa. idanunsa a lumshe batare daya buɗe ba, yakai hannunsa ya fara gyara mata towel ɗin jikinta dake ƙoƙarin barin jikinnata gaba-daya, idanuwansa bazasu iya jurar kallon jikintaba a yanayin dayakejinsa a yanzu. Seda ya tabbatar yarufe duk wani abu daze iya tayar masa da hankali a jikinta, sannan ya buɗe idanunsa da suka kada sukayi jajur ya sauke akanta. Cinyoyinta ya kurawa ido, yanajin tamkar yakai hannu ya shafasu amma yakasa koda daga danyatsansa ɗaya da niyyar hakan, blanket ya jawo ya lullubeta. zare hannun damansa yayi daga jikinta ya dafe kansa dake sara masa. “Me yake shirin faruwa dashine?” ya tambayi kansa cikin dacin zuciya. shi mutum ne meson yaga ya haifi ya’ya a rayuwarsa amma baya tunanin zega wannan ranar, tunda gashi ya ƙara tabbatarwa da kansa bashi da lafiya kamar kowanne ɗanamiji. ada canbaya abun baya damunsa kokaɗan, amma yau yaji yana bukatar shima yazama mutum kamar kowa, yana bukatar samun nutsuwa ajikinsa, yanajin feeling sosai a yanzu, amma baze iya tabuka komaiba. numfashi ya fesar daga bakinsa yafara kiran sunayen Allah aransa koyaji sauƙin abunda yake damunsa. A hankali nutsuwa ta fara zuwar masa, zuciyarsa ta fara sanyi daga kunar datake masa. cikin kwarin zuciya ya lallaba ya zame maryam daga jikinsa domin yaje ya watsa ruwa ko yaji sanyi ajikinsa. A hankali ya mike ya nufi toilet amma kafin yakai ga shiga yaji muryar Maryam a firgice tana kiran “yaya,Yaya, lizard!”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button