
Se wajen ƙarfe tara na bar part din ammi da abincinmu. Key ɗin hannuna nayi amfani dashi na buɗe part din. A kan dinning na ajiye abincin na wuce ɗakina nayi wanka nayi shirin bacci, abinci kawai yaragemun naci. falo na dawo na duba agogo naga har 9:32 pm. nayi mamaki sosai danaga har yanzu yaya be dawo ba, dan yanzu anayin sallar isha’i yake dawowa. ina ƙoƙarin komawa ɗakina ya shigo falon, ajiyar zuciya na sauke cikin jin daɗi. da fara’a na juyo na kallesa, yanda yayi sallama acici fuskarsa babu walwala se jikina yayi sanyi. Mustapha ɓacin ran umaimah be bar zuciyarsa ba har yanzu, amma ganin maryam da yayi se yaji zuciyarsa ta ɗan sanyaya. zama yayi akan kujera yana fesar da numfashi tare da lumshe idanunsa. “Sannu da zuwa” na faɗa cikin sanyin murya ina takowa zuwa inda yake. beko motsaba balle ya amsa. sosai naji babu daɗi a cikin zuciyata, nima ban ƙara cewa komaiba na nufi kitchen na ɗauko mana plate da spoon, abincin na zuba mana mu biyu saboda a kwanakinnan tare muke cin abinci shiyasama tun dazu banciba na tsaya jiranshi. A gabanshi na ajiye na dakko mana ruwa da juice da glass cups duk na ajiye. zama nayi a ƙasan na dubeshi nace, “yaya ka sakko muci abinci” Buɗe idonshi ya yayi ya kalli abincin a hankali yace, “kici kawai” kallonsa kawai na tsaya inayi cike da mamakinsa yanda yake mun yau, na lura amma ransa a bace yake. Cikin lallami nace, “dan Allah kayi hakuri ka sakko muci, Ni bazan iya ci ni kaɗai ba” shiru yamun kamar bejini ba. tashi nayi da nufin naje na kwanta dannima banajin zan iya cin abinci yanda nake jin zuciyata babu daɗi a sanadiyyar halin dana ganshi a ciki. Caraf naji ya riƙo hannuna ya maidani na zauna. A hankali ya zamo ya sakko shima daga kan kujerar ya zauna daf dani, batare daya kalleniba ya janyo kwanon abincin gabansa ya buɗe yasa spoon ya ɗiba ya kai bakina. kauda kaina nayi hawaye na zubomun da bansan dalilinsuba. Runtse idansa yayi zuciyarsa na masa ɗaci ganin hawayenta. maida abincin daya debo yayi cikin plate ya ja numfashi ya fesar, buɗe idonsa yayi ya kalleta hawayen take ba kakkautawa. “Ya Salam” ya furta a fili yana janyota jikinsa. Aransa yana mamakin saurin kukanta, kukanta har yayi yawa. Dan yatsansa yasa yana share mata hawayen fuskarta, shiru nayi na bar kukan ina sauke ajiyar zuciya dama abunda nakeso kenan najini a jikinshi. bece komaiba ya gyara mata zamanta akan cinyarsa, abincin ya debo ya ƙara kaiwa bakinta. buɗe bakina nayi a hankali ya zubamun. seda na cinye ya ƙara debo wani ze samun a baki nace masa, “kaima kaci” girgizamun kai yayi yace, “am ok” gimtse bakina nayi na turoshi gaba. bakina ya ƙara kai spoon ɗin yana tsuke fuska tare da mun wani kallo, ba shiri na buɗe bakin ya zubamun, da kanshi ya ciyar da ita, seda ya tabbatar ta koshi sannan ya kyaleta bayan ya bata ruwa da lemon juice tasha. Tashi nayi daga jikinshi na ɗauke sauran abincin na kai kitchen, kafinna fito harya wuce dakinshi. Ɗakina na wuce nima nashiga toilet nayi brush. Harna kwanta na tuna da wani sako da ammi ta bani nabashi dazu, banmasan meneba, abu nedai a cikin leda. ɗauka nayi na nufi dakinnashi. yana zaune yana operating system akan gado ta shigo ɗakin da sallama. batare daya dago ba ya amsa mata. ajiye ledar nayi akan locker nace, “ga saƙo, ammi tace na baka” dagowa yayi ya zuba mata lumshashshun idanunshi bece komaiba se ya kutota da yayi da hannunsa alamun ta ƙaraso. A hankali na taka na hau kan gadon na zauna a gefensa. har lokacin kallonta yake yana jin wani abu na yawo acikin zuciyarsa game da ita. kuncinta ya shafa yace, “Sarkin rigima, waya taɓoki?” kirjinshi na nuna da hannuna ina kwabe fuska. waro ido yayi yanajin wani nishadi a cikin ranshi kasancewarsu tare wanda harya mantar dashi ɓacin ran da umaimah ta sakashi. yace, “Ni kuma?” gyada masa kai nayi alamar Eh. fuskarsa ya matso da ita daf da tawa yace, “me nayi kuma?” lumshe idona nayi nace, “baka siyomun alawataba kuma kakicin abinci, kuma se ɓata ranka kake kana….” haɗe fuskokinmu dayayi guri ɗaya yasa na haɗiye zancena batare dana shiryaba bugun zuciyata na sauyawa. karan hancinsa yake gogawa akannata a hankali, kusan 40 seconds suna haka, kafin janye fuskarsa daga tawa yana sauke numfashi a hankali yace, “zan siyo miki sweet ɗinki insha Allah gobe idan naje Kano” “Kano kuma?” Na faɗa cikin mamaki ina buɗe idona. dagamun girarsa yayi alamar eh. marairaicewa nayi nace, “amma tare zamu tafi ko?” “Why” ya tambayana yana kallon cikin idona nace, “Ina son ganin gwaggo” ɗauke idonsa yayi daga kanta ya maida kan system ɗin sa, ba haka yaso ji daga garetaba. girgiza kai yayi alamar a’a. kalar tausayi nayi sosai domin harga Allah inason zuwan nace, “Please yaya kaje dani” yace, “zakije amma ba gobe ba” kamar zanyi kuka nace, “nidai gobe dan Allah” shiru ya mata, dama yasan indai yace mata zashi kano setace zata bisa. kashe laptop din yayi ya tureta gefe. kawar da zancen tafiyar yayi da faɗin “daddy yana gaisheki” nace, “ina amsawa, waya kukayi?” dagamun kai alamar eh. “Kakiramunshi nima mugaisa tunda nazo garinnan bamu taɓa wayaba” “dare yayi yanzu, ki bari idan naje gobe zan haɗaku a waya” shawabe fuska nayi sosai nace, “dan Allah katafi dani yaya, nayi missing Kano sosai Allah” kwanciya yayi ya janyoni jikinsa yana shafa bayana yace, “ammi tacemun za’ayi bikin freind ɗinki a mont dinnan ki bari time ɗin sekije.” cikin shagwaba nace, “Ni dai zan bika goben” yace, “sedai ki zaba ɗaya, idan kika bini gobe bazaki bikin ba kinyarda?” shiru nayi na fara ƙoƙarin tashi daga jikinshi, maidani yayi yasa hannunshi duka biyu ya zagaye bayana. Mutsu_mutsu tafarayi a jikinshi ta saki kukan zallar taɓara kukan da babu ko digon hawaye. bakinsa ya kai saitin kunnenta ya fara hura mata iska yana shafa ƙananun kitson kanta. Lumshe idona nayi ina ƙara cusa kaina cikin kirjinsa ina shaƙar daddaɗan kamshinsa……..✍️
By
Zeey kumurya
ABINDA KASHUKA….!
BY
ZEEY KUMURYA
7️⃣0️⃣
SUBSCRIBE
DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV
MARUBUTA DA MASU SON ZAMA MARUBUTA DA WANDA SUKE BUƘATAR MENTOR????????✍????
ASSALAMU ALAIKUM
AMINCIN ALLAH DA RAHAMAR SA SU ƘARA TABBATA GA ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)
- MARUBUCIYA CE KE, BAKI SAN YAYA ZAKI FIDDA LABARIN DUGU KO GAJERE BA..?
- SHIN KINA SON KIYI LITTAFIN SIYARWA KINA TSORO ZA’A SIYA KO A KA SIN HAKA…?
3 MARUBUCIYA CE KE,AMMA HAƊA LABARI YANA BAKI WAHALA,SANNANA IDAN KIN FARA LABARIN NA SAURIN YAKE MAKI…? - KIN DAƊE KINA RUBUTU NE AMMA HAR YANZU LITTAFANKI BASA KARƁUWA WAJAN MAKARANTA…?
- MARUBUCIYA CE KE? AMMA KINA DA MATSALA WAJAN RUBUTUNKI,KINA BUƘATAR WACCE ZA TANA GUIDE NAKI WAJAN RUBUTU, MA’ANA KINA BUƘATAR MENTOR…?
- A MATSAYIN KI MARUBUCIYA KINA DA MATSALA NE? AMMA KINA TSORAN FAƊAR MATSALAR KI SABIDA GUDUN WULAƘANCI…?
7.MARUBUIYA CE KE, AMMA BAKI SAN YADDA ZA KINA AMFANI DA, WATTPAD, TELEGRAM, FACEBOOK,OKADA BOOKS BA…? - MENE MATSALAR KI A RUBUTU? TSARA LABARI? ƘA’IDOJIN RUBUTU,SANIN AL’ADUN YARUKA DABAN DABAN?
- KINA SHA’AWAR RUBUTA LABARIN FILM MA’ANA YADDA AKE RUBUTA SCRIPT? KO KUMA KINA SHA’AWAR RUBUTA DRAMA?
- AT THE END KINA SHA’AWAR RUBUTA LITTAFIN YA ƘI NE AMMA BA KISAN YAYA AKE BA..?
GABA ƊAYA MARUBUTAN MU WANNNAN DAMA CE A GAREKU GA DUKKAN WANDA YA KESON SHIGA WANNAN ƘUNGIYA KO NACE GROUP ,BAWAI ƘUNGIYA CE WACCE AKE RUBUTU A ƘARƘASHIN TA BA, A’A WANNAN HAƊAKA NE, MAGANA DAI GROUP NE NA TAIMAKON JUNA DA BAWA JUNA SHAWARA,KO DA KINA DA ƘUNGIYA ZAKI IYA SHIGA WANNAN GROUP ƊIN MAI TAKEN ELEGANT ONLINE WRITER’S
GROUP NE DAYA SHIRYA TSAF DOMIN TAIMAKON ƳAN’UWA MARUBUTA DA KUMA MASU SHA’AWAR ZAMA MARUBUTA
_GA DUKKAN WANDA YAKE SHA’AWA MUNA DA TSARE TSARE DABAN DABAN SANNAN KUMA AƘWAI FORM DA ZA’A BAKA KA CIKE,BAWAI HAKA KAWAI ZA’A SAKA MUTUM BA MAI SON SHIGA WANNAN GROUP ZAI IYA TUN TU ƁAR WA ƊAN NAN NUMBOBIN KAMAR HAKA.
- 08069224458
- 09066710753
3.08167120325
SANAWAR DAGA SHUGABANNIN GROUP ƊIN NA EXCO ELEGANT ONLINE WRITERS.
Bismillahirrahmanirrahim
……..Bacci me daɗi ne yayi awun gaba da maryam cikin kankanin lokaci. A jiyar zuciya ya sauke jin saukar numfashinta alamun bacci take. a hankali ya lallaba ya janyeta daga jikinsa ya kwantar da ita a gefensa. filo yasa mata tare da gyara mata kwanciya ya tofeta da addu’a. tashi yayi zaune yana jin kamar kar ya matsa daga kusa da ita. Fuskarta ya kurawa ido cikin wani irin yanayi kamar me son gano wani abu a fuskar. a wani ɓangaren kuma sosai ta masa kyau yanda take yin baccin, zara_zaran gashin idonta sun kwanta har ƙasan idonta abun sha’awa, bakinta ya kalla yayi murmushi ta ɗan turoshi gaba kamar kodayaushe idan tana bacci. ɗan yatsansa yasa a hankali ya shafi pink lips ɗinta cikin sauƙi, kamar ya zugata ta ƙara turo lips ɗin gaba, hakan da tayi ba ƙaramin kyau ta ƙara masaba yana son yaganta cikin yanayin shagawa shiyasa some times yana sane yake tabota, amma bayason kukanta ko kaɗan. wayarsa dake gefensa yasa hannu ya dakko, kunnawa yayi ya shiga Camera ya fara ɗaukar face ɗinta a hoto, kala uku ya mata pics din, kuma tayi kyau sosai a hoton murmushi yayi ya ajiye wayar, blanket yasa ya lullubeta sannan ya sauka daga kan gadon. Toilet ya fara shiga yayi wanka, bayan ya shirya cikin fararen kayan bacci masu taushi ya fita zuwa falo. kitchen ya shiga ya haɗa cofee ya yasha. Light din falon da ɗakin maryam dana kitchen din ya kashe ya koma ɗakinsa. seda ya ƙara duba wani abu a laptop dinsa sannan ya kashe musu light din ɗakin ya hau gadon ya kwanta shima. janyota yayi jikinsa yana sakin ajiyar zuciya, sosai yake cikin buƙatuwa da ita, amma wani tausayinta yakeji danshi kallon yarinya ƙarama yakewa maryam, a ganinsa idan ya fiya takura mata kamar da matsala, lumshe idonsa yayi kawai ya ƙara mannata a kirjinshi kamar ze maidata ciki, mutsu_mutsu Maryam ta farayi hakan yasa ya sassauta mata riƙon daya mata ya shiga shafa bayanta, shiru tayi taci gaba da baccinta, shikam ya ɗan jima kafin bacci ya daukesa…..