
Ƙarshe azaba da wahala Maryam yau tashata, tayi kuka iyakacin ƙarfinta harseda muryarta ta dashe, duk wanda ta sani kuwa yau seda takira sunansa da neman agaji da taimakonsa har inna dake ƙasa yau tasha kira gurin Maryam. Mustapha kam bemasan tanayiba, yau Maryam ta kaishi duniyar dabe taɓa tunanin zuwantaba ko a mafarki, ta kaishi duniyar dabesan yaze misalta daɗin taba da sanya nutsuwa a zuciya da gangar jiki ga duk wanda yajeta. Rungumeta yayi tsam a kirjinsa bayan komai ya lafa, yanajin wani farinciki, nishadi, annashuwa, daɗi, nutsuwa dabe taɓa jin irinsuba a rayuwarsa. sauke numfarfashi kawai yake tare da ajiyar zuciya yana shafa kan Maryam, wadda tuni baccin wahala ya kwasheta. Addu’a kam yau Maryam tashata a wajen mustapha kamar ba gobe, sunfi 30 minutes a haka sannan da kyar mustapha ya iya rabata da jikinsa. A hankali ya yunkura ya tashi zaune, ciwon kan da yanayin dayake ciki da kasala, gabaɗaya sun barshi. sauka yayi daga kan gadon yana jinsa tamkar bashiba tsabar shauki, murmushi ne kawai yake subce masa batare daya san yanayiba. wani wasai yaji kansa tamkar ansauke masa wani abu me nauyi daga kannasa, duk wani kunci da damuwa dayakeji acikin zuciyarsa a yau duk ya kau, tarin farin ciki ne kawai acikin zuciyartasa yau. Toilet ya shiga ya sakarwa kansa shower, seda ya tsarkake jikinsa sannan ya fito daga toilet din daure da towel a kirjinsa. Light din ɗakin ya kunna haske ya gauraye ɗakin agogon dake manne a bangon ɗakin ya kalla, yaga har uku na dare ta wuce. Aransa yace, “lallai ya dade yana abu ɗaya” wardrobe ɗinsa ya nufa ya dauko boxer da wata jallabiyar yasaka a jikinsa. Dadduma ya dauko ya shimfida ya fuskanci alkibla yatada sallah. Raka’a biyu yayi, amma ya dade yana addu’a a cikin sujjadarsa akan Allah yabasu zaman lafiya da zuri’a dayyiba, ya kawar musu da duk wata fitina a zaman auransu. Bayan ya sallame ya koma kan gadon, zama yayi ya tasa Maryam a gaba yana kallonta, yana jin wani baƙon abu yana ratsa zuciyarsa akan Maryam ɗin, a hankali yake shafa fuskarta datayi jage_jage da hawaye cikin tsananin tausayinta, yasan wahala iya wahala ya wahalar da ita. Mikewa yayi da sauri tunawa da yayi tana buƙatar taimako a halin yanzu, be kamata ya barta hakaba. Toilet ya shiga ya tara mata ruwan ɗumi acikin bahon wanka, komawa dakin yayi ya dakkota cancaskat yasata a cikin ruwan hakan yasata farkawa daga baccin datake ba shiri, zabura tayi jin wata irin azaba na ratsata tare da fashe da kuka. Kwantar da kanta yayi akan kirjinsa ganin tana ƙoƙarin tashi, a hankali yake shafa kanta cikin tausayawa. Kuka sosai Maryam takeyi saboda wata azaba dake ratsata ta ƙasan ta kamar an jajjaga mata attaruhu a gurin haka takeji. idanunta a rufe suke gam duk da tafarka daga baccin datake, wata irin matsananciyar kunyarsa takeji. Seda ruwan yayi sanyi sannan ya ɗauketa daga ciki, barin ruwan yayi ya tsiyaye sannan ya ƙara tara mata wani. Seda ya canza mata ruwan sau uku sannan ya barta a ciki yace idan yayi sanyi tayi wankan tsarki ta fito. Banza ta masa bata amsa masaba. Murmushi yayi kawai ya fice. Ajiyar zuciya nasauke me ƙarfi, zuwa yanzu Ni kaina daɗin ruwan nakeji. radadin danake ji ya fara sassauta mun, seda ruwan yayi sanyi kamar yadda yace, sannan na barshi ya tsiyaye, wankan tsarkin nayi na lallaba a hankali na fito daga bahon wankan, taku ɗaya nayi na kwalla ƙara na tsugunna a gurin ina sakin kuka. Mustapha dake saka rigar filon zanin gadon daya sake ya barshi ya nufi toilet din da sauri. Ƙarasawa inda take yayi ya rungumota ajikinsa a rude yace, “meyafaru?” cinyata na nuna masa da hannu ina dungulewa guri ɗaya saboda babu komai a jikina. “Sorry” ya faɗi haka yana bubbuga bayana alamar rarrashi. ƙoƙarin daukata yayi naƙi, ganin yanda take dunkule jikinta ya gane metake nufi, murmushi yayi kawai ya mike ya dakko towel ɗinsa babba ya kawo mata. karba nayi har yanzu na kasa buɗe idona cikin shagwaba nace, “ka dena kallona to” juya mata baya yayi yana murmushi yace “to nadena” buɗe idona nayi a hankali kamar me tsoron kar naga wani abu, ganin ya juyamun baya nayi sauri na daura towel ɗin. juyowa yayi da sauri na maida idona na rufe ina turo bakina gaba. ɗaukarta ya ƙarayi still fuskarsa ɗauke da murmushi. A kan gadon ya kwantar da ita, shima kwanciyar yayi ya rungumeta a jikinsa yana shafa bayanta a hankali, ba jimawa wani baccin ya ƙara ɗauke ta…….✍️
By
Zeey kumurya
ABINDA KASHUKA….
BY
ZEEY KUMURYA
6️⃣4️⃣
Bismillahirrahmanirrahim
………A hankali ya lallaɓa ya rabata da jikinsa ƙoƙarin tashi yayi Maryam ta ƙara matsowa jikinsa ta kankameshi tana ƙara turo bakinta gaba, cikin lallabawa da dabara ya ƙara zareta daga jikinsa, filo yasa ya maye mata gurbinshi da shi. Kissing goshinta yayi sannan ya sauka daga kan gadon. AC’n ɗakin ya kashe saboda sanyin asuba daya fara busowa. zanin gadon da ya cire ya ɗauka ya shiga toilet dashi ya wanke. Da ƙaramin towel dauke a hannunsa ya fito, gashin kanta data jika gurin wanka ya tsane mata, sannan yaje ɗakinta ya dakko mata wata doguwar riga me ɗan kauri ya saka mata, bacci takeyi amma daga gani kasan na wahala take, yanda take dunkule jikinta yasan sanyi takeji. Fankar dakin ya kashe gaba-ɗaya ya ƙara lullubeta da bargo. Daze tafi masallacin sallar asuba yaso ya tasheta tayi sallah, amma yasan yana tashinta rigima kawai zataita masa ta hanashi zuwa masallacin shi kansa shiyasa ya fasa tashinnata. light ɗin dakin ya rage mata sannan ya tafi zuwa masallaci. Har ya dawo tananan yanda ya barta a ƙudundune, lallaɓawa yayi ya tasheta domin tayi Sallah, da kyar ta iya tashi tana zuba masa taɓara, ɗaukar ta yayi ya kaita toilet din ya taimaka mata tayi alwala, wani tausayintane yake ƙara lullubeshi ga jikinta yayi zafi zau alamar da Zazzaɓi ajikinnata, a zaune tayi sallar danko tsaiwa bazata iya yiba. Bayan ta idar da sallar ya ƙara lallabata ta koma bacci. Ajiyar zuciya ya sauke bayan tayi baccin, tana kwance akan faffaɗan kirjinsa ta kankameshi gam kamar zata koma cikinsa, bayanta yake shafawa a hankali cikin tsananin shauki. Farincikin dayake ciki yau baze misaltuba, tabbas a yau ya ƙara tabbatar da aure ni’ima ne. A hankali ya zare Maryam daga jikinsa, tausayinta yakeji sosai har can ƙasan ransa, dare ɗaya amma fuskarta hartayi fayau ta faɗa. Sauka yayi daga kan gadon ya ɗauki wayarsa dake kan bedside, duba time yayi yaga 6:32 am. Contact ya shiga ya lalubo number’n famili doctor din su ammi da ammi ta taba tura masa saboda tsaro kokuma idan irin haka ta faru yayi dialing, kira ɗaya yayi sa’a kuwa ta shiga, amma harta katse ba’a ɗagaba, ajiye wayar yayi ransa babu daɗi, yana ganin idan har bakwai tayi doctor’n bata biyo bayan kiranba ɗaukar Maryam kawai zeyi ya kaita asibiti a dubata, dan yanda ta kasa tafiyarnan ba ƙaramin tayar masa da hankali yayiba, yana tsoron kar yaje koya jimata ciwo ne. yana ƙoƙarin tashi wayarsa ta fara yin vibrate, dauka yayi ya duba, DR.husna ya gani yana yawo akan screen ɗin, da sauri ya daga bakinsa ɗauke da sallama. Amsa masa sallamar tayi suka gaisa duk da bata ganeshiba, a takaice ya mata bayani daga gidan dayake kiranta yace mata yanada patient ne. Doctor tace, “ok gidan marigayi Alh Nasir kenan?” Yace “eh” tace “Ayya Allah ya ƙara afuwa, yanzu ina shiryawa ne zani asibiti amma kajirani nanda 40 minutes insha Allah zan biyo ta gidan kafin na wuce hospital” godiya mustapha ya mata sukayi sallama ya kashe wayar. kan gadon ya koma, hannunsa ya dora akan wuyanta yaji har yanzu jikinta da zafi, gyara mata kwanciya yayi, sannan yayi kissing pink lips ɗinta da suke matuƙar burgeshi. Falo ya fito ɗauke da Alkur’ani mai girma. Akan Centre carpet ya zauna ya buɗe Alkur’anin ya fara karantawa cikin kira’arsa me daɗin sauraro…..