
Washegari, Bayan anyi sallar asuba Maryam ta shiga gyaran gida mustapha kuma ya koma baccinsa. Bayan na gama gyaran gidan na koma ɗakina nayi wanka na shirya cikin wata doguwar rigar a baya dark blue, an mata ado da Stones masu sheki da walwali a gaban rigar da kasan hannunta. Ribbom nasa na daure gashin kaina, wata hula nasaka me kyau Black colour gaban hular me V ne, hakan yasa gaban kitsona ya fito se yayi kyau sosai, kwalli kawai nasa da white lipstick me ɗan ɗanƙo, se barima da na sa a kunnena. amma ni kaina nasan nayi kyau. Agogo na kalla naga goma na safe saura 2O minutes, falo na fito da nufin naje ɗakin yaya, kafin na ƙarasa se gashi ya fito cikin shirinsa shima, sanye yake cikin wani milk ɗin yadi me matuƙar kyau da tsada. Kallonsa Maryam take kamar yadda shima ya kura mata ido yana kallonta, tayi masa kyau sosai ze iya cewa ma tunda suke take be bata ganin ta masa kyau irin na yauba, kallon idanunta yayi yanda take kallonsa se yaji gabansa ya faɗi saboda abunda ya gani, sosai ya cika da mamaki mara misaltuwa zuciyarsa na ɗan bugawa ya ƙarasa takowa gareta, daf da ita ya tsaya harsuna jiyo hucin numfashin juna. Ƙasa nayi da idona da sauri murya ƙasa_ƙasa nace. “Ina kwana” be amsamunba se haɓata daya kama ya dago fuskata, lumshe idona nayi da sauri ganin yasaka idonsa cikin nawa bugun zuciyata na sauyawa, numfashi ya furzar a hankali kamar me rada yace, “Please ki buɗe idonki I want see something” bude idonnayi a hankali amma ba’akan fuskarsaba dan bazan iya haɗa ido dashiba. kallon idonta yake sosai da yanda take kallon gefe zuciyarsa nacigaba da bugawa, ya kai mintuna uku yana kallon idonnata, a hankali ya saki haɓartata yana sauke numfashi. shafa gefen kuncinta yayi yana murmushin gefen baki yace, “kinyi kyau” kallonsa nayi da sauri dan be taɓa faɗamun hakaba tunda muke, gira ya dagemun yace, “sosai fa” ƙasa nayi da kaina a hankali nace, “Nagode” cikin tsananin jin daɗi, murmushi yayi ya kama hannuna muka ƙarasa muka zauna akan kujera. Kwantar da kaina yayi akan kafadarsa yace, “me kikeso in siyo miki tsaraba” ya ƙarashe zancen yana haɗe hannuna da dashi. girgiza kai nayi alamar A’a, yana kallon fuskata yace, “why?” nace, “banason komai nidai kawai ka tafi dani dan Allah” wayarsa dake gaban rigarsa ce ta fara vibrate, hakan yasa be bani amsaba ya zarota ya daga ya kara a kunnensa, 3 seconds yace “Wa’alaikumussalam” ya ƙara ɗan jim kafin yace, “ohk ganinan” katse wayar yayi yana duban fuskar Maryam yace, “ki faɗamun me kikeso zan wuce ne yanzu” dago kaina nayi daga jikinsa da mamaki nace, “yanzu zaka tafi?” gyadamun kai alamun eh. Nace, “baka cifa abinci ba” yana bina da wani irin kallo yace, “ehh zanci acan” zan ƙara magana ya tashi tsaye tare kamo hannuna nima ya tadani. Tafiya ya farayi still hannunsa riƙe da nawa, hakan yasa nima na fara binsa kamar raƙumi da alaƙa, a zuciyata ban yarda ko kaɗan tafiyar zeyiba da gaske, saboda babu wata alama data nuna haka , tunda bacin wayarsa banga komai a hannunsaba. a bakin kofa ya tsaya yana kallona ƙasa nayi da kaina cikin wani irin sanyin jiki, ɗayan hannuna ya kama ya haɗe a hannunsa fuskarsa ya matso da ita daf da tawa yace, “zan wuce kimun addu’a” dago da kaina nayi na kallesa kwalla na taruwa a idona cikin sanyin murya nace, “wai dagaske kake tafiya zakayi yanzu?” daga mata kai yayi cikin matuƙar tausayinta, jiyake kamar ya canza ra’ayinsa ya tafi da ita amma akwai dalilin dayasa baze tafi da itanba. hawaye sosai Maryam take yi, rungumeta yayi tsam a jikinsa yana ɗan bubbuga bayanta, riƙe shi Maryam tayi sosai itama kamar me tsoron kar a rabata dashi. sosai yakejin ba daɗi a cikin zuciyars, ga kukanta dake taɓa masa zuciya yanajin kamar tana watsa masa garwashi a cikin zuciyarsa. Sun kai 6 minutes a haka kafin a hankali ya rabata da jikinshi jin tayi shiru se ajiyar zuciya datake saukewa. Hannunsa yasa ya share mata hawayen fuskarta. Idanunta ya kalla yace, “menene?” Girgiza masa kai nayi alamar A’a sannan nace, “Allah ya kiyaye hanya ya kaiku lafiya” “ameen” ya faɗa cikin wata irin murya, yanajin wani abu na yawo acikin zuciyarsa akanta. ƙasa na ƙara yi da kaina, inajin zuciya ba daɗi kamar na fashe da kuka haka nakeji. Kallonta yakeyi tamkar yau ya fara ganinta, kamar ya fasa tafiyar haka yakeji shima, danne duk abunda yakeji a zuciyarsa yayi ya kalli tsadadden agogon hannunsa yaga lokaci, sakin hannunta yayi yace, “bye, kikula da kanki” dago kaina nayi hawayen danaketa ƙoƙarin maidawa suka zubo. Lumshe idonsa yayi ya buɗe, ƙara janyota yayi jikinsa ya share mata hawayen fuskarta yana jifanta da wani kallo, amma bece komaiba. Cikin sanyin murya nace, “yaushe zaka dawo?” “Gobe” ya faɗa cikin wata irin siririyar murya. Ajiyar zuciya na sauke nace, “Allah ya kaimu, ka gaishesu sosai” yace, “zasuji insha Allah” ya ƙarasa zancen tare da kissing forehead ɗina, murmushi nayi na lumshe ido ina ƙara lafewa a jikinsa ina jin tamkar mu dawwama a haka. Shima Mustapha a nasa bangaren haka ne, ga kamshin jikinta daya masa daɗi sosai harya sanya ya fara jin wani irin baƙon yanayi ajikinsa, daurewa yayi ya rabata da jikinsa, gefen fuskarta ya shafa ya fice batare daya yarda ya ƙara kallon idontaba, saboda karta karya masa zuciya. binsa nayi da kallo harya fice daga falon gabadaya, sosai nakejin wata irin kewarsa tun yanzu ta lullubeni, jan ƙafata nayi na faɗa kan kujera na zauna ina sauke numfashi. Mustapha shima jikinsa duk a sanyaye ya nufi part din ammi. A falo ya tarar da umaimah tana mopping tana ganinshi kamar wadda taga dodo ta zura da gudu tayi ɗakinta, tabe bakinsa yayi dan ba ita yakeba ya shiga ɗakin ammi. Ammi na dubansa bayan sun gaisa tace, “bangane tafiya zakayiba yanzu bakaci komaiba, yau bamu tashi da wuri bane shiyasa mukayi late gurin aiki” mustapha ya ɗan ja numfashi yace, “karki damu ammi zanci abinci idannaje can” ammi ta masa wani kallo, batace komaiba ta mike ta fice daga ɗakin. binta yayi da kallo cikin kaunar ta, shi kanshi yana jin yunwar amma yanda zuciyarsa take cike da ɗokin ganin daddy dasu haidar yasa baya ta abincin. Bayan wasu mintuna ammi ta dawo ɗakin hannunta ɗauke da cup data haɗa masa tea me kauri, batace komaiba ta mika masa. ba musu shima ya karba ya fara sha, a hankali yake kurba har yasha sosai, ya ajiye sauran, ammi bata kyaleshi haka ba seda ta bashi dabino me ɗan yawa tace yaci, be cinye dukaba a leda tasa masa sauran tace yaci a hanya. Sallama ya mata ya tafi, bayan ta kwarara masa ruwan addu’a tare da jaddada masa karya manta ya tahowa da Maryam da wayar hannu. daze tafi yana kallon part ɗinsu kamar ya shiga ya ƙara ganin yar matartasa, amma dai ya hakura be shigaba ya nufi inda driver’n ammi yake jiransa tun dazu…..
Tunda na zauna nayi jugum ni kaɗai, ƙwaƙwkwaran motsi banyiba, na kusa awa a haka da ƙyar na yunkura na tashi na shiga ɗakina na dakko hijabi na saka na fito zuwa part ɗin ammi. Suna falon duka matan gidan har mama nafisa datayi tafiya dangin mijinta se jiya da daddare ta dawo. danne damuwata nayi muka gaisa da kowa faran_faran nayiwa mama nafisa sannu da zuwa. umaimah se jifan maryam take da wani mugun kallo, ita dai maryam tunda ta gaisheta kota kanta bata ƙara biba. ɗaki ammi ta kaimun abinci tace inje inci, yanda nake jina wani iri abincinma bana son ci, haka dai na daure na cuccusa, duk da hakanma kaɗan naci na barshi…..✍️