
Bayan na gama cin abincin na fita falo muka ɗan taɓa hira dasu Aunty zuhura, har akayi sallar magriba wayar ammi na hannuna ina dakon kiransa amma naji shiru, ammi ma ta tambayeni ya kira nace mata A’a, har akayi sallar isha’i be kiraba. Ajiye wayar nayi zuciyata babu daɗi na kwanta akan gadon ammi, dan anan zan kwana, bacci ne ya ɗaukeni batare dana shirya masaba………
Mustapha be samu kansaba se kusan ƙarfe goma na dare, part ɗinsa na gidan anan ze kwana, daddy yayi zaton tare zasuzo da Maryam shiyasa yasa aka gyarashi tsaf idan sunzo su sauka. yana shiga ɗakin shi ya zaro wayarsa daga aljihunsa, missed call ya gani har 5, na ammi 2 sena Aunty 1 se kuma wata bakuwar number 2. Layin ammi ya kira dan cike yake da kewarsu musammanma yar meronsa. Ammi ta ɗaga wayar da sauri dama tana hannunta, mustapha ya mata sallama ta amsa ta ƙara da faɗin, “NOOR ina shiga ne inata jiranka baka ɗagaba?” Mustapha yace, “babu inda na shiga ammi, muna tare dasu daddy ne banma dakko wayarba se yanzu” ammi tace, “amma kasan ai zan nemeka inji ya kukaje kanon, yanzu hankalina harya fara tashi danaji shiru ina shirin kiran dad dinnakama tunda kai na kiraka baka ɗaga ba, kiranka ya shigo” mustapha yayi murmushi yace, “ayi hakuri Amminah kinsan mun daɗe bamu haɗu ba muna ta hirar yaushe gamo” ammi tace, “shikenan kunje lafiya?” Yace, “lafiya kalau” ammi tace, “Masha Allah” shiru yayi yanaso ya tambayi Maryam amma miskilancinsa ya hanasa, ammi jin yayi shiru tace, “kaje ka kwanta ka huta to, da safe mayi waya” yace, “Allah yakaimu” ammi tace, “Ameen, karka manta fa, idan Allah yakaimu goben kaje kagaida gwaggonta” yace “insha Allahu” ammi ta katse kiran. ajiyar wayar yayi ya rage kayan jikinsa ya shiga toilet ya watsa ruwa, be tsaya yin komai ba ya kwanta saboda gajiyar dake damunsa, lumshe idonsa kawai yayi amma sam bacci yaƙi zuwa, sosai kewar Maryam take damunsa, yanzu daya kwanta kamar an ƙara masa kewartata, ya saba kwanakinnan manne da ita yake bacci yana shaƙar kamshinta dayake matuƙar yi masa daɗi, yana shafa lallausar fatarta, secan dare ya samu bacci ya ɗauke sa bayan yagama juye_juye da rungumar filo…..✍️
By
Zeey kumurya
ABIN DA KA SHUKA….!
BY
ZEEY KUMURYA
7️⃣2️⃣
SUBSCRIBE
DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV
Bismillahirrahmanirrahim
……….Washegari haka na tashi sukuku dani kamar mara lafiya, baccinma gabadaya be mun daɗi ba, a daren jiya na farka ya kai sau uku, zuciyata babu daɗi ko kaɗan, kallo ɗaya mutum ze mun ya gane hakan. Gari na fara haske muka shiga kitchen nida ammi, duk dauriyar danake na boye abunda yake raina seda ammi ta gane. Ina cikin ferayar dankali ta dubeni tace, “ɗiyata jikinne dai?” A hankali nace “A’a, aina warke” ammi tace, “ki koma ɗaki ki kwanta, yanzu zuhura zatazo semu ƙarasa aikin tare, idan mun gama sena kaiki asibin” nace, “Toh ammi” na ajiye wukar hannuna na fice, ɗakin ammi na koma na kwanta akan gado. Lumshe idona nayi ina hango yaya a idona cikin matuƙar kewarsa, yanda nakeji a raina kamar bana tare da wani sashi na jikina, Har ƙarfe tara na safe inanan kwance, da naga kwanciyar bazata munba, sena tashi na hau gyaran ɗakin ammi, bayan na gama na fito falo da nufin na gyarashi shima sena tarar da umaimah tana mopping, bance mata komaiba kamar yadda itama naga babu alamar hakan a tattare da ita, ficewa nayi daga falon gaba-daya, umaimah ta raka Maryam da harara tana tabe baki. part ɗinmu na koma dannayi wanka, kafin nayi wankan seda na gyara gidan duk da babu wani datti a cikinsa, na daɗe a ɗakin yaya ina shaƙar kamshinsa dake manne a ɗakin kamar yananan, kamar kar na bar ɗakin haka nakeji, ba dannasoba na fito ɗaga ɗakin na koma ɗakina bayan na gama gyarashi, wanka nayi na shirya cikin sauri saboda nasan ammi tanacan tana jirana zamu asibiti. ina komawa part din ammi na tarar har sungama aikin sun karya, itama ta shirya jirana kawai take. Abinci na debo na faraci a ɗakinta, kafin na gama cin abincin ammi tayi baƙi, Bayan na gama cin abincin na fito falo muka gaisa dasu, mata ne guda uku se kallona sukeyi, ammi ta dubeni tace, “Maryam kinga nayi baƙi, ki bari gobe idan Allah ya kaimu sai muje” nace “Allah yakaimu lafiya” ɗaki na koma na ɗauka comp da kibiya na fara tsifar kaina…..
Da ƙyar ya iya tashi yaje masallaci yayi Sallah saboda baccin dake cinsa tunda besamu wani ishashshen bacciba a daren jiya, yana dawowa daga sallah ya ƙara bin lafiyar gado, wayarsa dake gefen kansa ta fara ringing wanda shine yayi sanadiyyar farkawarsa daga baccin. yana yatsina fuska na dakko wayar ya duba, Aunty ce take kiransa kafin ya kai ga ɗagawa har kiran ya katse, bin bayan kiran yayi, ringing ɗaya ta ɗauka tare yin sallama, cikin murya me cike da bacci ya amsa mata yana tashi zaune, ya ƙara da faɗin “ina kwana Aunty” aunty tace, “lafiya kalau Muhammad, bacci kake ne naji Muryar haka?” ɗan gyaran murya yayi yace, “ehh yanzu na tashi” Aunty tace, “Toh ko inbari later mayi maganar?” yace “A’a dama ina son kiranki naga missed call ɗinki jiya” aunty tace “ehh dama inason kamun transfer din kudi ne” yace “ok kamar nawa?” Aunty tace “1.5 ma is ok” aransa yana mamakin me Aunty zatayi da Kudi haka, amma ya danne mamakinsa yace, “ok zantura Miki anjima” Aunty tace “thank you, kana kanonne?” Yace “ehhh nazo tun jiya” Aunty tace “nima a satinnan zan shigo insha Allah” yace “Allah yakawoki lafiya” daga haka sukayi sallama ya katse kiran. jingina bayansa yayi da jikin gado yana lumshe idonsa, Maryam kawai yake hangowa a idonsa, tafiyarta, maganarta da yadda takeyin komai cikin sanyi duk yake tunawa, buɗe lumshashshun idanunsa yayi, wayarsa dake hannunsa ya latsa, pics ɗin daya mata tana bacci ya lalubo ya fara kalla, wani murmushi ne ya subuce masa, yayi missing shagwabarta sosai, yayi 10 minutes yana kallon hotonnata cike da shauki, zooming pic din yayi dai_dai pink lips ɗinta daketa kyalli kamar a zahiri yake ganinsu, wayar ya kai bakinsa yayi kissing pic ɗin, a fili ya furta “I MISSED YOU” badan yagaji da kallon pic dinba ya a jiye wayar ya mike a hankali ya nufi toilet. Ya ɗauki lokaci kafin ya gama shiryawa ya fito falo, a falon ya tarar da haidar zaune yana latsa waya. haidar yana ganinshi ya ajiye wayar hannunsa cikin murmushi yace, “ina kwana yaya” mustapha ma dan murmusawa yayi yace, “lafiya kalau” haidar ya nuna masa dinning yace, “your breakfast is ready, tun dazu Mami ta shirya maka” murmushi yayi ya juya ya nufi gun dinning din, da kanshi ya tsakuri ɗan abin da ze iya ci, yaci ya barshi, goge bakinsa yayi da tissue ya mike yana hamdala ga Allah. tsadadden agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ya duba yaga har 11am, ta wuce, wayarsa ya zaro daga aljihun gaban rigarsa yayi dialing number ammi, lokacin ammi tana falo tare da baƙin ta,Maryam kuma tatafi part ɗin Aunty zuhura domin tayata tsifa, ammi ta ɗaga bayan sun gaisa tace masa. “Ya me jikin kuma?” yace, “da sauƙi” ammi tace “Allah ya ƙara sauƙi” yace “ameen” haidar daya fahimci dawa mustapha yake wayar yace “yaya bani mugaisa da ita” mustapha bece komaiba ya miƙa masa wayar, tasowa haidar yayi ya karba, suka gaisa da ammi sosai cikin mutunta juna, ammi ta masa yame jiki tace kuma ya gaida daddy, miƙawa mustapha wayar yayi sukayi sallama da ammi ya kashe wayar, yanzuma miskilancinsa ya hanashi tambayar Maryam duk da yanda zuciyarsa take cike da tsananin kewarta, gashi ammi itama taƙi masa zancenta bare yasan halin datake ciki, sosai yake bukatar jin koda muryar tane ko yaji sauƙin a bunda yake a cikin ransa, kamar ya kuma kiran Ammi yace ta bata wayar haka yakeji, amma baze iyaba. siririn tsaki yaja ya fesar da huci, a ransa yace “da tana da wayarta da duk haka bata faruba” mikewa yayi yana duban haidar yace, “muje na gaida daddy da mami ka rakani wani guri” haidar ya amsa masa suka fito suka nufi part ɗin daddy, bayan sun gama gaisawa da daddy ya ƙara duba jikin Sadik dake ta bacci still, yacewa daddy zeje wani guri ya dawo, kasuwar sai da wayoyi yacewa haidar ya kaishi, waya me kyau da tsada ƙirar kamfanin samsun ya siyawa Maryam, suna komawa gida yayiwa Aunty transfer din kudin da tace ya mata.