
7:28 kamar yadda Dr.Husnah tace ta ƙaraso gidan, wayar mustapha ta kira ta sanar masa zuwanta, fita mustapha yayi domin ya taho da ita. tunda ya taho Dr, take kallonsa da alamun mamaki domin batasanshi a gidanba, ita a zatonta duk Saddam ne ya kirata har ya ƙaraso bata ɗauke idonta daga kansaba. Sallama ya mata ta amsa ta ƙara da faɗin, “kaine wanda mukayi waya?” daga mata kai mustapha yayi alamun eh. Kallonsa ta kuma yi tace, “ok muje naga mara lafiyar” gaba yayi ta bishi a baya. A falo ta zauna shikuma ya shiga domin ya tada Maryam. yana shiga ɗakin ya ganta zaune akan gado harta tashi. karasawa yayi gareta da sauri, Maryam kuwa tana ganin ya shigo ta fara matso hawaye. Rungumota yayi ajikinsa yana faɗin, “am sorry, na barki ke kaɗai ga doctor nan tazo zata dubaki” gyada masa kai Maryam tayi cikin dauriya tana cize lips ɗinta, ta dan jima da tashi daga baccin amma ta kasa koda sakkowane daga kan gadon saboda yanda takejin kafarta tamkar ba’ajikintaba, ga ƙasanta dake mata radadi har yanzu. rabata yayi da jikinsa sannan ya fita suka shigo tare da doctor. Dr,husnah ta ƙarasa gaban gadon, duk da yanda Maryam takejin jikinta haka ta daure ta gaisheta. Amsa mata tayi ta tambayeta jiki kuma. dakai maryam ta amsa mata. Tambayar Maryam tayi meke damunta, shiru Maryam tayi ta kasa bata amsa se satar kallon Mustapha datayi. Murmushi doctor tayi ta kalli Mustapha tace ya ɗan basu guri, be musaba ya fita falo. ƙara kallon Maryam dr tayi ta tambayeta meke damunta, batare da maryam tayi maganaba ta nuna mata kanta da kafarta, cikin hikima doctor take tambayarta ina da inane yake mata ciwo ita kuma tana bata amsa, murmushi doctor tayi lokacin data gano bakin zaren. Duba Maryam tayi sosai duk da dakyar Maryam ɗin ta bari ta duba kasannata, mustapha beji mata rauniba kamar yadda doctor tayi zato ruwan zafi kawai jikin Maryam ɗin yake buƙata. kama Maryam tayi ta kaita toilet ta gasa mata jiki tayi sosai da ruwan zafi, musamman ƙasanta da cinyarta da taketa complain akan tana mata ciwo. Ai kuwa Maryam taji daɗin gashin jikin da Dr, ta mata duk tsamin da jikinta yake mata yanzu babu, zugin datake ji a ƙasantama ya ragu sedai kaɗan_kaɗan da kantama ta lallabo ta dawo daki daga toilet din, kan gadon ta ƙara hayewa ta kwanta tana sassauke ajiyar zuciya. dubanta doctor tayi tace, “yanzu ya kika jin jikinnaki?” cikin sanyin murya Maryam tace, “naji daɗin shi sosai, kainane kawai har yanzu yakemun ciwo” doctor tace, “shima ze dena insha Allah, nizan wuce Allah ƙara sauƙi” a hankali Maryam tace, “ameen nagode” sallama doctor ta mata ta fice. yana zaune akan kujera idanunsa a lumshe, jin fitowar Dr, yasashi buɗe idon a hankali. doctor na murmushi tace, “to ango nizan wuce, Allah ya ƙara sauƙi ya kawo mana twins nanda 9 months” murmushin gefen baki yayi yace, “Amin nagode sosai” “babu komai ai, na mata duk abunda ya kamata, yanzu a samu a bata ko da tea ne ta ɗan sha, da kuma maganin ciwon kai, dan tanata complain kannata na mata ciwo.” Amsa mata mustapha yayi sukayi sallama tatafi, bayan yace tatura masa account number ɗinta. Doctor taso shiga su gaisa da ammi amma ganin har 8 ta wuce, kawai seta tafi, se yanzu data ƙara kallon Mustapha taga kamarsa da ammi, hakan yasa ta tabbatar ɗan tane. duk da bata da tabbas a hakan hakan, dan ta kwana biyu batazo gidanba, tun lokacin haihuwar Abul datazo Barka bata ƙara zuwaba sedai waya kawai sukeyi da mutanen gidan lokaci zuwa lokaci…..
Kitchen ya shiga ya tafasa mata ruwan zafi da kansa, a kitchen din ya haɗa mata tea me kauri a cikin wani madaidaicin cup din roba me murfi. Da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga ɗakin. ina jinshi amma ko matsawa banyiba sema ƙara rufe idona danayi gam gabana na faduwa. A jiye cup din yayi ya ƙarasa kan gadon, hannunsa yasa a wuyanta yaji zafin jikinnata ya ragu, ajiyar zuciya ya sauke Sannan ya fara ƙoƙarin dagota a hankali duk da yasan ba bacci takeba, yanda take ta kifkifta idantane yasa ya gane hakan. cire hannunshi nayi daga jikina hawaye ya fara zuba daga idona. Dafe kansa yayi a fili ya furta “ya Salam” ganin yanda take hawaye hannunsa yasa ya juyo da ita suka fuskanci juna, tattausan tafin hannunsa yasa ya fara share mata hawayen, kamar ƙara zugata yayi ta fashe da kuka, janyota yayi ya rungumeta tsam a jikinsa yana sauke numfashi, a hankali yasa hannunsa yana ɗan bubbuga bayanta amma bece mata komaiba, shi kanshi har kansa ya fara masa ciwo. daidai kunnenta yakai bakinsa murya ƙasa_ƙasa yace, “what happened? Ko jikinne? girgiza masa kai nayi alamun a’a ina ƙoƙarin sauka daga jikinsa. Riketa yayi gam da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma ya dago fuskarta a hankali ya matso tasa daf da ita, a hankali yasa harshensa ya lashe hawayen nata dasuke cigaba da zuba. dif na ɗauke kukan se jan numfashi kawai nake. seda ya shanye hawayennata tass sannan yayi kissing saman idonta duka biyun, wanda hakan yasa naji tsigar jikina na tashi yarrr…. finger ɗinsa yasa yana shafa cikakkiyar girarta da murmushi ɗauke a fuskarsa, yanda take ta kifkifta ido ne yake bashi dariya, tanaso ta buɗe idonta amma ta kasa. a hankali yace, “ki buɗe idonki karyaje ya manne yaƙi buduwa” make kafadata nayi na turo bakina gaba. yana dariya ƙasa_ƙasa yace, “shikenan tunda kinki buɗewa nidai babu ruwana idan idanki ya manne, bakisan mutum idan yayi kuka ya rufe idansaba kuma idan ya dade arufe mannewa yakeba.” Kafinma ya ƙarasa na buɗe idannawa da sauri, murmushi yayi cikin jin daɗi dama soyake kawai ya kalli cikin idonnata. ƙoƙarin sauka nayi duk da yadda nakejin daɗin zama ajikinnasa amma zuciyata cike take da tsoronsa kar naje ya ƙara tumurmusheni, kin bata damar hakan yayi. Kyabe baki tayi kamar zatayi kuka Ɗan sassauta riƙon da yayi mata yayi yace, “sorry pls karkiyi kuka” cikin shagwaba nace, “to ba kai bane” waro fararan idanunsa yayi waje yace, “me nayi kuma?” bata bashi amsaba se ƙoƙarin saka masa kuka datayi. Kwantar da kanta yayi akan kirjinsa yana danne dariyar dake cinsa, dan yasan yanda take kan darunnannata idan yayi dariya kuka zata sa masa. Luf nayi a kirjinsa ina shaƙar daddaɗan kamshinsa. tunawa yayi da tea din daya shigo dashi, dagota yayi daga kirjinsa yana faɗin. “Muje kiyi brush kizo kisha tea” maida kaina nayi cikin kirjinsa nace, “um’um bazanshaba” “why?” Yatambaya yana ƙara dago dani. Cikin shagwaba nace, “Ni bazanshaba kawai, kamaidani gurin ammi kuma bazan ƙara kwana a part dinnanba” murmushi yayi me sauti yace, “to se kinsha tea din sannan zan kaiki gurin ammin” tashi nayi daga jikinshi kamar zanyi kuka nace, “to zan sha” barinta yayi ta sauka daga kan gadon da kanta, so yake yaga kozata iya tafiya yanzu da kanta. A hankali kamar yar kaciya take tafiyar, tashi yayi da sauri ya kama hannunta suka ƙarasa toilet din, sabon brush ya dakko ya matsa mata MacLean ya bata. da kanta tayi brush ɗin dan da cewa yayi ze mata taƙi yarda, ƙara kama hannunta yayi suka fito, duk da yanzu ta ɗan kwarara tafiyartata ba kamar dazu dasuka shigoba. Akan cinyarsa ya ɗora ta, yana bata tea din a baki kamar wata yar baby cikin lallabawa. seda tasha sosai sannan ya kyaleta. kulawar da mustapha yake bawa Maryam ba ƙaramin daɗi takeji arantaba, duk da tasan bawai soyayyace tasa yake mata hakaba, saboda abunda ya matane, a nata tunaninfa. duk da tagama shan tea ɗin besauketa daga jikinsaba, a ganinsa idan ya kwantar da ita akan gadonma jikinta ciwo zeyi, yanda yakejin kansa a wani irin yanayi na shauki dazata yarda goyatama zeyi. knocking kofar falo dayaji anayine yasa ya sauketa daga jikinsa badan yasoba. Fita falon yayi ya buɗe Kofar bayan ya tambayi waye, umaimah dake ɗauke da basket na abincin breakfast dinsu ta amsa masa da cewa itace. Taci uwar kwalliya kamar aljana da safiyarnan, cikin rangwada da iyayi tana wani far da ido kamar wata sabuwar makauniya tace, “yaya NOOR ina kwana, dafatan ka tashi lafiya” “lafiya” ya bata amsa a takaice yana komawa cikin falon. Dinning ta nufa ta ajiye basket din, tana tafe tana satar kallonsa harta kusa tuntube. Mustapha dake tsaye yana kallonta yace, “ki zuba komai kaɗan_kaɗan ki kawomun ɗaki” bejira amsartaba ya juya ya koma daki. Cikin tsananin farin ciki umaimah ta shiga kitchen din Maryam ta dakko tire da ƙananun plates ta zuzzuba masa komai kaɗan kaɗan kamar yadda yace, jikinta har rawa takeyi tsabar zumuɗin zata kaiwa Mustapha abinci har ɗaki, domin damar data ɗade tana jirane yau Allah yabata. Zuciyarta cike fal da murna ta ɗauki tire din ta nufi dakinnashi tana wani karkada jiki yanda zata ƙara rikita mustapha ya faɗa tarkonta.(???????????????? Ni ba zance komaiba, Team ɗin umaimah da Maryam ????gareku)…..✍️