
Umaimah ce zaune a kan gadon ɗakin kawarta kuma aminiyarta farida ta rafka tagumi da hannu biyu. Faridance ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da plate data kawo mata ruwa. ajiye plate din tayi akan locker sannan ta hau kan gadon ta zauna itama tana duban umaimah tace, “kawata lafiya naganki wani iri kamar mara lafiya ko kuma me wata damuwar? Umaimah ta sauke numfashi tace, “inafa lafiya kawata, aini da abunda yake damuna gara ace cuta nake wlh” farida tace, “me ya faru tawan?” Umaimah ta ƙara sauke wani nannauyar numfashi tace, “ina cikin babbar matsala kawata” wai matsalar me? Ki faɗa mun abu, kinzo se kwana_kwana kikemun ki tafi kanki tsaye mana kinsan banason hakafa” farida ta fadi haka a ɗan hasale. Umaimah kamar zatayi kuka tace, “akan yaya NOOR ne” farida taja tsaki tace, “dama nasan tatsuniyar bata wuce ta koki, meyafaru to?” Umaimah tace, “ina ganin kamar fa ya gane ina sonsa” “meyasa kika ce haka” “saboda kulawar dayake nunawa matarsa a gabana kamar da gayya yakeyi” farida tace, “to so what, idan ya gane dama ai haka mukeso mu” umaimah tace, “inafa akeson haka, mutumin da yau yayi abunda ya kusa tarwatsa zuciyata, har kuka da seda nayi, Allah yasoma kukan be kufcemun a gabansu ba, shida shegiyar matartasa me kama da aljanu” farida tace, “me ya miki yau ɗin?” Cikin ɗacin rai umaimah taba farida labarin abunda ya faru yau, ta ƙara da faɗin, “wlh farida a lokacin nemar yawu nayi na rasa daga bakina, jikina kamar an zukemun jini haka naji saboda tsabar baƙin ciki, kuma duk abubuwannan dayake mun me makon sonnasa ya ragu daga cikin zuciyata sema karuwa yake, dan Allah kawata ki bani shawarar abunda zanyi na janyo hankalinshi gareni, yasoni nima, ya bani kulawa kamar yadda yake bawa matarsa” farida tace, “to waike kina nufin har yanzu baki fara aiwatar da abunda na baki shawara kiyiba” gyada mata kai umaimah tayi alamar alamar eh. “To me kike jira da baki faraba?” Umaimah tace, “bakisan yaya NOOR bane, yana da kwarjinin da bazan iya tunkararsa da abunda da kike cewa nayiba banmaga fuskar hakanba, ina tsoron kuma kar naje garin neman gira na rasa ido” farida tayi wani tsaki tace, “Ni dan Allah ki nunamun pics din Noor dinnan dakika dameni da zancenshi”
Batare da tunanin komaiba umaimah ta dakko ƴar ƙaramar handbag dinta ta zaro wayarta ta shiga gallery, hoton mustapha data tura a wayar ammi wanda yayi ranar idi cikin manya kayan ta lalubo. Miƙawa farida wayar tayi tace, “kingan shifa” hannun farida har rawa yake ta karbi wayar. “wow handsome guy, kutmar… Aini duk yanda nake tunanin yanda guy dinnan yake da yanda umaimah take fasaltamunshi ya wuce nan, jibeshifa sekace shi yayi kansa gaskiya dole umaimah ta ruɗe amma wannan guy din dani ya dace bada umaimah ba” farida ta fadi haka a cikin zuciyarta lokacin da idanunta sukayi arba da hoton mustapha. kallon Umaimah tayi tana shanye abunda takeji a cikin zuciyarta game da mustapha a kallo ɗaya data masa a rayuwarta tace, “gaskiya umaimah banga lefinkiba da kika ruɗe akan guy ɗinnan dan ya haɗu” umaimah tace, “hmmm, danma baki ganshi a fili ba, sema kinga yanda yake tafiya gently da yanda yake magana a yangance, ke a taƙaice dai komai nashi abun burgewa ne da ban sha’awa. musammanma, yanda yake nunawa matarsa soyayya yafi komai ƙara tsundumani a kogin sonsa, har hangoni nake kwance a kan faffaɗan kirjinnannsa nima yana bani kulawa, wayyo ranar senayi kuka dan murna” wani banzan kallo farida tayiwa umaimah a fakaice kallon baki da hankali sannan tace. “Shawarar dai danake baki a kullum ita zan ƙara baki idan zaki ɗauka to” umaimah kamar zatayi kuka tace, “inason gwada abunda kike faɗamun amma kuma ina tsoron kar kwabata tayi ruwa” farida ta tabe baki tace, “babu wani ruwa da kwabarki zatayi, wannan abun danake faɗa miki shine kawai mafita a gareki. Domin idan baki saniba ki sani, mazan yanzu yan iskane idan bada hakanba ba’asamun zuciyarsu bare ma ke kinga ke kike sonsa shi baya sonki…..” Mahaifiyar farida ce ta shigo ɗakin tana duban umaimah tace, “umaimah anzo ɗaukarki fa” umaimah tace, “to mama bari na fito” jakarta ta ɗauka ta yafa mayafinta ta sauka daga kan gadon tace “to kawata nizan wuce, ammi tace karna jima semunyi waya” Farida itama ta mike tana faɗin, “muje intaka miki” har gurin motar farida ta raka umaimah sukayi sallama umaimah ta shige motar suka tafi.
Wani murmushin mugunta farida tayi bayan wucewar su umaimah, tana sane ta bata guguwar shawarar datasan bazata fishshetaba, tun kafin taga hoton mustapha taji kawai tana ƙyashin umaimah ta mallakesa, yanzu kuma data ga hotonshi setaji bata da wani buri a duniya daya wuce itama ta mallakesa a matsayin mijinta, domin babu ƙarya guy ɗin ya haɗu ƙarshen haɗuwa……✍️
By
Zeey kumurya
ABINDA KASHUKA….!
BY
ZEEY KUMURYA
6️⃣8️⃣
Bismillahirrahmanirrahim
………. Umaimah suna tafiya a mota tana tunanin maganganunsu da farida, da kuma shawarar datake bata a kodayaushe akan Mustapha, duk da tsananin so da kaunar datakewa mustapha bazata iya tunkararsa da wata mu’amala ta banza ba, saboda hakan ba dabi’arta bane kuma ko ba don haka ba, bataga fuskar dazata iya tunkarar mustapha da wani zance na banza ba, mutumin da ko gaisuwarta seyaga dama yake amsawa ta ina zata iya tunkurarsa da wannan abun……
Bayan fitar umaimah ba jimawa Aunty zuhura ta shigo falon, bayan tayi sallama na amsa mata ta dubeni tace, “mamana ya jikinnaki?” A hankali nace, “da sauƙi” tace, “Allah ya ƙara sauƙi, dazu kuma nace miki zan dawo ban dawoba, aiki ne yamun yawa kinsa yau ni kaɗai ce” nace, “babu komai Aunty zuhura ainama warke” tace, “dama abu zan baki, amma idan babu damuwa yanzu kibini part ɗina sena baki” tashi zaune nayi ina ɗan yamutsa fuska nace, “ok muje to, amma bari na miƙawa ammi wayarta” tace, “to” ammi tana haɗa kaya na shiga ɗakin, bayan nayi sallama nace, “ammi sannu da aiki” tana dubana tace, “yawwa ɗiyata, ya jikinnaki dai” nace “naji sauƙi sosai ammi” ammi tace, “to Allah ya ƙara sauƙi, kindaici abincin ko?” “A’a banciba amma zanci kafin na kwanta.” Na fadi haka ina miƙa mata wayarta. Karba tayi tana faɗin, “har kin gama wayar?” Nace, “A’a taƙi shiga may be network ne” ammi tace, “ai haka yake dama wani lokacin, kema yakamata noor ya sai miki waya, na rasa meyake jira har yanzu yaƙi sai miki” murmushi nayi kawai na juya fita. Magungunan mata Aunty zuhura ta bani, dana sha, dana tafasawa a shiga ciki, dana tsugunno” na karba a kunyace na mata Godiya na koma part ɗina. Adanasu nayi a kitchen, inayin sallar isha’i na tsakuri abinci naci kaɗan nasha maganin ciwon kai, dan har lokacin kan na ɗan saramun. da kyar na iya watsa ruwa saboda yanda nake jin jikina, ina fitowa na shafa mai da turare sama_sama, na zira wata rigar bacci na haye gado na kwanta, ba jimawa bacci ya ɗauke ni…..
Mustapha tun yamma da Maryam ta tafi part din ammi yake aiki a system ɗinsa, jibi su daddy zasu dawo daga Saudiyya shine daddy’n ya bashi wani aiki yanaso ya kammala masa kafin su dawo, seda aka kira sallar magriba ya ajiye ya tafi masallaci, be ƙara dawowa gidan ba seda tara na dare ta wuce. Time ɗin daya dawo maryam tana ɗakinta tana wanka, be mayi zaton ta dawo ba, saboda sanda zata tafi part din ammi ce masa tayi acan zata kwana. ɗakinsa ya shige shima a ɗan gajiye yake hakan yasa ya rage kayan jikinsa ya faɗa toilet. Bayan ya fito ya shirya cikin wata jallabiya brown colour, wadda ta masa kyau sosai se tashin daddaɗan kamshinsa yake. wayoyinsa ya kwasa guda biyu a hannu ya fito ya fice daga part din gabadaya ya nufi na ammi domin yakirawo maryam. Umaimah ce kaɗai zaune a falo tana cin abinci, yau da yunwa ta wuni saboda ɓacin rai seyanzu da taji yunwa ta kusa kasheta shine tana dawowa ta sauka akan abincin. Yana turo ƙofar tun kafin ya shigo daddaɗan kamshinsa ya fara kai wa hancinta ziyara, lumshe madaidaitan idanta tayi tana ƙara bubbuɗe kofofin hancinta yanda zata shaki kamshin yanda yakamata. sallama yayi babu yabo ba fallasa. Umaimah ta gyara zama tana tattaro nutsuwarta ta buɗe idonta ta sauke akansa cikin iyayi da neman suna ta amsa masa sallamar ta ƙara da faɗin, “yaya NOOR sannu da zuwa, ina yini” beko kalli inda take balle ma ya nuna yasan da zamanta a falon ya nufi ɗakin ammi ganin bata falon ita da wadda yazo nema. Ita kuma sakarya ta bishi da kallo baki buɗe. kamar koyaushe baya shiga ɗakin ammi se yayi knocking, yanzunma knocking din yayi. Ammi dake tsaye a gaban madubi tana fesa turare ta ajiye turaren ta nufi kofar ta buɗe. Sallama yayi cikin sanyin murya, ammi amsa masa tare da bashi hanya ya shigo cikin ɗakin. Ammi tana k gyara kayan kan mudubinta tace, “inata jiranka tun dazu ka shigo najika shiru har ina shirin kwanciya” yace, “kwanciya kuma da wuri haka ammi?” Ammi tace, “ehh na gajine yau baccin wuri zanyi” yace, “ayya sannu” ammi ta amsa da “yawwa, ta ƙara da faɗin. “Yaushe daddynka ze dawo ne, dazu munyi waya da uncle ɗinka yacemun yau yaje sun haɗu, harma daddy’n yace masa a cikin week ɗinnan zasu dawo.” Mustapha yace, “jibi yace mun zasu dawo” ammi tace, “Allah yakaimu lafiya, kukuma se yaushe zakuje?” Yace, “Ran laraba insha Allah, amma ni kaɗai zani” ammi ta juyo ta dubeshi tace, “kai kaɗai kuma banda Maryam?” yace, “ehh” atakaice. Ammi tace, “shikenan, dama naji tana za’ayi bikin kawarta a cikin watannan seta biya ta dubashi idan taje” bece komai ba, saboda shi sam bayason wata alaƙa dazata ƙara haɗa Maryam da Sadik. ammi ta nufi kofa ta fita batare ta ƙara ce masa komaiba. wayarsa dake hannunsa ya shiga latsawa yana jin zuciyarsa babu daɗi. Ammi da plate ɗin abinci ɗauke a hannunta ta dawo ɗakin, agabansa ta ajiye tana faɗin “NOOR sakko kayi dinner” yamutsa fuska yayi bece komaiba ya sakko ya zauna a saman carpet din bakin gado, yasan ko yace baze ciba, ammi seta tursasashi. Ammi taga yanda yayi da fuska tayi kamar bata ganiba, tasan yanda taga ransa a bacennan ba ƙaramin aikinshi bane ya kwanta beci abincinba, shiyasa bazata barshi ya tafi ba seya ci abincin ko kaɗanne. dawowa ɗakin ta ƙara yi dauke da ruwa da ƙaramin cup ta ajiye a gabanshi tana kallon fuskarsa, shima kallonta yake cike da tsananin kaunarta. Hannunta ya kama ya sumbaci tafin hannunta, a hankali yace, “thanks UMMUNAH” murmushi kawai ammi tayi batace komaiba, zama tayi a kusa dashi tana kallonshi cike da so da kauna. A hankali ya fara cin abincin cikin nutsuwa kamar bayason ci bayan yayi bismillah. kaɗan yaci ya ajiye spoon din ya rufe abincin ya dakko ruwa ya tsiyaya ya sha. A fili ya furta “Alhamdulillah” mikewa yayi ya ɗauki wayoyinsa yayiwa ammi sallama ya tafi. ammi tayi murmushi bayan ya fita, komai idan mustapha yana yi se taga kamar midibbontane, komai nasu iri ɗaya ne sak babu ta inda Mustapha ya bar mahaifinsa seta yanda yake kallon abu da yanayin idanuwansa shine kawai ya dakko na ammi. abincin ta ɗauka ta fice dan ta kai kitchen tana jin zuciyarta babu daɗi itama, saboda tuno tsohon mijinta datayi………